Showing 66001 words to 69000 words out of 279257 words

Chapter 23 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34625

sha'awar uwarku ta dawo ta rike yayanta

Tana fadan tana hawa sama har ta haye ta shige dakinta, Mai aikinta kam tuni ta san inda dare yayi mata. Hurriya ta bi ta kallo har ta haye stairs din, ji ta yi kamar ace wani na nan ta fada jikinsa ya rumgume ta yi kuka ammab babu wannan damar, saukowa ta yi daga saman kujera ta zauna kasa sai ta dora kanta sama kujera ta takure guri daya. Ta rufe ido hawaye na sauko mata. After like 30min ta ji an zungureta sai ta farka da sauri gilashin idonta ya fadi da sauri ta dauka ta saka ta gyara mayafin abayarta ta kalli Musib dake tsaye kanta.

 Miye na yi ma mutane bachi a kujera kin wani takure salon wani ya shigo ace ke ce marar gata a gidan ke ga munafuka, wato kin dawo babu zaman lafiya, mun rabu da Hamad ke kuma zaki kirkiri mugun abu ko?

Kamar wani mace haka yake fada da ita yana gautsina fuska, gently ta mike tsaye domin ita ma bata san bacci ya dauke ta sai da ya tasheta. Tafiya ta fara yi ta haye sama ta dade a tsaye tana kallon kofar dakin Hamad tana jin kamar idan ta tura zata ganshi kwance ya ba kofar baya kamar yadda ya saba kwanciya. Wani hawayen ya sake cika idonta wani abu mai kama da dutse ya tsaya mata a tsakiyar zuciya ya mata nauyi. Cikin karfin hali ta kai hannu ta tura kofar dakinta ta shiga sai da maida kofar ta rufe ta jingina jikin kofar ta rumgume hannayenta not knowing what to do ita dai ba kuka take ji ba a yanzu, hawaye ne kawai ke mata zuba, tunanin dake mabanbantan duniyoyi ya hade mata guri daya, idan ta tuna Hamad ta tuna Amma, ta tuna Appa. Jin ta yi an yi knocking kofar dakin wani abu mai kama da tsoro ya fisgeta ta tashi tsaye da sauri jikinta na rawa ta yi baya tana kallon kofar, Namra ce ta turo kofar ta shigo da far'arta.

 Hurriya kin dawo

Kamin ta rufe baki Yasir ya shigo cikin yanayi na damuwa yana kallonta.

 Hurriya

Ta kasa amsawa Namra balle Yasir da ya shigo bayanta, ta hade yawu da karfi tana kallonsu. Yasir ya nufi gadonta ya zauna ya rasa me zai ce mata shi kansa be jin dawowarta gidan a yanzu mafita ne a gareta, babu yadda be yi ba wajen ganin ya fahintar da Hajiya Kaltume akan ta hana Appa dauko ta amman ta kasa fahimtarshi.

 Hurriya zauna

Ta zauna a gurin kamar wata wadda tunani ya birkicewa kwakwalwa. Namra dai ta tsaya jikin kofar ita ma tara ran duk babu dadin ganin yar'uwarta cikin damuwa.

 Hurriya ki yi hakuri dan Allah, idan kina kukan nan sai ki saka kanki a damuwa

Yasir ya daga ma Namra hannu alamar ta daina maganar sai ta yi shuru ta juya ta fice daga dakin, dan zumudin da ta zo da shi na murnar dawowar Hurriya sai ya gushe.

 Hurriya kina son zama nan ko kin fi son zama gurin Amma? Idan gurin Amma kike so zan mu tafi tare da ni dake mu yi ma Appa magana, idan be amince ba sai mu fadawa Hajiya Binta

Ta girgiza kai alamar bata aa.

 Kina son zama nan din?

Ta daga masa kai.

 Shi ke nan zo ki kwanta, kin yi sallah ko?

