Showing 204001 words to 207000 words out of 279257 words

Chapter 69 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34658

ya taba ta sosai har ya zama jijiyar dake aika sako a idonta zuwa kwakwalwarta ta tabu, idon ya rufe gaba daya

 Duka sukurinka ya fada mana haka, babu kalar haukar da be mana ba akan Hurriya

Wannan karon Alhaji Munzali ne yayi magabar. Appa ya kalli Daddy ya ce.

 Ranka ya dade ban gane inda ka dosa ba, Wallahi

Daddy yayi murmushi ya sake yin murmushi sannan ya dora.

 Mun zo jaje ne da rokon iri, na baka auren kanwata yau kuma ina zaune a gidanka ina nemawa ana Captain Jamal auren yarka Hurriya.... 

 Ranka ya dade Hurriya?.... Dan ka ranka ya dade..... Danka....

Appa ya saka kalmar shahada yana jin abun wani iri a lokacin da be saka ran faruwar hakan ba.

 Ranka ya dade Huriyya dai ko wata dabam a cikin yayana

 Hurriya dai Alhaji Haruna...

Daddy ya nanata masa, a gudun kuskure ko samun akasi Appa ya sake share gafe ya shimfida musu abun da ya faru.

 Ita ce yarinyar na da kake maganar an yada hotunan ta fa

 Za mu hukunta wandanda suka yi haka fiye da yadda kai zaka yi, kuma ina tabbatar maka zamu rike da mutunci da girmamawa

 Ranka ya dade Hurriya bata gani sam a halin yanzu da nake maka magana

 Za mu nema mata lafiya kuma za a dace da yardar Allah

 Allahu Akbar....

Idon Appa ya cika da kwalla, ba dan baya iya yin abun da Daddy yace za su yi na Hurriya ba, sai dan gata da ya zo mata daga Allah na mallaka mata AA Turaki a matsayin suruki, a lokacin da duniya take zaginta kuma ta rasa idonta, aka nemawa yaron da ake ji da shi a Family su aurenta.

 Ranka ya dade na baka, na mallakawa Captain Hurriya Halak Malak

Daddy yayi murmushi na musamman yana farinciki da farincikin ansa.

 Alhamdulillah... Amman Alhaji Haruna baka yi gaggawa ba? Ya kamata mu ji ta bakin yarinyar ko tana son ana

Appa ya saka hannu ya tsargar da hawayen da suka so zubo masa.

 Hurriya yarinya ce mai tsananin Biyayya ranka ya dade, tana da gudun bacin rai ba zata ki zabin mahaifinta ba, kuma na san ban zaba mata mugun abu ba, na san waye kai kuma na san waye Jamal, babu uban da ba zai so Jamal ya zo masa a matsayin suruki ba

 Maa Shaa Allah na yi farinciki da jin haka, daman kuma na yi tsammanin samun haka a gurinka, halinka na kirki shiyasa mahaifinmu ya baka auren Nafisa kuma Alhamdulillah aure yayi albarka

Appa yayi murmushi jindadi marar misaltuwa.

 Ranka ya dade idan ba zaka damu ba, zan yi ma ana Yasir magana sai a daura auren yanzu a nan

Appa yayi hakan ne saboda yana ganin kamar labari zai iha canja ko kuma shedan ya shiga ciki daga baya..

 Toh ka yi mana irin abun nan na iyayen zamani, hakan zai saka ana a farinciki sosai gashi kuma ba mu zo da sadaki ba, kuma ba a yanka mana

 A biya sadakin daga baya

Alhaji Sadiq ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin 100k ya aje.

 Wannan yayi?

 Aa Jamal yace min yarinyar mai tsada ce, ya kamata mu siye ta da ?ima, je ka yi magana da anka, ni ma zan yi magana da Nafisa

Appa ya tashi yana sauri ya fice daga falon cikin zumudi da murna. Daddy ya kalli kanensa

 Alhaji Munzali a fita a samo mana goro da Dabino ko?

 Toh Alhaji

Alhaji Munzali ya tashi ya fice, Daddy ya daga wayarsa ya kira Momy, sai gata ta sauko da far'arta domin zuwansa ya faranta ranta.

 Yaya har kun kare

 Aa tukuna dai, Nafisa a cikin sarkokinki an zinarina wacece ta fi tsada?

 Wanda na siye 50 million, ban taba saka ya na siye na aje ne dai kawai a matsayin kaddara

 Dauko min ita yanzu nan?

