Showing 234001 words to 237000 words out of 279257 words

Chapter 79 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34714

shiryen dawowa da ita a garin nan kusa da ni, domin halin da na same ta last week da na je garin nan ban jidadi ba

 Wannan ma wani abu ne da ya kamata ka yi tuntuni, ni har mantawa nake da kana sa ya a kauye saboda dadewar da take bata zo ba, kuma mu ma ba ma zuwa amman idan a nan ne ka ga tana kusa da mu, na jidadin kudurinka Tsoho Allah ya maka albarka ya kara yaye damuwa ya haskaka rayuwa

 Ameen Hajiya

 Sai ka cigaba da rike addu'a, kuma idan da hali ita ma Kaltume ka dawo da ita cikin yayanta, ta ci albarkacinsu

Ajiyar zuciya Appa ya sauke yana jin kamar Hajiya Binta na matso masa da mutuwa kusa.

 Wato Hajiya da dai za a kara daga min kafa wata kila a gaba zuciya ta raya min haka, amman a halin yanzu matar nan bata gabana ko kadan, da ina tunanin idan ta cika idda zan fada mata ta koma gidanta ko Family House dinsu, domin bana bukatar zamanta a gidan nan da sunan zaman Yayanta

 Ba saboda ita zaka yi ba Tsoho saboda yayanka zaka duba, Yasir da Ruma domin ba zan saka da Khairy ba

 Idan umarni ne Hajiya zan bi idan kuma shawara ce zan duba

 Shawara ce, Iyami ma da take kyautata min nake kaunarta cilasta maka maida ita ba balle Kaltume da ba dan darajar Yayanta ba da ko kallonta ba zan yi ba, babu kalar cin mutuncin da bata yi min ba, amman shi babba ba ya zama kamar yaro kuma abun da duk ka aikata mai kyau ko marar kyau zaka girbe shi a kusa ko a nesa, wannan fadin Allah ne

 Haka ne, Kuskuren kuma daga ni ne Hajiya ban tsaya na duba background din ba kamin na dauko, kaddara ta riga fata

 Wannan ma zai wuce tsoho, ka kyautata zamanka da Iyalinka gwargwadon yadda zaka iya, kuma ka kwatanta adalci a tsakanin ?a?anka ita soyayya an sani Allah yake sakata, amman sai mutum ya bar abun a zuciyarsa ba sai ya bayyana ba domin bayyana ko nuna fifiko akan wani shi ke bude kofar abubuwa da yawa da baka yi tsammani ba

 In Shaa Allahu Hajiya

 Allah yayi taimako ya hada kan Iyalinka

 Amin

Ya amsa sannan suka yi sallama ya sauke wayar ya kalli ragowar furar da Sapna ta daka masa da kanta ta aiko masa bayan dawowar daga kasar Maradum. A yanzu jin kansa yake a free kamar wanda ya fito daga wani kangi ya samu yanci haka yake jin a ransa, nishadinsa na da yadda tsarin rayuwarsa na baya a yanzu jinsa yake a normal a yadda ya saba yi.
A yanzu din ne yake jin marmarin abokiyar rayuwarsa fiye da koyaushe be taba bakincikin rabuwa da ita ba sai a yan kwanakin nan gaba daya ta shige masa a rai wani sabon kaunar Amma yake ji a ransa, be tabbatar da ya tabka babban kuskure na sakinta ba tare da ta yi masa laifi ba sai a yanzu bata kusa da shi, gashi idan ya tuna da yaransa Hamad Hurriya da yan biyun da ta haifa masa sai ya ji tausayinta ya kara kama shi.
? ?
Lokuta da dama ya kan nutsa a duniyar tunanin dalilin sakin nata sai ya rasa, gaba rayuwar baya ta zame masa kamar mafarki yayi wasu abubuwan da yayi ma Amma da Hurriya da kuma iyayenta idan ta tuna sai ya ji babu dadi, kuma ya rasa dalilin haka, kamar yadda a yanzu ma ya rasa dalilin tsanar da yayi ma Hajiya Kaltume, macen a da ko tari ta yi jikinsa rawa yake ya amsa mata, a yau ita ce yake jin baya bukatar zamanta a gidansa ita ce a yau yake fatan ta gama zaman idda ta bar masa gidansa, a yau ita ce macen da baya son kallon bangarenta idan zai fita.
? Zancen da Hajiya Binta ta yi masa cewar mata ne suka dace da siyayyar kayan dakin Hurriya ya saka shi kiran Number Amma, kamar wani yaro haka ya aje wayar a gabansa ya dauke hannayensa yana kallon number tare da fatan Amma ta daga kiran amman bata daga ba har kiran ya katse, ya sake gwada kiran a karo na biyu sai kuwa ta dauka hannunsa ya kai ya taba speaker dake jikin wayar, sallamarta kadai nishadi take kasa shi tana tuna masa da rayuwarsa da suka yi a baya.

