Showing 273001 words to 276000 words out of 279257 words

Chapter 92 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34696

kasa sai ya dago ya kalleta da karfin hali irin na maza sai ta yayi mata murmushi.

 Hurriya...

 Yayana ka yi hakuri dan Allah na san baka cancanci haka ba..

 Kaddara bata duba cancanta, hakuri kuma ya zame mana dole. Sai a yanzu nake kara jinjina kokarinki a lokacin da Amma ta tafi ta barki, yau ji nake kamar ba ni da kowa a duniyar nan, i Felt Empty, da zarar na tuna cewar Hajiya bata da lafiya sai ta ji komai ya tsaya min cak, and ba ma wannan ba taya zamu kalli duniya da abun da Hajiya ta aikata..?

 Kowa yana kuskurea Yayana, na tabbatar da ace kana sane ba zaka bar Hajiya ta aikata haka ba, komai ai kaddara ne ka fada, ya kamata idan ta same mu mu rumgume ta da hannu biyu...

 Haka ne Hurriya Allah ya ba mu ikon cinyeta...

 Ameen

Ta amsa tana kallonsa cike da tausayawa.

CAPTAIN POV.

Da zazzabi ya isa gidansa, har ya faka mota yana kokarin fita sai kuma ya tuna da wani abun da ya kamata yayi, hakan ya saka shi komawa motar ya sake yi mata key mai gadi ya sake bude masa gate. Unguwarsu Salim ya nufa ya shiga har cikin gidansu ya aika a kira shi, mai aikan yaje ya dawo ya sanar masa da Salim baya gidan. Captain ya sake juya kan motar yana tunanin a ina zai ga Salim a yanzu, ya kira shi a waya ko kuma dai ya gwada ziyarar gurin da yake dan taba zuwa da dare. Da shawara ta biyu zuciyarsa ta aminta dan haka ya nufi wani gurin da Salim yake yawan zuwa idan yana free da dare.

Captain ya faka motarsa waje ya fito ya shiga gurin yana duddubawa sai kuwa ya ci karo da Salim zaune shi kadai yana lasa wayarsa. Captain ya karasa gurin yaja kujera ya zauna, Salim ya dago ya kalleshi gabanshi na dan faduwa.

 Na dauka ka ce babu ni babu kai, me ya kawo ka nan? Zuwa ka yi ka ci min mutunci a gaban mutane?

 Ba wannan ya kawo ni, zuwa na yi na buga maka warning na karshe, kuma na fada maka abin da baka san na sani ba...

Captain ya bude wayarsa ya nunawa Salim duk wani evidence da ke nuna shi ya aikata abun da yake zarginsa.

 Ka cutar da Hurriya Salim, saboda bakar zuciyarka ka runtse ido ka yada an'uwanka da yarinyar da baka isa ka hana ni sonta ba, hakan duk be maka ba sai da ka sake aikata a karo na biyu bayan mun yi aure, wannan abun zai iya saka ka rasa aikinka ba wannan aikin Soja ba har wani aiki a nan gaba ma, kuma zai iya daureka a gidan kaso ka sani ko? Kuma zai iya lalata character dinta a idon duniya... Ina ka samu hotunan?

Yayi shiru zuciyarsa kamar zata cire sabisa yadda take bugawa da karfi.

 Wata rana ne na dauki wayar Adam zan tura abu, sai na ci karo da hotunan, abun ya daga min hankali sosai kuma na yi mamaki amman a lokacin na yi tunanin da gaske Hurriya ta aikata hakan da Adam ne, ban ce masa komai ba na tura hutunan da abun da zan tura na goge na bashi wayarsa, har sai zuwa lokacin da muka tafi Ethiopia tare na ganka kana kallon hotunanta da ban san a ina ka samu ba, sai ya fahimtar da ni son Hurriya kake yi, kuma ka san ka yi betrayed dina tun da ka san ina son yarinyar nan be kamata ka so ta ba...!

 Saboda ubana ne kai? Kamin na nuna ina son Hurriya kai baka nuna ta nuna bata bukatarka ba? And let me tell you something Wallahi ban fara tausayi Hurriya da taimakonta saboda na fada soyayya da ita ba, ban kawa wannan a kusa ba, sai tsintar kaina na yi abun kuma haka Allah ya tsara, me yasa baka karvi Kaddara ba ka hakura sai ka zabi cin zafinta...

 Na yi tunanin ta aikata da gaske ne, shiyasa tun muna Ethiopia na saka aka yada hotunan, kuma na yi tunanin hakan zai canja alakarku

 Ka bari zuciya ta yaudareka ka aikata amininka mummunan aiki na cin mutuncin Iyakinsa, a yau da na gane gaskiya idan ina so zan iya hukunta ka Salim ta ko wace siga, amman ba zan yi ba, kasan saboda me?

