Showing 186001 words to 189000 words out of 279257 words

Chapter 63 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34667

duk na minene? My mind is telling me son yarinyar nan kake a boye Captain? Is that the reason da yasa idan na yi maka maganarta kake fushin dina away? Ba abun kunya ba ne a gareki ka yi soyayya da yarinyar da ni na fara? You betrayed me Captain....

Salim ya juya gurin Hurriya dake tsaye ya kalleta.

 Thank you da kika rufe kofafin soyayyarki a gareni, na gode da baki ba ni damar dandana bakinciki da yanzu ya zame min abun kunya ba, ashe kin san tarayya kike da cousin dina Adam shiyasa baki karbi soyayya ta ba, tir da ke babu uban da zai so mace mai two face irinki green snake under green grass, kowa ya san wacece ke yanzu


Duk wata kalma da Salim ya fadawa Captain be dago ya kalleshi ba har sai da ya kai ga taba Hurriya. At that time Captain ya kalleshi sai kuma ya daga kansa sama ya kyalkyale da dariya ya daga kafarsa sama ya buga a kasa.

 Hahahahaha Salim.. Haba Salim....

Ya sauke kan ya kalli Salim kamar bakin maciji da ke shirin yin sara. In less than second Captain ya mike tsaye ya cire bindigar jikinsa ya taka ta isa gurin Salim ta dora masa bindigar a kasan makoshi ya daga kansa kasa.

 One bad word for her, sai na tashi kanka sai dai ni ma a kashe ni, and you know i can do it...

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Namra ta dora hannu akai, Momy kuma ta fashe da kuka ta nufi Captain ta rike shi ta ja shi baya, tsoro take ayi kisan kai a gidanta.

 Ba ni ba kai Jamal daga yau... Kuma duk wani abun da yake da alaka da kai na datseshi daga yau ba nan nigeria ba har wanda yake Ethiopia...

 What are you waiting for?

Captain ya furta a kakkausar muryar as his responsed ga Salim. Salim ya kalli Namra ya kalli Captain yayi murmushi sannan ya fice daga falon.

 Na rasa gane me yake faruwa? Me kika aikata wai?

Hurriya na jin tambayar da ta fito daga bakin Momy ta san fadan gurinta zai dawo, sai ta juya zata bar gurin Captain ya ware kafarsa yaja yayi hanzarin rikota ya jefar da ita kan kujera.

 Ban aikata komai ba Wallahi ni ban yi soyayya da Adam ba...

Captain ya ciro wayarsa ya kunna data ta sauke hotunan da Salim ya turo masa ya jefawa Hurriya wayar. Hurriya ta dauki wayar da sauri ta duba, duban da take da ma ace idonta ya rufe gaba daya bata ga komai ba, wani tashin hankali da gurbacewar rayuwa a hango a cikin wayar, idanuwanta suka yi arba da makwafin mutuwarta, da gaske ita ce din ko mai kama da ita? Adam take gani Adam din da ya zame mata fitina a rayuwarta, yaushe ta dauki hoto da shi? A ina? Da yaushe? A lailai a yau ta gane wani garin ya fi gaban kuku, domin kuka ko kadan be kusanto idonta ba hawayen da yake ma a yanzu sai suka tsaya cak.... Tun tana ganin hotuna daidai har suka koma mata biyu ta gizon yayi yawa suka rabu gida uku, ta dago kai sai ido ya mamaye ilahirin idanuwanta bata iya jin sautin komai saboda an dauke jinta a lokacin, wayar dake hannunta ce ta fara faduwa kasa sannan jikinta ya bi baya, daga Momy har Namra da Captain suna kallonta har ta jikinta ya kai kasa kanta ya bugu numfashi yayo halinsa, aka rasa mai riketa. Momy ta karasa ta dauki wayar ta duba

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Shi ne abun da ya fito daga bakinta tana rufe ido, Namra ta karaso gurin da sauri ta karbi wayar ta duba, bata gama ta tantancewa ba Captain ya karbe wayar a hannun Namra, ya duka ya kai yatsansa biyu ya taba wuyan Huriyy, sannan ya dago

 I will be very happy idan na samu babu hannun kowa a cikin nan

Momy ta dauke shi da wani kallo.

 Baka ma yarda ta aikata ba kenan? Kuma idan sheri aka yi mata mu kake zargin mun aikata mata right?

