Showing 36001 words to 39000 words out of 279257 words

Chapter 13 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34623

yi?

 Me zai hana? Ki dai ki zuba masa kudi kawai, ni ma kudin zan zuba masa, kuma a hannun Alhaji zan karbe su, kudin sarkar zinarin da ya siyawa Hurriya da kudin da ya bawa Iyami duk sai na fanshesu a hannunsa, yanzu ne za su gane sun yi kuskuren taba mace kamar ni, kuma Wallahi sai na malleke Alhaji ko ta halin yaya, sai ya dawo a tafi hannuna Iyami da ?a?anta sai sun WanWana kuWarsu, Iyami sai ta gane kuskuren da ta aikata na aurar min miji, sai ta yi nadamar hada shimfida da Alhaji, matsayin da ta taka a baya na tana Matar Alhaji ina Matar Alhaji sai na saka ta yi nadamar haka... Ba ita ba har Nafisa sai na sake mata sabon karatu na goge mata hadda. Dukansu sai sun dawo a tafin hannuna

Ya daki tafin hannunta tana kashe ido alamar yanzu ta shiryawa rashin imani, da kuma fada da Iyami da Momy.




________________



Hmmmmmm Allah yasa kuna hango abubuwan da nake hangowa >??

Tafiyar fa duk duka yanzu aka fara.... Ku daura Wamara ku zage damtse domin domin alkalinmin da zafinsa ya zo =??

Kar a manta idan an karanta ayi sharing >?p?
[10/18, 6:15 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: &A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?

Hello Habibaties =?
?>?p?
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy


5???5???5???5??? 1?? 2??

Musib ya aje ma Captain keys din motar Momy da ta bada umarnin a dauko masa. Kallon Keys din yayi sannan ya mika hannu ya dauka ya mike tsaye. Tsabar bacin rai zuciyarsa har zafi take kamar zata fashe, baya jin yana da sauran wata magana a yanzu kuma baya bukatar yi ma Momy sallama bayan an bata masa tayun mota a gidanta. Shi ya fara fita sannan mahaifiyarsa ta bi bayansa Momy da Musib suka biyo shi suna ba shi hakuri kamar su suka masa laifin shi dai be ce uffan ba ya matsa key hannunsa motar ta fita key ya sannan ya nufita har suka bar gidan kalma daya bata sake fitowa daga bakinsa. Ran Momy be yi dadi ba ganin an an'uwanta da take ji da shi ya fita cikin bacin rai.

 Ni abun nan ya ba ni mamaki, wai waye yayi wannan aika-aikar

 Zai wuce Kaltume? Ai bata son kowa da alheri a gidan nan kuma ta ga mota mai tsada ina za so haka, ballantana fitowar nan da ta yi dan uwa ko daya be je ya mata barka da fitowa ba

 Amman Momy Yasir dai ba zai yi haka ba kin san ko da ta saka shi

 Su matan fa? Kuma shi ma ba munafurci ba ne da nuna soyayyar ido, ai ta ciki na ciki dan'uwa be taba son dan'uba ba har abada

 Ko kuma ta aiko wani yayi ba

Ta juyo tare da Musib suka shigo falon, ko zama ba su yi ba motar Appa ta faka a harabar ya bude ya fito ya shigo cikin falon fuska a dauke.

 Ku ba mu guri zan yi magana da mahaifiyarku

Appa ya fada immediately after ya rufe kofar falon, Musib ya dubi Miwan sannan suka tashi suka haura sama, Momy kuma ta zauna ita ma nata ran a bace tana sauraren da wacce Appa ya zo.

 Nafisa ina son na tambaye ki, akwai laifin da Hurriya ta yi miki ko kuma Hamad?

 Wani abun aka fada kuma?

