Showing 81001 words to 84000 words out of 279257 words

Chapter 28 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34710

number ta?

Hurriya ta ji gabanta ya fadi.

 Ni kuma? Wallahi ban bashi ba ko sunana ni ban san inda ya ji ba

 Bana son ki min karya, kuma bana son ki aikata wani abin da zai zubar miki da kima ko gidanmu, saboda haka ki kiyaye karki wani abu ya sake hadaki da shi, na san gayen nan na yaron kwarai ba ne, idan ba haka ba ni ma zan saba miki

 Toh Yaya amman Wallahi ban san shi ba

 To ya aka yi ya sami number ta?

Har zata ce bata sani ba, sai kuma tuna da ta karbi wayarsa ta kira Yasir.

 Da wayarsa na kiraka, lokaci da yace na saka masa number ta sai na kiraka na ce ka zo ka dauke ni, ai har na fada maka Adam yace I'm not safe here

 Na tuna, zan ja masa kunne

 Toh Yaya

Ta amsa tana gyara zaman littafin da Gwaggo ta bata a hannunta.




_________________
Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo...

Page 13

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar? MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne? cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai? shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
5??5?(?5?(?5?$? 5??5?0?5?(?

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

5??5??5? ?5?? 1?? 1??

Hajiya Kaltume na tsaye rumgume da Hanayenta Yasir ya faka motarsa ya fito, sannan Hurriya ma ta fito sau daya ta kalli gurin da Hajiya take ta dauke kai ta fice daga apartment din ta nufi na Momy, wata kalar harara Hajiya take watsawa Yasir har ya iso.

 Ina ka fito?

Ya juya ya kalli Hurriya da tuni ta fice daga bangaren sannan ya kalli mahaifiyarsa.

 Mun sauke Rukayya ne

 Kun sauke Rukayya kamar ya?

 Hajiya dare yayi shiyasa na kaita gida a mota, daga can Hurriya ta duba Amma

 Ita bata san dare yayi ba ta kama hanya ta zo? Kasan ma a ina ta fito? Wace yarinya mai tarbiya ce zata fita yawon dare?

 Hajiya Stop...

Ya fada yana kokarin danne bacin ransa.

 Ba sai ka min turanci ba, daman yaran zamani ne ku ai, sai ka zage ni ban sani ba, amman dai bari ka ji na fada maka ka fitar sapgar Rukayyar nan ba yarinyar kirki ba ce

 Hajiya please karki munanawa Rukayya zato, yarinyar nan tana da hankali da tarbiya, na san wacece ita, saboda ta yi dare baki san dalilin da ya saka ra yi haka ba, ki daina fadar bata da tarbiya bata min rai kike, yanzu da wani yayi abun da Khairi ta yi da yanzu kin zage shi, amman kin tsallaketa kina ganin laifin yar wasu, dan Allah wannan ya zama na karshe da zaki fadi wata magana marar dadi akan Rukayya

Yana gama fadar haka be tsaya jin abun da zata fada ba ya wuce ciki ya barta a gurin tsaye da mamaki.

 Ikon Allah baka son a fadi wata magana marar dadi akan Rukayya saboda Rukayya kanwar uwarka ce? Anya dai Iyami bata Zuba maka ka sha ba, kai duk wani abu da ya shafeta sonshi kake, daga kan Hurriya har Iyami yanzu kuma abun ya koma kan kanwarta, eh lallai tun da ka ga farar fata, to Wallahi baka isa ba ba Rukayya ba ko keya ce sai na ga bayanta, wato ma wani abu ne a cikin zuciyarka da har idan an fadi sunanta da mugun abu ranka yake ba ci, har da wani tashi ka kaita gida kai ga Sharukhan baban Soyayya, to da ni kake zancen

Ta juya ta bi bayansa tana masifa, a falo ta zame shi zaune yana lasa wayarsa yana ganinta yayi saurin tashi ya nufi stairs dan ya san fada zata masa, da kallo da bishi har ya haye sama.

