Showing 147001 words to 150000 words out of 279257 words

Chapter 50 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34719

ka dauko mana macijiya gashi nan ta haifa ta bar mana bala'i a cikin gida

Appa yayi murmushi mai sauki.

 Iyami baiwar Allah, matar nan bata da matsala ko kadan, kawai dai anyi daidai da wa'adin auren ya kare ne

 Bayan ita yanzu ba wata zaka dauko ba

Ya kalleta da kamar zai yi mamaki sai kuma ya tuna alakar dake tsakanin yarinyar da yarsa Salma.

 Ina kika samu labarin nan Kaltume?

 Abun duniya ai ba boyuwa yake yi ba, daman komai yayi tsami jinsa ake yi, yaushe Iyami ta rafi mun samu wata firinar ta laba yanzu kuma zaka kwaso mana wata? Haba Alhaji dan Allah kar rashin iyami yasa ka kara aure

 Aa ko kadan, karin aure al'adarta ce, kamar yadda take al'adar Malam Bahaushe kuma Sunna, ko da iyami tana cikin gidan nan zan kara aure, shiyasa na yi bangare hudu ba biyu ko uku ba, ko Iyami na nan ko bata nan wannan abu ne da zan yi kuma ba dan kun gaza a komai ba

Ta saka kuka.

 Amman Fisabilillahi ka rasa wa zaka aura sai karamar yarinyar sa'ar Salma? Ko kunya ba zaka shi ai sai mutane su ce maka mai budurwar zuciya, haka ka yi min daga kawo Iyami aiki a gidan nan ka yalla ido ka aureta, ka saka a unguwa da dangi sai labarina ake yi

 A cikin mutanen da zasu zage ni, akwai mai ba ni naira biyar na kara gurin aikin? Ko akwai wanda na tafi neman abun da zan ciyar da Iyalina a gurinsa? Kaltume wannan kishin fa ba naki ba ne, ina ce idan za'ayi ta uku ta biyu aka yi ma, idan za'ayi ta hudu ta uku aka yi ma, ki bar Nafisa ta yi wannan fadan, kuma aure fa ba zan fasa ba, burina ne aurin mace hudu kuma sai na cija wannan burin da yardar Allah

 Alhaji dawo zaka yi da Iyami kenan? Kuma ka kara aure?

A take Appa ya fusata a yanzu kam ta kai shi kul.

 Idan zan dawo da ita akwai wanda zai hana ne? Me ye matsalarki da Iyami ne wai? Ta bar gidan amman bata fita a bakinki ba? Ban san wani abun da ta yi miki ba bayan alheri, amman kin dauki karan tsana kin dora mata, matar da lafiyar jikinta ma bata wadace ta ba, ba a aure aka haife mu? Ko kuma ba a aure ni na aureki? Kina da yaya shekararmu nawa tare da ke, to miye matsalarki da karin aure, idan mata dari zan aura miye matsalarki da hakan? Akwai abun da na rage ki da shi? Ko kuma da kudinki zan kara auren? Ke ce babba amman kullum ke ce mai fitina ta, na fara gajiya da hallayenki nan Kaltume na fara gajiya, daga ke har Nafisa idan ba zaku gyara ba to ko tabbas abun da ya ci Iyami zai ci ku, ita din ma da bata min komai ba balle ku da kuke neman haddasa min fitina

Ya sauke kafafuwansa ya saka talkaminsa cikin bacin rai ya nufi bandakinsa. Kallonsa ma Hajiya Kaltume bata yarda ta sake yi ba, balle ta furta masa wani abu, gaba daya jikinta yayi la'sar, a take ta shiga sake-saken zuci tana neman bakin zaren lamarin.

 Yau ni Alhaji yake fadawa haka? An samu matsala kenan, wata kila Malam ya fara karya aikinsa ne shiyasa Iyami ta fara tashi? Kuma Alhaji ya fara son wata bayan ya min alkawarin babu waa a zuciyarsa da yake so yake jin tsoron bacin ransa fiye da na uwarsa kamar ni? Saboda yana somu yi min milkin mallaka irin na Hajiya fatee, ni ko ba zan yarda ba, wata kila kuma Iyamin ce ta dukufa a wasu safgogin tun da gashi har yana tunanin dawowa da ita, ko kuma dai wannan fitinannniyar yarinyar ce da zai aura ce ta fi ni iya shiga da fita? Shiyasa har Malam ya ce ta gagareshi sai an tafi gurin Malaminsa? Zata iya mallake Alhaji ta karya duk wani abu da na yi? Waya ni m ko ita take aiko min da faduwa so take na fadi na mutu, ko ma Iyami? Kai Nafisa ma zata iya shiga nata tsabgar fa? Gaskiya zama be gan ni ba, idan ban motsa da wuri ba, za a min Zagon Kasa a lalata min tsari

Haka ta raya dare da tunani kala kala, idan ta yi wannan sashen ta fado wani, ta rasa wa zata zarga da karya mata aiki ko kuma kokarin rabata da mijinta, kamin safiya ta waye har ta tsuma saboda burin da take da shi na tafiya kai kukenta ga wanin Allah. Da asubar fari ta baro bangare Appa sallah ma a bangarenta ta yi, kana ganin idonta ka san bachin da ta yi kadan ne, ga ciwon kafa na damunta. Tana sallame Allah ta dauki wayarta ta kira Khairy bata daga ba, ta kira Salma bata daga ba, ta kira wayar Ruma ita ma duk daya. Bata aje wayar ba ta kira Yasir shi kadai ya dauka

 Yasir

 Hajiya ina kwana?

