Showing 96001 words to 99000 words out of 279257 words

Chapter 33 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34704

tura ya shiga ya dauki kudin a bangarenta, idan ma ba wanda yake bangaren ba waye zai san gurin da take aje kudinta, da sarka har a dauka, ko dai masu aikinta ko kuma ita wannan mai siffar macizan ce

 Ni fa zuciyata ta fi yarda ma ita ce, amman kin ga yadda ta wani sha jinin jikinta sai kuka take ita munafuka, har Appa ya tausaya mata, wannan yarinyar da film take da ta kwashi kudi dominbta iya acting

 Bar shi ai sai na masa magana akan haka, dan yau yaushe za a shaideshi ne, har da wani cewa wai duk abun da yake mata ba sonta ne ba shi ba, kin ji min wata maganar banza

Sai da Khairi ta kalli kofa domin tabbatar da babu wanda zai shigo sannan ta kalli Hajiya Kaltume ta ce.

 Ya Yasir ma da wani ne sai yayi masa dukan mutuwa kamin ma a gane gaskiya, amman kin ga da yake Hurriya ce uffan be ce ba, balle har ta kai ga ya doketa, ai Wallahi Salma ta huta da tafi yin masters dinta a waje, Maama kuma ta yi aure babu mai shan wahakarsa sai ni, daman ni ya tsaneni a gidan nan

Hajiya Kaltume ta daga mata hannu.

 Ni yanzu ba ta Yasir nake ba, maganar nan ba zan bari ta wuce ba, ba a dora min sata da kurciyata ba yanzu da yayana ba za a dora min sata na kyale ba, kuma Wallahi sai na bawa Nafisa mamaki sai na maidata abar tausayi

Khairy ta dan kalli wayarta da sakwannin ke appearing saman screen din wayarta, ta dan bata fuska kadan da alamar damuwa sannan ta fara taba wayar tana reply kaminnta mike tsaye ta nufi dakinta. Hajiya Kaltume kamar tashinta take jira sai ta tashi ita ma ya nufi nata dakin ta dauki wayarta ta kira aminiyarta da bata iya boyewa komai, sai dai ga mamakinta sai da wayar ta yanke har sau biyu ana uku Hajiya Fatee ta amsa cikin wata murya dake bayyana damuwarta.

 Toh sawun giwa ya take na rakumi aka ce na kira na fada miki damuwata kuma na jiki a cikin wata damuwar lafiya Hajiya Fatee

 Ina lafiya anje gyaran kai an kare wuya, Hajiya Kaltume ina nan cikin matsalar cikin nan, jiya da shekaranjiya ko bachi ban iya yi ba, na rasa madafa

 Subhanallahi, baki sake kiran Malam ba? Ba na ce ki kira shi ba?

 Na...

Har zata yi subutar baki ta fada ma Hajiya Kaltume yadda suka yi da Malam sai kuma ta tuna gargadin da yayi mata.

 Toh zan kira shi, ni tsoron kiransa nake kar ya fada min wani abun da zai daga hankali na, domin na lura kamar akwai matsala

 Aa ki kwantar da hankalinki Hajiya Fatee, kuma ki nuna masa damuwarki, kuma ki bi duk wani abu da zai fada miki, na san ba zai wuce kudi ba, ko kuma ya ce sai kin siya mishi wani abu, komai dai minene karki yarda cikin nan ya bayyana Hajiya Fatee domin bayyanar cikin nan matsala ce da ko mun mutu sai mun bar abun fada, duk tsanani karki yarda sirrinki ya bayyana

Shiru Hajiya Fatee ta yi na dan lokaci kamin ta amsa.

 Toh Hajiya Kaltume, abun kunya ne kam sosai amman kuma idan ya fada min wani abun da ba zan iya yi ba fa?

 Kamar ya? Haba ta wajena karki karyar da zuciyarki mana karki yarda ta fada miki akasin abin da na fada miki, yo Allah na tuna ko cewa yayi sai kin bashi kanki ko kin bashi jini ko rabin dukiyarki ai kya aikata saboda rufin asirinmu

Hajiya Fatee ta yi murmushin takaici mai sauti.

