Showing 45001 words to 48000 words out of 279257 words

Chapter 16 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34631

biyar na ce a mallake min Alhaji ba, tsantsar biyayya ne kawai da kawar da kai da kuma jin maganar duk abun da ya fada, ni yanzu ko zaki dora wuka a wuyana ba zan iya fada miki sunan Malami daya da na sani ba a garin nan, ban taba yi ba, Gwaggo ma bata taba ta yi ba mu ba mu da kowa sai Allah

 Na sani, to ai tambaya ake kin ga har na tsarin jikinki sai ki sha kuma ki bawa yayanki, domin su ma ba barinsu zata yi ba

 Ni dai ba zan iya ba, na kai kukana ga Allah shi zai min magana, ko yanzu ai ba yadda suke so suka samu ba, duk wata sai ya aiko min da abinci da kudi saboda cikin nan, yanzu kuma kina ganin yadda aka cika harabar gidan nan da itace saboda na shiga watan haihuwar, na san idan ra'ayinsu za a bi ba zasu so haka ba, yarana kuma idan ya auna lokaci ya kan aiko da su su gan ni na gansu, an rabu ne kawai amman kamar ana tare, idan Allah yayi zan koma sai ki ga na koma kamar yadda ban saka ran auren Alhaji ba Allah yayi kuma aka yi auren

 Toh Allah yasa haka shi ya fi alheri, amman dai da kin tafi ba a san inda za a dace ba

 Allah ya hada mu da dacewar

 Ameen

Ta amsa ba dan ta jidadin yadda Iyami ta ki amincewa da zuwan ba.
[10/20, 6:26 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: &A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?

Pease ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy


5???5???5???5??? 1?? 5??

Salame na turo number Malamin Hajiya Fatee ta kira shi a waya, suka gaisa ta fada masa abubuwan da suka faru ya jajanta mata, ya kara mata da cewar shi ma layinsa aka rufe shiyasa bata ji shi ba. Hajiya Kaltume ya karba suka gaisa sannan ta dora masa da banin abun da ya sami Hajiya Fatee, daga karshe suka yanke ranar da zai shigo garin. Sannan Hajiya Fatee ta iya fita dakinta ta samu ruwan tea ta sha domin bata iya cin komai. Hajiya Katume bata jima a gidan ba Fadeel ya shigo gaishe da mahaifiyar, da zai fita Hajiya Kaltume ta bukaci ya sauke ta gida.



*** *** ***

Ba kadan ran Momy ya ba ce ba, jin cewar Captain ya zo gidan tana bachi, kuma ya fita da bacin rai saboda Hurriya.

 Oh to wai miye na siya mata gilashin ma?

Namra ta aje spoon din hannunta.

 To nidai ranar da ya zo last na ganta da shi cirko cirko, gilashinta a kasa tana lalabe to shi ne yau take fada min ai marinta yayi saboda sun yi karo

 Ai gara da mareta ma, yarinyar nan bata da hankali, sannan yanzu ya zo ta ki ta karbi box din wata kila ba zai sake dawowa gidan nan ba kuma, ta ja min ya fara fushi da ni kenan

 Shi ma fa Captain din nan ya cika zuciya ga zafin hannu, amman dai bata kyauta ba da bata karba ba

 Bar yar iska bata san su waye iyayensa ba ne shiyasa, shi ma dai miye na kawo mata glass ko makancewa ta yi iya ruwansa

 Kila ya ga be kyauta ba, ko kuma...

Momy ta kalleta da duba kyama.

 Ko kuma me? Allah ya kiyaye ai ko mata sun kare duniya Captain ba zai yi komai da wannan yar tatsitsiyar yarinyar na duka ma nawa take shekaranjiya ta yi 16yrs fa, kuma shi da yake da matar da zai aura

 Toh ba sai idan anyi auren ba, wannan me bakar zuciyar? Ba kowa ce zata iya zama da shi ba

 Ai ko fasawa aka yi sai dai ya aureki, daman Hajiya Turai ta so a hada wannan zumunci shi din ne ya ki, kuma kin san basa masa dole 

 Ni

Namra ta nuna kanta domin bata taba jin makamacin haka daga bakin Momy ba.

 Ke fa mun sha yin maganar da Hajiya Turai ai, amman shi Jameel din ne be yarda ba, yanzu dai ya samu wadda yake so an huta

Namra bata ce komai ba ta maida idonta kan abincin da take ci tana motsa shi a hankali kamar mai tunani. Momy kuma ta tashi daga dinning din tana ta masifa saboda Namra bata tasheta daga bacci ba.

