Showing 189001 words to 192000 words out of 279257 words

Chapter 64 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34659

ce ya sallameka kuma wai stressed ne, zaka je England a can za a duba lafiyarka da kyau za su gano ko minene

 Saboda stressed din ne Ammy ko a can ne haka za su fada, ni kaina na san bana samun hutu, kuma wannan asibitin da kike gani asibiti ce mai kyau da akw kula da marar lafiya kamar a waje, asibitin Barrack ce fa, Barrack din ma babba

 Idan haka ne me yasa ya sallame ka a yanzu? Ko da stressed din ne ai ya kamata ya rike a nan ka huta ko na kwana uku, ko dai suna son su kashe ka ne?

 Da na musu me?

Ya tambaya yana murmushi Momy Ikilima da Momy kuma suka yi dariya, daman sun san Ammy duk wani abun da ya shafi danta bata daukarsa da sauki bata saka wasa a ciki.

 A gida zan fi samun hutu, yanzu zan tafi na rubuta musu takardar na hada da shaidar takardun da za su tabbatar da ba ni da lafiya, na saka hannu na aje musu, Idan suka yi bincike suka tabbatar da gaskiya za su daga min kafa na kwana uku ko sati ko kuma wata, wata kila ma har shekara ya danganta da abun da likitan ya fada musu da kuma yanayin ciwon nawa da yadda suka gamsu

 Dole sai na yi haka? Kuma dole kai zaka yi?

 Aikin Soja ba kamar sauran aiki bane Ammy, dole na bi dokoki da ka'idodin manya kamar yadda na kasa da ni ma za su bi ni, zan iya tafi na yi yanzu?

Permission kawai ya roka daga gurin Ammy sai ta kara masa da tukuici.

 I will escort you

Duk yadda ya so ta zauna yaje yayi abun da ya kamata da akansa be samu haka ba, sai da Ammy ta raka danta da kanta har gurin da ya kamata shi kadai ya shiga sai da ya karya dokar ya shiga tare da ita. After ya dawo abokan aikinsa suka yi ta shigowa suna masa ya jiki, ciki har da manyansu and da yawansu sun san Engr AA Turaki wato mahaifinsa ba dan yana aikin sojan ba sai dan connection da kuma kudi mai sa asan mutum dan dole. Wasu kuma suka shigowa ne saboda Captain jindadin aikin da suke da shi da kuma kokarinsa. Momy bata bari sun fita a office din ba sai da Captain ya wanke bakinsa ya yi breakfast sannan suka fito wasu sojojin na take masa baya har gurin da aka faka manyan motocin gidansu, Daya ta Momy, daya wanda Ammy da Engr suka shigo sai kuma dayar da bodyguards din mahaifinsa suke ciki, dayar kuma ta Momy Ikilima ce. Captain ya kalli Mahaifiyarsa ba tare da fargabar komai ya ce.

 Kamin mu wuce Ammy ina son muje mu duba Hurriya asibiti....

Ammy zata yi magana Engr yayi saurin girgiza mata kai alamar kar ta hana, sai kuma ya tari numfashin mahaifiyarsa ya amsa masa.

 Okay zamu fara zuwa mu dubata tukuna sai mu tafi gida ko Family House?

 Family House

 Okay My Son

Direban ya bude masa mota ya shiga baya, tare da iyayensa Ammy da Engr, wani Knight ya shiga Front seat, Hajiya Nafisa wato Momy da Momy Ikilima ma a dole suka bi Captain da iyayensa dake kokarin cika masa kudirinsa. A harabar Federal Medical Center wato FMC suka faka, security dake gaban motar Engr ya bude motar da sauri Captain ya fito tare da iyayensa, Bodyguards na take musu baya. Ko kadan Momy bata so zuwa duba Hurriya a asibiti ba, ba dan Captain ya so haka ba kuma iyayensa suka biye masa ba zata taba zuwa dubata ba, domin ta fi jin tsanar Hurriya a yanzu fiye da koyaushe, sanadinta suka fara samun da Captain gashi kuma yanzu ta ja musu abun kunya, sai dai babu yadda ta iya saboda an an'uwanta ya so haka. A dokar asibitin lokacin da suka zo ba lokacin ganin marar lafiya ba ne, amman ba a hana su shiga ba domin ko na goye ya san kura.

 Ina ne?

Captain ya tambayi Momy ba dan ita ma ta sani ba, sai da ta sauke ajiyar zuciya ta kalli yayanta sannan ta daga wayarta ta kira Namra.

 Gamu mun shigo asibitin, wane daki ne?

