Showing 162001 words to 165000 words out of 279257 words

Chapter 55 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34681

nan ta kama Namra da kokawa

Ya saketa ya mike tsaye ransa a bace.

 That's mean wani abun aka yi da ya kufular da yarinyar nan, idan ba haka ba babu yadda za'ayi ta kama ????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
Namra da kokawa, yarinyar da ko yatsa aka saka mata a baki ba zata ciza ba, ban san me ya faru ba amman zan iya shaidar ita ke da gaskiya

 Captain baka san me ya faru ba, be kamata... 

Tasss ya wanke fuskar Namra da mari tun kamin ta karasa furucinta. Ya nunata da yatsa wani abu na fisgeshi yana kokarin ninka masa bacin ransa.

 Idan kika sake kai hannunki a jikin yarinyar nan....!

Sai kuma yayi shiru be karasa ba sai wani mugun kallo yake watsa mata. Namra ta rike fuska daga ita har Momy mamaki ya hana su sake cewa komai. Ya juya ta nufi gurin da gilashin Hurriya yake ya dauka ya kama hannunta da take lalabe da shi ya danka mata gilashin. Sai ta karba ta saka ta kalleshi.

 Na gode, na gode da ka zo...

Ta furta wasu hawayen na sauko mata, ta san ba dan ya zo in time ba wata kila da yanzu an yi gawa ta biyu a gidan.

 Me ya faru?

A madadin ta yi magana sai kawai ta fashe da kuka, daman haka take ko a can da idan suka yi fada da Hamad bata iya maida magana saboda kuka, Hurriya irin yaran nan ne da idan aka yi fada basa iya bitar abun da ya faru ko da kuwa su suke da gaskiya saboda kuka. Tausayinta sai ya kara kama shi, daman zuciyarsa ta raya masa tana nan bata ci abincin dare ba, wata kila ma har da rana domin ya lura da yanayinta a dazun shiyasa har ya dawo gidan da dare, ashe da rabon ya tararda wannan fadan ne. Namra ta lumshe ido sai a lokacin kuka ya zo mata, Momy ta kama hannunta suka nufi stairs tana kuka, Momy kuma rai bace an taba mata yar gudaliya gashi babu halin ta yi magana saboda Captain ne, ta san idan ta yi magana zai iya cewa saboda ba ita ta haife shi ba shiyasa ta yi magana dan yi mari Namra, wata kila ma yayi fushi, kuma idan abu yayi zurfi ba zai tsaya iya tsakaninsu ba.
Hurriya ta mike tsaye ta share hawayenta, ta kama hannun kanenta.

 Su waye wadanan?

 Kanena ne

Ta amsa tana jansu, shi ma dai ya tambaya ne saboda confirmation amman ya ga kamanin a fuskarsu ai. Hurriya ta haura sama da yaran ta shiga dakinta ta saka Hijab dinta ta sauko tare da su, a lokacin Captain na zaune a sofa yana kallonta har ta sauko tare da su.

 Ina zaki je?

 Gida zan kai su

 Cikin dare?

 Daman Gwaggo bata so su kwana a nan ba, ni ce na takura su kwana a nan, kuma gashi yanzu saboda su ana yin fitina

 Je dakinki ki kwanta

Ya bata umarni kai tsaye.

 Daman Amma bata son...

Bata karasa ba ya daka mata tsawa.

 I thought na fada miki bana maimaita magana

Ta juya da sauri jikinta na rawa ta nufi stairs, daman tsoronsa take balle yanzu da ya mari Namra a gabanta. Twins na ganin ta nufi stairs suka fashe da kuka suka bi bayanta, Captain ya kallesu.

 Dawo ki zauna a nan

Kamar umarni take jira ta juyo da sauri ta dawo ta zauna sai suka nufeta suna zauna suma kusa da ita suna kuka.

 Ki rarrashe su mana, ki zubo abinci ku ci

Ta mike tsaye ta nufi dinning tana waigensa, daman dai bata isa tace masa Momy ta hana ta taba abinci idan bata ci ba, kar yayi mata fada, babba plate ta dauka ta zuba abincin ta dawo tsakiyar falon, ta koma ga dauko ruwa sannan ta zauna ita da kanenta suka fara cin abincin kamar wasu marayu. Hamid sai kallon Captain yake abun da Hurriya ta kasa yi gaba daya tsoronsa ya cika mata zuciya, hantar cikinta sai kadawa take.

 Wuta....