 Kiransa zan yi yanzu Allah yasa ya daga, kar wannan yar filfilwar ta jazamin masifa ni Nafisa

Nan ma Namra bata ce komai b ta cigaba da motsa abinci tana tauna wanda yake bakinta ta kasa hadewa sai tunani take. Kamin ta juyo ta kalli falon da aka bude, Hurriya ce ta shigo kanta ba dankwali rabin kan nata a tsire.

 Yi sauri ki dauki abun da zaki dauka ki fice kamin Momy ta fito, dan na san sai ta miki fadan kin karbar box din da Captain ya baki

 Abinci zan zuba

Ta nuna abinci tana kallon stairs gabanta sai tsananta faduwa yake.

 Zo ki zuba

Ta nufi dinning din da sauri ta dauki plate ta zuba abincin mutum biyu ita da Hamad ta saka naman kaza a sama ta dauki spoon biyu ta saka.

 Ke da Hamad zaku ci?

 Eh

 Dazun shi ya hana ki karbar glass din ko?

 Na ga ya bata rai yana hararata, na san idan na karna zai iya min masifa kuma yayi fada ni, ko ya dukeni

 Ke dai Hamad ya raina ki ya maida ke kamar kanwarsa, ko dan ya ganshi babba ke kuma ba ki ba

Hurriya ta yi dariya mai sauti ta shiga Kitchen ta dauko tray ta dora ruwa da lemu a kai sannan ta fito ta dauki plate din abincin ta dora a tray ta dauka ta fice da sauri. A harabar Apartment din Hajiya Kaltume ta dawo ta zauna a balcony kusa da Hamad ta aje tray.

 Hamad zo mu ci abinci

Ya kalli abinci sai ya bata rai.

 Waya ce ki hade? Waye zai ci abinci da ke to?

 To ai ni ina sauri ne, Yaya Namra ta ce Momy nemana take zata min fada saboda ban karbi abun da bakonta ya ba ni ba

 Toh ina ruwana ki je ki zuba wani

Ya saka hannu ya dauke abincin da ba zai iya cinyewa shi kadai ba ta dora a cinyarsa.

 Idan ba zaka ci da ni ba, ba sai ka je ka debo na ka ba?

 Ba zan ce ba, ni ki daina ba ni umarni

 Wannan dai nawa ne ka ba ni abinci na Hamad

Yayi mata kunne ne shege yana ta cin abinci ko kallonta be yi ba. Har ta tashi zata tafi debar wani sai kuma wata zuciyar tace mata Momy na nan falo, sai ta koma ta zauna ta dauki lemun ta sha tana ta kallonsa yana cin abinci. Ita ma dai kamar mantawa ta yi Hamad be cin abinci da kowa kuma be cin ragin kowa har da na Appansa da na Amma. Hakura ta yi ta saka masa ido ta can kuma ta ji ba zata iya ba tunawa da ta yi baya son gashi idan yana cin abinci sai ta cigaba da sifar kan tana kallonsa wai ko zai ji kyama ya aje abinci. Instead of yayi haka sai ya kifar da plate din ya riko gashin kan nata a daidai lokacin da Mota ta faka harabar Hajiya Kaltume. Da wani irin karfi yake fisgar gashi da karfi bata san lokacin da ta fara ihu tana rike hannunsa ba. Da sauri Fadeel ya bude motar be ko tsaya kashewa ba ya fito ya nufi inda suke daker ya banbanre hannun Hamad Hurriya ta koma bayansa da sauri tana kuka.

 Kai wannan ai sai ka tsinke mata gashin ka rage mata sadaki, miya hada ku?

Hurriya bata iya magana saboda kuka, Hamad kuma ba gwanin maida magana ba ne daman sai cika yake kamar wani zaki. Hajiya Kaltume tana kawowa kusa da su ta ce

 Ai haka suke, uwa daya uba daya amman baya raga mata, basa zaman lafiya kamar Annabi da Kahiri suke

Cikin mamaki Fadeel ya kalli Hamad.

 Wai kanwarsa ce yake mata wannan jan gashi haka?

 Ita ce yayar ai, dan ka ganshi da girma shi ne kanen ai, baya ragawa kowa a gidan

Hamad ya juyo yana watsawa hara Hajiya Kaltume dake korawa Fadeel bayani saboda ta tabo shi tun da ta ce be ragama kowa.

 Idan ba kai ba, wake fada da mata? Ba yayarka ba ce?

Ya juyo ya kalli Hurriya da ta boya bayansa.

 Ke kuma ki rika kiyaye, yi hakuri ki daina zama babu dankwali ba kyau

 Ai Allah yasa ma aljannu da ifiritai da shaidan duk su tattara su shige a cikin kan nata, ita ma ai ba karamar marar jin magana ba ce

Hurriya ta kalli Hajiya Kaltume dake fadar haka tare da yin gaba da bar su a gurin. Ta share hawayenta ta kalli Hamad sannan ta kalli Fadeel.

