Showing 246001 words to 249000 words out of 279257 words

Chapter 83 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34679

sosai kamar yadda kukanta ya saka yar autarta Ruma kuka.

 Hajiya ko zaki ma su Baba Musa da Baba Lawal a bawa Appa hakuri

 Babu wanda zan yi ma magana Ruma, babu wanda be san abun da ake ciki ba amman ba su yi kokarin sasantawa ba, ba zan kai kukana a gurin kowa ba, Wallahi hakki ba zai taba barin iyami ba ba zata taba ganin daidai a rayuwarta ba

Ruma ta dubi Mahaifiyarta cikin rashin fahimta inda uwarta ta dora.

 Hajiya Amma bata gidan nan fa, taya wannan issues din ya zama laifinta? Wata kila ma dai kisan da kika saka ka yi ma Hamad ne nake bibiyanmu...!

Hajiya Kaltume ta kalleta ta sauri ta buge mata baki.

 Kul.... Kul... Kul... Kika sake furta magana irin wannan, kul... Zuciyarki ta sake raya miki wani abu makamancin wannan... Ni ban kashe Hamad ba ban kuma ce a kashe shi ba, su suka aikata a karan kanku dan haka babu zancen bibiyar hakki a nan, Iyami kuma ita ce silar komai tun farko dole na fadi haka, ke yarinya ce ba zaki gane abun da nake nufi ba, kuma ba zan bawa Alhaji Hakuri ba, ba kuma zan nemi kowa ya shiga maganar aurenmu ba, da yardar Allah sai Alhaji ya kawo kansa yana kuka yana rokon na yafe masa

Ruma ta kalli Hajiya Kaltume domin ta gama fahimtar inda ta dosa, ta san kuma wanda yayi nisa baya jin kira mahaifiyarta ba zata taba fahimtarta a yanzu ba, dan haka ta share hawayenta ta tashi ta bi bayan yar'uwarta.

 Duk yadda za'ayi na gyara al'amurrana sai na yi sai dai na rasa komai amman ba zan zauna na zuba ido ina kallon abubuwa suna tafiya ba daidai ba, ni da mijina shekara da shekaru kuma ace ni zan koma baya? .

Ta share hawayenta wasu na sauko mata, zuciyarta na da yakinin zata iya wannan yakin kuma ta ci nasara, bin bokaye da yan bori ne take jin yanzu ta fara domin ta gwada ta ga riba.


MOMY POV.

Miwan ya sauko hannunsa daya a aljihu dayan kuma yana rike da wayar da ake yayi yar zamani, daga inda Momy take zaune ta dago kai ta kalli danta cike da farinciki da kuma alfahari.

 Kamar jiya kuka bar kasar nan gashi yanzu har ka dawo Alhamdulillah

Miwan ya zauna yana murmushi gashin kansa yayi tsiro kamar wani dan kwallo.

 Momy muma muna alhari da ke wannan duk jajircewarki ce, da mun bi ta Appa? ba zamu yi masters din nan ba, Namra ma ya kamata ta je ta yi, domin yanzu degree ya zama ruwan dare masters ce ke dan karawa mutum girma

 Ita ma zata yi ai In Shaa Allah, da zarar abubuwa sun daidaita zata yi

 Wai me yake damunta ma? Tun da na dawo ban taba ganinta a falon nan ba ba

Momy ta aje cup din lemu dake hannunta.

 Ina ce shekaranjiya ma mun yi maganar nan da kai?

Ya dan daga kafadunsa.

 Na ji ni ma ban so Captain ya auri Hurriya ba, amman ya zamu yi? Tun da mai faruwa ta faru? Kuma ba ga ta inda wannan abun zai zame mata abun damuwa ba har da su boye kai a daki

 Saurayi biyu Namra ta rasa saboda Hurriya, na farko be wani dame ni ba? ni ban ma wani san shi ba, amman Captain har yanzu zuciyata aci take saboda be auri Namra ba

 Amman ya nuna yana son Namra ne? Ko kuma dai ke kuke ta hasashenku ne? Wata kila ku kuka saka mata rai ita din ba shi take ra'ayi ba, ko dai yaya ya kamata ta hakura mana tun da mai faruwa ta faru

 Daman ai dole hakura zamu yi, amman tabbas yayana da Captain sai sun yi nadamar abun da suka aikata, ba dai dangin Iyami ba ne?

 Ta ji sauki wai?