Har ta yi kamar ta tambaya dalili sai kuma wata zuciyar ta nuna mata idan ta yi haka bata kyauta ko ma minene ai zata ji daga baya. Sama ta koma ta shiga dakinta ta bude akwaitin sirrinta da take aje yi kudi ta dauko sarkar dake cikin wani box da shi kanshi abun kallo ne, tare da receipt dinta ta sauko ta aje ma Yayanta.

 Gata yaya

 Shiga ciki zan kira ki idan na gama

 Toh

Ta juya cikin rashin natsuwa da tunani ta koma dakinta. Daddy na zaune a gurin Appa ya shigo falon da saurinsa.

 Ranka ya dade Bismillah ga shimfida na yi a waje

Daddy da kansa dauki sarkar ya miki tsaye tare da yan'uwansa suka fice daga falon, babbar harabar gidan Appa ya shimfida Carpet, sai da Daddy ya fara zaunawa sannan sauran suka zauna. Yasir ya ba su hannu suka gaisa daya bayan dayan sannan shi ma ya samu guri ya zauna, Appa ya gayyato har da masu aikin gidan domin shaidar daurin auren Hurriya a gurin aka daura auren, Daddy ya wakilta Alhaji Sadiq a matsayin wanda zai karbawa Captain aure, Appa kuma da kansa ya bada auren Hurriya, bayan ya karbi zinarin a matsayin sadakin Hurriya. Bayan an daura auren ne Alhaji Munzali ya dawo gidan, ya fito mota ya bude bayan motarsa Appa ya saka masu aikin suka kwaso goro da dabino, Daddy ya sa an fasa goro da dabino ya cire dabino uku da goro daya ya saka aljihunsa, sannan yayi musahaba da Appa yan'uwansa ma suka yi.

 Ba sai mun koma ciki ba, rigimar Nafisa ba zan iya da ita ba a yanzu, zata ce an yi komai ba tare da ta sani ba, ka sanar mata a madadina

 Ranka ya dade na gode, Allah ya baka danka ikon riketa amana

Appa yana rike da hannun Daddy yake fadar hakan.

 Ameen, babu kai babu mugun suruki da yardar Allah Jamal zai rike yarinyar nan fiye da yadda kake fata

Daddy ya kara tabbatar masa da yarsa bata shiga mugun hannu ba. Appa ya takasu tare da Yasir har gurin motarsu suka shiga sannan ya koma ya cire dabino da goro ya nufi bangaren Momy yana murmushi kana ganinsa ka san yana cikin farincikin da ya dade be yi ba. Yasir ne ya rabawa mutanen da suka shaidin daurin auren a gurin sannan ya dauki sarkar Zinarin da Appa ya ba shi riko ya shiga bangaren mahaifinyarsa yana murna. A falo ya tararda Hajiya Kaltume da Khairy zaune a kujera daya.

 Hajiya kina nan har yanzu

 Wallahi kuwa, ka ga tun da na raka Hajiya Fatee nake zaune a nan muna hira da Khairy, wai kiran me mahaifinka ya shigo yana maka a gaggauce?

Ya zauna saman kujera yana rike da kwatin na zinari.

 Auren Hurriya aka daura...

Khairy da Hajiya Kaltume suka kalleshi jin abin banbaragwai.

 Baka da hankali wane irin aure kuma?

Yasir yayi murmushi daman ya san ba lallai kowa ya ji ya yarda ba.

 Aure dai Hajiya, Wallahi aure aka daura mata yanzu nan, wasu ne suka zo tambayar aurenta Appa ya ce ba za su tafi ba sai an daura auren

 Allah sarki to su ba su da labarin abun da ta yi ne? Ko kuma yan'uwan Adam din ne suke neman a rufawa juna asiri?

 Ba su ba ne, yarinyar nan fa ta rantse Hajiya bata aikata ba, be kamata ki fadi haka ba

 To ko da bata aikata ba ai dai mutuncin ta ya zube, duk wanda ya aureta kila ba zata wuce gobe ba zai sake ta, da alama ba su da labari ne, shiyasa suka zo shi kuma Appanku yana neman a raba shi da abun kunya a dole ya rike su a daura auren a gurin, ko dai shi yayi sadaka da ita? Wa ta aura dan baro ko dan shara? Ko cikin masu ban ruwan fulawoyin gidan nan

Yasir girgiza kai yana murmushi, ya bude akwatin zinari dake hannunsa.

 Wani ne mai daraja Hajiya, dan'uwan Momy ne da Zinari mahaifinshi yayi sadakinta, na naira miliyan hansi...

A take fitsari an tsirin ya kubucewa Hajiya Kaltume ta cire dankwalin kanta ta aje a cinyar Khairy tana kallon zinarin kamar zata yaga ido....