 Ba shakka, wato ubanka ya dandana nan bakin cikin Iyami shi ne kai ma zaka gwada naka ko? Dadin abu kai haihuwar ka na yi ba aure ba, baka da ikon kanka sai ikon da ake da shi akanka

Ta zauna a inda ya tashi tana jin zuciyarta na wani irin zafi, domin bata da makiya a yanzu kamar Iyami da iyalinta...


HURRIYA POV.

Da sallama ta shiga falon Momy ta dago ta kalleta ta dauke kai, Namra kuma dake kwance cinyar Momy labarin da take da Momy ya hanata amsa mata.

 Ni Wallahi tausayi yake ba ni gaba daya ya koma kamar ba shi ba, dan murmushin da yake da yanzu duk ya daina

Momy ta shafa goshinta.

 Fadan kuma ya karu ba, sai bakar zuciya da ganin laifin kowa

 Ai dole

Hurriya ta risina tana yi ma Momy sannu da dare.

 Ina kika fito?

 Tare da Yaya muka fita ya aje Mama Rukayya a gida ne, ni kuma na duba Amma

Hurriya ta amsa tana jin kamar ace ita ce take kwance a cinyar Amma, Amma na shafa kanta yadda ta shigo falon ta tararda Momy da Namra abun ya burgeta sai ya kara mata kewar mahaifiyarta sosai. Namra ta tashi zaune

 Wayyo ban sani ba da naje dubata ya jikanta Hurriya

 Da sauki

 Allah ya kara sauki

Hurriya ta amsa da amin sannan ta mike tsaye ta, Momy ta bita da wani kallo kamar na tuhuma tana tsire baki. Hurriya ta shiga dakinta ta cire hijabin jikinta ta nufi gaban madubi ta zauna tana kallon kanta, sai hawaye suka fara zubo mata. A take ta sauke kanta kasa tana kallon hannayenta.
Rayuwar baya take tunawa lokacin da take cikin farinciki, Amma na kusa da ita Appa yana kaunarta ga dan'uwanta abokin fadanta kuma mai tare mata fada. Ta tashi kamar marar lafiya ta nufi gadonta ta zauna sannan ta cire gilashin idonta ta kwanta. Bata farka ba sai asuba, bata fito dakinta ba sai 12pm shi ma kuma saboda yunwa ta matsa mata lamba ne daman bata son fita ko'ina sai idan tana bukatar abinci, yanzu ba irin da ba ne da take zuwa makaranta balle fita ta zame mata dole, tun bayan da ta kammala Secondary school ta samu yancin zama a gida domin Appa be yi making wani effort da zai nuna yana son ta cigaba da karatu ba. Ita kuma tana tsoron yi masa magana sai dai ta yi ma yayanta shi kuma idan ya tunkari Appa da maganar sai yace masa akwai abun da yake jira. Daga Momy har Hajiya Kaltume kuma babu wanda ya damu da karatunta da ta yi da kar ta yi duk daya suke a gurinsu, Momy da yaranta take da kanta daman rayuwar wani bata dame ta ba, Hajiya Kaltume kuma bata son Hurriya da alheri ta ina zata damu da karatunta.
A hankali ta sauko kasa tana sanye da doguwar riga kanta babu dankwali, gashin kanta a dan yamutse saboda rashin gyara shi da bata yi ba after ta yi wanka.

 Yauwa Hurriya dan Allah ki shirya anjima kadan zaki raka ni Mall na siye wani abu

Ta juya ta kalli saitin gurin da Namra take zaune tana shafa abu a fuskarta.

 Toh Yaya Namra

Sannan ta juya ta shiga Kitchen din ta hada tea ta fito ta nufi dining ta zuba abun da zata iya ci ta dauka ta sake dawowa dakinta ta zauna a kasa ta nade kafafuwanta ta fara ci, bata wani ci sosai ba ta fi ta koshi sai ta ja komai gefe ta aje. Tana zauna a gurin har aka yi azahar, bata sake fitowa dakin ba sai da Namra ta tura kofar ta leka ta.

 Kin shirya kuwa?