 Lafiya Kalau dan Allah ka tashi yan'uwanka su shirya mana abun karyawa ina son na fita da wuri

 Okay

Ta aje wayar a kusa da ita ta cigaba da jan carbinta abubuwan da suka gudana tsakaninta da Appa na musayar yawu suna dawo mata yau da asubar nan, har yanzu mamaki take waya saka ta gaba. Ta aje carbin ta rafka uban tagumi kusan bata taba shiga damuwa irin yau ba, ga aure Appa zai kara gashi yana kokarin juya mata baya har yana ikirarin abun da ya sami Iyami zai iya samunta.

 Sallamu Alaiku Hajiya

Ya juya ta kalli kofar dakin tana samawa Yasir

 Ya jikin Hajiya?

 Alhamdulillah

 Zan shirya da wuri sai mu tafi asibitin

 Aa na hutar da kai tare da Khairy zan tafi

 Hajiya saboda abun da ya faru jiya ne?

 Ke nan dai kasan abun da kake kokarin aikatawa ba abu ne mai kyau ba

 Miye abun rashin kyau a ciki Hajiya? Idan ma akwai wani abu tsakaninki da Amma ita Rukayya meye nata a ciki?

 Ai tun da sonta kake yi ba zaka gani ba, ni dai ko tsumma ne wannan tsumma na Iyami ba zan taba sonshi ba, daga Iyami har yayanta har wani abun da yake da alaka da ita ba zan taba son shi ba

Ya mike tsaye ba tare da ya sake cewa komai ba ya fice daga dakin.

HURRIYA POV.

Bata yi irin saka ci da ta yi jiya ba, sai yau ta hana kanta bachi ta fito da wuri ta zauna falo, kusan ita da masu aikon gidan duk daya, domin sai da Momy ta gama karyawa sannan ta nufi dinning ta zauna ta zuba nata abincin ta fara ci, sosai ta cika cikinta sanin cewar da rana ba lallai ne ta samu na damar ci kamar haka ba. Ta dawo falo ta zauna a nan bachi yayi gaba da ita bata farka ba sai sha daya da rabi, shi ma sanadin tashinta da Namra ta yi ne.

 Idan bachi zaki yi ki shiga dakinki mana, kin fi kowa sanin Momy bata son ana nata bachi a falo

Mika ta yi ta mike tsaye tana hamma, tukuna ta fara tafiya, har ta haye stairs din bata juyo ba, kai tsaye ta zarce bandakinta ta yi wanka ta fito daure da tawul ta tsaya gaban madubi tana kallon yadda kashin wuya ke mata ado kamar sarka, ta cikin madubin ta hango Hajiya Binta dake sanye da onion Hijab dinta hakoranta na makka guda suna kyalli a tsakanin hakoranta na gaba. Hurriya ta juya tare da zubawa da gudu ta rumgume Hajiya Binta.

 Hajiya yanzu kika zo

Har Hajiya Binta ta zauna Hurriya bata sake ta ba, tana rike da ita kamar zata shige jikinki.

 Hurriya yanzu nake tafe Hurriya kuma tafiyar taki ce ke kadai

Ta dafa kirjinta dake bugawa saboda murnar ganin Hajiya da ta yi.

 Ni kuma Hajiya? Allah yasa ba fada kika zo yi ba, ki ja min wata rigimar kuma

 Sarkin tsoro tashi ki tura kofar ni ba shi ya kawo kawo ni ba

Sai a lokacin Hurriya ta saki Hajiya ta nufi kofar dakin ta rufe ta dawo ta zauna dafe da Hajiya dake bude hand bag dinta, gorar ruwan sai dai wannan ba ruwa ne a ciki ba rubutu ne cike da gorar ta mikawa Hurriya.

 Hajiya menene?

 Sha zaki yi, ki kasa uku a rana, kuma na kwana uku ne, wannan kuma da nono zaki sha, idan zaki sha safe da maraice, kuma idan zaki sha ki hau kan gadonki ki tsaya a tsaye sannan ki sha tare da bismillah

Ta mika mata dayan maganin da yake kulle a bakar leda, sannan ta dauko mata nono.

 Na san samun nonon zai miki wahala shiyasa na nemo miki tun a can, ki rika amfani da shi kina sha

Ta saka hannu ta karba ta dora maganin a bedside drawer dinta ban da corar nono da ta bari a hannunta ta fara budewa.