Little Hamad ya fada yana nuna kitchen din. Gaba dayansu suka dago suka kalli kofar kitchen dake cikin da hayaki, Captain ya mike tsaye da sauri ya nufi kitchen din, hankalin Hurriya ma ya tashi ita ma ta bi bayansa kamin su karasa suka ji ihun Namra, Hurriya ta yi zaton wutar kitchen din ce ta fito da ita daga dakinta har take ihu.

 Kunamu a dakina sun cijeni akan gadona suka har uku wayyo Allah na....

Sai suka ji wani abun na dabam, sai kuka take tana sosa bayan rigarta kamar zata fita daga hayyacin, har wani tsalle take tana saukowa kai kace ma fadowa zata yi a stairs din. Captain ya kalli Twins din dake ta cin abincinsu, dayan yana kallon Captain dayan kuma yana kallon Namra dake mirgina a stairs tana kiran Momy.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?


32

Ya dauke idonsa daga barin kallon yaran ya kalli Hurriya dake tsaye a rikice.

 Hurriya zauna ki rarrashi yaran nan

 Ba kuka suke yi ba

Ya watsa mata wani kallo irin na karki bari na maimaita kaina. Ta koma ta zauna ta dafa su.

 Ku yi shiru ku yi hakuri ku yi shiru

Tana yi tana kallonsa a ranta tana mamakin hikimarsa ta yin haka bayan yaran ba kuka suke ba cin abincin suke yi. Shi kuma ya nufi kitchen din gaba daya hayaki ya cika ko'ina, gurin da wutar take ya nufa electric kettle din Momy ce ta kama da wuta, haka ya lalaba ya kai hannunsa ya taba socket din da niyar kashewa sai ya ji a kashe, hakan yana nufin wutar ma a kashe take amman a haka sai da ya kama da wuta. Abubuwa yayi ta budewa har ya samo mociya ya dauko ya bugawa kettle din ta zubo da ita kasa amman wutar bata daina ci a jikin butar ba. Tab ya kunna ya rika watsa ruwa a banza, da gudu ya fito daga kitchen din yana tare.

 Baka yi komai ba, Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, bari a kira fire service

Momy ta fada hankalinta a tashe.

 Baku da fire-extinguisher a nan ne?

 Akwai yana nan ta baya

Momy ta wuce gaba da gudu kai kace ta kwashe kibar ne ta watsar, ta nuna masa gurin ya dauko ya dawo kitchen din ya fesa, amman wutar taki mutuwa, sai ya sake fita ya samo bargo ya jika shi da ruwa ya lulluba saman wutar, tana mutuwa wata ta kama jikim gas a nan fa hankalin Captain ya tashi ya san gas ba shi da wasa. Ya fito da sauri daga kitchen already Momy ta yi waya a kawo fire service, masu aikin Momy da duk sun shigo falon suna kallon wutar har da masu aikim gida, wasu suka fara zuba ruwa a gas.

 Nono ku daina zuba ruwa, wacan ma dan na sauke ta kasa ne ya sa na zuba ruwa

Ya hana masu zuba ruwan sannan ya kalli Hurriya.

 Ya sunan wannan?

 Little Hamad

Ya kama hannunsa.

 Zo muje mu kashe wuta

Hurriya na jin haka ta yi hanzarin riko kanenta tana shi bayanta.

 Karamin yaro ba zai iya kashe wuta ba

 Zan mareki Hurriya, idan ba su suka kashe wutar nan ba ba zata mutu ba, saboda an bata musu rai ne duk silar abun

Ya nufeta yana matsawa baya ya riko Little Hamad din ya dagashi sama yana masa wasa domin ya san ba zai iya sakawa su yi da karfi ba. Ya nufi kitchen da shi daga bakin kofar ya tsaya ya bashi fire-extinguisher din suka rika su biyu suka hura iskar zuwa inda wutar take amman bata mutu ba, ya dawo da shi ya dauki Hamid yayi masa kwatankwacin yadda yayi ma Little Hamad, sai a ga wutar ta mutu a take kamar an taketa. Captain yayi murmushi mai sauti ya sumbance shi a kumatu.

 That's my boy

Ya aje abun ya juyo ya fito da shi falon yana dagashi sama ya jefa ya cha, yaron sai dariya yake sosai, dayan ma ya zo da gudu ayi masa daman ko a gidan Amma haka suke idan aka yi daya abu sai an yi ma daya, idan ba haka ba babu zaman lafiya, ga su so friendly da kowa basa bakunta kuma basa fasa kiriniya a ko'ina.