 Ina wuni

Dariya yayi.

 Lafiya Kalau, Allah ya tsare gaba Hurera ko?

 Hurriya

Ta gyara masa.

 Yeah ki rufe kanki

 Toh

Ya juya ta sauka balcony din ya nufi motarsa dake kunne har lokacin sai da ya shiga motar daga mata hannu sai kallonta yake sannan yayi reverse ya fice.


Two Week Later....

Hajiya Fatee ta gyara zama ta kalli kawarta kamin ta kalli Malamin da suka sauka a garage din gidan.

 To yanzu Malam akwai yadda za'ayi a danne cikin nan kar ya bayyana? Kuma wannan tofe tofen yawun da kin cin abinci da nake ga kasala duk na daina shi?

Malamin dake sanye da babbar riga ya kalli Hajiya Fatee yana murmushi.

 Za'a iya sosai kowa, ba yau na saba ba, za a iya danne cikin nan har tsawon shekarun da kike so

 Alhamdulillah, ina son a danne min shi har nan da shekara dari, na san dai ba zan yi shekara dari a duniya ba

 Ko kuma nan da lokacin da zaki yi aure ba, Hajiya yadda kike da surar nan Maa Shaa Allah, ai sai idan mutum be samu dama ba, shekarunki ba ba za a ce kin yi ba, ai na san ba za a rasa namema ba ko?

Maganar yake yana dariya kamar wata abokiyar wasarsa.

 Aa kai aure kuma? Wake ta aure yanzu? Aa mun bar wa yara, ni dai yanzu bukatata a fara danne cikinki, idan an samu nasara hakan yayi sai a shiga yi Farraqu tsakanin yaron nan Fadeel da Matarsa Afrah domin ina kwana da bakincikinta a kullum Wallahi

. Babu Matsala Hajiya, za a danne ciki, matukar ba a daga dutsen da zamu saka layar mu rufe ba, cikin nan ba zai taba tashi ba har abada, amman fa zaki zuba kudi kam

 Karka damu zan biya ka ko nawa ne, ammam dan Allah a saka dutsen a inda ba za a iya dagawa ba

 Aljannu za mu saka su yi aikin, karki damu

Hajiya Fatee ta kalli Kaltume suka yi murmushin jindadi sannan Hajiya Kaltume ta kora da nata bayanin.

 To ni Malam na ji shiru, kasan na baka kudi akan za ayi ma Iyami aiki ina son komai nata ya lalace amman har yanzu ba labari, kuma ni yanzu so nake a mallake min kowa a gidan nan daga mijina har Nafisa ikon kowa ya dawo karkashina, ina son Alhaji ya zama be iya aiwatar da komai sai abun da na fada masa, kuma ina son a shiga tsakaninsa da yaran nan, ya maida su banza a cire masa su a rai, ya ji baya bukatar ganinsu ma, domin na ji yana zancen fitar da su waje karatu, kuma ko be fitar da su ba, ita wannan da take da kokari na san gwanati ko wasu za su iya kaita waje karatu, so nake a lalata karatun nata, kai ni duk wani abu da zai saka Iyami farinciki bana sonshi a toshe komai Malam

 Hajiya, aiki ai mun aiwatar jefa muka mata kuma yana nan yana tafiya kin san jifa wani lokacin tana dauka lokaci kamin ta isa, amman kuma da zarar ta isa zaki sha mamaki ba dan karami ba, sai kin tabbatar da ba ki min biyan banza ba, mijinki kuma zaki mallake shi a hannu, sai dai wannan Nafisa kishiyar taki fitinanniyar mace ce akwai yan ?wan?wanmai a kanta, kin san mai yawan masifa da mai addu'a asiri be cika saurin kama su ba, amman zamu gwada

 A gwada Malam zan biya ko nawa ne karka ji haufi

Malam ya san washe baki.  To Mallada ai mu haka muke so

Hajiya Fatee ta ce.

 Toh ni Malam ya za'ayi na gane idan cikin ya dannu?

 Idan na yi aiki, zaki ji motsi sosai a cikinki idan motsin be daina ba har safe, to cikin ne dannu ba wata kila sai mun sake yi, idan kuma kin ji motsin kadan to aiki yayi kuma zaki daina duk wasu dabi'u da kike na masu ciki, cikin kwana biyu

 Alhamdulillah, ni da zaka cire cikin ma ni ka dauki cikin na bar maka, ko ina da aure me zan yi da mugun iri? Balle kuma an kwana biyu har na kai ga jikoki

 Komai zai wuce Hajiya karki samu damuwa

A ranar da farinciki Hajiya Kaltume ta dawo gida, saboda ta samu fadawa bokanta abun da take so kuma ya tabbatar mata da zai iya. Wani karin abun farincikin ma sai da babbar yarta Mace mai bin Yasir wato Umm Kaltoon da ake ma inkiya da Maamata saboda sunan Hajiya Kaltume mata albishir da mai cewar mai son ta zai zo ya gaishe da Hajiya da Appanta sai Hajiya ta rasa ina zata saka kanta dan dadi, daga ita har Hajiya Fatee sun kwana da farinciki a daren kowa da bukatarsa da kuma burinsa, Hajiya Fatee bata da burin da ya wuce a danne cikin nan kuma a raba Fadeel da matarsa Afrah saboda ta tsokane mata ido.