 Wutar data halba a zuciyata ba zata bar ni na yarda ta aikata hakan ba, kuma kowa abun zargi ne a gurina because kowa yana da target dinsa akan Hurriya, and the innocent soul a saw in her ba zata aikata ba, akwai wanda ya shirya wannan abun..

 Kuma wani nan kanwar ubanka ce uwa daya uba daya ko?

Ya dafe kansa.

 Momy please...

Kamar wanda magana ta karewa a baki haka ya yanke kalamansa ya kasa kara wani furucin ya fice daga falon.

Momy ta juyo ta kalli Namra cikin tsananin takaici da bacin.

 Wai ni Captain zai zarga?

Namra ta duka ta taba Hurriya dake kwance a suma kamar gawa tana fadin.

 Kamin mu yi tunanin abun da Captain yayi mu kai yarinyar nan asibiti bata motsi fa

 Ke da kika ji zaki iya sai ki yi, ni ko mutuwa ta yi a yanzu Alhamdulillah, zamanta a nan be kara mjn komai ba sai bakinciki da damuwa, dramer queen

Momy ta saka kafa ta take ta wuce Hurriya ta haye sama, Namra ta bita da kallo kamin ta kalli Hurriya hankalinta a tashe. Da gudu ta nufi kitchen ta kunna tap ta dauki roba ta zubo ruwa ta zo ta zubawa Hurriya ta girgiza ta amman shiru.

 Hurriya Hurriya...

Ta kara mata ruwan ta sake girgiza ta nan ma shiru, tsoron kar ta mutu a gurin ya saka ta tashi da gudu ta fice daga bangaren Momy zuwa bangaren Hajiya Kaltume, and abun mamaki ta isa gurin a daidai lokacin da Khairy take nunawa Ruma hoton Hurriya.

 Ba sai kin fada mana ba, mu ma mun gani video ta is all over the internet...

 Ba wannan ya kawo ni ba

Namra ta kawar ma Khairy kai ta nufi stairs tana kiran sunan Yasir domin ta san shi kadai zai iya taimaka mata a yanzu.

 Ya Yasir ya fita Yaya Namra

Ta juyo ta sauko da sauri.

 Dan Allah zo ki kama min Hurriya mu kaita asibiti kar ta mutu, faduwa ta yi kuma bata motsi

Ruma ta mikawa Khairy wayar da sauri ta bi bayan Namra suka fice a falon cikin tsananin tashin hankali. Khairy ta bi su da kallo then ta maida idonta kasa tana kallon wayarta dake hannunta. Contact dinta ta shiga ta yi dialing number Adam sai kuma ta yi saurin yanke kiran ta fadi zaune kan kujera kamar mai mamaki.





CAPTAIN JAMAL POV.

 Wasu hotuna zan turo maka yanzu, ina son ka yi aiki mai kyau akansu ka gano min idan editing aka yi, kuma ina son ka bincika a ina aka dauki hoto nan kuma ka gano ne waya watsa hotunan a media

 Okay Sir

Ya sauke wayar daga kunnensa ya shiga Whatsapp ya aika masa da hoton sannan ya goge su a wayarsa, ya saka wayar aljihu ya nufi gaban teburinsa ya dafa teburin ya rumtse ido....

Zuuuuuu zuuuuu wayarsa dake aljihunsa ta yi vibration alamar kira, ba tare da ya bude idon ba ya saka hannunsa aljihun ya ciro wayar, bude idonsa ya kalli wayar shi ne abu na biyu da yayi sannan ya kara wayar a kunnesa kansa ya mugun tsarawa har yana jin jiri.

 Salam

 Captain me ya hada ka da Momy?

Ita ce tambayar da mahaifiyarsa Hajiya Turai ta fara yi masa a madadin amsa sallamar da be karasa yi ba. Yana jin haka ya san Momy ta yi magana da mahaifiyarsa kenan.

 Ammy ba zan iya miki bayani yanzu?

 Why? And she told me to wannan yarinyar kake so is that right?

 YES

Ya amsa da manyan baki, sannan ya mike tsaye gaba daya ya nufi windows din office din.

 I Love her unconditionally Ammy, ni ma ban sani ba sai yanzu ita ce haske rayuwata! Amman wani yana kokarin shata layi mai hudu a tsakaninmu, and the most painful thing is yarinyar tana shan wahala rayuwa, i just..... 

Yayi shiru, sai Ammy ta karasa masa.

 You just want to marry her and make her a princess? Haka zaka fada min?