Ta fada musu har da number dakin, a nan suka juya zuwa wani ward din da ba wannan ba, ko'ina suka wulga sai ya kallesu kana ganinsu ka san ba kananan mutane ba ne. A lokacin da suka isa dakin da Hurriya take sai Captain ya kalli iyayensa ya ce.

 Wata kila ba zata so ta gan mu tare da ku ba, zan fi jindadi idan na shiga ni kadai, na san idan na ce ku zauna a mota na shigo ni kadai ba za su yarda ba shiyasa ban yi magana ba

A nan kam Momy kasa hadeye maganar ta yi cikin bacin rai ta ce.

 Mu iyayenka mu zamu jiraka har sai ka shiga duba wata banzar yarinya tukuna mu tafi? Sai kace kai ka haife mu?

 Idan hakan zai faranta ransa me ye a ciki? Shiga ka yi abun da zaka yi son zamu jiraka a mota

Daddy ya fada sannan ya kalli bodyguard dinsa daya.

 Ka tsaya a nan idan ya fito ku same mu a mota

 Okay Sir

Daddy ya juya tare da Ammy domin komawa gurin motarsu, Momy ma dole ta bi bayansu iyayen yaro sun goyi bayansa ita a su ta ki bi, a nan ta samu damar karanta musu kabli da ba'adi na Hurriya, tana ta kusheta. Sai da suka wuce sannan Captain ya murda kofar dakin ya tura ya shiga, tana zaune saman gadon ta lankwashe kafafuwanta tana fuskarta hadu da kofar dakin.

 Kai kuma kai ne wa?

Gwaggo ta tambaya tana kallonsa. Sai a lokacin ya tuna be yi sallama ba. Dan haka ya jadada sallamarsa sannan ya karasa cikin dakin yana gabatar da kansa.

 Sunana Jamal amman an fi sanina da Captain ni dan Momy dan yayanta...

 Toh ko me ya sa ka zo?

Ya kalli Hurriya da babu gilashi a idonta hawaye na zubo mata ya ce.

 Na zo na duba Hurriya ne? Namra ta fada mana tana nan

 Namra ta tafi gida tun dazu, kuma dan Allah ba ma bukatar kowa, daga dangin Nafisa har na Kaltume, wannan kiyayyar ta yi yawa, ba bar uwa ba a bar ya ba, babu kalar azabar da ba a nunawa yarinyar nan ba yanzu abun ya wuce nan har sai a hada da kazafi? Kazafin ma na zina? Ita da gidan ubanta amman bata da walwala? Bata da jindadi? Akan me? Yanzu gashi nan kun yi sanadi idanuwan nata sun rufe gaba daya, bata iya gani ko da gilashin, buri ya cika tun safe da ta farka bata cewa komai ba, an kashe yarinya tana ji tana gani

Gwaggo ta karashe fadan da kuka, Captain ya sauke idonsa kasa hawaye suka zubo masa.

 Ina kyautata zaton ni ne mutum na farko da ban yarda Hurriya ta aikata wannan abun ba, ban zo nan domin cin mutumcinta ba, ita ma ta sani kawai dai na kasa natsuwa ne har sai na zo na dubata, ban san matsayinki a gurinta ba, amman dan Allah ina rokon Alfarmar ki bar ni na ga Hurriya

 Gata nan ka ganta, amman ba zan je ko'ina ba, kai ma ba zaka dauki hotonta ka yadawa duniya ka bata mata suna ba, kuma ko waye da hannu a lamarin kada Allah ya bar shi da salama, daga yaron har kowa

 Ameen

Ta saka yatsansa ya cire hawayen sannan ya karasa gaban gadon Hurriya saitin inda take zaune ya tsaya yana kallon fuskarta. Hawaye take malalarwar irin malalar da gulbi yake idan ya kawo, babu yankewa kuma babu fasa zuba, yanayin yadda take kallon saitin da yake tsaye ya isa ya kara tabbatar masa da bata iya tantance fari da ja a yanzu, sai bakin da ya rufe ganin idanuwanta.

 Hurriya...

Bata amsa ba, motsa ba bata bar masa wata alama da zai gane tana jin muryarsa, ibadarta kawai take ta kuka. Cikin kuka Gwaggo ta ce

 Bata cewa komai, kuma bata gani

Captain ya hadeye yawu mai matukar aci fa ma?a?i a ma?oshi.

 Likita ne ya ce bata gani ko kuma ke kika ga alamar bata ganin?