Sai ta sauko saman gadon ta nufi gurin madubi ta dauka ta gyara kanta ta saka ribbon ta dauki mayafin abayar ta rufa.

 Eh mu tafi yanzu

Namra ta yi dariya ta girgiza kai sannan ta juya ta fita tana fadin.

 Shiyasa lokacin zuwa makaranta kike late ba zaki shirya ba sai a lokacin da ake jiranki

Murmushi kawai ta yi ta jira tare da Namra suna sauka tare, Hurriya na ganin Momy ta yi saurin risinawa kamar yadda ta saba gaishe da manya.

 Momy barka da yamma

Momy ta watsa mata harara.

 Sai yanzu kika ga damar gaishe ni, ba kin san ina cikin gidan ba? Me yasa baki gaishe ni ba sai yanzu

Ta yi shiru ba dan bata da abun fada ba, sai dan ta san tana fadar wani abu Momy zata iya tsinka mata mari, kamar yadda bata isa ta shiga dakinta da sunan ta zo gaishe ta, sai dai ta tsaya jiranta idan ta fito ta gaisheta kamar wata yar aiki, wannan ne abin da Hurriya ta kasa yi, Momy kuma take jin haushinta.

 Momy mu dai mun tafi

A take murmushi ya cika fuskarta tana kallon yar gudaliyar yarta mace daya tak data haifa.

 Allah ya tsare, ya dawo lafiya yar Auta

Ta yi murmushi sannan ta yi ma Hurriya alama da ta tashi su tafi, Hurriya ta tashi suka fice tare. A tare suka shiga motar Namra na tuki Hurriya na zaune gaba tana sauraren sautin da Namra ta kure a motar idanuwanta kuma suna kallon wani gurin dabam har suka isa Sarauta Mall. A harabar Namra ta faka ta fito sannan Hurriya, after ta rufe motar suka nufi cikin Mall din tana fadawa Hurriya abubuwan da take son siya.

 Zaki iya daukar wani abu da kika ga kina so amman fa kar ya wuce 20k

Fuskar Hurriya ta cika da murmushi.

 Na gode Yaya Namra amman ni ki ba ni kudin akwai abun da zan yi da su

Da mamaki Namra ta kalleta tana kokarin kai hannu ta dauki turare.

 Me zaki yi?

 Wani abu dai bana son na fada, amman yana da muhimmanci sosai

 Shi ke nan to idan mun koma ki turo min account dinki sai na miki transfer

Take a gurin Hurriya ta rumgume ta.

 Na gode Yaya Namra ke ma kina so na kamar Yaya Yasir

Namra ta yi murnushi suka ci gaba da siyayyar after sun gama suka nufi gurin biya, Namra ta bude jakarta ta dauko cart dinta ta mika.

 Aa an biya muku Hajiya

 An biya kuma?

 Eh ba na yau kadai ba har ma da wanda zaku sake zuwa nan gaba ko da kuwa za ku yaye shagon nan ne gaba daya

 Waya biya? Wanene wanda baya son kudinsa haka?

 Gashi can bayanku

Daga Hurriya har Namra juyawa suka yi kallon mai neman barar da kudi saboda be san kimarsu ba. Suna hada ido kowanensu ya gane waye. Shi kuma ya nufo inda suke idonsa na kan Hurriya.

 Kai ka biya kudi?

Namra ta tambaya tana hade masa rai.

 Eh

 Saboda me?

Ya kalli Hurriya dake tsaye tana kallon ikon Allah.

 Saboda Hurriya

 Miye tsakaninka da ita? Kuna da wata alaka ne?

 Alakar dai nake kokarin kullawa, waye ke?

Wannan karon Hurriya ce da kanta ta tari numfashin yayarta ta amsa masa rai a bace.

 Yayata ce, kuma daga yau karka sake nuna ka san ni domin ni ba yarka ba ce, kuma karka sake kiran Yayana a waya kana cewa a hada ka da ni

Adam yayi murmushi.

