Showing 144001 words to 147000 words out of 279257 words

Chapter 49 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34716

farin lace ta mikawa Hurriya wayar.

 Duba ki gani, daman wani Lace ne nake son na siya muku

Bata yarda ta karbi wayar ba, a madadin haka ma sai ta bi Hajiya da wani kalami.

 Aa Hajiya na gode

 Toh har da kyautar Iyami ta hanaki karba?

 Aa Hajiya ai Amma bata iya magana, bata ce min kar na ki karbar kyautar kowa ba, ni ce dai ban karba a karan kaina

 Toh tashi ki kara gaba, daman duk yadda aka muku mutuncin sai kun ce ba ayi ba, an riga an gado bakin hali, daman ni ai ba so na zaku yi har abada

Hajiya Kaltume kamar wanda ta zare haka ta rika fadawa Hurriya kalamai marar dadi, Hurriya dai bata dauki ko daya a nan gurin da ta fada mata su a nan ta bar su, ta fice daga dakin. Fitar Hurriya da kamar minti goma Kulu ta shigo dakin ta zube kasa tana dagawa Hajiya hannu kamar wata sarauniya ko matar sarki.

 Ranki ya dade gani, Khairiya ta fada mjn ina nema ma na fito har na kusa sai na hango ta doso nan tare da Hurriya shiyasa na koma

Hajiya Kaltume ta yi kamar bata ji ba ta shiga wani bangaren na wayarta, kamin ta kara wayar a kunnenta.

 Yasir kana kusa?

Yasir ya amsa a dayan bangaren.

 Eh ina nan waje, muna tare da Kamal ne

 Asibiti nake son mu tafi idan ka gama

 Waye ba lafiya

 Ni ce, amman dai da sauki, ka bari sai ka gama ni ma akwai abun da zan yi yanzu

 Toh

Ta sauke wayar ta kalli Kulu, sai a lokacin take amsa mata maganar da ta yi.

 Ai kara da kika yi haka, saboda kaucewa ido

 Duk wani abun da zai saka Momy ta ji ko ta gane akwai alaka a tsakaninmu ina kokarin ganin na gujewa haka

 Kin kyauta, dabam na ce a kira min ke ne, saboda mu yi wata magana da ke, kamin nan tashi ki tura kofar dakin

Kulu ta kike tsaye ta nufi kofa da ta bari a bude ta rufe, sannan ta dawo ta zauna ta natsu sosai tana sauraren matar da ta fi tsoronta a yanzu fiye da uwar dakinta.

 Aminci ne ya saka na nake tambayarki abu ko na saka ki yi, na san ba dan kin dauki sarka da kudi ba, wata kila ba zamu san juna ba, amman bana son kina kallon wannan a yanzu, ni daman tuni na tattara wannan abun na aje a gefe daya

 Hajiya ai ba dan karki ce na yi karya ba, nikam da nace satar nan ta zame min alheri domin sanadinta na hadu dake

Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya ta marairaice fuska.

 Kulu ke da yar'uwata duk daya a yanzu, shiyasa har na kira ki nake son na fada miki damuwata, kuma neman samun mafita a gareki

 Hajiya tafi kanki tsaye, duk wani abun da kike so zan miki shi, yadda kika rufa min ba ni da kamar ke a duniyar nan

Dogon numfashi Hajiya Kaltume taja ta sauke sannan ta furta.

 Kulu ina cikin damuwa da matsala kala kala, amman wanda ta fi min yawa, ita ce ciwon kafar nan dake damuna, yanzu haka kiran da kika ga nayi ma Yasir ita zan kai asibiti, na dade ina ciwon nan amman har yanzu babu sauki babu alamarsa, tun ina barin ciwon a cikina abun ya fara min yawa, to yanzu kuma sai abin da biyo har da mafarkai da ba su dace ba, kuma ciwon nan sai cigaba yake, abun ya ba ni tsoro, ga maganin asibitin nan yi ake amman a banza

Kulu ta dukufa a tunani har wani kada ido take tana jinjina kai.

 Hajiya ba zaki gwada na hausa ba? Ko Allah zai saka a dace?

Kamar an yi ma Hajiya Kaltume albishir haka ta ji, saboda Kulu ta sosa mata gurin dake mata kaikaiyi.