 Waya san mata can ita ta sani, ni har yau ban leka gidan ba, ko last time da mahaifinku zai tafi sai da ya ce min ko zan je na ce Allah ya tsare ni da zuwa gidan Iyami, shekaranjiya ma ina jinsa yana zancen zai biya min ummara ni da Sapna na san ba zai wuce dafe dafe ba daga karshe yace albishir din maida Iyami ne

Miwan ya dan dago ya kalli Momy yana murmushi

 Ni Allah har mantawa nake ina da yar'uwa Sapna wai tana nan dama

 Da ta mutu ai da ka sani kamar yadda ka sani a lokacin da Salma ta mutu

 Haka ne kuma, mutuwar Salma ta ba ni mamaki Wallahi haka sidda

 Babu yadsa mutuwa bata zuwa ga bawa ai, ba a mamakin mutuwa sai dai fatan kyakkyawan karshe

Ta tabe baki ya cigaba da taba wayarsa. Momy kuma ta kawar da fuska tana wani tunanin na dabam.


CAPTAIN POV.

Abubuwa da yawa be saka ran Ammy zata yi ba zai a auren nan su take ta kokarin shiryawa a kuraren lokaci ciki har da Walima da wanki ango da kamu, mutane da yawa da ta Boyewa zancen auren yanzu su take aikawa da katin gayyata wasu kuma tana sanar musu ta waya yadda za'ayi bikin, tana yin haka ne kawai saboda farinciki danta, so take kallon da yake Mata na macen da bata son aurensa ya tashi zuwa mai son cigabansa ba kuma dan tana son Hurriya ba sai dan haka ya zame mata dole ta aikata a matsayinta na uwa.

Captain kawai ya zauna ne yana kallon yadda abubuwa suke gudana, wasu daga cikin cousins dinsa da friends sai a yanzu suke kiransa suna taya shi murna da yawansu sun fi tambayar yaushe ne dauren auren idan ya fada masu an daura sai su yi ta mamaki wasu kuma su ce ya boye musu wasu su ce be gayyace su ba, haka dai yayi ta fama wani gurin ya samu wanke kansa wani kuma sai dai ya kyalesu su yi ta complain. Ran Momy be kara baci ba sai da ta ga mini iv da Ammy ta saka ayi mata ta raba na gayyatar walima da wunin biki, bakinciki be bar Momy ta leka walima ba balle wunin biki kirkiri ta fitar da hassadarta a fili, daman ta wani bangaren tana ganin kamar har da laifin Ammy na bari Captain ya tare da Hurriya bata bude masa wuta ba, ta bangaren Ammy kuma tana ganin kamar Momy ta zafafa da yawa domin ita ma da take uwa ta hakura ta bar abun a zuciyarta balle Momy da take kanwar uba, a yanzu take kara yarda da zancen Captain ba, Momy ba tana bakinciki auren ne saboda ba Namra ba ce not just because of Hurriya tana yar mijinta.

A family House din Mijinta Ammy ta yi Walima da wunin, ba daga arewa kadai ba har daga kudancin Nigeria da yan'uwanta da na mijinta da suke wajen kasar nan da wasu daga matan abokan kasuwanci Mijinta sai da suka yanke uzuri suka halarci walimar da wunin biki, saboda sun san daga Daddy har Ammy a aya suke da shi Captain balle su ce idan ba su samu zuwa a wannan ba idan wani bikin ya tashi za su tafi. And ba su taba aurar ba sai akan Captain saboda haka dole ayi musu kara.

Walima aka yi ta gani ta fada, idan baka da gate pass baka isa ka shiga ba, kana shiga kuma za a bude bayan motarka ka a zuba maka gift din Walima da kaza daya da aka soya aka yi package dinta da kyau, idan kuma baka da mota za a baka abun ka a hannuna ne ta inda Ammy ta banbanta abun ta gurin raba abun da yake cikin jakar kayan walimar ne, masu hannu da shuni ta saka musu manyan abubuwa na masu arziki, wadanda aka raina capacity dinsu kuma sai ta saka musu na su kanana, Ammy da kanta ta aika da motoci aka dauko Hurriya da yan gidansu, daman ta saka an sanar musu da abubuwan da ta shirya tun gabani zuwan ranar, Ammy bata son kowa ya gane Hurriya bata gani dan haka ta fada mata ta yi acting smart kar ace anta ya auri makauniya. In a code way aka yi komai na walimar sai dai haka be hana wasu noticing something is wrong with Hurriya ba saboda yadda bata respond ma mutane idan aka yi mata murmushi, and bata iya daga kai ta kalli mutane da kyau, team babu ruwanmu da gulma ba su kula ba har ayi aka gama.

