Showing 117001 words to 120000 words out of 279257 words

Chapter 40 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34697

shigo, wata kila ma ita ce take kiranka kasan sarauniya ce wani lokacin sai dai ta kira ta tambaya abun da kake so ta zo maka da shi, ba kamar mu da bama raina lada ba

 Aa ba ita take kira ba, wani.... Sakatarenmu ne... 

Ya amsa kamar marar gaskiya. Cikin rashin kuzari na abun da ya faru ta kora masa da bayanin abun da Hurriya ta yi har Hajiya Binta ta aiko musu da sako. A take Appa ya hade fuska ya bata rai sosai daman a yanzu baya ganin farin Hurriya sai bakinta.

 Wai yarinyar nan me take son zama ne?

 Toh ka gani dai idan baka daukar mata mataki ba, sai ta lalace kuma nan gaba ba a san me zata yi ba, kai kanka idan baka dauki mataki ba sai ta hada ka da Hajiya, kara tun wuri ka rabata da gidan Hajiya ka maida ita can gurin uwarta ko kuma ka dawo da ita nan din, domin ni dai ina jin tsoron shairin yarinyar nan, kara nan tana karkashin kulawarka zaka saka mata ido

 Bana bukatar Hurriya a gidana

Appa ya fada a fusace.

 To ya muka iya da abun da ya fi karfin wuta, in ji kishiyar konanniya, hakuri zaka yi tun da hannunka baya rubewa ka yanke ka yar kar dai ta zauna gurin uwarta ko gidan nan, nan din ma zai fi saboda Hajiya zata iya cewa ba zata zauna gurin uwarta ba, kuma idan ma ta zauna can zata iya sulalawa ta koma gidan Hajiyar ba tare da saninka, kara tana gabanka kana ganinta, albashi ka samu ko masinja ne cikin ma'aikanta ka aura masa ita mu huta...

Uffan Appa be sake cewa ba ya bata rai sosai, domin sam maganar da Hajiya ta fada masa na abun da Hurriya ta yi be masa dadi ba

5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5??


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


5??5??5? ?5?? 2? 1??



Appa be raba dayan biyu ba Momy ta turo kofar dalon ta shigo, yadda ta tararda Appa da Hajiya Kaltume a kujera daya ya saka ta daure fuska ta fara wani kallo na uku saura kwata.

 Miye haka Alhaji? Ina ce yau dai girkina ne, ko kuma irin abun da ake yi ma Iyami shi za'ayi min?

Hajiya Kaltume ta tabe baki, har ta juyar da fuska sai kuma ta juyo ta kalli Momy.

 Magana ce ta kawo ni, maganar da zata taimake ke ki ta taimake ni kuma ta taimaki wanda muke neman aljanna karkashin kafarsa, magana ce akan Hurriya kuma yarki aka aiko da sakon shi nake fadawa Alhaji

Momy dake tsaye ta dauke kai domin haka be gamsar da ita ba, cikinsu babu wanda yake son ganin abokin zamansa a bangaren mijinsa idan ba girkinsu ba ne, sai dai Iyami suna mata haka, su kam shiga su yi magana da Appa ko da tana ciki wani lokacin har sai Appa da kansa ya nuna musu baya so, ita kuma tana kiyaye yin haka idan ba girkinta ba ne.

 Toh tun da kin fada ai sai ki kama hanya ko kuma maganat bata kare ba ne

Hajiya Kaltume ta yi murmushi kamar ba ita ba.

 Nafisa... Hajiya Nafisa... Ya fa kamata ace mun aje kishi a yanzu, ya kamata ace mun san girma ya kama mu a yanzu, ni idan ma kina son kwanan idan girkina ya zagayo ai sai na yafe miki, ni dai ina neman mafita ne acikin lamarin nan, domin Hurriya ba ni kadai ta sako a gaba ba har da ke.. Da kuma mahaifinta, wata kila nan gaba kadan idan tana zaune a gidan Hajiya zata iya sakawa ta tsine mana gaba daya, ko kuma ta cilastawa Alhaji rabuwa da mu

Appa yayi karaf ya ce.

 Aa Hajiya ai tana da hankali da tunani, ba zata yi haka ba

 Baka da tabbaci kai kanka idan aka fada maka Hurriya zata aikata abun da zai saka ka koreta a gidan nan zaka yarda? Amman da yake butuluce kamar uwarta ai gashi nan ta je ta zage ka a wani gurin ta saka makota suna maka kallon azzalumi, nan gaba kadan kuma baka san abun da zai biyo daga gurin Hajiya ba, kasan dai yadda take son Hurriya take daukar shawararta

Sai a lokacin Momy ta kai zaune, bayan Hajiya Kaltume ta gama rattaba bayannanta.