Ta amsa masa da kai sannan ta nufi gadon ta kwanta shi kuma ta tashi ya fice, kai tsaye bangaren mahaifinsa ya nufa sai dai yayi rashin sa'a be tararda shi ba, domin tuni ya fita after ya kai Hurriya bangaren Momy daman ita kawai yake jiran a dawo da ita gidan ya fita, saboda Hajiya Kaltume ta fada masa idan be yi da gaske ba Amma ba zata ba shi Hurriya ba.
Hurriya bata tabbatar da mahaifinta ya daina yayinta ba sai da ya canja mata makaranta ya saka ta makarantar government, yayinda sauran yan'uwanta da suke ajin karshen a private school suke can suna karatu. Ita kuma aka bata direba daya da zai rika kaita makaranta yana daukota ita kadai, ba karama ta kaddama aka yi ba kamin Appa ya saka ta government school, domin malaman dake karantar da ita a private school suna sonta sosai saboda kokarin da take da shi, ga kuma gasar da suke ta shirye shiryen turata. Har komiti suka hada na manyan makarantar suka zo har gida suka tarardar Appa suka tattauna da shi tare da nuna masa illar cire Hurriya a makarantar amman ya ki saurarensu saboda Hajiya Kaltume ta ba shi shawarar kaita makarantar Government, daga karshe ma sai suka rabu cikin rashin dadin rai domin Appa rufe su yayi da fada ya nuna musu Hurriya yarsa ce shi ke da iko da ita babu wanda ya isa ya fada masa me zai yi akan yarsa hukuncin da ya yanke ke nan kuma babu fashi.
Ta bangaren Hurriya ma hakan ya taba ta sosai domin yin sabin abokai da kuma canja wasu abubuwa na karantu domin malaman ba daya ba be ya zama abu ne marar sauki a gareta, hakan sai ya saka ta zama weak ta yadda bata iya maida hankali ta yi karatun yadda ya dace, gaba daya ta koma kamar ba ita ba, karatun da take ganewa a can bata ganewa yanzu, sai ayi darasi a gama bata fahimci komai ba, tunani da damuwa suka taru suka yi mata yawa, gashi kullum ita ce cikin kebe kanta bata son shiga cikin yan makarantar da bata saba da su ba.




**** **** ****

Hindu ta mika mata jaririn dake kuka.

 Iyami ina ta fada miki banza bata fitar da ke gidan Alhaji, amman kika sa kafa kika yi biris da maganata, yanzu gashin bayan fitar da ke ta dauke hankalinsa daga kan Yayansa, bayan an a kashe miki daya, kuma han karbe dan abun da yake hannunki, ina dadi ka haihu gari daya da miji amma yaki ya tako ya duba yara, ke da da ns yadda Alhaji yake sonki ai kin Allah kadai ya san yadda zai rika dauki yana hauka kin haifa masa yaya biyu kuma maza

Amma ta Hamid dinta dake shan nono ta ce.

 Hindu ban saba irin abubuwa nan ba, ni Wallahi ban san kowa mai irin wannan aikin ba, kuma ni ina tsoron kauce hanya

 Babu zancen kauce hanya, ai ba shirka zamu yi ba, kuma ba cewa zamu yi ayi mana na Sherri ba, aa mu dai kawai a karya sihirin da ta yi miki da na yayanki hankalin mijinki ya dawo ki koma gidansa ki rike yayanki, domin nan gaba kadan ma zai iya cewa su ma wadannan karbe su zai yi, tun kina cikin idda na so a nemi taimakon nan kika ki gashi yanzu har sai an sake daura aure

 Hindu da dai mun hakura, komai fa yana da iyaka wata rana zai karye ko da ba ayi komai ba indai asiri ne.

 Toh shi ke nan zauna a gurin, kina sakawa zuciyarki bakinciki ki lalace a banza ki zama bar tausayi daman haka suke so, yar ki kuma ta koma yar aikin gidan, idan ma ta yi sa'a kenan ita ma ba su kashe ta ba, nan gaba kadan idan ta girma ki rasa wa zai aureta, domin Wallahi ba zata yarda Hurriya ta yi aure ba ga nata yayan ko da kuwa sun yi aure, yanzu kina kallon yadda aka cireta ko ran mahaifinta, makaranta ma sai ya sakata a jnda karatunta zai lalace ba dan kuma ba shi da hali ba, sai dan an shiga tsakani

Amma ta kalleta tana nazarin kalamanta ita kanta a yanzu ta yarda ba a banza Appa ya canjawa Hurriya makaranta ba, yarinyar da yake alfahari da basirarta har yana ikirarin fitar da ita waje ta yi karatu amman a yanzu ya cireta daga makarantar kudi ya maida ita makarantar government.