 Na ga alama, sa safe da ta tashi zata shiga bandaki ga gilashi a idonta amman lalabe take, na fada Likitan da ya shigo suka duba idon suka ce ua samu matsala, shiyasa suka canja mana daki ai, yanzu ba maganar sumanta ake ba, maganar idonta ake Likita biyu ya duba idon zamanmu a nan sun ce sai an yi aiki wai jijiyar dake hada idonta da kwakwalwarta ta samu matsala

Captain ya daga kansa sama kamar zai fashe da kuka.

 Ya Rahma....

Ya ambacin mafi rahamar masu tausayi, sannan ya sauke kai ya kalleta pointing finger dinsa ya kai saitin idonta kamar zai tsokale ido amman bata matsa ba, a nan ya tabbatar da bata gani da gaske.

 Jiya kin zo min a suma, kin fada min baki aikata ba, kuma na yarda da ke. Yau kuma ina tsaye a gabanki ne domin na fada miki wani abu, kowaye ya aikata miki wannan abun Hurriya, ba zai sake samun farinciki ba a rayuwarsa, sai ya kunyata fiye da yadda ya so ya kunyata ki, sai na sa duniya ta tsine masa irin tsinuwar da zai ce ina ma be aikata ba

Ya kama hannunta ya rike a gaban Gwaggo.

 Na miki wannan alkawarin Hurriya, kamar yadda na yi miki alkawarin dawo miki da dan'uwanki, shi ma wannan ki rubuta ki aje nauyin yana kai na....

Gwaggo ta share hawayenta ta taso daga inda take zaune da sauri tana fadin.

 Kai kai kai sake mata hannu, ban san sharin da ka zo da shi ba kai ma

Captain ya sake mata hannun ya nufi kofa yana share hawaye, be ma kula maganar Gwaggo ta halin da ya ga Hurriya da damuwar da yayi arba da ita a fuskarta ta tafi da tunaninsa. Gwaggo ta kama hannun Hurriya ta shafe mata da hijabinta.

 Babu abokin yarda a cikinsu, ni da na san haka rayuwa zata miki Hurriya da ban bari kin zauna a gurin Ubanki ba, ko da kuwa shari'a ce zan yi da shi...

Wani irin numfashi Hurriya ta fara fitarwa da karfi, kamin ta daga kanta sama ta kwala wani uban ihu....

 Gwaggo ban aikata ba....!

Gwaggo ta rumgume ta da sauri tana kuka.

 Wallahi ban aikata ba....!

 Na sani, babu wanda ya yarda kin aikata daga ni har Rukayya

 Allah ka hana, wanda ya aikata min wannan abun farinciki, Allah ka hana shi jindadi da kwanciyar hankali, Allah ka nisanta shi da natsuwa ka kusantar da shi ga kunya da damuwa, fiye da yadda yayi min

Cikin tsananin kuka Hurriya ta yi ma kanta addu'a tana fatar mahallincinta ya amsa mata.

 Ameen Hurriya Ameen

Gwaggo na amsawa Hajiya Binta ta turo kofar dakinta ta shigo da sallama. Hurriya na jin muryarta ta juyo ta kai hannu tana lalaben inda take.

 Hajiya komai ya kare min, idanuwa sun tafi, mutuncina ya zube... Na barar da kimar Appa da Ammana a idon duniya, komai ya kare yanzu babu abun da ya rage min, kullum bakinciki ne yake kusanto ni yana nisanta ni da farinciki....

 Share hawayenki yarinyar, farincikinki mai kyau shiyasa yake da tsada, duk mai hassadarki yana son ganin bayanki sai ya dawo karkashinki, wannan alkawalin Allah ne mai hakuri yana tare da riba Allah da kansa ya ce dukannin tsananin sauki yana nan damansa, idanuwanki za su bude Hurriya, damuwa zata yaye farinciki sai ki samma wani, karki damu da hotunanki sun shiga duniya, ko karuwanci zaki yi, ki je ki yi ki dawo Hurriya ni FATIMA BINTA zan karbe ki... 

Hajiya Binta ta fada tana dukan kirjinta da karfi, kana ganinta kasan tana cikin bacin rai...
If you read my book ba tare da kin biya ba, indai hakkina ne Wallahi ban yafe ba, ku kuma masu sharing Allah ya muku yadda kuke min. I rest my case =?L?


CAPTAIN POV.