 Shiyasa na kiraki ai, kin san ku ne mutanen kauye, kun fi sanin irin abubuwan nan, wata kila ba zaki rasa sanin masu irin aikin ba

 Akwai su Hajiya kala kala, akwai wata mai aljannu tana bada taimako sosai, kuma akwai namiji ma yana yi

 Yauwa namijin dai zai fi, ni ban cika son mata masu aljanu ba, na fi son inda zan tafi a fada min ko minene, jifa ce ko kuma ciwo ne ko iska ne

 Aiko kina tafi gurin Malam na gangare zai fada miki ko menene, domin shi baya son ma ka fada masa abin da ya kawo ka shi zai baki labarin komai, har abun da baki sani ba, da madubi yake aikinsa yana kallo madubi ya fadi magana ta tabbata, kuma ko minene a take zai rabaki da shi, idan jifa aka yi miki ko turbuda a take ma zai ciro shi

Hajiya Kaltume ta dauki filo ta dora a cinyarta ta kwantar da hannayenta akai tana gyada kai.

 Yauwa irin su nake so masu aiki kamar yankan wuka masu zafi

 To idan kika kai gareshi magana ta kare, domin shi ko mutum kika ce ya kashe miki zai kashe

 Irinsa ya dace, kin ga ko minene a take zai fada maka kuma ya karya shi, a ina hake Kulu?

 A kauye uku yake, dake nan cikin bunguWu

 Babu nisa sai dai ban san yanayin hanyar ba?

 Hanya lafiya kalau take, ai garin mu babu irin bata gari, su kansu suna tsoron mutanen yankin

 Maa Sha Allahu, sai dai kuma tafiyarmu kamar ba zata yi a tare ba, saboda uwar dakinki Nafisa ba zata bari ba nake gani

 Wannan ba matsala ba ne Hajiya, kina shiga garin Bunguu ki dauke hanyar kauye uku, da kin isa ki ce gidan Malam Ashiru mai Yasin da Allon karfe kike nema, ko karamin yaron zai kai ki, idan kuma kina jin ba zaki iya haka ba ke nemi gidan su Kulu taroro kina shiga gidan ki ce ni na aiko ki gurin Malam Ashiru za a kai ki, zaki iya ma kira na yi magana da su

 Allah dai ya saka miki da alheri Kulu, ina ganin ma ba zan tafi asibitin nan ba, gobe ina gama karyawa zan kama hanyar garin, zan iya tafiya da direba na ma ya kai ni garin

 Daman Hajiya tafiya da daren ba ai ya fi sirrin da sauki

 Haka zan yi, zan fara zuwa gidan na ku sai na kira na ba su ku gaisa idan ya so sai kun iso gurin Malamin zai fi sauki

 Toh Hajiya, Allah ya bada lafiya

 Amin

Hajiya Kaltume ta mike tsaye daker tana cige baki kafar kuma kamar zata yi gurmanta da ita haka ta taka ta isa gurin kayanta ta bude wardrobe ta dauko wani lace da ba a dinka ba ta jefawa Kulu.

 Ahhhhh Kai Hajiya duk ni kadai? Alhamdulillah Hajiya na gode na gode, Allah ya kara rufa asiri ya biya bukata, Allah ya kara lafiya ya tsare ki daga duk wani sheri

 Amin, wani abun kulu ai sai na samu lafiya ma, da yardar Allah idan bukata ta biya zan kyautata miki, ta shi ki tafi kamin Yasir ya shigo

 Toh Hajiya, amman zan bar leshin a nan saboda idon mutane, sai idan na ga sarari zan zo na karba

 Dadina da ke wayo Kulu kin iya sirri

 Gidan na mu ne Hajiya sai da haka, kamin a fara fadar ana ganina bangarenki 

Hajiya Kaltume ta yi murmushi. Ita kuma ta mike tsaye ta yi mata sallama.

 Mu kwana lafiya

Kamin ta isa kofar dakin ta bude Yasir ya bude sai dai be shigo ba ya bata hanya ta fita yana amsa gaisuwar da take masa.

 Me ta zo yi nan?

Hajiya ta nuna masa lace din dake kasa

 Nafisa ta aiko min da lace?

 Ke kuma?

Ya tambaya kamar mai shakku, Hajiya dai bata sake ce masa komai ba ta nufi gurin da ta tashi ta zauna da tafiyar nan nata kamar zata yi dingishi.

 A kafa kike jin ciwon ne?

