Showing 33001 words to 36000 words out of 279257 words

Chapter 12 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34634

ba?

Ya tambayi kansa, sai dai ya san ba su taba masa haka ba, idan tana bukatar abu zata yi masa magana kuma idan ma ta dauka zata fada masa. Fitowa yayi daga bangaresu ya nufi bangaren Momy, kamar ance masa juya ka gani, yana juya ya kalli bangaren Appa sai ya hango Hurriya tsaye tare da Appanta ta rike hannunsa tana ta bata rai da alama makiya take masa kan wani abu. Fasa nufar bangaren Momy yayi sai ya nufi bangaren mahaifinsa domin tambayarta ko ta dauko gilashin be sani ba.

 Appa dan Allah daga wannan ba zaka sake yi ba

Ta fada cike da shagwaba tana kara rike hannunsa.

 Haramun ne, ba kyau Hurriya ni bana sha'awar irin abubuwan nan

Appa ya fada yana kallon Yasir da ya iso gurin fuska a sake.

 Me take so Appa?

 Birthday kuma ka sa be da kyau ba al'adar mu ba ce hausawa wannan dabi'un turawa ne

 Oh Appa yanzu kai ya waye fa, ba wani abun ba ne kawai dai ana samun tsabanin fahimta ne ga mutane, kuma yanzu zamani ya canja ba kamar lokacin baya ba

 Ko zamani ya canja ni ban canja ba Yasir, abun da duk ba tarbiya ba bana sha'awar

 Appa sau daya zamu yi fa, daga wannan ba zaka sake ba? Appa please kawaye na duk ana musu sai ni

Tana maganar tana son yin kuka Appa yayi murmushi.

 Shi ke nan na ji, za a dafa shimkafa fara ayi sadaka

Ta buga kafa daya a kasa tana kukan da babu hawaye, Yasir kuma ya saka dariya.

 Appa dan Allah dai Appa

Ba kasai Hurriya take zuwa masa da bukata ba, kusan duk wata bukata da take gabatar masa da ita kidayayyyiya ce, hakan ya sak idan ta zo masa sai ya biya mata ko dan tausayinta da yake na lalurar dake tare da ita, balle kuma yanzu da tausayinta ya ninku a zuciyarsa saboda rashin Amma a gidan, sai yake ganin yaransa kamar wasu marayu da uwarsu ta mutu ta bar su.

 Na ji amman daga wannan ba za'a sake ba?

Ta amsa da sauri tana tsalle.

 Na yarda Appa na yarda Allah ya saka da alheri, Appa Allah ya biya maka bukatunka na alheri ya rabaka da Hajiya Lafiya ya kara buda maka a kasuwanci ya kyautata karshenka

Ta masa kwatankwacin addu'ar da Amma take masa idan yayi mata wani abun kyautata da ta ji dadi. Appa ya shafa kansa yana jin zuciyarsa da tausayin da be san na minene ba. Yasir ma murmushi yayi yana taya ta murna yadda Appansy ya amince da wuri.

 Bari mu fara neman Gift din da zamu bawa mai birthday

 Har da kyauta ake badawa?

Appa ya tambaya sai Yasir ya amsa masa.

 Eh Appa idan mutum yayi birthday ana ba shi kyau sosai ma, kowa da kalar abun da yake ba shi

 Oh toh saboda ki ci kudinmu kike son yi birthday kenan?

Cewar Appa yana kallonta da zolaya, sai ta saka dariya kamar ba ita ta rufe idonta.

 Appa ba da kai ba an yafe maka

Shi ma dariyar yayi, ya bita da kallo domin tuni ta nufi bangaren Momy domin labartawa Hamad cewar Appa ya yarda zai mata birthday kamin ya isa gurin hawaye ya cika idonta domin ta saba idan aka mata albishir Amma take fara fadawa sai dai a yau babu Amma a gidan kuma ta san babu wanda zai taya ta farinciki da murna sai dan'uwanta. Tana ahiga falon sai ta ja ta tsaya tana kallon Musib da ya hada hannayen Hamad ya rike yana zabga masa mari.