Ya kalli green grass din dake harabar windows din ya girgiza kai.

 Not a princess but a QUEEN....

 That's back then ban da yanzu, ko a da can idan ita ce ba zan yi farinciki ba, sai dole, ka tafi ka bawa Momy hakuri kuma ka watsar da lamarin yarinyar nan? Is not your type

Ya kai hannunsa ya taba saitin zuciyarsa.

 Har yanzu tana nan cikin zuciyata Ammy, wutar son yarinyar nan sai ruruwa take a zuciyata little bit confused little bit angry

Daga can cikin wayar Ammy Ammy ta yi dariyar da ta fi kama da almara.

 Captain ka fara fita hayyacinka ne? Are you crazy?

Yayi shiru for some seconds.

 Ammy zai fi idan ba mu maganar nan a yanzu ba

 Why?

 I'm felling dizzy...

Ya rike haif curtains din dake jikin windows yana jingina kansa jikin glass window...

 Where are you?

Amsar da be samu bata ba kenan ya wayar hannunsa ta fadi kasa, ya rike curtains din da karfi sosai yana runtse ido ya bude be daina gani dizzy ba, Curtains din cirewa suka yi suka fado sai dai Captain ya rigasu isa Kasa...!


Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
37
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/COM8NE7rDs8HAG0Oqfr9wm


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cik??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????in aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


Da sauri ya rikota tsoro ya cika zuciyarsa na abun da take kokarin aikatawa.

 Hurriya kashe kan ki zaki yi?

Ta daga masa kai tana kuka.

 Mutuwa ta fi rayuwata a yanzu

 Rayuwarki tana da amfani mana Hurriya karki kashe kanki

Yayi saurin kankameta ya saka a kirjinsa.

 Ban Aikata ba Jamal ban aikata Wallahi ban aikata ba, ban aikata ba, ban aikata ba

Shi ne abun da take ta maimaita sai ya daga kansa sama yana kallon ruwan da aka sako ba tare da hadari ba...

 Captain... Captain

Ya bude idon a hankali har a lokacin dizzy yake gani kamin fuskar Momy ta fito masa clear, duka hannayensa biyu suna rumgume a kirjinsa dayan mai drip dayan babu.

 Sannu...

Ya kalli wata yar'uwar mahaifinsa dake tsaye a kansa, a lokacin ne ya gane mafarki yake na rumgume Hurriya da kokarin hanata aikata kisan kan da take son yi. Maida idon yayi ya rufe zuciyarsa na wani irin fisga. Momy ta kai hannu ta taba kansa

 Jikin nasa babu zafi kuma

 To Doctor ya kamata a kira, sun ce idan ya farka a kira su

Cewar kanwar Momy Hajiya Ikilima, Momy ta mike tsaye tana rike da wayarta dake ringing.

 Namra ce

Ta fada sannan ta amsa wayar

 Eh ya farka..

 Ita ma sai yanzu ta farka

 To yayi kyau sannu da kokari uwarta, ta farka ba dole sai kin sanar da ni ba

Captain ya bude idon tun gabanin Momy ta yanke wayar.

 Bari na kira likita

Momy ta fice da sauri domin kiran Likita, Hajiya Ikilima kuma ta zauna a gurin da Momy ta tashi tana kallon Captain da ya tsayar da gudun ruwan ya cire drip din hannunsa ya sauko da kafafuwansa.

 Ina zuwa? Kai da ka tashi yanzu? Hankalin kowa a tashe yake tun jiya baka farka ba sai yanzu, saboda yana asibitin sojoji ne suka hana kowa shigowa sai ni da Alhaji Usman suka bari sai kuma Hajiya Nafisa

Be ce mata komai ba ya sauko daga kan gado sai ta mike tsaye ta rikoshi.

 Ina zaka je wai?

Be samu amsa mata ba, Hajiya Turai ta turo kofar dakin ta shigo tare da Mijinta Engr Aliyu Turaki, Ammy ta jefar da jakarta ta rumgume Captain da sauri tana kuka sosai. Sai a lokacin ya samu kuzarin yin murmushi cikin nauyin baki ya ce

 Ammy I'm fine

 You're not... Baka taba suma ba tun da na haife ka, kuma ka dauki lokaci baka farka ba, na tsorata da na rasa ka ban san ya zan yi ba

Cikin kuka take maganar tun a jiya da ya kasa amsa tambayarta take cikin tashin hankali har zuwa yau da ta yi zuwan da bata shirya ba, ta dago tana shafa kansa ta taba jikinsa.