 Wa'alaikissalam...Hajiya an wuni lafiya?

 Alhamdulillahi

 Maa Shaa Allah, Ina yarana duka suna lafiya

 Lafiya kalau

Ta amsa a takaice domin bata son wata maganar da ta wuce sha'anin yara ko gaisuwa ya wuce tsakaninsu. Shiru ya dan yi na lokaci kamin ya ce.

 Yanzu na gama magana da Hajiya nake fada mata yadda muka yi da ke na siyayyar wasu abubuwan na Hurriya, nake fada mata ina son siyayyar kayan dakinta da kaina kamar yadda nake yi ma sauran Yaya Sapna da Maama, wai take cewa su ma siyen kayan daki ai na uwa ne, iyaye mata ya kamata su yi

 Haka ne

 Shi ne na ce idan babu damuwa sai ki shirya tare da mutanenki mu tafi Kano a duba mata kaya masu kyau wadanda hankalinku ya kwanta da su, da ice ita din babu lalura a tare da ita da sai mu tafi tare da ita ta zaba da kanta kamar yadda sauran yan'uwanta suka yi

 Already mun yi order kayan Kitchen gurin Khadeeja Candy, zata saka a kawo mana daga Kano har gida, kuma wasu abubuwan Gwaggo zata tafi tare da Hindu Lagos su siyo

(Duk mai bukatar kayan kitchen, Bedsheets da kayan kawata falo ko daya, akwaituna da kayan lefe kamar su laces shadda atamfa materials da Shoes and bag, sarka yan'kunne turareka zai samu a gurin Khadeeja Candy Store cikin sauki da rahusa, muna aikawa ko'ina a fadin Nigeria da sakashen dake makota da mu kamar irin su Nijar Togo da Ghana cikin aminci da yardar Allah, mai bukata sai ya tuntube ni a business line dina kamar haka :- 080361266660)

Appa ya sauke ajiyar zuciya jin kamar Amma bata fahimci inda ya dosa ba ya ce.

 Kayan daki nake magana kamar gado da kujeru da sauran abubuwa na cin abinci, gidansa da ke Kaduna za a iya siya a Kd a saka a can ko kuma a siya daga Kano a kai can, da son samu ne ma a siyo mata komai a waje na fi aminta da kayan can fiyeda na cikin gida

 A Kanon ma babu kalar kayan da babu, suna dauko kayan waje domin saukakawa masu gaggauwa ba sai an kashe kudin jirgi ba wata order ma sai ka yi bata iso da wuri ba, zaka iya zuwa Kano ka duba mata

 Da zamu tafi tare ai da zai fi domin ke ce idonta a yanzu, kuma duk yadda zan yi zabe ba zai kai ga ke yadda zaki zaba ba

 Babu wata hujja da zata saka na shirya baka tafiya da kao Alhaji ko dai ka manta ni din nan ba matarka ba ce?

 Ba daga ni sai ke nake nufin tafiyar ba tare da familynki, shiyasa zan baki dama ki yi shawara da su daga nan zuwa gobe abun da kika yanke sai ki fada min

 To shi ke nan mu kwana lafiya

Yayi saurin dakatar ta ita daga kokarin yanke wayar da take.

 Idan ba zaki tsaya mu gaisa ba, toh ina yarana Hassan da Husaini?

 Sun tafi Islamiya

 Hurriya fa bata kusa?

 Rukayya karbi mikawa Hurriya waya

Amma ta cire wayar a kunnenta ta mikawa Rukayya da ta mike tsaye ta nufo gurin da suke zaune ta karbi wayar ta fice daga dakin zuwa dakin Bappa da Hurriya ta shiga dazun tana ganawa da kakanta.

 Ka ji min wata magana wai Hajiya Binta dake Saudi gurin Ummara ta ce masa zaben kayan daki na mace ne

Baaba Uwani wadda ta kasance kanwa ga Gwaggo ta bude hannayenta jin an sosa mata gurin dake mata kaikayi.

 Daman ai na fada, dama nan ya bar zabin komai zai fi, domin dai zaben Kaltume ko wannan Hajiya Nafisa ba za su zabo ma Hurriya abun kwarai ba

 Daman ni ban saka ran da Kaltume za a je ba, domin babu aure yanzu tsakaninsu, Nafisa nake saka ran zata taimaka masa gurin zaben kayan ita na san ba zata zabo abun kirki ba domin ba son Hurriya take ba kuma tun da aka daura auren nan har yau bata tako gidan nan ba

Hindu dake bude giWa ta ce

 Da gaske wai bata zo ba?

Amma ta waiga ta kalli kawar da za'a iya cewa yanzu ta zama yar'uwarta ta ce.