**** **** **** ****

Bayan Daddy ya rufe motarsa, suka jero tare da yan'uwansa suna tafiya ya ce.

 Mahaifinta yayi dabara ni ma na jidadin haka, ka ga mun tsallake ma duk wani tarko a yanzu, shi kan shi Jamal sau biyu ana saka ranar aurensa ana fasawa saboda fushi da wasu hujjoji da ba su kai ba, mu kuma muna biye masa ne saboda farincikinsa muke nema, amman yanzu ka ga wannan duk ya kau a yanzu

 Gaskiya haka ya fi, ka ga an huta da fitinar Hajiya Turai

 Daman fitinarta ai zan iya da ita, matata ce fa abun da dai nake tsoro ta canjawa Jamal din ra'ayi gaba daya

 Wannan gaskiya ne

Cewar Alhaji Sadiq. A falon Nene suka zauna gaba dayansu, sai Daddy ya sa a kira masa Captain dake dakin sama tun safe be fito ba, kamin ya fito Daddy ya kalli Momy Ikilima ya ce.

 Ikilima ki shiga gurin Turai a cikin kayana akwai wata shadda irin wannan ta jiki sabuwa ce a cikin leda, a dauko ta ta hado miki da sabuwar hula, da turaren da ba a fasa ba

 Toh Yaya

Ta tashi ta fice, domin bangaren da Daddy yake sauka dabam idan ya zo gidan. Fitarta da minti biyu Captain ya shigo falon, a kasa ya zauna ya gaishe da iyayensa.

 Ya karfin jikin Captain

 Alhamdulillah daman stress me kawai Abba na ji sauki

Ya amsawa Alhaji Munzali, kamin ya daga kansa yana kallon dinkakkiyar Shaddar dake Ikilima take mika masa, ya saka hannu biyu ya karba.

 Shiga ka yi wanka ka saka wannan shaddar ka feshe turaren nan gaba daya a jikinka

 Daddy why?

Ya tambaya da confused.

 Ina son ka raka ni airport ne kuma ina son mutane su ga yarona cikin mutunci, kuma karka dade ka fito yanzu nan ina jiranka

 Toh Daddy

Captain ya mike tsaye ya fice daga falon na Nene. Dakin da ya zama masaukinsa ya shiga ya cire tufafin jikinsa yayi wanka ya fito ya shafa mai ya saka shaddar ya dauko turaren ya feshe jikinsa gaba daya sai da kwalbar turaren ta kai kasa sannan ya dauki hula ya saka a kasan shi kansa, ya dubi kansa a jikin madubi shi kanshi ya san yayi kyau abun da ake kira da kyau, farar shaddar ta haske shi matuka... Wayarsa ya dauka ya saka aljihu da wallet dinsa sannan ya nufi kofar dakin ta bude ya fita yana wani irin kamshi mai sanar da zuwansa tun kamin ya iso. Ga mamakinsa sai ya samu babban falon na kakarsa a cike da mutane ciko har da mahaifiyarsa da kakarsa da abokiyar zamanta da duka wanda yake gidan a lokacin. Da mamaki ya sauko falon yana kallon kowa kowa kuma yana kallonsa...

 Zo nan Jamal...

Daddy ya fada yana murmushi, Captain ya nufi gurinsa sai Daddy ya mike tsaye ya saka hannunsa aljihu ya ciro goro da dabino ya ce.

 Bude min hannunka... 

Captain ya bude tafin hannunsa na dama ya mikawa Daddy, sai Daddy ya zuba masa dabino da goro dake hannunsa.

 Mun je jaje, kuma mun roki iri, kuma an ba mu, na nema maka auren Hurriya a yau, kuma an daura mun bada zinari na miliyan 50, a matsayin sadakinta, saboda dka fada mana mai tsada ce, shiyasa muka siye ta da kima, yau mai tsada ta zama mallakinka, Hurriya ta zama matarka halak malak...

Kamar an aje hoto haka falon yayi tsit kamar babu wani abu mai rai a ciki, daga Captain har iyayensa babu mai motsi....



MASU KARATU BA BIYA A ZO A BIYANI HAKKINA A SAUKE NAUYI A HUTA

500 to Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
42

Da farinciki Appa ya shiga dakin Momy ya nufo inda take zaune fuskarsa da annuri ya zauna gefen gado. Da mamaki yake kallonsa daman kam mamakin kiran da Daddy yayi mata ya karbi sarka be gama fita mata ba.

 Alhamdulillahi

 Allah abun godiya

Ta amsa sannan ta kalli goro da dabinon da ya shigo da su gabanta na faduwa.