Salim yayi shiru ya kasa cewa komai.

 Ba zan manta alherinka a gareni ba, kuma saboda mahaifiya zan daga maka kafa, amman dai alaka da ni da kai na yankata har abada, and duk lokacin da ka sake batawa Hurriya rai zaka rasa damar abubuwa da yawa

Captain ya mike tsaye ya bar shi a gurin yana gumin tsoro da kunya a lokaci daya. Misalin Tara da rabi na dare Hurriya na zaune tare da Hamad da Amma suna hira kiran Captain ya shigo wayar Amma har ta yi kamar ta bawa Hurriya kai tsaye kuma ta amsa suka gaisa sannan ya tambaye matarsa.

 Amma Hurriya na kusa zan yi magana da ita ne...

 Eh

 Hurriya ga mijinki zai yi magana da ke

Hurriya ta tashi ta karbi wayar ta koma ta zauna.

 Ke shiga ciki mana idan magana ta sirrin yake son yi dake fa?

Ta tashi ta nufi stairs domin cika umarnin Amma. Sai da ta shiga dakin sannan ta rufe kofa sannan ta ce.

 My Noor ya jikin?

 Ba dadi har yanzu zazzabi nake ji, i just call to say Hi and kin ci abinci?

 Na ci, kai fa ka ci...

 Na sha tea shi kadai na ji ina so, ya kike..?

 Lafiya kalau

 Ya Baby na?

Ta bata rai kamar yana gabanta.

 Ba kyau ka daina

 Me ye ba kyau? Tambayar babyn nawa?

Ta masa banza sai yayi dariya.

 I miss you so much, ina jin kamar mun yi shekara ba mu hadu ba haka nake gani

 Dazun fa kawai muka rabu

 Yeah kin san na yi alkawari i will spend every hour keeping you safe kuma yau bana tare da ke maybe that's why na kasa natsuwa

 I'm safe My Noor baka bukatar ka damu

 I love you

 I love you more more more

Yayi murmushi sannan ya ce.

 Wane hukunci Appa ya yanke? Akan Hamad? Na manta ban tambaya na yana lafiya?

 Yeah... Amman har yanzu ba su yanke hukunci ba

 Okay... Je ki kwanta kin ji mai tsada, sleep tight

 I will i love you

 Ki yi mafarki kin ji babyna

Ta yi dariya ta kashe wayar, ta bude dakin ta fito a lokacin da ta sauko sai ta samu Hamad da Amma suna hawaye little Hamad yana kan cinyar Hamad yana rike da hannunsa.

 Me aka yi ma kuka kuma?

 Farinciki, ban yi tsammanin rayuwa zata sake ara min lokaci na ga wannan ranar ba, ban yi tsammanin dawowar Hamad ba, yanzu iyalina sun cika maza uku mace ta daya

Hamad ya share hawayensa ya kalli Hurriya.

 Da ace da gaske kowa ya mutu, da ba zan sake farinciki ba, kullum ina tunanin rayuwar baya, idan na tuna ni kadai ne a raye sai na ji na tsani kaina ina yawan tuna gargadin da kike mana na zaman lafiya da juna ni da Hurriya, a lokacin da na yi zaton bata raye my heart keep bleeding, kullum ina tunanin da ma ace ban yi ba

Amma ta kalli Hurriya still tana hawaye.

 Jamal yaron kirki ne sosai, mai tunani da hangen nesa mai rikon amana mai tausayi ba tare da duban mai zai samu a gaba ba, karki yarda ko da wasa ki batawa mijinki rai Hurriya, ba ko wane namiji ba ne an kunama, Jamal namijin da ko wace mace zata dauka uba ne har ta goya da zane, kar wata rana yayi miki wani abu ki manta duk wannan, Allah baya son mai butulci

 In Shaa Allahu Amma

Ta maida kanta kasa tana kara godiya ga Allah, a yanzu kam abubuwa da yawa sun daidaita a rayuwarta...



*** *** *** **** ****

BAYAN WA?ANSU SHEKARU....

Ruwa aka sheka yau a Calabar kama da bakin kwarya, sanyi ya sauko ta ko'ina ni'imar Allah ce da rahma. Ko ina yayi tsit abubuwa da yawa sun tsaya saboda ruwan da aka yi wasu na tuni suka shige gidajensu. Ta bangaren bangaren Hurriya ma haka labarin yake daman ba sanin kowa ta yi a garin da aiki ya kawo mijinta ba, idan ma ta sani ba barinta fita yake ba, ya saba mata da zaman katon gidan da sojoji suke gadinsa by fire by force, tun tana complain har ta gaji ta karbi dokar ta zuba masa ido.
Jamal ya fito bathroom yana daure da bathrobe ya nufi dansa dake kuka yana ta masifa.