 Ya fada miki kenan? Na kira Khairi ta ki hada ni da ke, the last kiran da na yi ma yayanki ma be saurare ni ba ya rufe ni da fada, Na gode Allah ma da na ganki a nan

 Eh saboda basa son kana kirana kuma karka sake, sunana ya fita daga bakinka, mu tafi Yaya Namra

Namra ta bita da kallo she never thought Hurriya zata iya bude baki ta yi masifa haka. Shi ma kallonta yake domin bata yi kama da irin yan matan nan masu masifa ba. Adam ya maida dubansa gurin Namra da ta mika hannu ta dauki ledar kayanta.

 Khairiyya ce ta ce muku ni dan'iska ne?

Namra ta kalleshi sama da kasa at his age ba zai wuce 25-26 ba that's mean ya bata shekara daya kenan ko biyu.

 Malam Hurriya ba irin matan nan ba ne, dan Allah ka kama gabanka

Ta dauki ledarta ta nufi kofar fita, suka bar shi a gurin kunya kunya ma'aikatan gurin na kallonsa. Ko da Namra ta isa gurin motar Hurriya na tsaye ta hade rai ya rungume hannayenta tana jiran fitowarta.

 Ashe kin iya fada

 Ya bata min rai fa, jiya saboda shi Appa kamar zai dake ni, Kuma Yaya yayi ta fada sosai

Ta fada ba tare da ta kalleta ba.

 Shiga muje

Hurriya ta bude motar ta shiga, Namra ta fara tukawa. A motar Namra sai zaginsa take yana tsine masa tare da fadar daman irin samarin nan haka suke.

 Ni da na sani ma ba zan birthday din ba

 Abun yar'uwa ace ba za aje ba? Ai dole ka je Khairy dai ta zama wata kalar mace daman tun kamin ta kare karatun na wata friend dinta ke fada mana tana shan shisha, kamar kar ta fara sami'ar nan sai ta hadu da friends din banza suka canja mata rayuwa gaba daya ta canja

Tana maganar tana kokarin kwaucewa motar take gabansu. Overtaking take son yi amman mai motar ya hanata hanya, kasancewar titi express ne idan ta yi dama sai ya koma can idan ta yi hagu sai yayi hagu. Horn ta danna da karfi shi ma ya mayar mata, at first ranta ya baci har ta yi kamar ta bugu motar dake gabansu sai kuma ta danne zuciyarta.

 Mai motar nan lafiya yake kuwa?

 Ko yayi shaye shaye

 Maybe

Namra ta rage gudun motar shi ma sai ya rage, the second thing she did was laugh irin abun yanzu kuma ya zama out of sence. Ta dan gwada kara gudun shi ma sai ya kara, ta sake raguwa sai ya rage. Tana samun sa'a ta yi overtaking ta wuce da gudu, shi ma sai ya danna a guje ya wuce, wannan karon har da Hurriya sai da ta yi dariya, Namra ta sake yin gaba ta wuce shi sai ta sauya hanya, ga mamakinta sai ya biyota a baya ya wuce, daga lokacin ne suka fara tseren gudu ita da shi ba dan sun san waye a motar ba. Ita dai daman gilashin motarta a bude yake daga ita har Hurriya ana kallon yadda suke shakar dariya su ne basa iya ganin wanda ke cikin motar. Da gangan Namra ta sake sauya hanya tana dariya tana kallon nearby mirror bata ga ya biyo ba, sai da?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? suka kusa isa karshen Titi sai gashi ya bullo ta gabansu.

 Mun shiga uku Hurriya waye mutumen nan?

Hurriya dariya kawai take ta kasa cewa komai, domin a gurinta abun is so funny ita bata tsorata kamar yadda Namra ta fara tsorata yanzu ba. Namra ta rage gudun motarta ta sauka gefen titi shi ma sai ya rage gudun ya sauka gefen titi ya faka gabansu.

 Ki daina dariya what if he want to kidnap us? Ko kuma wannan saurayin ne na dazu?

Hurriya ta ji gabanta ya fadi a take ta daina dariyar, A daidai lokacin da

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login