 Ba zaka yi magana ba? Waye yaje ma fadawa Appa karya da gaskiya ya zo ya rufata ta fada? Tsakanin kai da Hurriya

 Ni ce

Ta amsa kai tsaye domin ba zata jure ganin ana duka dan'uwanta ba da yaki yayi magana kuma ya ki yayi kuka sai dai idanuwansa sun kada sun yi ja sosai sai wani cika yake yana batsewa alamar zuciyarsa ta gama kawowa.

 Okay zo nan bakar mufuka wato daga dawowarku za ku fara hada Momy fada da Appa ko?

Bata zo ba kamar yadda ya bukata sai dai kuma bata matsa daga inda take tsaye ba ssi hawayen da ta shigo da su suka fara sauko mata, Hamad ya juya ya kalleta har lokacin be ce komai ba, daman tun shigowarsa falon Musib ya rike shi wai sai ya fada masa waya fadawa Appa gulma har ya shigo yana mata fada ta yi kukan, Hamad ta kafiya ya ki magana hakan ya saka Musib dukansa. Musib ya saki hannun Hamad ya nufi gurin da Hurtiya take tsaye ya fara kai mata duka sai ta boye fuskarta ta fara kuka, yadda Hamad ya nufo gurin da suke tsaye sai ka dauka zai yi dambe yayansa Musib ne, ficewa yayi daga falon Musib na kokarin rikoshi ya fisge ya fice da gudu, be zame ko'ina ba sai gurin da Garden din gidan yake ya samo manya manyan duwatsu ya dauko har uku ya fito da su ya nufi gurin da Motar Momy take ta fara jefan gilashin a take ya fasa mata gilashin mota ya koma dayan bangaren ya sake jefawa. Kamin yayi na uku Appa da Yasir da suke tsaye a gurin da Hurriya ta bar su, suka iso gurin da sauri domin sun lura da lokacin da ya dauko duwatsu sun san ba za'ayi mai kyau ba, Yasir yayi saurin rike Hamad.

 Kai miye haka?

Sai a lokacin Hamad ya fashe da kuka yana maida magana.

 Ya Musib ya yi min mari hudu, kuma gashi can yana dukan Hurriya, wai ya ce mun yi munafurci mun hada Momt da Appa fada

Appa da ransa ya bace saboda abun da Hamad aikata, a take abun da ya fada ya gusar da bacin ran abun da Hamad yayi. Ya nufi falon fuska a hade Yasir dake rike da Hamad har lokacin yana ta zillo sai ya sake kwaso wasu duwatsun ya fasa motar ya bi bayan Appa. Da karfi Appa ya tura kofar falon ya shiga sai ya samu Hurriya duke kusa da kofar ta rufe fuskarta tana kuka marar sauti.

 Musib...!

Appa ya aika masa da wani irin kira da karfin murya mai razanarwa. Musib dake boye kitchen ya fito baki kofar kitchen din yana amsa kiran muryarsa na rawa.

 Na'am...

Appa ya taka ya karasa har inda yake ya dauke shi da mari. Daidai lokacin da Momy ta sauko tare da Namra.

 Akwai wanda na taba duka cikinku? Akan wani dalili zaka dokesu? Kai da ya kamata ka ga wasu musguna musu ku shigar musu kai zaka saka hannu da kanka ka dokesu? Karka sake! Ina gargadinka ba su ba Hurriya da Hamad kadai ba duka yayana kar ka sake saka hannu ka dake su

Appa ya juyo ya kalli Momy dake tsaye kamar hoto tsabar mamaki ya ce.

 Na rantse da Allah idan wani ya sake dokar min ?a?a sai na masa abun da zai yi bakinciki da na kasance ubansa, ban doka ba ba zan yarda wani ya dokar min ba

 Saboda ?a?an Iyami ne?