 Ni abun da nake gani kawai ka yi hakuri ka dawo da ita gidan nan, idan ba haka ba ma zata iya lalacewa

Momy ta dubi Hajiya Kaltume ta ce.

 To miye amfanin korarta da Alhaji yayi? Ai sai ta dawo ta cigaba daga inda ta tsaya tana hada mutane

 To ai mun san halinta yanzu, ko da ta fada ba zamu yarda kuma dole a ja mata kunne

 To sai dai idan bangarenki zata zauna, ni dai na gaji da zamanta a gurina, balle kuma yanzu

 Aa ni da take kallon a matsayin makiyiyarta, ta ina ma zata yarda ta zauna a gurina

Appa ya gyara zama ya kallesu one after the other ya ce

 Kar wanda ya sake bani shawara ko zabin gurin da Hurriya zata zauna, idan har zan dawo da ita cikin gidan nan a inda nake son ta zauna zata zauna, daga gidan har ku da yayanku a karkashin ikona kuke, musamman ke Nafisa na lura da bakinki ba shi da linzami akan irin wannan maganar, kai tsaye kike furtawa, na yi miki kashedi amman baki ji ba, wata kila sai kin ga zahiri... 

Da mamaki Momy ta kalleshi bakinta a sake ta ce.

 Allah da iko yake, in ba dan ana son a maida laifi gareni ni da aka raina ba, ai Kaltume ma ta yi maganar ba zata zauna a bangarenta ba, amman sai ni kake yi ma radda wato ga ni itace mai dadin hawa, to Allah ya baka hakuri ta zo ta zauna, daman korar ai ba ta Allah da Annabi ba ce, tun da ga shi har kuna son a dawo da ita

Appa ya dakawa Momy tsawa domin ita kadai ce yake yi ma fada a yanzu, Hajiya Kaltume kuma an saka masa tsoronta ko da ta yi ba daidai ba ba zai iya magana ba, and ba zai iya bijirewa umarninta ba.

 Nafisa... Akan yayana zaki iya janyo wa kanki masifar da zata daukeki daga gidana, bana son ana aibanta min yaya dukansu, ki sani Hurriya ko kisan kai ta aikata Hurriya Haruna Mai Yadi haka za a kirata babu wanda ya isa ya kankare wannan, kin fara kai min hanci kuma ina daf da fyatoki, idan baki rike rike girmaki ba, baki dauke idonki akan Yayana ba za ki sha mamaki

Hajiya Kaltume dake murmushi cikin rai, ta kalli Appa da ciki wani yanayi dake nuna da gaske take yi ta ce

 Haba Alhaji yanzu saboda Hurriya sai ka ce zaka fadi wani abu marar dadi akan Nafisa, adai yi hakuri shekara nawa ana tare, yanzu ga yaya sun girma ana zancen aure kuma zaka bari shaidan yayi tasiri akanka? Kara dai ayi hakuri duniyar ma duka duka nawa take? Ni ko Iyami ban jidadin rabuwa da ita ba, tun da ga yaya biyu ko da yake yanzu Hurriya ce kadai ta rage, amman dai ba dadi ai, da yanzu tana nan da duk ba zamu samu wannan tsabanin ba, tun da yarta taba hannunta

Cikin fushi Appa ya ce
 Ko yanzu ai zan iya kai mata ita, ba dole sai ta zauna nan gidan ba

 Aa kara dai ta dawo nan din, can ga uwa tana jinya abun ai sai ya taru ya zama biyu, wahalar ta yi musu yawa, kana ganin wannan halin da hurriya ta fara idan ba a nan take ba ai kara baci zata yi, ni da kaina zan shirya mu tafi tare a daukota daga gidan Hajiya, ko yanzu ai ta horu

Momy dai bata sake cewa komai ba, domin bata son Appa ya sake furta mata wata maganar marar dadi a gaban Hajiya Kaltume.

 Ni zan tafi bangarena sai da safe...

Appa ya mike tsaye ya nufi dakinsa, kama yadda Hajiya Kaltume ma ta fice daga falon bayan ta yi musu sallama. Duk wani damuwa da tunanin tonuwar asirinta ya gushe a zuciyarta saboda farincikin ganin fadan Appa da Momy. Da murmushi ta shigo bangarenta tana maida kofar dakin ta rufe Kulu ta mike tsaye hannunta biyu a hade tana murzawa.

 Hajiya an fito, na ga ita ma Momyn ta fita shiyasa na zo da sauri, sai kuma aka ce min kin shiga bangaren Alhaji shi ne na ce bari na jiraki

Hajiya Kaltume ta dan yamutsa fuska yayinda ta kawo gurin da Kulu take tsaye da daurin zanenta irin na masu siyar da ganye.