 Hajiya Kaltume ni yanzu me nake da shi? Wannan bakar matar da Fadeel ya auro ai duk ta ga bayan komai nawa, duk wani boko ko malami da kika sani a garin nan babu wanda be ci kudina ba, saboda wannan bakar yarinyar kuma kudi ba kadan suke karba ba, amman babu biyan bukata ni na rasa gane wani irin abu ne wannan, shiyasa na fara yakin yanzu da bakina

 Waya san da me ta mallake miki da, ai wasu yayan dangin maguzawa ne Hajiya Fatee, kuma su ma fa Malam nan sun iya tsibbo sosai, suka yi ma wasu ma balle yaransu, zata iya yiyu mahaifinta ne ya tsaya mata, kuma yayi mata wani abun da za a lalata duk wani shiri nake

 Toh yanzu idan magani be yi ba, zan yi yaki da halshena, shiyasa na fada masa ya zaba ko dai kara aure ko sakinta ko kuma na yafe shi har abada kuma Wallahi zan iya saboda kura ta kai bango ba da ita da Iyami su suka ja mana shiga wahala, kara ma Iyami tana san tana amsar nata hukuncin amman ita wannan sai kara samun gurin zama take

 Toh amman Hajiya wannan hukuncin be yi tsauri ba? Kina ganin zai iya aikata daya daga ciki? Matar nan fa ba karamar mallaka ta yi masa ba

 Dole ya zama ba, kuma zan fada masa Khairi nake son ya aura domin ita kadai zata share min hawaye na

Hajiya Kaltume ta yi murmushin jindadi.

 Da yardar Allah kuwa, daman duk cik??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in yayana babu mai halina irin Khairi ta fisu fahimtar duniya ta san ciwon kanta sosai

 Na lura da haka ai, sai dai kuma ki ja mata kunne ta jajirce gurin jan hankalinsa sosai saboda ta dauke hankalinsa daga gurin wacan tun kamin ma ta shiga

 Haka za'ayi, Allah dai ya hada kansu ya ba mu nasarar wannan aikin jihadi da zamu yi

 Ameen

Daga haka suka yi sallama kowacce ta sauke waya da tunani na dabam, musamman ma Hajiya Kaltume da take jin idan har Khairi ta auri Fadeel ta yi sa'a domin namiji ne mai kyau ga hankali ga kudi ga iya kula da gidansa, musamman ma idan aka kure matarsa yaransa kuma a maida su hannun uwarsu ko Hajiya Fatee gida ya zama na yarta ita kadai.

 Matukar kika auri Fadeel Khairi kin yi dace, amman na lura ke ma kamar kina son raba min hankali biyu toh ba zan dauka ba

Magana take da kanta, ta sake daukar wayarta ta kira Malaminta ta fada masa abun da ya faru har tana zargin ko aikinsu ya fara karyewa ne, sai ya bukaci ta bashi minti goma zai sake kiranta, after ten minutes ya kira yana fada mata abun da ya faru.

 Daman na san ba zai karye ba, ai ba karamin aiki na yi ba, haba Hajiya duk bayan sakamakon da kika min ga kudi ga Makka da kika kai ni, sai kuma na bari ki ji kunya? Sam ai ba zan yarda ba, kawai dai abun yana dan fisgo masa ne, kin san fa ya fi son yarinyar nan fiye da sauran yayansa domin na duba na ga haka a zuciyarsa musamnan ma yanzu da abubuwan nan suke faruwa, kawai dai mun danne son ne a zuciyarsa ba zai iya nunawa, kuma muka kawo tsana muka saka a tsakaninsu

Hajiya Kaltume ta ji dadi sosai.

 Haka nake son ji, amman Malam ta bangaren Nafisa fa Malam, matar nan ta zame min karfen kafa, na rasa ya zan yi da ita, amman maganar gaskiya tana jefani a damuwa sosai, ka duba ka gani kirikiri an mata sata amman sai ni ta dorawa, kai ba dan gidan nan ba ne ai sai na yi kararta

 Karki damu, ita ma zamu maida hankali a gurinta, kuma zamu zafafa na Alhaji ta yadda ba zai iya yanke shawarar komai ba, sai dake, kuma zan saka masa tsananin tsoronki sannan mu cire Nafisar a zuciyarsa kamar yadda muka cire iyami

 Haka nake so Malam, anjima kadan zaka ji sako mai nauyi

Ya amsa da dariya.

 To Maa Shaa Allahu, sai dai kuma ina son na fada miki ki maida hankali gurin Hurriya, domin yanzu haka da na duba matsalalolin gidan na duba na duba na kasa ganin komai ta bangarenta

 Kamar ya Malam?

 Idan na je gurin bincikenta sai wani haske ya zo ya tare yadda ba zan iya ganin komai ba sai ma na yi saurin kawar da ido saboda kar ya illata ni, kuma na duba na ga ko ta can bangaren mahaifiyarta ake mata wani abu ban ga sun mata komai ba, wata kila wannan haske ne ma ya hana Mijinki hukunta ta, na rasa gane ko minene Wallahi

 Toh Malam ko wani lakani ta samu kuma? Shiyasa ta fara sata? Zan saka a bincike min dakinta tsab a duba ko'ina idan ma wani abun ne ta yi a dauke shi

 Ba ita ta yi sata ba, a cikin masu aikinta ne wata ta dauka, wata yar guntuwa baka mai jiki ita ta sata, kudin da sarkar suna nan bayan dakunansu ta boye a cikin itacen fulawa

Hajiya Kaltume ta rike baki.