Momy ta tambaya tana jin wani tu?u?i a zuciyarta, shi kuma ya amsa mata ba dan suna ?a?an Iyami kaWai Sa sai dai baya daukar a zalinci kowa, amman saboda ta ji haushi sai ya amsa mata da haka.

 Eh saboda suna ?a?an Iyami...

Yana fadar hakan ya juya ya fice daga falon, a nan ma Yasir da har lokacin yana rike da Hamad dake ta jan numfashi da karfi saboda zuciya, ya rufa masa baya tare da Hamad din, Hurriya kuma da ta tuni kuka yayi mata bankwana ya tafi ya barta tsaye tana kallon dramar da ake ta bi Appa da kallo kamin ta juyo ta kalli Momy.

 Ba hakka, haka ne... Daman ance maza ke bude wata kofar wani lokacin yau na gani, kuma ya bude muku kofa, za ku wahala a gidan nan. Musib yi hakuri

Ta juya ta fara hawan stairs din daman bata sauko gaba daya. Musib ya watsawa Hurriya wani mugun kallo ya dauke ido ya bi bayan mahaifiyarsa. Zaunawa Hurriya ta yi a gurin ta rafka uban tagumi, gaba daya kwakwalwarta ta rike ce ji take kamar ba zata iya dauka ba.



*** *** ***

BAYAN WATA UKU....

Tun daga lokacin sai Hurriya da Hamad suka samu salama, ta duka Hamad kuma ya samu ta magana, ba a dukansa ba a fada masa magana marar dadi, saboda ana tsoron ya fadawa Appa, Musib da Miwan ma sai duk suka shafa musu lafiya, sai dai tsanar da Hajiya Kaltume take mata sai ya karu, har ta kai a gaban Hurriya Hajiya Kaltume take zagin Iyami sai dai ba zata yi a gaban Hamad ba, Hurriya tana jin zafin abun sosai sai dai bata taba fadawa kowa ba sai dai ta bar abun a zuciyarta. Hurriya na tsaye ita da Hamad suna wanke motar Yasir Hajiya Kaltume ta fito rike da jakarta Yasir din yana bayanta rike da makullin mota.

 A gaishe da ku, amman idan Appa ya gani karku ce ni na saka ku ku ce ku kuka saka kanku dan kar ya fara fada ya ce ban kai wankin mota ba na saka ku yi

 Hamad ya fada masa zamu wanke maka mota ai kamin mu fara, ya ce mu je mu yi Allah ya mana albarka

Hurriya ta amsa tana watsawa motar ruwa, domim wankin mota yana daga cikin abun da yake matukar burgeta, kuma ta taba yi sau daya a motar Appanta tun a lokacin da Amma take gidan. Hajiya Kaltume ta kallesu irin kallon nan na rasa ya zan yi da ku ta dauke kai ta nufi motar da za su shiga, tana nufar motar gabanta na kara tsananta faduwa har sai da taja ta tsaya.

 Yasir anya ba za mu fasa tafiyar nan ba? Gabana sai faduwa yake Wallahi tsoro nake ji ganin nake kamar wani abun zai sake faruwa

Yasir ya ce.

 Babu abun da zai faru Hajiya dan Allah ki kwantar da hankalinki, ki yi imani da Allah, kuma kin ga tun da abun nan ya faru baki sake fita ba, yau kusan wata uku kenan dole ki ji haka

Ta girgiza kai domin bata gamsu da kalaman Yasir ba.

 Ko dai mu hakura har wani lokacin?