 Zuwanki ai ba shi da wani amfani kulu, kullum babu wani abun da kike kawo wa, tun lokacin da na saka binciken dakin Hurriya baki kawo min komai ba

Kulu ta shiga rantsuwa.

 Wallahi Hajiya na bincike dakin Hurriya kaf har kayanta sai da na duba amman ban samu komai ba, kin ga kuma dole na fada miki gaskiya ba zan miki karya ba

 To yanzu me ya kawo ki?

 Dazun ne ina cikin Kitchen ina wanke kayan da suka ci abinci, kin san Momy bata son a bar kaya ya kwana ba a wanke ba, to ina cikin wankewa sai ga wani bakon Momyn ya shigo, yana ta masifar wai an kori Hurriya Momy bata yi komai ba, har umarni yake bata wai ta dawo da ita, ita kanta Namra da ta saka baki a maganar sai da yayi kamar zai mareta

 To waye shi?

 Ina tunanin dan yayanta domin can da yana zuwa gidan sosai kuma danta take kiransa tana nuna masa so sosai, haka suke ce masa kefin

 Miye alakarsa da Hurriya?

 Toh nima shi ne ya ba ni mamaki ai, na ce ko sonta yake yi, ya ma daina zuwa an fi shekara uku yanzu sai yanzu ya dawo, amman ita ma kanta Momy da Namra ina jin suna tsinewa Hurriyar suna cewa bata da albarka

 Ai dole, tun da ta fara hada munafurci, amman duk da haka ni da kaina zan tafi na dawo da ita gobe, sai na nuna mata hankalin Babba dabam dana yaro, kuma idan za a asake korarta sai daia yi nata korar da zata tafi nesa da garin nan gaba daya, ba wai ta tsaya a kusa da Hajiya ta hada mu ko kuma Appanta ba

 Shi ke nan Hajiya, daman na ce bari na fada miki ne abun da na ji

 Kin kyauta kuma ina son cigaba da abun da kike yi, da zarar kin ji kyas ki zo ki fada min, tun daga kan Hurriya har Nafisa da kasuwancinta

 Toh Hajiya na gode mu kwana lafiya

Hajiya Kaltume ta daga mata kai, sannan ta bita da kallo tana tauna maganar da ta fada mata a ranta. Waye yaje yana masifar a dawo da Hurriya? Sonta yake ko kuma me? Waya sani ma ko kanta take bashi ko yake neman samu saboda ta zama marar aji yanzu, tun da uwarta ta bar gidan, kuma gashi har wani dan iskan ma Adam ya ce yana sonta.

 Hajiya...

Ta juyo ta kalli Yasir dake saukowa yana sanye da jallabiyar da ya siye a Khadeeja Candy Store, sai shinning take kamar an zuba mata mai.

 Yasir ka dawo?

 Eh, na shigo ai baki dakinki Khairy tace kin tafi bangaren Appa

 Eh na je na yi magana da shi ne akan Hurriya, kasan kai baka son laifinta shiyasa ban fada maka abun da ta yi ba

 Kararta kika kai gurin Appa kuma? Haba Hajiya? Duk bayan wannan abun?

 Aa ba kararta na kai ba, sako Hajiya ta aiko mana wai muna takurawa Hurriya magana dai babu dadi ji, ni kuma na je na samu Appanku na bashi shawarar dawowa da Hurriya a gidan nan zai fi, ka ga mun guje bacin ran Hajiya kuma mun shirya ta da mahaifinta

Yasir yayi murmushi dake fitowa har daga zuciyarsa.

 Haka na ke son ki zama Hajiya, kuma na ji dadin haka Allah ya saka miki da alheri

 Amin

Ta kalleshi sama da kasa.

 Yau ka dawo da wuri baka tafi gurin hirar ba ne

Ya dan yi murmushin kunya ya shafa kansa, tare da cira kafa ya nufi dinning, Hajiya ta bishi da kallo na kauna da alfahari.

 Wai ni kam wace yarinya ce wannan mai tsada, har yau baka kawo min ita mun gaisa ba, kamar fa baka daukar komai naka da muhimmanci, ni bana son Miwan da Musib su rigaka aure, ka san kuwa suna dawowa kasar nan babu abun da za su yi sai aure

Kai ya rankwafar alamar damuwa kadan na bayyana a fuskarsa.

 Hajiya, su dabam ni dabam idan ma sun riga ni aure miye a ciki? Komai fa lokaci ne, ni ma kuma yanzu yarinyar da nake jira ta kare karatu kuma ina son na maida hankali gurin gini na da hada kayan lefe, sai dai ni da ita muna tsoron yadda iyayenmu za su karbi abun ne, musamman ma ta bangaren iyayenta

Hajiya ta Kaltume ta nufi gurin da yake

 Miye abun tsoro, ka tafi kanka tsaye ka fada musu waye ubanka a garin nan, dole a karba maka uwarka ma nan gaba kadan za a fara sakawa da ita cikin manya mata yan kasuwa na garin nan ko ma na ce na arewa gaba daya

Ta karasa yayinda ta dora hannunta a kan kujerar da yake zaune. Juyowa yayi ya kalleta da murmushi a fuskarsa.