 Eh gurin da na taba jin ciwo kwanan baya, a nan na sake jin ciwo haka nan kawai sai na ji kamar an tureni na fadi kasa

 Ko santsin gurinki ne ke janki

Ya soma duba kafar da ta dan dago masa tana jin kamar ana yanka gurin sai sululi yake mata kamar an watsa ruwan zafi.

 Aa ba wani tsantsi shekara nawa ina gidan nan da can tsantsin be ja ni ba sai yanzu? Turo ni ake yi fa

 To wa yake turoki Hajiya

 Yo ina zan sani tun da abu ne na aljanu, amman tabbas ba faduwa ce zallar faduwa ba, turo ni aka yi

Yasir yayi murmushi tare da kai hannu ya latsa gurin.

 Ban san me yasa ku mata kuke yarda da irin abubuwan nan ba, haka Last week Rukayya take ce min wai ance aljannu ne a jikin Amma, ku dai komai kun fi son ace aljannu ne, wani abun fa daga Allah yake kai tsaye idan ana na asibiti zaki ga an dace, ita kanta Amma da za a fitar da ita waje a dubata duba mai kyau za a gane Matsalarta

Hajiya ta janye kafarta da sauri saboda lasa gurin da Yasir yake yi.

 Ku kuma ba ku yarda da aljannu ba ko?

 Mun yarda da su mana, amman ba lallai komai ace su ba, kin ga kafar nan take da zaki iya daurewa mu bari sai da safe mu tafi asibitin, hoto za su miki su duba matsalar

 Eh haka zan yi, mu hakura da tafiya asibitin nan sai gobe da safe

 Ba sosai kafar take damunki ba

 Yanzu dai ta min sauki ba kamaf dazun ba, kai Allah sarki na tausaya wa Iyami gaskiya, a kafa kawai ina jin ciwon nan kamar zan mutu balle ita da ta ke kwance bata iya komai shekara da shekaru, wai har yanzu bata iya tashi da kanta?

 Rukayya ta ce min tana tashi da kanta yanzu, kuma da kanta take cin abinci, rayuwar Amma akwai ban tausayi sosai, gashi ba wani karfi yanzu sosai 

 Munafuka Hurriya wato kin iya kini bibi ko? Ni zaki yi ma karya?

Ta fada a ranta tana wani kashe ido, a zahiri kuma sai ta ce.

 Allah ka raba mu da wahalar duniya, wato Yasir yanzu ka zama dan gidan ka san ciki da waje

Murmushi yayi ya mike tsaye.

 Daman can ai dan gida ne ni, ba wai sai saboda Rukayya ba

 Haka ne, Allah ya zaba abun da ya fi zama alheri amman dai ina son ka sani ba zan taba yarda ka dauko yar'uwar makiyiyata uwa daya uba daya ka kawo a gidanka ba da sunan mata

 Hajiya Amma ce makiyiyar? Idan ma kuna kallon junanku da wannan ne ban isa na canja ba, amman matsalarku dabam be kamata ta shafe mu ba, musamman ma ita Rukayya meye nata a ciki?

 Wai dan Allah duk matan garin Gusau ka rasa wanda zaka so sai ita? Me ta fi mata da shi ne?

 Hajiya ni dai ita nake so kuma ita zan aura da yardar Allah

Hajiya ta daure fuska sosai tana watsa masa danta da be kishinta harara.

 Ina fada maka bana bukatarta a matsayin suruka kana karanta min ita zaka aura, saboda kai ne uba ni ce ya ko? To mu zuba ni da kai shege ka fasa, ko saboda ka ga wacan karon ka min magana na maka sanyi? Ina duba gudun ruwanka ne? Amman Wallahi ko Rukayya ita kadai ta rage a duniya ba zaka aureta ba

Gudun sa'insa da ita ya saka shi ficewa daga dakin ba tare da ya ce mata komai ba, sai dai kana kallon fuskarsa zaka san kalaman na Hajiya Kaltume ba su masa dadi ba.

 Wallahi ba zaka aureta ba, ni gaba daya ma kamar an canja min kai, kai kenan namiji Allah ya ba ni amman baka min biyaya, idan ina kiyayya da mutum kai sai ka dauke shi masoyi, haka kake rawar jiki akan Hurriya sai ka ce ni na haifi yarinyar nan

Ta yi ?wafa, kamin ta juyar da fadan gurin Hurriya da bata san tana yi ba.