Ranar wunin biki Hurriya ta chaba ado da farin lace da farin mayafi domin farar rana ce da ko wace ?a mace take fatan gani a rayuwarta, kallo daya zaka yi ma Hurriya ka fahimci babu yaki babu ja Captain ya zabo daya a cikin dubu, innocent face dinta ta sha light makeup, an gyara gashin kanta ya kwanta baya kamar ba a taba kai masa hannu ba, farar kafarta ta sha jan lalle mai daga hankali kowa ne jarumin namiji mai son ido da kwalliya, ga jiki ya sha dilka ta ko'ina kyali take kamar tsadadden lace dake jikinta. Ya yadda mutane suke fada yadda ta yi kyau take auna irin kyau da ta yi, domin a nan aba a lamunce mata da ga yadda kyauta yake a fili ne. Duk shagalin da ake na bikinta bana ganin kowa sai dai ta yi saurare a nan ma sai da yarda ta rasa wasu masoyan da Allah yayi alkawarin wanda ya rasa su kuma yayi hakuri zai masa sakamako da Aljanna, wato masoya biyu idanuwa. Hurriya na zaune dakin Gwaggo akan gadonta tare da Husna da wasu daga cikin kawayenta na makarantar su da boko da islamiya da Husna ta gayyato Amma ta shigo dakin tana sanye da lace mai tsada brown color ita ma ta sha nata lallen sai dai nata na hausa ba yayi baki sosai yayi mata kyau.

 Husna ke da kawayenki ku dan ba ni guri zan yi magana da Hurriya

Husna ta tashi tare da kawayen suka fice, zuwa falo wasu kuma suka fita harabar gidan da Appa ya saka aka gyara ko'ina saboda Hurriya. Amma ta zauna tana kallon yadda fuskar yarta ke sheken amarci.

 Kamar jiya aka haife ki, ina tunawa lokacin da mahaifinki ya shigo me ya Gwaggo ta bari aka haife ki a gida, saboda baya son matansa na haihuwar gida, ya fi son a tafi asibiti, sai Gwaggo tace ai na haihu lafiya kuma ya amsa ?a mace,mahaifinki ya shigo ya saka hannu biyu ya karbe ki, a take a gurin ya rada miki suna ba tare da yayi shawara da ni ba, ya ce barka da zuwa Hurriya, Allah yayi miki albarka yasa ke din mai amfanarmu ce, kuma ya nuna mana aurenki, ashe Allah ya amsa


Amma ta sauke kai kasa tana taba akwatin sarkar zinarin dake hannunta.

 Ina cikin wani irin farinciki a yau marar misaltuwa, burin ko wace uwa ta ga auren yarta, kuma da mijin da yarta take so yake da halin kwarai, Wallahi ban yi zaton rayuwa zata ara min lokaci na kawo yau ba, ashe dai zan tashi zan yi magana zan aurenki Hurriya

Amma ta bude akwatin sarkar zinarin dake hannu ta dauko sarkar da take a matsayin sadakin Hurriya ta yaye mayafinta ta saka mata a wuyanta.

 Ina miki murna ganin wannan rana mai daraja, Allah yasa ki shiga gidan aurenki a sa'a kuma ya baki yaya masu yi Miki biyayya kamar yadda kika yi min, ina kaunarki ?ata Allah ya bawa wannan yaron ikon yi miki adalci da kaunarki kauna ta hakika ta har abada

Hurriya ta rumgume Amma da sauri tana kuka irin yar da bata son rabuwa da uwarta.

 Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana

Amma ta yi ma Allah godiya tana kuka kamin ta dago Hurriya daga jikinta ta kama hannayenta ta rike.

 Ban sani ba ko ba zan samu yin magana da ke na anjima ko kuma ya kasance cikin mutane ne ba zan iya fadar wani abun ba, dan haka nake son baki wani sirrin zaman aure a yanzu wadda uwata ta ba ni kuma shi ya taimaka min har ake ganin kamar na mallake Appanku

Hurriya ta natsu sosai ta mika hankalinta a gurin mahaifiyarta.