 Tun da na shiga wanka yaron nan yake kuka amman kin gagara rarrashinsa, saboda kawai baki san zafin haihuwa ba

 Shi din ne ya cika zuciya fa, wai idan ya fara kuka ba a kama shi ba shi ba zai hakura ba, to ni za a nunawa zuciya ni da nake da Hamad da...

Ya dora dansa a kafada sannan ya juyo ya kalleta.

 Da wa?

 Da oga Jamal...

 Wato idonki yayi kwari har wani kiran sunana kike kai tsaye ko?

Ta kashe masa ido daya.

 Wayar kai tana ta ringing dazun

 Waya kira?

Ya nufi wayar ya dauka yana jijjiga dansa.

 Har five missing calls miyasa baki dauka ba?

 Yaya Namra ce fa, ko na dauka idan ta ji ni ce ba zata yi magana ba, ka san ai ta saba kira idan ta ji muryarna ba zata ce komai ba sai ta kashe waya

 Amman ai wani baya zama daya da wani, idan ita tana yanke alaka dake ke sai ki sada ai ke din jininta ce babu yadda zata yi

 Amman dai Allah yana gani na yi iya yadda zan iya na janyo ta a jikina ta ki ba ni hadin kai, idan na kirata da waya bata dagawa idan na mata magana bata amsa min, haka haihuwar nan da ta yi ina shiga gidanta sai ta bata rai ta dauke min fuska to ya zan yi?

Ya zauna bakin gadonsa ya maida Aliyu a hannunsa.

 Zo ki ba shi nono, laifinki ne da kike bari yayi kukan ai baki kusa...

 Ni yar aikinsa ce da zan rika zama kullum kusa da shi saboda kar yayi kuka?

 To miye aikin ki a gidan idan ba kula da yarana ba? Kin ga ni Baby idan kika yi wasa Allah zan ki sha wahala a garin nan kin san dai baki da kowa a nan sai Allah ko? Ina Manal?

 Na siyar da ita miliyan biyar na ci tsire

Yayi dariya ya girgiza kai

 Wallahi da ke ma sai na siyar da ke, bukin nan na Musib da za mu je kawai Appa ya ga babu ke...

 Wallahi Appa ba zai barka ba, idan ya fara maka masifa sai ka rikice

 Baki san Appa ya fi so na dake ba yanzu?

 Ni kuma Daddy da Ammy sun fi ko da kai...

 Aa aa dama dai jikokinsu kika ce sai na yarda amman ke din? Ta ina?

Ta bude ido.

 Zan nuna maka kuwa, Allah ya kai mu Kaduna lafiya

 Ameen bashi nono dan Allah kuma ki daina wofintar min da yaro dan Allah

 Ban masa komai ba kawai zuciya ce fa, Ammy tace haka ka yi kana karami da an kyaleka sai kuka sai fushi....

 To miyasa za a aje ni din? Kuma Ammy ta daina zama da ke tana baki labarin kurciyata haka kawai

Ta ra kwafar da kai tana daga masa gira daya.

 To yaya?

Yayi dariya yana mika mata Babanshi.

 Wato baki horu ba ko? Duk abun da na yi Miki jiya sai da kika samu baki fada min magana yau har da su daga gira?

Yana fadar haka sai murmushin dake fuskarta ya gushe ta bata fuskar.

 Na bari yi hakuri

 Matsoraciya, babu abun da za a fasa yarinya, kara ma ki saba soja fa kika aura ai sai hakuri kawai

Ya sumbanci goshinta sannan ya mike tsaye yana dariyar keta ta fara shafa mai. Tana rumgume da Haydar tana ba shi nono har ya gama shirinsa ya saka uniform sannan ya zauna kusa da ita yana amsa kiran da Namra ta sake masa.

 Lafiya Kalau ya yaranki?

 Lafiyarsu kalau, Ya Hurriya da su Manal? Da Daddy

 Lafiya Kalau

 Captain daman ni ce nake son na je Gusau yau kuma babu flight, shi ne nace bari na tambaya ko zan samu ta bangarenka lefen Musib za a kai kuma bana son aje ba tare da ni ba

Captain ya daga hannunsa ya dafa matarsa.

 Wallahi Daddy ya karbe komai nasa a gurina, ya cire sunana a komai ba ni da ikon komai nasa yanzu sai dai ki kira shi ki yi magana da shi

 Me yasa?

 Saboda na ki yarda na aje aiki na tsumduma a harkokinsa

 Okay bari na kira Momy sai ta mishi magana ko Ammy

 Okay ki gaishe da Sadiq

Captain na sauke wayar Hurriya ta kalleshi sai ya sumbanci idonta

 Yaushe yayi haka?