 Hajiya idan baki kawar da komai a ranki ba, babu ranar da zaki sake fita, rasuwa nawa aka yi baki je ba, ga haihuwa ba an yi ba daya ba amman baki fita ba, Hajiya Fatee ma tare abun nan ya same ku amman zuwanta biyar gidan nan, dan Allah ki daina tsoro babu abun da zai faru da yardar Allah

 Toh Allah yasa

Ta amsa tare da bude motar ta shiga ba dan ranta ya so ba, sai dan fitar ta zame mata dole ne saboda kiran da Hajiya Fatee ta yi mata tana kuka ba zata fita ba, balle kuma da ya kasance gidanta na farko da zata fara zuwa tun bayan da aka yi kidnapping dinsu, sai take ganin kamar hakan zai sake faruwa ne. A hankali Yasir ya rika jan motar suna tafiya yana dan taba mata hira, ita kuma ta kasa cewa komai sai kallon gari take har lokacin tsoro be fice ta ba, garin kuma tana ganin kamar ya sake saboda dadewa da ta yi bata fita ba.

 Bismillahi

Ta furta yayin da ta bude motar zata fita, zuciyarta nata rawa, Yasir ya rakata har cikin falon Hajiya Fatee, yan aikin Hajiya Fatee suka fara gaisheta.

 Lafiya Kalau Ina Hajiya Fatee

 Tana dakinta

Hajiya Kaltume ta juya ta kalli Yasir.

 Bari na kirata ku gaisa

 Okay

Ya nufi kujera ya zauna, Hajiya Kaltume kuma ta nufi dakin Hajiya fatee ta tura kofar ta shiga da sallama. Kuka ya hana Hajiya Fatee amsawa sai dagowa da ta yi ta kalleta da idanuwanta da suka gama kumbura.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Hajiya Fatee abun har ya kai haka

 Ya wuce, Hajiya Kaltume ina cikin bala'i da tashin hankali

Hajiya Kaltume ta juya ta leka falon saitin da yasir yake zaune.

 Yasir ka tafi kawai idan zaka dawo daukata sai ku gaisa, amman fa da zarar na kiraka ka zo da sauri

 Toh Hajiya

Ya tashi ya fice cike da ladabi. Sannan Hajiya Kaltume ta koma dakin ta zauna kusa da kawarta da rabin kibar jikinta ta zube saboda tashin hankali.

 Wannan abu be yi dadi ba, yanzu miye abun yi?

Hajiya Fatee ta share hawayenta ta kalli aminiyarta.

 Ban sani ba Hajiya Kaltume, wannan shi ne likita na uku da ya fada min haka

 Hajiya Fatee duk laifinki, da tun farko kin yarda anje asibitin an duba lafiyarki da duk be kai ga haka ba?

 Haba Hajiya, ina zan yarda aje asibiti a fadawa ana abun da mutanen nan suka min? Tsoron kar ya kalleni da abin kuma kar bakinciki ya zauna masa a zuciya ya saka na ki amincewa da zuwa asibitin, kuma ni ma na san idan har ya sani ba zan samu salama ba

Hajiya Kaltume ta rafka tagumi.

 Wallahi duk wannan Iyamin ce ta ja mana, ba zan tana yafe mata ba, ni kaina yanzu sanadinta har tsoron fita nake

 Ni yanzu ba ta Iyami nake ba Hajiya ta kaina nake, kar asirina ya tonu, ga ni ta surukar da bata kaunata, ga makiyi babban tashin hankali kuma rashin auren nan, yau shekara goma da rasuwar Alhaji me zan fadawa duniya idan abun nan ya fito da shekaru na haka har da jikoki

Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya.

 Hajiya ko dai daurewa zamu akara yin allurar nan ne? Ko Allah zai saka abun ya zube

Hajiya Fatee ta dauki robar yawu ta tsargar da yawunta cikin ta aje ta kalli Hajiya Kaltume.

 Likita nan fa ya fada min, ta farko ma da na auna arziki ne, da yanzu na wuce, ni kadai na san azabar da na sha lokacin da aka min allurar nan kuma gashi bukata bata biya ba, kuma cirewar sun ce ko na mutu ko na yi rai ne

Hannu biyu Hajiya Kaltume ta dora saman kai ta fashe da kuka tana taya aminiyarta alhini.