 Akan wani dalili zaki nemi banbanta su da sauran yayanki? Fada min banbanci dake tsakinsu da Namra ko Miwan, dukansu ba Yayana ba ne? Akan wane dalili zaki ce Hurriya sai dai ta share dakinta da kanta kuma idan zata hau stairs ko ta sauka ba ta hau kamar yadda Namra ko Musib suke yi ba?

Momy ta rike baki.

 Oh Allah na ni Nafisa, yaushe aka yi haka? Kuma shi kenan daga fada maka zance karya da gaskiya sai ka hau ka zauna har da zuwa gurin fada ba tare da ka tsaya ka bincika ba? Shiyasa ka dauko su ka kawo min? Me yasa ba a kaiwa Kaltume ba? Ita da yake tsoronta kake sai Nafisa da aka raina itace mai dadi hawa, gashi sai mulki take mana ciki gidan ita da yaranta

 Daga ke har ita karkashin kulawata kuke kuma karkashin ikona, dan haka duk gurin da nake ra'ayi a can yarana za su zauna, kuma ina gargadinki wannan ya zama na karshe da zan sake jin wani abu marar dadi akan Hurriya da Hamad, zan iya canja mata ban zanja yaya ba, gaba daya yarana babu na yarwa kuma bana son a batawa kowa

 Eh amman ai ka ware wadanda kake so kake kauna, na tabbatar da nawa yayan Kaltume ko Iyami take yi ma wani abu ba zaka yi magana ba, amman da yake yayan mowa ne ai gashi nan ka shigo falo cikin bacin rai saboda an taba yan gold, ni da zaka nuna musu kauna ka dawo da uwarsu ai da duk yafi wannan nema musu yanci da kake, idan ya so sai ta rike yayanta na rike nawa

 Abun da na ga damar aiwatarwa shi zan aiwatar, babu mai fada min gabas, na san Allah, daman ke haka kike banta zuwa da wata magana ba ki musa min ba, ban taba fada kin yi shiru kin saurareni ba sai kin fada, sa'insa da ni ba yau kika fara ba, daga ke har Kaltume babu wadda nake jin sanyinta kowacce ku da lagon da take matsawa ta bata min rai

Momy ta fashe da kuka domin kalaman Appa sun mata zafi, ta san abun da Appa ya fada akam Iyami gaskiya ne, domin ya saba yi mata fada ko a gabansu kamar yadda su ma zai iya musu a gabanta ko kuma ya tara su gaba daya yayi musu fadan idan wani abu ya faru, su kan tanka shi su kare kansu ko maida martani amman Iyami bata cewa idan yana fada har yayi ya gama, ko daga kai ba zata yi ta kalleshi ba, wannan ta saka suke yawan yi mata kallon munafuka, hawaye shar Momy take yi daman kuma bata gama hucewa daga bacin ran abun da aka yi ma Captain ba.

 Eh sai Iyami, abar kaunarka, yanzu gashi nan ka rufe da fada akan yayanta, matarka Kaltume kuma ta takura min ta takurawa bakina, yanzu Captain ne ya zo, ka san dai yadda nake da Captain amman haka matar nan ta saka aka fasa mata tayun mota saboda bakin ciki, ban gama huce wannan haushin ba gashi nan kai kuma ka zo ka rufe ni da wani, toh Wallahi ka jawa yayanka kunne su daina munafurci, kuma ka jawa matarka matarka kunne ta fita safgata da ta bakina babu ruwanta da ni idan ba haka ba Wallahi za 'ayi tashin hankali da ba taba yi ba ko a lokacin da ka auro karamar yarinyar can Iyami

 Ni dai na fada miki, karki sake banbanta min to ?a?a duk daya suke a gurina, babu wanda ya fi wani, zan iya canja mata ban canja ?a?a ba bana ni da kamar ?a?ana!