 Lallai Malam ka kai Malam wannan da kudi na ne sai kawai na je na dauko kuma na kori mai aiki, amman ina.... Sai dai ma na yi addu'ar Allah ya kara bata sa'ar daukar wasu

Malam yayi dariya yana jinjina muguntar Kaltume.

 Hajiya na lura ke ma ba ?yale ba ce

 Malam mutane ai sai da haka, na gode sosai sai ka ga sakona

 Toh shikenan Hajiya sai na jiki

Ta sauke wayar da mamaki a ranta, me Hurriya ta yi? Gashi yarinya ce balle tace ta fara shige shige kuma gashi Malam yace ba Iyami ce ta bata komai ba.

 Toh minene? Bari Khairy ta zo zan saka bincika min yarinyar nan, ni kam na san ba a banza ba Alhaji ya wanke ta a gaban mutane

Ya cije baki ta kashe ido tana motsa kafa.



HURRIYA POV.

Tana shiga dakinta ta kalli gabas ta fadi ta yi sujadar godiya ga Allah na abun da Appa yayi mata a yau, domin ta gama katsewa ta dauka zai yarda ta aikata ne har ma yayi mata hukunci, amman sai gashi yayi abun da ba ta zata ba a yanzu. Rumgume hannayenta ta yi tana jin kamar ace Amma ko Appan Hamad suna kusa ya rumgume wani saboda jindadi. Cikin kuzari ta tashi ta fara gyara dakinta da aka yamutsa tana maida komai a yadda yake. Har ta zo kan box din da aka hargitsa da Adam ya kawo mata, takardar ciki ta fara dauka ta warware tana dubawa.

_Hey Beautiful... How are you? You're doing good i guess. Na aiko miki da wannan sakon ne just to say sorry for what happen at Mall na lura kamar baki ji dadin haka ba, i promise you ba zai sake faruwa ba matukar baki so. And duk lokacin da zaki gama karanta sakon nan ina nan waje harabar gidanku a cikin mota ba zan tafi ba ko da kuwa ko wa zai zo ya ganni_

Ta yi saurin daga kai a lokacin da ta kai gabar da yake fadar haka, sai ta nufi windows dinta gabanta na faduwa da sauri ta daga curtains din tana rike da takardar ta bude window tana kallon Motocin Momy dake gurin bata ga wata bakuwar mota ba. Ta sake maida idonta gurin takardar

_Oops... Sorry wasa nake miki na san yanzu gabanki yana nan yana faduwa, relax take a deep breath_

Ta yi taking deep breaths din kamar yadda ya bukata tana daga kanta sama ta sauke. Sannan ta sake maida idonta gurin takarsar mai kyalli da zanen heart.

_Na san kin je kin duba ko zaki ganki i fooling you_

Ta yi murmushi kadan..

_You're Smile_

Sai ta saka dariya mai sauti mai dadi.

_And you're laughing_

Ta daga kanta sama gaba daya tana dariya tare da mamakin yadda aka yi ya sani.

 Oh my God, ya aka yi ya sani?

Ta duba karshen sakon.

_Daman muradina kenan ki yi murmushi, i just want you to be happy and healthy... Have a nice Day, ki boye teddy nan da kyau and spray that perfume, till the bottle cried out for help, and also the chocolate can't wait to be on your soft mouth_

_Adam_


 Adam

Ta maimaita sunan kamar yadda ya ke rubuce a jikin kakardar sannan ta kalli white teddy din dake kasa, ta kalli kwalin turare da chocolate dake kasa at the same time. Gurin ta nufa ta zauna ta dauki chocolate din ta fara ci, sai gata tana lumashe ido saboda dadinsa. Ta dauki turaren ta bude ta fesa kadan tana jin kamshinsa. And his words keep rolling in her head wani be taba mata haka ba, ita da bata ma taba tsayawa da wani da sunan hira ba. Kamar an jefo mata tsawa haka gargadin Appa da yayanta ya dawo mata a rai da kuma maganar da aka fada akansa cewar ba yaron kirki ba ne. Cikin sauri ta maida komai cikin box din ta rufe ta saka shi karkashin gado.
*I know littafin nan zai fito, i know zai yi yawo har ya iso gareki. Na fada kuma zan saki repeating Wallahi duk wanda ya karanta min littafi ba tare da ya biya ba, na barshi da mai mafaWar rana da fitowarta. Daga masu sharing har masu karantawa ba tare da biya ba na barku da Allah...!*

Bayan Sallah Isha'i tana kwamce dakinta, Namra ta turo kofar dakin ta shigo, Hurriya ta tashi zaune da sauri tana jiran jin abun da zata karanta mata.