 Wallahi bata tako ba, kuma kin ga ko cikin danginsa da suka zo bata biyo su ta zo ba kuma bata zo ita kadai ba Namra ma bata da tako nan ba

 Allah da iko yake, da alama ma fa ita ma bata son auren nan, ke bi ba dan na ga yaron ba tubarkalla Maa Shaa Allah da shi da zan iya cewa aura mata shi aka yi saboda sun ga ba mutunen kwarai ba ne, ina fatan dai an bincike halinsa ba shi da wani nakassu

Ta karasa zancen tana jefa giWa abakinta. Amma ta Wan taSe baki.

 Bashi da shi gaskiya domin shekaran jiya kamiN Hajiya Binta ta wuce Ummara ta zo gidan nan yi mana bankwana take fada mana Appan Hurriya yayi saka an masa bincike a akan yaron ta hallayarsa ta zamankewa da mutane kuma ba su ji wani aibu ba, Allah ne fa ya wanke Hurriya kuma yayi mata sakamako da wannan, ki duba ko video nan na Khairy yanzu da ya cika gari Appanta yace shi ne ya shiga ya fita ya ga komai ya warware, an goge hotunan Hurriya ta inda zai iya kuma ya saka suka bata hakuri, kuma shi ya cilastawa yaron fadar gaskiyar abun da ya faru, kina jin yadda aka daura auren nan da sadakin kin san abu ne kawai min indin Allahi, karki so ki ga yadda ya zo gidan nan, baya ma iya daga ido ya kalleni, son kakarsa ma ta zo ita da abokiyar zamanta da kanen mahaifinsa su biyu da yayar mahaifiyarsa dukansu kuma ban ga wani abu a tare da su ba, idan ba dayar ba dake ta hankada tana harare-harare

Gwaggo da ta gama sallame sallah a yanzu ta ce.

 Daman ai ba za a taru a dangi ace kowa sai ya so ka ba, dole za a samu wanda ba ya ra'ayinka, balle dai yadda yaron nan yake ba za su rasa matar ba shi ba

 Gwaggo ai gabanki Hurriya ta fada mana yadda Namra da Momy suka mata gargadi akan yaron, ashe dai shi ne mijin ba su sani ba

Amma ta fada tana mike kafarta da har yanzu bata gama warke mata ba, tana kallon Gwaggo ta cire hijabinta tana fadar

 Ki kwantar da hankali ki cigaba da yi mata addu'a ita ma kuma ta cigaba da yi domin ba bari abun da aka zaba za'ayi ba musamman Kaltume Allah kadai ya san hassadarta akan auren nan, kuma kin ga Saurayi ne ba mai mata ba balle ki daga hankalinki da tsoron abun da zai biyo baya

 Ko mai mata ne ma Gwaggo ya zan yi tun da mahaifinta ya riga ya bada ita? Ai babu yadda zan yi sai hakuri, dan yasan Hurriya ?ata ce ai ya saka shi yin haka, da Momy ce ko Kaltume ba zai taba yi ma yaransu haka ba a daura aure ba tare saninsu ba, kuma na ji dadin da be bawa kowa siyayyar kayan ba ya kawo kudin nan yace a siya komai

 Yanzu fa ya dawo hayyacinsa kina ganin yadda yake rawar jiki da yaran nan wai ni me yace ma kiran da yayi yanzu na ji kina masa zancen ya siya can?

Amma ta fadawa Gwaggo abun da ya bukata, Hindu ta kyalkyale da dariya, Gwaggo da Baaba uwani suka yi murmushi.

 Ba wani nan shiri yake nema, yana son ya kyautata miki ne kuma ya samu kanki

Amma ta tabe baki tana wofintar da zancen Hindu da be kama kanta ba.

 Hindu ke dai baki rabo da zance a bakinki, ni yanzu ina ni ina Alhaji Haruna? Daman can kaddara yara ce ta kaini kuma an haifa, Wallahi yanzu ni baya gabana gidansa be burge ni sam, ke ni fa auren ma ya fita a raina ma gaba daya na wasun mazan ma, balle na Alhaji Haruna mai mata irin Kaltume ko makiyi ba zan so ya zauna da kishiya irin Kaltume ba, kamar dai kun manta inda aka fito? Magana wannan ina son na yi amman na kasa daga kwance sai kwance babu abun da zan iya kawarwa bayan an raba ni da aurensa an juye kansa, hakan duk be wadata ba aka koma a gurin yarana? Shi kuke gani da fatan zan iya komawa? Ai har abada...!

 Allah dai ya zaba abun da ya fi alheri amma mace ai bata cewa ba zata sake aure ba, kuma idan da yara ko an rabu kamar ba a rabu ba ne yanzu ba gashi ba? Kuma idan baki koma ba ai ita Kaltume ta samu abun da take so kenan

Cewar Gwaggo domin ita ma a yanzu ta gano zaman auren ya fi babu, ko da wani namijin ne balle kuma uban yayanta da aureta tun tana budurwa gashi har an kai ga aurar da ?a.