 Tun ina Amarya lokacin da aka hade mu, ta taba ce komai ta dade sai na bar mata mijinta, kuma sai ta saka ni na yi nadamar auren Alhaji, har abada kuma ba zata taba son ko ta so yayana ba, domin kallon da take min na yar aiki be canja ba a idonta, sai ta kakkabe ni kamar yadda ake kabe tabarma a gidan da yardar Allah, tun da na ci amanar ta sai na gani

Hawaye ya sauko mata.

 Gashi kuma na fara gani, Wallahi da na san zuciyar Hajiya Kaltume ta kai haka da ba zan yarda na auri Alhaji ba duk kuwa da irin magiyar da zai min

 Oh Allah mai iko, toh wai haka zaku zuba mata ido shikenan ta kashe Hamad ta ci bulus

 Ba mu da tabbacin ita ta kasheshi, ba Hamad din muka gani ba balle ya fada mana ita ce ko ba ita ba, ko da ma ance yana raye ba lallai ne ya gane ita ta aikata ba, kuma ba jami'an tsaro suka kamata ba, ba mu da wata hujja ta cewar ita ce kawai dai zato muke yi

Hindu ta sauke ajiyar zuciya ta yi tagumi.

 Toh ni Kam Alhamdulillah ina da kishiya amman Wallahi ba kamar ta ki ba, ba a aure aka aurota miye laifinki wani yace kar ta iya kula da mijinta, ba mai aiki ba namjji ko uwarki aka hallata masa aure Wallahi wani sai ya aureta balle kuma mai aiki, har yaushe zaka dauki hakki ka dorawa kanka

 Wallahi ni kadai na san abun da yake damuna, wata rana ji nake kamar na yi ta ihu wani lokacin kuma na ji kamar na bi hanya na yi ta tafiya, wani sa'in na ji kamar zan yi hauka, gaba daya ni ma neman fita hayyacina nake

 Au kuma shi ne kike zaune? Kuma Gwaggo ta saka miki ido? Wallahi zama be gan mu ba, idan ma ke ba zaki iya ba ni zan nema idan na kawo miki karki sha

Hindu ta mike tsaye a fusace ta figi mayafinta tare da jaka ta nufi dakin Gwaggo, domin fahimtar da ita abun da Iyami ta gagara ganewa. Amma ta share hawayeta da ya zuba a fuskar Hamid.

 Wallahi na yi damar auren mahaifinku, na janwa kaina bala'i na kai kaina cikin manyan mata da ba su da imani babu tausayi, gashi na jefa yarana a cikin matsala, ban san kuma gaba ba me zan gani ba

Ta fashe da kuka sosai tana jin zafin mutuwar Hamad, ga zafin rabata da Hurriya da Appa yayi ga kuma zafin mutuwar aurenta a lokacin da bata yi tsammani ba, ga kuma zafin ta haihu ya kasa zuwa ya duba abun da ta haifa balle ya saka musu albarka.



______________

Wai ni kam Tsakanin Hurriya da Amma waya fi kowa ban tausayi?

A Next page zamu dunguma a labarin Hurriya, karku manta sunan littafin Hurriya, a yanzu ne zai amsa cikaken sunansa.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?

Page 7

5??5?(?5?(?5?$? 5??5?0?5?(?

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660


5??5??5? ?5?? 6??


Two days later...

Hindu ta ciro gorar ruwa dake cike da rubutu ta aje a gaban Amma.

 Yace wannan ki sha shi a tsaye kuma ki shafa zaki yi haka har kwana 7, na karya sihiri ne da tsari sosai

Amma ta kai hannu ta dauka tana juya rubutun.

 Rabawa zan yi har bakwai kenan

 Eh wannan kuma na hayaki ne, wato matar nan ba karamin asiri ta yi miki ba na shiga tsakaninki da Alhaji, kuma yanzu haka tana nan tana shirin yin wani akan Hurriya

 Shi ma dai tsafin yake kenan?

 Aa ba tsafi yake ba, kawai dai yana duba ne da kasa, ke ya dubo mana abubuwa da yawa fa, Wallahi ya ce yanzu haka ta yi miki jifa kuma tana daf da samun idan kuma ta same ki rayuwarki zata canja sai kin zama abar tausayi, ya ce idan baki tashi tsaye an yi yanka ba an maida mata da jefarta to zaki koma kwance ne, kuma ya tabbatar min idan aka yi haka ba jefarta ko asirin da ta yi sai ya karye

Amma ta aje rubutun da sauri.