 Hurriya yau ba zaki ci abinci dare ba hala?

Ta yi shiru ta sauke kanta kasa.

 Baki jin yunwa ne?

 Ina ji i thought kun tsane ni ne

Ta fada shagwabe, Namra ta yi murmushi ta karasa kusa da ita ta zauna.

 Why zamu tsane ki, ko da gaske ce kina sata Hurriya ke fa jinina ce dole haka zan so ki, balle ma ba halinki ba ne daman ni ban yarda kin aikata ba, baki jidadin da naji ba a lokacin da Appa ya wanke ki, ni nafi kyautata zaton masu aikin Momy ne suka dauka ko kuma wasu daga cikin gidan nan, amman ke da ake fadar kin fi mu kyau hali a gidan nan ai ba zan yarda kin aikata ba, besides Momy tace ba zata bari ga Allah ba kin ga ko waye zai bayyana kansa, ki daina damuwa tashi muje mu ci abincin dare

Hurriya ta sauko ganin Namra ta mike tsaye suka fita tare, suka sauka kasa a plate daya Namra ta saka musu tuwon semu da miyar yauki ta saka manshanu sosai, ta dauko ruwa ta zauna a kasa.

 Sauko mu ci

Hurriya ta tashi ta shiga Kitchen ta wanke hannunta ta fito ta zauna kusa da Namra, a madadin ta ci abincin kai tsaye sai ta kwantar da kanta jikin Namra.

 Yaya Namra na gode, ke da Yayana kawai kuke so na a gidan nan

Namra ta yi murmushi.

 Ba komai yar kanwata, ni wannan abun da ake cewa yan ubanci bana miki kallon haka, ina kallonki ne kamar uwa daya uba daya muke, tashi ki ci abinci

Ta tashi ta gyara zamanta sai dai kamin ta kai hannunta cikin abinci Khairy ta shigo sanye da karamin mayafinta wayarta a hannunta, is like kamar an mata dole haka ta tsaya bakin kofar falon babu ko sallama.

 Hurriya taso muje

Hurriya ta kalleta.

 Ina?

 Ki taso idan zaki taso Malama

Namra ta daga kai ta kalli Khairy da duba na wulakancin.

 Ba zata tashi ba abinci zata ci

 Okay sannu uwarta, bari naje na fadawa Yaya uwarta ta hanata zuwa, ita ma kuma ta ce ba zata je ba

Hurriya na jin kiran na Yayanta ta tashi tsaye da sauri zata nufi kofar.

 Dauko mayafinki Hajiya

Ta juya ta dauko mayafin kamar yadda Khairy ta bukata, sannan ta bi bayanta suka fice, at first ta yi zaton bangaren Hajiya Kaltume za su nufa sai kuma ta ga ta nufi gate.

 Ba yaya kika ce yana kirana ba?

 Yana waje

Huriyya ta bi bayanta suka fita gate, close to gate din wata mota ce fake da ba ta gidan ba. Gurin motar suka nufa ta bude ma Hurriya baya.

 Shiga

 Amman wannan ba motar Yayana ba ce... 

 Zaki shiga ko sai ya fito ya mareki? Ba shi ya ce mu jira shi a mota ba

Hurriya ta shiga da sauri, Khairy ta rufe bayan sannan ta bude front seat ta shiga ta zauna tana taba wayarta. After like five minutes aka bude motar ta Driver seat aka shigo, tana leken fuskarsa yana juyo ya kalleta wa zata gani ba Adam ba.

 Thank you Khary

 This should be the last time sa zaka cilasta min fitowa da yarinyar nan

Ta fada a kufule. Hurriya ta kalleta fuska kamar zata fashe da kuka, murya kamar a shagwabe ta ce.

 Amman yaya Khairy kin san me Appa yace ko kuma kin san Yayana zai yi fada idan ya sani

Adam yayi saurin tarar numfashinta.

 Ba dadewa zamu yi ba Hurriya, kawai ina son na ganki ne kuma na baki hakuri abun da ya faru, and na aiko da box an baki?

Khairy ta watsa masa wani kallo.

 Okay ni zan hana mata box din kenan?

 Waya sani, tun da har kika iya bata ni a gurinta ai zaki iya hana ta ganin box din

 Ni ban bata ka ba

 And why take min kallon mutumen banza? Ni ba iskanci ne ya kawo ni gurinta ba, ki daina fada mata bad things about me, na ga ai natsantsiya ce not like you that's why i like her

With shock Khairy take kallonsa.

 Adam what's the meaning of all this?

 Sonta nake yi, and I'm ready to prove it, i want to talk to her parents da duk wani mai son hana alakata da ita tafiya I'm serious

Khairy ta tsaya kallonsa for some seconds kamin ta dauke

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login