Yana kawai nan ya juya ya fice, cikin motarsa ya koma yaja ta zuwa bangare ya ajeta ya fito ya taka da kafa ya nufi bangaren Hajiya Kaltume yana shiga ita ma ya salllami yaranta suka haura sama ban da Yasir da baya gidan ma a lokacin ya fita gurin safgoginsa, Namra kuma ta fita zuwa bangarensu. Fada yayi mata sosai yana ja mata kunne akan abun da ta saka aka yi ma Momy.

 La'ilaha Illallahu ni Ummul Kultoon, yaushe kuma aka yi haka? Ni miye ruwana da Nafisa balle kuma bakinta, yanzu Fisabillahi na rasa me zan saka ayi mata sai fashe tayar baki? Abu dai kamar karamar yarinyar? Ni da nake ta kaina ma? Yaushe na fito daga daji? Kofar daki ma bana sha'awar fita balle kuma har na saka ayi wani abun, shigowar nan da ka yi ma hankalina sai da ya tashi

 Ni dai na gargadeku, bana son wani tashin hankali kowa ya zauna lafiya kuma ya tsaya a iya matsayinsa, ku bar ni da abun da yake damuna, kullum ni ne cikin fitina kamar akaina aka fara mata aure da mata biyu

 Mata uku dai Alhaji, yaushe ka saki yarinyar can Iyami da har zaka dawo kanmu nu kadai, musamman ni, taya za a ce na fasa tayar mota? Yara ma wa zan saka yayi wannan aiki? So take ta zugaka ka koreni a gidan kamar yadda ka kori Iyami, to Wallahi ni kam zama daram dam dam dam sai mutuwa, kuma Alhaji dan Allah ka rika bincike kamin ka fara fada, Wallahi sheri ne kawai na kishiya da neman hada mata da miji, abun da ba ayi ba da kurci ayi shi yanzu

 Na dai ja muku kune, kowa ya tsaya iya matsayinsa bana son sake jin wata fitar

Har Appa ya fice Hajiya Kaltume bata gama mamakin jin irin kagen da Momy ta yi mata ba, Salma ce ta fara saukowa sannan Khairi suna tambayar me ya faru domin sun lura da yadda mahaifinsu ya shigo cikin fushi.

 Wai munafurci matar nan ta hada, wai na tura an fashewa bakinta tayun mota, shi kuma babu tsayawa bincike da yake ta mallake shi komai ta fada masa shi yake yi kawai ya zo ya rufe ni da fada, ai bari Wallahi ita ma sai ta bar gidan nan Kamar yadda Iyami ta fitar da ni, waya sani ko gurin tsafinta ta tafi aka bata wani asirin ace ta zo ta hada mu, gaba daya ta mallake Alhaji ta juye masa kai komai ta fada sai ya hau ya zauna

 Tab Lallai Momy ta yi nisa, wane irin fasa tayun mota kuma?

Hajiya Kaltume ta kalli Salma dake maganar.

 Sheri ne kawai a samu yadda za a hada ni fada da Alhaji sai ya sake ni

Haka Hajiya ta yi ta jininin maganar tana ta masifar har yamma.




*** *** ***


Hajiya Binta dake gidan baya tana shafa kan Hurriya dake kwance jikinta ta ce.

 Tsoho kamin ka kai ni gida, ina son ka biya da ni gidansu Iyami na dubata yaranta ma su ganta

Kamar wadda aka cewa ya shiga ramen wuta haka Appa yaji, ko kadan be son abun da zai kusantashi da Iyami gashi kuma be isa ya musawa Hajiya ba.

 Toh Hajiya amman idan na aje ki Yasir zai zo ya dauke ki ya maida ke gida su kuma yara ya dawo da su

 Toh zamu tafi gidan makiyiyarka ba, Allah ya kyauta

 Haba Hajiya irin wannan maganar be dace ba a gaban yara ban da alheri me iyami ta yi min da zan dauki kiyaya na bita da ita

Hajiya dai bata sake cewa komai ba har Appa ya canja hanya ya dauki hanyar gidansu Iyami. A bakin gate din ya faka, ya fito ya budewa Hajiya ta fito tare da Hurriya sannan Hamad ya bude front door ya fito.