 Kai wayyo Allah wannan Iyami wannan Iyami Allah ya isar mana gareki, kin aure min miji kin fitine ni yanzu kuma sanadin nan mun fada cikin bala'i, ni Wallahi ma rasa ya zan yi da matar nan da yaranta, kin ga cikinta ya shiga wata na tara kenan wani zata haifowa Alhaji, yayanta da suke gidan ma be hada kowa da su ba, birthday nan da Hurriya ta yi sarkar zinari ta miliyoyan kudi yayi mata kyauta, ni da nake matarsa be taba siya min ba, sarkar da Nafisa take ta kuri da ita yau Alhaji ya siya irinta ya mallakawa Hurriya, ga birthday Hamad tafe waya san iya abun da zai masa shi ma, kuma saboda ita yanzu ya budewa kofa kofar birthday, abun da da ya hana

Hajiya Fatee ta daki kirji.

 Sarka Hajiya? Lallai Iyami ba zata gama da duniya lafiya ba, ta mallake shi yanzu ta bar gida ta bar muku ya ku yi kishi da ita

 Hmm abun nan ya ishe ni, ai saboda na san kina cikin taki matsalar ne ya saka ban kawo miki kukana ba, amman ciwon matar nan yana nan a kirjina, a yanzu bana da burin da ya wuce na ga Alhaji ya fita lamarin yaran nan, kuma dukiyar da ya bata ta lalace

 Ba ke ba, ai ko ni ba zan iya yafewa Iyami ba Hajiya, sanadinta yara kanana sana'in yayana suka daure mu a daji babu kalar wulakancin da ba su min ba, yanzu kuma ga wani abun bakinciki ya sake biyo baya, ban san ya zan yi ba

Ta karashe zancen tare da fashewa da kuka.

 Toh ni dai ina ganin abun da ya kamata kawai mu saka a nemo mana malamin nan ko Allah zai saka mu dace

Hajiya Fatee ta mata wani kallo galala.

 Waya zai koma a wannan dajin? Ko gawata ba za a kai ba

 Aa ina fa? Ni ma ai ba zan yarda ba, ba komawa zamu yi ba nemansa zamu yi idan ya so shi sai ya zo ya same mu

 Ta ina? Duka wayoyin mu suka karbe fa, ba ni da number ba, kuma da aka yi welcome din Sim din har yanzu be kira ni ba, waya sani ma ko shi ya turo a dauke mu? Mutanen nan kauye nan fa ba su da kyau

 Kai bana tunani haka, kin ga ni fa na ga kyau aikinsa domin shi kadai ne yayi min aiki kuma aikin yayi yadda nake so har Iyami ta bar gidan nan, shekara nawa ina kashe kudi a banza ban dace ba sai a gunsa, sa zaki yi a nema mana shi waya nuna miki gurin Malamin

 Wata kawata ce Salame

 Toh ita zaki saka ta je ta dauko mana shi, sai mu saka gurin haduwa da shi ba dole sai ya san gidan mu ba, mu gabatar masa da bukatanmu mu basa kudin aiki, daga nan ma sai na tambaye shi ina aka kwana zancen aikin Iyami, ke kuma sai ki saka yayi miki na wannan mugun abun da yake cikinki

Kallon rashin fahimta Hajiya Fatee ta yi mata

 Ya danne miki shi mana, ba zai taba tashi ba har ki mutu, ko baki san ana haka ba? Na Iyami ma so nake a danne shi kar ta haifa ma Alhaji mugun abu, dan na san duk wayonta be wuce Alhaji ya mutu ta ci gado ba

Hajiya Fatee ta kalleta wata rahma na saukar mata a ruhi, jin kamar ta samu mafitar masifar da take ciki.

 Kuma kina ganin hakan zai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login