 So da yawa kanyi abu basan alherinsa ba sai a gaba, wani abun kuma Allah ya barwa kansa sani, ban tana jin farinciki da alfahari da aurenki ba sai yau, Allah ua miki albarka Nafisa sanadinki yau na fita bakinciki an shafe min duk wata damuwa da nake jinta a raina saboda faruwar abubuwan nan

Momy ta yi murmushin rashin gamsuwa.

 Daman ai Yaya akwai karanci, wani abun yayi maka ko?

 anki Jamal kuma dansa ya nemawa auren Hurriya, kuma be bar gidan nan ba sai da aka daura auren

Momy ta kyalkyale da dariya har da daga kafa sama da buga a kasa.

 Yau kuma ni ake yi ma zolaya, taya za'ayi daurin aure a cikin gida ba mu sani ba kuma daga kai sai yan tairarun mutane? Kila dai aurenka ne za a daura ko kake min kwano kwano

Appa yayi murmushi mai kyau.

 Shi aure ai ba dole sai an tara mutane ba, amman amsu aikin gidan nan da yayanta Yasir sun shaidin auren Hurriya aka daura da Jamal a yau, kuma yayanki ya bada Zinari a matsayin sadaki

Ya aje mata goro da dabino na daurin auren a gadonta.

 Kin ga goro da dabino nan!

Ta kalli goron da dabino har lokacin dariya take domin maganar Appa ba magana ce mai kama kai ba, sai dai kume? Appa ba zai mata wasa ba, ba zai ce anyi ba alhalin ba ayi ba. A take dariyar ta bace mata bat ta daga kai ta kalli Appa.

 Da gaske Alhaji? Yayana ya zo gidan nan ya nemawa Captain auren Hurriya?

 Har an daura, yace ba zai iya da rigimarki ba, dan haka ya wuce yace ni na sanar miki....

Momy ta mike tsaye wayar dake cinyarta ta fadi kasa.

 Aure Alhaji? Auren Hurriya aka daura da Captain?

 Kwarai, kowa ya ji zai yi mamaki, kuma tabbas Alhaji Turaki ya kai mutumen kirki har ya wuce, ya yaye min bakinciki kuma na yarda zai rike yata da amana

Momy ta dafe zuciyarta.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un
La'ilaha Illallahu Muhammad Rasulullahi Sallalahu Alaihi Wassalam

Appa ya bita da kallon al'ajabi ganin yadda ta yi kamar wadda aka fadawa mugun abu.

 Yanzu duk matan duniyar nan Captain ya rasa wa zai aura sai Hurriya? Yarinyar da duniya ta gama ganin tsiraicinta? Yarinyar da ko ido bata shi a yanzu? Anya Captain yana cikin hayyacinsa?

 Ita Hurriya ba mace ba ce? Da kike fadar ya rasa wa zai aura sai ita? Wane irin magana kike haka ne Nafisa?

 Captain ya fi karfin Hurriya bata cancance shi ba, rantsuwa fa na yi cewar Captain ba zai auri Hurriya ba, shi ne Yaya zai shammace ni? Kuma ya biya sadakinta da zinarina da ban taba sakawa ba? Naira miliyan hansi akan makauniya yarinyar da duniya ta gama da ita?

Appa ya mike tsaye ya daga hannu kamar zai mari Momy sai kuma wata zuciyar ta hana shi, a madadin haka ya nunata da yatsansa.

 Ki san abubuwa da kike fada akan Hurriya, kamar kin mace a gaban waye kike tsaye ni fa na haifi Hurriya, a madadin ki yi farinciki jininki ya auri jini sai ya zama abun bakinciki a gurinki

 Idan kai ne mahaifin Hurriya sai me? Na yi farinciki an an'uwana ya dauko yar kishiya ya kawo a matsayin suruka? Ya tsallake Namra ya tsallake duk yaran family ya fada gurin Hurriya

Appa yayi murmushi yayi girgiza kai.

 Yanzu na fahimci komai, Allah ya huci zuciyarki yara kuma Allah ua ba su zaman lafiya... 

Appa yayi dariya mai sauti ya fice daga dakin. Momy ta dora hannu a kai tana ta rawa kamar mai jin sanyi.

 Daman wannan ne dalilin zuwa? Har kana fada min Captain ya hakura? Ni kake yi ma wayon Yaya? Ko ba zai auri Namra ba me yasa zaka amince masa ya auri Hurriya? A cikin falona za a nemi auren yar kishiyata ba yata ba, duk tarin dukiyar Yaya da ta matarsa a aya da suke ji da shi ya rasa wa zai aura a duniya sai Hurriya?

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login