 Ba zaka tsaya ta fito ku gaisa ba?

 A gaishe ta dai Hajiya

Ya amsa yana kin hada ido da Hajiya Binta, girgiza kai kawai Hajiya ta yi ta cira kafa suka karasa bakin madaidaicin gate din da tuni Hamad ya bude har ya shiga ciki. Yanayin yadda Hajiya Binta ta tararda Iyami be mata dadi ba, daman kuma ta san za'a rine wai an saci zanen mahauciya, mai ciki ba a rabata da laulayi balle kuma ita da take cikin damuwa, sai dai ganin Hajiya Binta ya saka ta ji kamar an dauke mata ciwo, suka ta yi hira kamar yadda suka saba.

 Jiya muke zancenki da Gwaggo na ce ina tuna haihuwar Hurriya da irin hidimar da kika yi

Hajiya Binta ta yi murmushi.

 Abu kamar jiya, yanzu Hurriya ta cika sha shida cif

Hurriya ta wara ido tana mamaki yadda ta manta birthday dinta.

 Eh fa Hajiya amman ai sai October 10

 To October ba ya kusa ba? Miye rage yan kwanaki ne kawai

 Hajiya zaki yi ma Appa magana yayi min celebration please

Iyami ta ce.

 Kin san halin Appanki ba son irin abubuwan nan yake ba, shi gaba daya rayuwarsa irin ta mutanen da ne

 Zan masa magana da kaina, maybe zai yi min gashi ma dazun ya fada mana a falon Hajiya ya ce ni da Hamad a waje zamu yi karatu

Mamaki ya cika Amma har sai da ta bude baki ta kalli Hajiya dake murmushi.

 Shi da kansa?

 Shi da kansa fa, sai dai ki yi ta addu'a kuma ki yi musu, ai maso uwa ya so yayanta, abu dai ne idan ya zo babu yadda za'ayi sai hakuri kawai, amman sakin nan ba karamin mamaki ya ba ni ba

Amma ta sauke kai kasa tana jin wani rashin dadi yana ziyartar zuciyarta. Hurriya ta tashi ta fice zuwa dakin Anty Rukayya haka take jjnta kamar wata sa'arta saboda tana wasa da ita sosai kamar yaya da kanwa, wannan ya saka Hurriya bata kallon Rukayya a matsayin kanwar Amma sai idan babin girmamawa ne, ba ita ba ko Hamad wasa yake da ita, daman kuma hausawa sun ce karamar uwa madaukar zunubi. Amma ta ce

 Haka Allah ya so Hajiya komai Allah ne yake tsarawa Allah dai ya ba mu ikon cinye jarrabawar wannan jarabarwar

 Toh Ameen ina nan ina ta addu'a, da yardar Allah Iyami sai kin koma dakin domin sakin nan naki har hawan jini yake son tasar min, Allah ya sauke ki lafiya, da na shiga gidan ma sai na ji duk yayi min dabam

 Ameen

Amma ta amsa tana jin zafin barin gidan Appa da ta yi, ba tare da laifin komai ba. Gwaggo ce ta shigo suka suka ta hiran kowa yana fadin abun da ya fahimta game da lamarin, Amma kuma tana fadar yadda Appa ya canja mata tun kamin sakin. Cikar da cikin Hajiya Binta yayi a gidan danta be hana ta cin abinci a gidan Amma ba, saboda tana son Amma kuma ta san idan bata ci ba Amma zata ji babu dadi domin abinci Amma take fara ci kamin ta ci na kowa wani lokacin ma bata taba abincinsu sai ta ce ta koshi. Bayan sallah la'asar Yasir ya iso gidan daukar Hajiya Binta kamar yadda mahaifinsa ya umarce shi, cikin gidan ya shigo suka gaisa da sannan ya fito tare da su Hurriya a daidai lokacin da Rukayya ta sallami bakonta ta nufo karamar kofar shiga tsakar gidan da suka fito.