 Ni dai na hakura da Alhaji Haruna, idan har auren alheri a gare ni a gaba Allah ya kawo min wani mai mutunci da sanin ya kamata, kuma ya ba ni abokiyar zama ta gari

 Amin, idan kuma akwai alheri Allah ya maidake dakinki Iyami, ko dan yaranki, nan gaba kadan zai ce zai karbi yaran nan kuma idan baki a gidan ba za su jidadi ba, ni dai a matsayina na mahaifiyarki ina rokon idan ya nemi maida aurensa karki juya masa baya dan Allah

Amma ta kalli Gwaggo idonta na cika da hawaye.

 Gwaggo ban manta wahala da azabar da na sha saboda auren bawan Allah nan ba, kuma ke da kanki kika ce inda shi ne ba zan koma ba, ko da fari ku kuka karfafa min guiwar aurensa kuma... 

 Kuma hakan be haifar miki da komai ba sai alheri, ki rika duba wannan ina son ki sani ita kaddara a rubuce take ko da Kaltume ko babu ita sai kin yi irin wannan ciwon sai haka ta faru, ita dai ta zama sanadi ne kawai kuma yanzu gashi ai kin samu sauki jinyar kuma ta zame miki ibada, bari na dubawa Hurriya maganin Infection da muka siya gurin UMMU SA'ADA WOMEN'S SHOP 09160547983

Gwaggo ta mike tsaye ta fice daga dakin tana amsawa Baaba Uwani dake yaba kyau maganin na infection.

 Ai da yana da daci ko tsami ma Hurriya ba zata yarda ta sha ba, yadda na san Hurriya da son zaki ba zata sha ba idan yana da daci

Cewar Amma tana share hawaye Hindu ta ce.

 Shiyasa ai nake jindadin maganinta, ba shi da daci kuma baya saka zawo ko tashin zuciya ki sha abinki kamar kina sha tea, ga aiki a jiki kuma gashi da saukin kudi daga 500 yake farawa har zuwa sama za ki ga yadda wanke marar mutum ta yi tass shiyasa aka ce kar mai ciki ta sha, gashi har kala biyu take yi da mai kamshin takafarnuwa da wanda ba shi da shi, saboda wasu basa son masu warin tafarnuwa, kuma zaka iya sha tare da miji da yara matukar sun haura shekara biyar

 Gaskiya na ji ana yabon maganinta, mu ma dai mun fara ganin aikinsa a yanzu, Allah dai ya sa a dace kawai

 Amin

Wannan karon Baaba Uwani ce ta amsa sannan ta mike tsaye ta bi bayan Gwaggo da ta fice dakin. Hindu ta daki cinyar Amma.

 Ke Wallahi ki koma dakin mijinki wannan kame kamen da yake ba na komai ba ne sai na neman aure, kin san yanzu aurensa ya koma kasa saboda kin cika idda dole shi ma ya shiga cikin manema, iyaka a nemi tsari kuma ki rike addu'a ba dare ba rana, ni kam da zaki bi yawa Wallahi Iyami karki bar mijinki, Gwaggo ma shi take so

Amma ta kawar dai tana dauko wani zancen domin ita dai a yanzu har ga Allah bata son komawa dakin gidan Appa ita kadai ta san halin da ta shiga kamin ta samu kanta a yau. Kwana da yin haka Appa ya sauka gidan da kansa tare da wani dan'uwansa da Momy ya so a zo gidan sai dai yadda ta juya masa baya a lamarin auren nan ne ya saka dole ya aje lamarinta a gefe, Bappa da dake zaune a madaidaicin falo ya kalli Alhaji Haruna a natse sannan ya fara magana.

 Akan maganar da ka yi ne, ita Iyami tace tana ganin a tafi da kanwar Gwaggon yara wato Baaba Uwani da kuma kanwata Innar su Nasiru da Ibrahim dake can sokoto zan yi waya da ita ta zo sai ayi tafiyar da ita, da kuma Hindu, sai su ku duba kayan a tare da naka yan'uwan

Appa ba haka ya so ji ba, domin ya so ayi tafiyar ne da Amma, kamar yadda yayi da Kaltume a lokacin da za su zabawa Maama kayan daki.

 Hakan yayi Bappa na gode sosai Allah ya saka da alheri, hakan ma wata alfarma ce, ina godiya Bappa kuma ina kara bada hakuri akan abubuwan da suka faru, ita kaddara haka take a yadda aka rubuta haka take zuwa, wani lokacin sai ido ya rufe hankalin ya gushe ka aikata abun da baka yi tunani ba, ba dan Allah ya rubuto haka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login