Ko da suka isa Family House dinsu, gidan yana cike da mutane, abun ka dake mai jama'a, daman sun tun a lokacin da yake asibitin suka tafi ganinsa aka hana su shiga. Kowa sai murna ganin Captain yake kamar wani Sarki, domin kowa a familynsu yana son Captain ko dan duniyar Ubansa da Hajiya Turai. Duba daya zaka yi ma Captain ka fahimci baya cikin farinciki ko kadan, ya zama so silent daga lokacin da ya baro asibitin da Hurriya take zuwa motar har kawowa gidansu. Wani abun da ya bawa Ammy da Engr AA Turaki mamaki shi ne takardar sammacin kotu da suka tarar an kawo a gidan. Engr ya karanta takardar ya sake karantawa ya dago ya kalli yan'uwansa dake cike da katon falo na Mahaifinsa.

 Waya kawo takardar?

 Ma'aikacin kotu?

Wata kanwarsu dake zawarci a gidan ta amsa masa. Momy ta tabe baki.

 Daman na raya a raina na ce sai abun nan yayi tsananina, karya yaron mutane fa Captain yayi kuma ya fasa masa hakora!

Ammy ya kashe ido.

 Ashe kariya ce ma kawai shi nw za a kai ana asibiti? Ko kashe shi Captain yayi ba zan bari ya tafi kotu ba balle kuma karaya kawai da zubar da hakora

Engr ya sauke ajiyar zuciya cikin takaici ya ce

 Anya Bashir Sarauta ya san Jamal ana ne kuwa? Har zai yanko sammacin kotu ya aiko a gidan nan? Kuma ana yake kara? Ni Bashir Sarauta zai saka ana kotu? Bashir Sarauta talaka a cikin masu kudi? Bashir Sarauta da yake karkashin inuwar dukiyata...! Ai wani sarkin kakan wani sarkin ne... Amman ya ba ni mamaki, ni ma kuma zan ba shi mamaki

Momy ta ce.

 Ai duk Hurriya ce sanadi, gashi masu arziki za su yi fada akanta, yarinyar da bata kai ba

Captain ya kalleta kamar daman jiran yake tace wani abu a kan Hurriya.

 That's it, Hurriya this Hurriya that... Komai Hurriya kike blaming, yarinyar da bata isa ta daga idonki ta kalleki a matsayin uwa ba, yarinyar da bata isa ta shiga dakinki ta rokeki wani gata ba, yarinyar da bata isa ta shiga Kitchen dinki ta zuba abinci ta ci ba, yarinya kamara kun matsa mata kun firgita mata kwakwalwa, yanzu ga wata bakin hayakin ya rufe ta amman still baki ji tausayinta ba?

Ammy ta kalleshi tana kai hannu ta taba shi kuma ta kwantar masa da zuciyar dake fisgar anta.

 Captain you can't talk to Momy this way... Haba.. 

Cikin lalama take fada tana dan kallo Momy. Captain ya kalli Ammy.

 Kiyayyarta da yarinyar nan wani abun ne da ya shafe ta na dabam, babu ruwana a ciki ni dai abun da na sani babu abin da zai hana ni auren Hurriya...

 God forbid...

Ammy ta dauke hannunta daga jikinsa da sauri kamar ta taba mugun abu.

 Yarinyar da duniya ta gama ganin tairaicinta? Yarinyar da bata da kamun kai? Karuwa? Kuma makauniya? Ba zan karbe ta a matsayin suruka ba har abada

 Enough....!

Daddy ya daka mata tsawa, sannan ya kalli Captain ya ce.

 Tashi ka shiga ciki ka huta

Captain ya mike tsaye ya kalli mahaifiyarsa hawaye na zubo masa.

 A halin yanzu, Wallahi duk duniya Ammy ke kadai kika kai ki kira Hurriya da karuwa, na hade ban ce komai ba, kuma ban dauki mataki ba... Ki gafarce ni Ammy ni dai kam ban taba jin tsananin son wata mace a zuciyata ba kamar yadda nake jin Hurriya a yau, i love her more than life....

Kowa kallon Captain yake domin yau yayi abun da be taba ba, fadar yana son wata a gaban kowa, kuma har ya zubar da hawaye.

 Ko Aljana ka ce zaka aura Jamal zan aura maka ita matukar hakan ne farincikinka, kuma zan raba ka da wanda baka so matukar hakan zai dada ranka... Ka bar wannan maganar a hannuna tafi ka huta....

Cewar Daddy yana nuna masa hanyar bedrooms din dake stairs... Captain ya nufi bedrooms din yana jin kamar za'a raba kirjinsa gida biyu, Hurriya ce aka watsa hotunanta amman shi da ita ne suke raba nauyin bakincikin.




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
38

Yana shiga

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login