 Kasuwanci zaki fara Hajiya

 Sosai kuwa, ina son na bude shagunan tufafi masu kyau da tsada, kuma zan bude gidan mai ba da jimawa ba

 Kuma Appa zai yarda?

 Me zao hana shi yarda? Nafisa ma ba kasuwancin take ba? Ina ce nan take siyar da sinari a shagonta ga kuma shagon aski da na gyaran jiki da na cin abinci da take da shi a garin nan, babu mai kalar shagunanta, sai kuma yace zai hana ni? Ai ba zata sabu ba

 Toh Allah yasa albarka kuma ya hadaki da mutane na gari, amman ki kula sosai da wanda zai kula miki da abubuwanki

 Amin, ai kai nake son ka zama shugaba

 No ba zan iya ba, harkar kasuwanci ai sai Appa, ni ko zan iya sai nan gaba, yanzu akwai abubuwan da suke gabana?

 Aure? Tun da na san ka gama karatu kuma kana aiki

Ya daga mata kai.

 Aure Hajiyata

 Wacece to? Da har kake tsoron iyayenta su ki karbarka? Ai babu yarinyar da zaka so a garin nan ita ko iyayenta su ce maka a'a

Ya karkato ya fuskance da kyau.

 Har da Rukayya?

 Ko Wacece kuwa, amman wace Rukayyar?

Sai da yaja dogon numfashi ya aje ya sauke idonta saka dan kar ya hada ido da Hajiya Kaltume sannan ya bata amsar tambayarta

 Rukayya yar wajen Bappa

 Ka kara batar da ni a duhu

 Yar wajen Gwaggo, kanwar Amma, little mom din Hurriya...

 Eeeehhh..... 

Hajiya Kaltume ta dage hannunta da sauri matsa can baya kama wanda ta ga abun tsoro.

 Ba a gidana ba, da yardar Allah ba a gidana ba, duk wani sihiri da suka ma mahaifinka ya kama shi har Iyami ta aure kai kam ba zai kama ka ba, Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, yau na ga bala'i ganin ido... Rukayya kuma yarinyar da ta fi Iyami rashin mutunci da raina mutane? Haba Yasir duk matan duniya ka rasa waye zaka so sai jinin Iyami?

Yasir ya mike tsaye.

 Jinin Amma me ye matsakarsu? Suna da tarbiya suna duk wani abu da ake nema a gidan mutunci, meye matsalar Rukayya

 Bana sonta Yasir, ni da jinin iyami har abada, Hurriya ma rokon nake Allah ya raba ni da ita balle kuma ka dauko min wasu yan baki gida, ba ni ba yan baki gida har abada, kai kanka ba a banza suka barka ba

 Komai dai na magani ne a gurinki Hajiya, kin ce Amma ta mallake Appa da mallaka ce me zai saka ya saketa? Ni dai In son Rukayya kuma ita za aura, matsalata a yanzu na yadda iyayenta za su karbe ni ba, ba kuma saboda kowa mai sai dan ke Hajiya

Ya bar dinning din ya nufi stairs ransa a bace, sometimes ya kan gane kan mahaifiyarsa, ita kam binsa kawai ta yi da kallo zuciyarta na karanta mata cewar ba a hayyacinsa yake wannan maganar ba. Irin abun da aka yi ma Appa ne aka yi masa, wato son suke ta ko'ina su mallake mata da da miji. A ranar da tunani ta kwana washe gari Sallah asuba kawai ta yi ta dauki wayarta ta kira Hajiya Fatee ta fada mata abun da ya faru, kamin ta kira Malaminta ta gabatar masa da bukatar.




HURRIYA POV.

Kafafuwanta a nade fuskarta kuma dauke da kayataccen murmushi take kallon Amma dake cin abinci da kanta, duk kuwa da kasancewar hannun nata rawa yake rabin abincin na zubewa, abun da bata iyawa tun a lokacin da ciwon ya same ta, gaba ta tisa Amma tana ta kallonta kamar zata cinyeta tsabar murnar mahaifiyarta ta fara samun sauki. Bayan Amma ta gama, Hurriya ta dauke plate din da cup din ruwa ta fitar sannan ta dawo ta zauna kusa da Amma.

 Allah na gode maka da ka fara bawa Ammata lafiya

Amma ta yi murmushi domin shi ne kadai abun da take iya yi Idan farinciki ya same ta, idan kuma damuwa ce sai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login