 Yasir ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ya gida

Ya sake mika masa gaisuwa a karo na biyu bayan gaisuwar farko da suka yi a lokacin da ya shigo.

 Mutumen da na gani saurayinki ne?

Wani kallo ta yi masa jin yadda yayi mata tambayar kai tsaye kamar da zolaya kuma kamar gaske, domin murmushin dake fuskarsa ya hanata fahimtar komai.

 Dan makarantar mu

 Dan makarantarku har cikin gida? Lallai yana da matsayi da alama

Murmushi kawai ta yi ta maida dubanta gurin Hajiya da Amma ta rakota suna tafiya suna hira.

 Allah ya kiyaye hanya, Hurriya sai kun dawo

 uhmmm za a shiga a cigaba da karatun ko? Ko last time da na zo har na fita baki sani ba tsabar karatun littafan soyayya, to aje a karasa kar a manta page din da ake

Ta girgiza kai still tana murmushi.

 Yasir ka cika shiga min hanci fa... Haka kemin idan na je gidanku ko zama na yi sai ka ce ba daidai na zauna ba

 Toh ki fyato ni mana idan kin isa

A nan ma murmushi ta yi ta shige ciki, shi ma ya bita da kallo yana murmushi Hurriya da Hamad kam tuni sun kai cikin mota, inda sabo sun saba da ganin tsokanar yayansu akan kanwar Mamansu ba sabon abu ba ne a gurinsu Amma ma ta saba gani balle kuma su. Amma da kanta ta budewa Hajiya mota ta shiga ta rufe sannan ta juya ta koma ciki Yasir ya shiga ya fara jan motar.

 Yasir na ce ko a fara sabunta kayan dakina ne na kusa samun kishiya?

Hurriya ta saka dariya Hamad kuma yayi murmushi tare da cewa

 Hajiya yanzu kuma kin fasa aurena?

 Eh ga babba me zan yi da yaro! Yasir ya ishe ni gashi har yana nema min kishiya, ko da yake Kaltume ai ba zata yarda ka dauki wannan ba sai dai wata

 Ke tsohuwa waya fada miki har yanzu ana irin zamaninku da ake yi ma mutane auren dole? Ni zan zabo wadda nake so na yi aurena

 To Allah ya nuna mana, kuma ya bada ta gari

 Ameen

Ya amsa yana cigaba da jan motar. Sai da ya fara isa gidan Hajiya ya sauketa sannan ya juyo ya kama hanyar gidansu, a harabar Hajiya Kaltume ya faka motarsa ya bude ya fito Hamad ma ya fito tare da Hurriya gaba dayansu suka nufi hanyar falon Hajiya Kaltume.

 Hurriya me ya samu gilashinki?

Yasir ya tambaya domin tun zuwansa daukarsu ya lura da fashewar gilashin nata. Ta kai hannu ta taba gilashin.

 Faduwa na yi

Karaf Hamad yayi ya ce.

 Karya take wani bakon Momy ne ya mareta ni kuma ya na fasa masa tayun mota gaba daya

Daga Huriyyar har Yasir tsayawa suka yi kallonsa da mamakin furucinsa.

 How?

 Wuka na saka wukar Momy ta yanka ?ashi na yi ta cakawa ina yanka har da sai da na fashe duka tayun

Maganar yake yana nuna yadda yana yana cize baki alamar ?eta. Cikin mamaki Yasir yayi dariya ya bugo kan Hamad.

 Baka da kyau yaron nan bura'uba

Hurriya ta yi murmushi for the second time ta sake jin Hamad ya burge ta a yau, bayan da ya fadi cewar zai zama likita saboda yayi mata aikin ido yanzu kuma ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login