 Wutar ta mutu kuwa ikon Allah

Momy ta fada tana leka Kitchen din, bayan Captain ya aje su ya dubi Momy.

 Ba dole ba, wannan shi ne me wutar wacan kuma ina jin shi ne mai kunamar, ko kuma duka Hamid din ne

 To akan me? Ina mafari ina dalili? Daga zuwa bakunta sai su haddasawa mutane gobara da kunamu? Na ga kunama ni ma daya a dakina ta shige under bed na fito na fada kenan na zo na tararda wuta

Captain yayi saurin girgiza mata kai.

 Momy karki ja su kara yin abun da ya fi wannan, ba a bata musu rai, ina tunanin ko dai kin musu fada ko kuma taba Hurriya da kuka yi ne ransu ya bace, Ke ma idan kina son zaman lafiya ki ba su hakuri

Ya karasa yana magana da Namra da ke zaune a kasa tana rusar kuka har lokacin tana lalaba bayanta, gaba daya ta cire zip din rigar amman zabin da take ji sai take jin kamar kunamar tana nan bayanta, tun da ta zo duniya kunama bata taba cizonta ba, sai yau.

 Ya zan yi na ba su hakuri ya ake bada hakuri, dan Allah ku yi hakuri ku yafe min...

Tana kuka tana rokonsa har da hade hannayenta guri daya. Hurriya bata san lokacin da dariya ta subuce mata ba sai ta yi saurin rufe bakinta ta juya baya. Kowa sai da ya kalleta Momy ta yi kamar ta yi mata fada saboda ta yi dariyar Namra, sai kuma ta tuna ta kalli twins din ta shanye maganarta. Captain ya sauke kansa kasa a hankali yana murmushi dariyarta is something else da ya daukeshi ya jefa shi wata duniyar ta nishadi, sautin giggles laugh dinta na ta maimaita kansa a kunnunsa.

 Shatu shiga ki dauko mata hijab dinta mu tafi asibiti

Momy ta fada cikin bacin rai, ba dan tana gudun ran yaran ya kara baci wata Matsalar ta sake afkuwa ba da sai ta yi ma yaran duka kuma ta ci uban Hurriya saboda dariyar da ta yi. Tare da Shatu suka haura sama ita ta shiga dakinta ta dauko keys din mota Shatu kuma ta dauko Hijab din Namra, Momy ta sauka Shatu ta saka ma Namra Hijab din ta rikata ta mike tsaye tana kuka. Momy ta yi zaton Captain zai ce ya kai Namra Asibitin amman be yi wani unkurin ba har direbanta ya shigo ya karbi keys din suka fice. Inna Kulu da Shatu ma suka fice daga falon, aka bar Hurriya daga ita sai kanenta da Captain. Sai a lokacin Hurriya ta samu natsuwar kwashe abincin da twins suka zubar ta zuba a plate ta dauke komai ta nufi kitchen tana aje plate din ta kunna tap ta wanke hannunta, sai ta ji magana a bayanta.

 Kin iya dariyar keta ko?

Me zata yi idan ba dariyar ba, ta sake kyalkyalewa da dariya irin dariyar nan da baka iya controlling, idan ta tuna yadda Namra ta yi a dazun sai ta kasa rike kanta, ta juyo tana fadar

 I wish ni ma twins ce da an bata min rai... 

Ta kasa karasa a yayinda ta kalli fuskarsa, tunawa da shi din ba abokin hirarta ba ne kuma ba yayanta ba, hasalima bata da wata alaka da shi, sai dai kuma murmushin da ta yi arba da shi a fuskarsa ya saka ta dan ji sakewa fiye da yadda take ji idan ta kalleshi a baya.

 I'm your twinned, duk wanda ya taba ki, will see my reaction Immediately, trust me Hurriya i hear the whole story, i know the pain behind this precious smile of yours

Magana yake daga zuciyarsa zuwa ga Hurriya dake tsaye gabansa yayin da yake rike da murfin fridge.