 Subhanallahi, Subhanallahi Hindu kin ji abun da nake gudu, wannan ai shirka ne

 Wane irin shirka kuma? Ke fa matsala ne da ke, mu da muke neman warware sihiri? Ba fa sheri zamu yi ba warware ne

Amma ta girgiza kai.

 Hmm hmm Hindu ba zan taba komai nasa ba, ba zan iya kauce hanya saboda duniya ba, komai mukaddari ne daga Allah

Hindu ta rike baki.

 Toh ke ma dai ba a banza ta barki ba, wato sai da ta kwantar da ke ta yadda ba zaki iya yin komai ba

 Ko ma dai minene ni dai ba zan yi yanka ba, ba zan aikata wani abun da zai hana ni kwanciyar kabari lafiya ba, saboda rayuwar duniya mai karewa, ni dai na bar komai ga Allah shi zai isar min, Allah ka isar min ga duk wanda yayi min cuta, ga duk wanda ya hana ni zama da mijina, ga duk wanda ya raba tsakanin Uba da Yarsa, Hindu Wallahi ba zan iya shirka ba, ki yi hakuri dan Allah zan baki kudin da kika kashe

 Ba sai kin biya ba, ai na san mai kudi kika aura Hajiya Iyami, ni dai ban tafi gurin wani na ce yayi min tsafi ba, kuma dai ina sane ba zan yi shirka ba, amman na miki alkawari daga yau ba zaki sake jin bakina akan neman taimako ba kin yi da yar halak

Ta fara tattara kayan tana sakawa a jakar, Amma na kokarin fahimtar da ita amman bata saurareta ba ta fice daga gidan cikin bacin rai. A gurin Amma aikata irin abubuwan nan shirka ne, neman taimakon wani wanda ba Allah ba shirka ne, Hindu kuma tana ganin matukar ba shari suka je nema ba, kuma ba wata ibada suka yi da Allah kadai ake yi ma ba, to ba su aikata shirka ba, fahimta ta sha banban sai aka samu sabanin ra'ayi kowa ya kasa fuskantar inda dan'uwansa ya dosa. Gwaggo ce ta fito daga dakinta ta zauna falon cikin yanayi na rashin jindadin abun da ya faru domin tana jin komai dake faruwa.

 Ai da baki mata haka ba, da sai ki karba ki aje ba dole sai kin yi amfani ba, kuma abun da be tsabawa addinin ba, ba a hanawa kai aikatawa Iyami, ke kanki kin san ruwa baya tsami banza kuma na tsorata da lamarin matar nan domin bata da imani

 Gwaggo idan na karba kamar na yarda ne, kuma idan Kaltume bata da imani ta aikata tsafi mu ma sai mu biyeta mu aikata? Saboda namiji? Namijin da ko babu asiri zai iya cewa ya gaji da zama da ni, namijin da zan iya faduwa na mutu yau da dare ya sadu da abokiyar zamana? Ni kam ba zan yarda na zama daya daga cikin matan da Annabi ya ce mafi yawansu suna wuta ba, domin farkon abun da ke shigar da bawa a wuta tsabawa Allah ne da kin bin dokokinsa

 Duk da haka dai, Iyami ki nemi tsarin jiki kuma ki nemi na karya sihiri ban ce ki yi tsafi ba, amman ki yi tunani

Gwaggo ta tashi ta fice daga falon zuwa harabar gida. Amma ta girgiza kai.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, wai duk saboda kishi zai saka Kaltume ta aikata min haka kuma ta aikatawa yarana? Duk saboda namiji? Ka bata lahirarka? Appan Hurriya dama ban aureka ba, ina ma ban je gidan aiki ba

Tana maganar hawaye na sauko mata. Ta dora duka hannayenta a kai tana jin kamar ta bude bakinta ta saka kara ba tare da an mata komai ba, gaba daya duniyar ta rikice mata kashe ya hade ta rasa ina zata sa kanta ta ji sanyi ina zata saka rayuwarta ta ji sassauci.
(Ni kan na ce anya akwai irin su Iyami kuwa>??)

Kuka ta yi sosai har sa da ta gode Allah, sannan ta tashi ta nufi dakin Gwaggo ta shiga ta wanke fuskarta ta fito ta nufi dakinta dake wajen falon, kamin ta karasa ta soma jin gabanta na faduwa irin faduwar da bata saba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login