 Ki rike hakuri, hakuri wani abu ne mai wahala aiwatar ba, amman ba shi da wahala ga wanda ya dauki rayuwa da sauki, da hakuri na mallake zuciyar Appanku, idan yana magana ko yayi fushi bana katse shi, saurara nake na ji kalamansa kuma na yi hakuri ko da kuwa sun bata min rai, idan ya ba ni rashin gaskiya karba nake na rike ko kuwa ni ce mai gaskiyar, sai bayan ya huce sai na lurar da shi kuskuren inda aibu yake, ko kuma na fada masa gaskiyar a inda take, idan na ga yana son abu ina kokarin na ga na fi sonsa, shiyasa ban taba nunawa yayansa kiyayya ba, na rike mahaifiyarsa kamar tawa ina kyautata mata ina mata biyayya kamar yadda nake yi ma danta, ina sa yawan kyauta saboda dangin miji da makota basa son mace mai rowa ko mai tsananin son abunta, idan na ga yayi wani kuskure ina nuna masa illar haka kuma na nuna masa hanyar da ta fi saukin bi, ban taba nuna masa ina kishin Nafisa ko Kaltume ba, kuma ba dan bana yi ba, sai dan na fi karfin zuciyata na boye abun a raina, shiyasa baya taba yarda cewar bana son matansa saboda na iya takuna, kuma na rike girki na iya tuka tuwo yayi kyau na yi dadddar miya Appanku da ku kanku kuna ci suna santi, na rike tsabta na rike kamshi mahaifinki ya taba fada min idan ya ji kamshi turaren da ba nawa sai ya ji a dabam, duk abun da na san mahaifinku zai bukata kamin ya fada na aiwatar idan kuma na kyama ne ina gudun nake kauce masa, da wannan na gagari matan ubanki har suke ganin kamar na mallake shi na masa magani, idan girkina ya dawo da wuri Appanku yake dawowa gida, ke ma ai kin sani saboda ina masa hira, ina ba shi labarai masu dadi, na yi masa hira mu tattauna abubuwa da yawa na yadda rayuwa take ciki, ni ce radio sa ni ce tv sa idan ina kusa da shi bana yarda hankalinsa ya tafi ko'ina zai a gurina, idan kuma ba girki ba ne ina kokarin kiyayewa na ga ban shiga hakki abokan zamana ba, idan zai yi zabe ni nake zaba masa komai, ban tana yarda Appanku ya saka kayan da yake ra'ayi ba a ranar girkina, saboda kwalliyar tawa ce ba tashi ba, ni nake zaba masa kayan da zai saka, sai kuma na yi sa'a shi din mutum ne mai tsananin so na mai saurarena mai gudun bacin raina...

Amma ta yi murmushi tana tuna baya.

 Idan Appanku ya ce Iyami kar ayi kaza, Wallahi bana aikatawa saboda ya ce kar ayi, ina ba shi lokacina sosai ina jin maganarsa ina bin dokokinsa, saboda ni ce a kasa shi ne a sama shi din jagorana ne, Allah ya riga ya ba shi wannan girma, ni kuma dole na bi saboda na samu aljanna ta, kuma kar ki yarda wani ya fahimci irin zaman auren da kike da mijinki ba mai dadi bane ko da kuwa kun samu tsabani, ki sama ma'ajiyar sirrinsa mai rufe duk wani asirinsa, kuma ki rika lura wane hali miJinki yake shiga idan yana ciki damuwa idan yana fada ya yake, idan yana farinciki ya dabi'unsa yake, abun da duk kika ji zaki iya dauka ki nuna masa tun farkon zamanku, wanda kuma ba zaki iya dauka ba ki fahimtar da shi da wuri ba sai daga baya ba, karki yarda ki raina mijinki ko da kuwa shi din abun rainawa ne a gurin wasu mutane, ki zama macen da idan ran mijinki ya bace ke zai rika tunanin ko ma ya nufo saboda ke kike kwantar masa da hankali. Kin ga abubuwan nan da na fada miki, wata rana sai kin zo kina fada min yan'uwan mijinki suna tunanin kin mallake shi, kuma wata rana mijinki ko aure ya kara zai yi ta ganinki ne wata macen ta kasa sarrafa shi saboda karatunki ya saba dauka, wani darasin zai masa wahalar zama a kai, da haka na gaggara a gidan mijinki sirrin ba na iya kyau bane kawai har da na iya zama, ai wata macen bata da kyau amman a haka mijinta yake sonta fiye da kyau, karki yarda wata macen ta fi ki a gurin mijinki

Amma ta saka hannu ta share hawayen Hurriya dake zuba tana murmushi.

 Allah ya miki albarka

 Ameen Amma na gode

Ta fada cikin kuka wasiyar Amma na ratsa jikinta. Rukayya ce ta shigo dakin tana sanye da anko kamar sauran yan gidan, ta yi matukar kyau blue atamfar ta karbe ta sosai.

 Amma gasu nan sun iso, tare da mai hoton amman Gwaggo tace a fara kai masa Hurriya su gaisa kamin mu shirya a fito hoton

Amma ta kalli yarta dake hawaye har lokacin tana murmushi.

 Amarya tashi tafi ki gaisa da angonki

Hurriya ta ji gabanta ya fadi, irin faduwar gaban dake samun ko wace amarya a ranar wunin aurenta, daman tun da aka daura auren har zuwa yau ganin take kamar mafarki take ba gaske ba. Kamin ta yi wani yunkuri Gwaggo ta shigo daki tana masifa wai fitowa da amarya ya gagara a bar ango a can yana jira.

 Ai dole ya jira Amaryar ta mu mai tsada ce Amma

Rukayya ta fada, Gwaggo ta gwatsaleta.

 Dan Allah can rufe min baki marar kunya uwar kawai

Gwaggo ta kama hannun Hurriya ta fice da ita daga dakin.






Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login