 Me yake damunka? Me kake ji?

Yayi baya baya ya zauna yana kallon mahaifinsa da ya kasa cewa komai sai damuwa da tsantsar kulawa ke dawainiya da shi.

 Ya jikinka Jamal?

 Na ji sauki Daddy, da ba ku zo ba ai Momy ta isa ga Momy Ikilima ma sun wadatar

 Da ba mu zo ba, hankalinmu ba zai kwanta ba

Daddy ya fada yana kai hannu ya taba kan Captain cikin tsananin so da kauna. Ammy ta shafa kansa da fuska tana taba ko'ina na jikinsa hawaye na sauko mata.

 Na yi waya da Dr George na saka Mustapha yayi booking appointment tun a yau, ko da ka farka ko baka farka ba zan mu fitar da kai England a duba lafiyarka

 Ammy wannan duka na minenen? I'm

Ta girgiza kai tana kuka sosai tana shafashi ji take kamar ta bude cikinta ta saka shi ciki ta rufe, tsoro take kar ta rasa a aya tilo da Allah ya mallaka mata iyakar zamanta a duniya.

 You're not sauran kadan ni ma na mutu a jiya, da na kira Momy ka ta zo kuma na kira abokan aikinka suka shigo suka fada min ka suma, na fi son na tabbatar da lafiyarka... 

Yayi murmushi a kokarinsa na karfafawa iyayen nasa guiwa.

 Ba zai wuce stressed ba, kin san yanayin aikin Ammy babu hutu kullum

 To zaka aje aikin da daga yau...

Daddy ya fada kai tsaye da fuskar dake nuna ba da wasa yake ba, Captain yayi masa kallon mamaki.

 Is this a joke?

 No... I have alot of money, ina da arziki ina da dukiya ina da hannayen jari dabam dabam, ina da Campany's ba daya ba, ina kasuwancin jiragen ruwa Alhamdullah... Ina da komai Jamal kai ka zabawa kanka wannan aikin ba dan ka rasa komai ba, kuma ba dan bana bukatarka a cikin kasuwanci na ba, ina da arzikin da har ka mutu ba zaka iya cinyewa ba, har jikokinka sai sun gada, fada min akan wane dalili zaka wahalar da kanka? Idan har wannan tarin duniyar bata hana ka gajiya ba da samun hutu miye amfaninta?

Wannan karon dariya yayi mai sauti ya kama hannayen mahaifiyarsa da suke fuskarsa ya rike yana kallonta.

 Na musu alkawari ina lafiya, kuma zan kara samun wata lafiyar dan Allah ku kwantar da hankalinku

Ya rumgume mahaifiyarsa tana kuka har lokacin. Momy Ikilima dake kallonsu gwanin sha'awa ta ce.

 Dole hankalinsu ya tashi, mu ma hankalin mu ya tashi balle kuma su? Kar ka ga laifinsu

Ya kalleta yana murmushi kamin ya kalli Momy wanda ta dawo dakin tare da Likita.

 Hajiya Turai ashe kun iso?

Ammy ta dago ta kalleta fa jajayen idanuwanta tana share hawaye.

 Eh mun iso Sannu da Kokari Hajiya Nafisa

 Haba dai? Sai ka ce wata bare?

Cewar Momy sannan ta nufi gefen gadon tana yi ma Captain ya jiki. Likitan ya duba shi da kyau sannan yayi masa sannu.

 Rashin hutu ne kawai yake damunsa, akwai bukatar ya samu ya huta kuma ya bi dokokin maganin da zamu dora shi akai da kuma shawarwari

 In Shaa Allahu zai bi mun gode Likita

 Allah ya bada lafiya

Cewar Likitan sannan ya nufi kofa, Captain ya kira sunansa.

 Dr Rafiq ko zaka taimaka ka ba ni sallama yau? Idan ba haka ba iyayen nawa ba za su yarda stressed ne ba kawai, kuma ba za su bar ni na huta ba

Likitan da aka kira da Dr Rafiq ya dawo ya dauki takardun Captain yayi rubutu akai yana murmushi.

 Zai iya bari asibitin a duk lokacin da ya so

Sai ya fice daga dakin sannan Ammy ta girgiza kai.

 Ni ban yarda da wannan asibitin ba, ba ayi wani gwaji ba'a duba komai ba kawai ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login