 Ita kuma tsohuwar makira wai ita nan har ta iya canja labari ta fada min Iyami bata ji sauki ba, wannan yarinyar da wata babbar mace ce da ni zata yi kishi nan gaba, amman zan maganinku duka

Ta mike tsaye tana daga kafar ta nufi bandakinta.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 28
Ita ke da girki yau, amman sai ta saka Khairy ta kai ma Appa komai a bangarensa, saboda ba zata iya zirga zirga da kafar ba, daman kuma tana jin wani abu mai kamar haushin Appa a ranta yanzu. Dan haka bata leka bangaren ba sai after goma da wani abu, sannan ta saka kayan bachinta ta dora bakar abaya a sama, yau kam bata damu da yi ma mijinta ado ba, daman kuma ba wani yabawa hake idan ta yi ba, bata sani ba ko dan bata da kyau ne ko kuma saboda an dade tare da juna, amman ta tabbatar idan Iyami ce ba zai kyale ba, tun asali can Appa irin mutunen nan ne dake da rayuwar da, wani abun zuwan Amma ne ta canja shi, wani kuma Momy ce ta yi sauya mata ta karfi da yaji.

Bata bar annuri da fuskarta ba saboda damuwa ta mata yawa yanzu, har ta rasa ina zata kama, haka ta shiga barayar mijinta ba tare da sallama ba, Appa ya aje wayar dake hannunta yana kallonta da yanayinta, a gaban gadon ta zauna cikin wata muryar dake kara bayyana fushinta ta ce.

 Sannu da zuwa?

 Yauwa, amman yau lafiya kike kuwa?

 Me ka gani?

Ya gyara zamansa yana kallonta irin kallon nan na mazan da suka kwashe shekaru a duniya kuma suka fahimci rayuwa.

 Na ga yau Ummul Khairi ce ta kawo abinci, kuma kin shigo babu wani walwala a tare da ke, kayan bachi da kika saba sakawa a nan ma yau can kika saka kika zo da su?

Ta dan tabe baki.

 Ashe kana lura da al'amurrana

Appa yayi dariya irin ta can cikin makoshin nan ya dubeta a natse ya ce

 Shekara nawa ana tare Kaltume? Uwargida ran gida? Uwargida sarautar mata? Kuma sai ace ban lura da yanayinki ba? Ai shi miji kamar....

Ya ja zaren furucin yana sosa gafen idonsa tare da aje wayar hannunsa.

 ....Uba yake wani lokacin duk wani abun da mace take yi yana lura da shi, ita kuma mace kamar gidan uba take a karkashin miji, wani ikon ma har ya fi na uba, shiyasa Allah yake cewa ku tsiratarta iyalanku daga wuta, wanda makamashinta su ne Mutane? duwatsu, ku ai kuyo ne a gurinmu, dole sai muna kiyayewa, kuma kuna taya mu idan ba haka ba abubuwan sai su mana, a duk lokacin da na tuna cewa zan tsaya a gaban Allah amsa tambayarsa sai hankalina ya tashi matuka

Ta juyo ta kalleshi a tsanake.

 Saboda me?

 Alhamdulillah dukiyata halak dina ne, kuma ta hanyar da ya dace nake tafiyar da ita, amman duk da haka sai na amsa hanyar da na sameta da hanyar da na kasheta, za a tambaye ni kam ibada a gangaro kan iyali wannan abun yana daga min hankali, ko a gaban alkali ka tsaya ya tambaye ka ina ka samu kudin jiya da yau ina ka kashe su, ya ka yi ibadarka ta yau da jiya, ya ka tarbiyarta iyalinka ai akwai tashin hankali balle Allah abun akwai ban tsoro Kaltume, a dalci ma a tsakanin yaya dole ne ka tsayar da shi, kuma ka kula da tarbiyarsu, wani abun da idona yake rufewa na aikata Kaltume yana damuna matuka, amman na rasa gane ina matsalar take, ga yarki Ummu Khairy abubuwan da take yi bana jindadinsu, Yasir yana yawan kawo min kararta amman ina bashi hakuri na daga mata kafa saboda ke, idan ba haka ba kin san gidana ba a wasu abubuwan

Hajiya Kaltume ta mike tsaye ta yaya rigar after dress dake saman kayan bachinta tana fadin.

 Duk kasan da wannan kuma kana tsoro amman kake ta karma karmar waso mata? Idan ma ni ban wadace ka ba, ga Nafisa ka hada matanka biyu fara da baka amman duk haka be maka ba sai da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login