 Zaki iya haihuwar twins ai, yawanci gadonsu ake, idan kika yi aure zaki iya haifawa mijinki twins ko Tripple, i love twins too

Ta kara fadada light smile dake fuskarsa kamin ta sauke kanta kasa ta fice daga kitchen din, ba tare da ta sake cewa komai ba. Ya dan daga girarsa kadan ya kai hannunsa ya dauko lemun kwalba ya bude sannan ya rufe fridge din, ya dawo bakin kofar kitchen din ya tsaya shi baya cikin falon shi baya cikin kitchen din ya jingina yana kallon Hurriya dake haurawa stairs tare da twins dinta gwanin sha'awa. Sai da ta haye gaba daya sannan ta juyo ta kalli kofar kitchen din, daman jikinta ya raya mata akwai idon wani a akanta, lemun dake hannunsa ya daga mata yana murmushi, ita ma ta yi murmushi kadan sannan ta dauke kai ta karasa saman ta isa bakin kofar dakinta, ta nan kam baya iya hangota ita ma bata iya ganin wanda ke falon. Dakinta ta tura sai da yaran suka shiga sannan ta shiga ta rufe kofar, kan gadonta dayan ya fada, dayan kuma ya nufi gurin da madubinta yake ya fara yi mata tabe tabe.

 Hamid bari mana, zo ga chocolate

Ta dauko ragowar chocolate dinta ta mikawa musu. Ko da su Momy suka dawo Captain ya bar gidan, a daren Namra bata yarda ta kwana dakinta ba dakin Momy ta kwana saboda tsoro, washe gari da safe Momy ta kira masu kula da fulawa suka bincike dakin na Namra babu kunama babu alamarta, dakin Momy ma da aka daga gadon ba a ga komai ba.

Misalin karfe goma sha biyu na rana Maryam da wata yar'uwarta suka sauka airport din sokoto, Appa ya aika da mota a sirrance aka daukosu tun daga sokoto har garin Gusau, bata samu isowa gidan sai karfe biyu da rabi, saboda yanayin tafiya. Ko da ta shigo gidan yana cike da mutane kamar jiya, masu zuwa gaisuwa da gaske da kuma masu zuwa cin abinci, ta fito motar tana sanye da mask sai doguwar rigar Abaya da ta rufe jikinta kovina ruf. Cousin dinta ta ma ta fito motar kowacensu tana rike da jaka, suka shiga bangaren na Hajiya Kaltume, tun a waje suka gaisawa da mutane suna musu ya hakuri har suka shiga can ciki gurin Hajiya Kaltume dake kwance a kan gado zazzabin na dawainiya da ita. Sosai Maryam ta yaba halin kawarta na kirki tana kukan rashinta, ita kanta mutuwar ta taba ba kuma ta zo mata bagatatan a lokacin da ba ta yi tsammani ba, na ita kadai ba mutuwar Salma ta bawa kowa mamaki, ko da yake ba a mamakin ikon Allah, sai dai jin cewar tana lafiya kalau gashi bata dade da gama karatu ba, ya saka kowa tausaya mata. Bayan Maryam ta yi gaisuwa sai kuma ta yi kuskuren gabatar da kanta a gurin Hajiya Kaltume saboda ta san wacece ita, ba dan tana son auren mijinta ba sai dan abotar dake tsakaninsu da Salma.

Hajiya Kaltume dake kwance ta tashi zaune ta gyara hijabinta tana kallon fuskar Maryam.

  Daman ke ce yarinyar? 

Maryam ta dago ta kalleta, ba ta yi zaton Appa ya fada ma Hajiya komai a game da maganar aurensu ba, domin shi da kansa ya bukaci su bar maganar a sirrance har sai idan an daura aure sannan kowa ya ji, ta dayan bangaren kuma bata zaton Salma zata boyewa mahaifiyarta wacece ita saboda ta gargade tun a ranar da suka yi bankwana a airport.

 Ke ce yarinyar da kika haddasa mata bakinciki?

Maryam ta maida kanta kansa tana jin kunya na rufeta. Hajiya Kaltume ta fashe da kuka tana jin kamar da wuka a kusa da cakawa Maryam ta kasheta.

 Ke ce fitsarriyar yarinyar da kika hakikance sai kin auri ubanta? Duk saboda ku yata ta mutu, ke da Iyami ba za ku gama da duniya lafiya ba, Allah ya tsine muku albarka

Maryam ta san wacece Iyami domin tana labarin yadda gidan Appa yake ciki da waje, ba ta gurinsa ta ji ba ta gurin bincikar yadda rayuwar gidansa take ta ji.

 Shi ne saboda baki da kunya kika dauko kafa kika zo yin murna ko?

Maryam ta dago da sauri.

 Subhanallahi wake murnar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login