Washe gari...

A tare da Hamad Hurriya ta fito bangaren Momy da far'arta tana hira da Hamad, kai ka rantse ba sa fada da juna labari take ba shi na wata class mate dinta da ya sani sai dariya yake. Sai da suka fara zuwa gurin Appa suka karbi na na su lemun da Chocolate Hurriya ta masa godiya, sannan suka nufi box din dake kai su makaranta suka shiga. A makarantar ma sai suka wuni kamar ba su ba, daman tare suke breakfast amman kowa da abincinsa dabam, a ranar duk abun da Hamad ya siya sai ya iskota har cikin ajinsu ya bata, kasancewar ajin maza dabam na mata dabam. Misalin karfe daya da rabi suka tashi suka tafi Masallaci suka yi sallah sannan suka tsaya jiran direbansu dake zuwa karfe biyu daukarsu gaba dayansu yan gidan. Biyu da mintuna ya iso suka shiga box Hurriya tana can baya Hamad kuma yana a inda ya saba zama, wato front seat babu mai zama a gurin sai shi kuma baya zama da kowa sai shi kadai. Kilometers kadan ne tsakaninsu da Family house dinsu wata bakar motar ta shiga gabansu ta tara musu har sai da direbansu ya tsaya gashi gurin babu mota ni motoci ma ba kasafai fa, shi ma direban yana biyo hanyar ne saboda ta fi saurin kawo su gida.

 Malam baka gani ne?

Ya fada cikin tsawa ganin yadda yake masa ganganci kamar ba akan titi suke ba. Bude motar aka yi wasu maza hudu suka fito fuskarsu a rufe biyu daga cikinsu na rike da bindiga suka bude ma direban da tuni ya fara salati ya fito Hamad ma ya bude ya fito jikinsa na rawa suka sa ya zagayo gurin direban sannan suka bude gambun bus din.

 Kowa ya fito

Kowa ya fito cikinsu na rawa suna ihu.

 Ku yi shiru ko na halbe mutum yanzu

Dayan ya fada sannan biyun da ba sa rike da makami suka iso gurin dayan ya rika Hurriya dayan kuma ya rika Ruma suka fara jansu zuwa motar. Hamad ya fashe da kuka sosai yayi saurin riko Hijabin Hurriya da ita ma kukan take, kamin ta kai bakinta ta gantsawa wanda ya rike mugun cizo a hannu, aiko ba shiri ya sake ta sai ta ranta ana kare, abun ka da marar jiki kamin dayan ya rikota ta yi nisa, sai yayi wuf ya cafke Hamad dake kokarin guduwa, suka dauke shi tare da Ruma sai motarsu. Suka shiga da sauri suka fisgi motar sannan Salma da Khairi suka fara ihu tare da Namra suna kuka, Hurriya kam tun da ta sa gaba bata dawo ba sai da direban ya wasu mutane da suka tsaya bayan bata garin sun gudu suka bi sawunta, sai suka same ta tsakanin wani gida da kwararo ta duke a gurin ta runtse idon ta saka hannayensa ta danne kunnuwanta.

 Hurriya

Ta razana ta bude ido jikinta da zuciyarta na rawa, gilashinta ya fadi gurin gudun da dake, shiga kwararon ma da ganinta dishe-dishe ta shiga lalabe ya taimka mata, shi ne silar tsayarwa a gurin ma, domin da tana ganin hanya da kyau ba zata kusa ba guduwa zata yi. Jin muryar direbansu ne ya saka ta fashe da kuka, tana lalabensa shi ya rikota yana matsar kwalla suka fito gurin. Kin yarda ta yi su koma gurin saboda tsoro sai da direban ya janyo motar ya kawo gurin sannan ta yarda zata shiga.

 Ina Hamad?

Ta tambaya yana taimaka mata ta hau bus din har lokacin kowa kuka yake, ita kuwa bata ji kukan dan'uwanta ba kuma bata ji muryarsa ba.

 Sun tafi da shi

A take ta saki hannun direban ta yi shiruuuuu kamin ta fara haki.

 Wayyo Allah

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login