 An kwana biyu

 Amman kansan baka kyauta masa ba ko? Be kamata ka yi haka ba

 Babyna mutum be da ra'ayin kansa ne? Bana son kasuwanci Allah ya gani na fi jindadin aikina

 Haba Noor idan baka maka ba wa zai masa? Kai kadai yake da shi fa, kuma wani abun ko bama so haka zamu daure mu aikata saboda iyaye

 Baki fatan na kai Major General ne? Yanzu gashi an kara mukami kuma a haka sai na bar aikina na koma ga wanda ban saba ba, ba wai ba zan yi ba ne gaba daya, zan yi amman na hada biyu

 Ni daman ba son aikin naka nake ba, kullum muna wannan garin gobe muna can ni dan Allah ka aje ka ka bi abunda Daddy yake so if not...

Ta aje masa babynsa ta mike tsaye sai yayi hanzarin mikewa ya rumgume ta ta baya.

 Me zai faru haba yan matana my one and only daga ke ba kari idan ina soja, idan na zama dan kasuwa kuma... That's the whole different story

Ta Bude baki ta juyo ta kalleshi.

 To me kake nufi

Da dariya yayi ya rumgume ta yana sumbantarta.

 Uwargidata kuma amarya wasa nake, kar a hana ni abinci a yau

Ta yi dariya tana lilo a jikinsa.

 Karamin aikina ne kuwa

Ya shiga gyara mata girarta.

 Ai na sani, uwar Manal da Haidar sarakuwar AA Turaki in-law din Hajiya Turai, yar gatan Jamal farincikin Amma, sanyin idon Appa, aminiyar Hamad

Ya sumbanci bakinta yana shafa jikinsa kusan a kullum kamar amarya take a gurinsa, saboda sonta da yake mata ya fi wanda take masa, ita kuma tana kokarin ganin ta kyautata masa ta rike kambunta a gurin mijinta.

 Dadadadadada..

Yana jin muryar Manal yayi hanzarin dauke bakinsa a na ta ya kauce daga shu'umin rikon da yayi mata ya kalli kofar dakin da aka turo. Yarinya ce yar shekara biyar rike da pen da ipad ya raba gashin kanta gida biyu an mata two babys da pink ribbons. Kusan fuskarta gaba daya fuskar Captain ce kadan ta debo daga Hurriya. Captain ya rage tsayu ya duka daidai yarsa yana gyara mata gashin kanta.

 Ammyna ina ta tambayarki...

 Ina daki ina drawing, Dada na zana ka look

Ta nuna mishi zanen dake ipad dinta sai ya karba yana yabawa.

 Wow Ammyna kin yi kokarin excellent

Manal ta yi dariya ta yi tsalle tana jindadi. Captain ya sumbance ta sannan ya daga ta sama ya dauke ta ya fice daga dakin.


*** *** ****

An yi bikin auren Musib da Ruma da aka hade lokaci daya, cikin jindadi da barin naira, domin Musib shi ne dan Momy na karshe da zata aurar a yanzu, bayan Miwan da ya auri wata Abokiyar karatunsa da kuma yar gudaliyarta Namra wadda ta auri Dr Sadiq abokin Yayanta Miwan, hakan ya saka Momy ta fitar da kudi ta yi hidima sosai kamar yadda ta yi a sauran bikin yayanta ko ma fi.

Amma ta zage dantse wajen ganin ta zamewa Ruma uwa duk kuwa da irin abubuwan da Hajiya Kaltume ta yi mata a lokacin da take gidan, Amma bata duba wannan ba daman hali ba daya ba, dan haka ta rike Ruma kamar yarta, duk wata siyayya da za'ayi ta auren Amma ce ta yi domin Momy tana can tana fama da nata hidiman na auren danta.
Duk wata hidima da ya dace uwa ta yi Amma ce take yi, domin bayan komawar Ruma da Khairy a gurin yan'uwan mahaifiyarsu sai zaman yake yi musu dadi, bakinciki sai ya taru yayi musu yawa, suna kallon mahaifiyarsu da bata iya komai sai tona asirin kanta har ta kai ana rufe ta a daki sai idan za a bata abinci ko abin sha ko gyara mata jikinta sannan za a bude ta, ko kuma idan wani ya kawo mata ziyara. Gashi kuma ba sa jindadin zaman gidan, Ruma da kanta ta zabi dawowa gidan mahaifinta a karkashin kulawar Amma ta san ko ba komai zata fi rika ta da daraja fiye da Momy da har yanzu take nuna musu banbanci. A lokacin da ta dawo sai Amma ta saka hannu biyu ta karbe ta kamar komai be faru ba, har zuwa lokacin da ta kammala karatunta ta samu Miji Amma ta yi mata komai da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login