 Kuma ban da wasa, ban ce kuma ki aje shi a fili idan aka zo aka gani ki ce ni na baki ba, addu'o'i ma mi rike Hurriya, kana idan kika yi sallah ki roki Allah bawa mahaifiyarki lafiya, ya karkato da hankalin mahaifinki a gareku

Hurriya ta daga ta kai bakinta tana sha.

 Ke ba fa Nonon zaki shanye haka nan shi kadai ba, sai da magani

Hurriya ta saka dariya.

 Na sani ai Hajiya

 Toh na san halinki fa, kar na tambaye ki ce kin manta ba ki sha ba, baki san nawa na biya aka karbo min maganin tsarin nan ba, kuma ta tabbatar min idai Malami zai zauna a kan ruwa be nutse ba, to sannan zai miki aiki ya kamaki, shi ma Tsoho sake na yi ban kula da ba shi irin wannan ba, shi kuma be kula da addu'a ba, ai ko ba dan abokan kasuwanci ya kamata ya nemawa kansa gambun karfe, amman be kula da ko daya ba, wata kila da duk wannan abubuwan ba su faru ba

 Kaddara ta riga fata Hajiya, haka Allah ya tsara

 Haka ne

Hajiya ta amsa sannan ta sauke ajiyar zuciya.

 Ina saka ran zuwa Umara ma wannan wata, da na ce zan daga sai wata na gaba amman ina son tafiyar a yanzu, ko dan na yi muku addu'a, a zan zan roko miki na gari

Ta karashe maganar tana jan kumatun Hurriya, Hurriya ta yi murmushi mai sauki.

 Allah ya kaiki lafiya Hajiya, ya karbi ibada, Hajiya karki manta da Amma

 Ina zan manta da ita kuwa? Zan mata addu'a kuma zata samu sauki da yardar Allah

 Allah ya sa Hajiya, Hajiya tashi mu tafi falo kar Momy tace kin shigo nan kin zauna

 Hurriya

Hajiya ta kirata, sai ta amsa ta dago ta kalleta.

 Ummm

 Nafisa matar ana ce, ba uwata ba, ni nake a matsayin uwa a gareta, kuma na shigo gidan nan ne saboda ke, ba saboda matar da bata dauke ni a matsayin uwa ba, matar da bata san ta taka gidana ba sai idan wani abun ya faru, shiyasa da na shigo na cewa mai aikin ta nuna min dakinki kai tsaye

 Haka ne, amman dai tashi mua tafi falo Hajiya

Ita tsoron take ace ta saka Hajiya Binta a daki ta kulla mata munafurci na gaskiya da karya. Closet ta nufa ta dauko doguwar riga ta zuba ta dauki dankwali ta daura, sannan ta dawo gurin gadon ta kama hannun Hajiya alamar tana son ta tashi su tafi. Murmushi kawai Hajiya Binta ta yi ta mike tsaye domin ta san babba baya biyewa yaro ayi ta jayayya balle kuma Hurriya da bata son musu. Suna fara sauko stairs din Momy da Namra suka dago suna kallonsa a takr Hurriya ta ji wani iri ta kasa daga ido ta kalli kowa har suka sauka.

 Hajiya sannu da zuwa

Momy ta fada dan babu yadda ta iya, if not ba zata gaishe d????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  a surukarta ba saboda bata zauna a falon ba, bata jira an kira mata kowa ba ta shige dakin Hurriya.

 Sannu da gida Nafisa, ya yaran?

 Lafiya Kalau, ya tsufa

 Gashi nan muna ja

Namra ta gaisheta cikin muryar da ke nuna an mata dole.

 Hajiya ina wuni

 Lafiya Kalau

Ta amsa sannan ta zauna. Namra ta tashi ta shiga Kitchen ta dauko mata lemu da ruwa da dan abun tabawa ta aje mata. Ruwan kawai Hajiya ta sha shi ma dan kar Momy ta ce bata sha komai na ta ba. Bata wuce minti talatin a falon ba ta ce zata tafi.

 Da wuri haka Hajiya, na dauka nan zaki wuni, na ga idan kin zo har yamma kike kaiwa

 Irin wacan tafiyar kai tsaye daga gida nake fitowa zuwa nan, amman ta yau daga wani gurin an fito sai na biyo nan na duba ku

Duk suka mike tsaye ganin Hajiyar na ta mike tsaye.

 Allah ya saka da alheri mun gode ai a haka ma, bari na kira Alhaji a waya ina jin be san da zuwanki ba

 Aa ba bukata na fada miki ba zuwan da na saba ba ne, ko bangaren Kaltume ma ba zan biya ba, sai dai wani lokacin

Ta kalli Namra
 Namra an kammala karatu kuma sai mu ji shiru

 Sauran Service, mun kusa zuwa

 Aure nake magana, ga Khairiyyah ana ta maganar duk dai be turo ba amman ke mun ji shiru

 Ni ma ina kusa Hajiya

 Toh Allah ya nuna mana, kuna da labarin Musib da Miwan

Wannan karon Momy ce ta amsa mata da kanta.

 Eh muna waya da su, suna kusan dawowa shi dayan ya gama nasa karatun ma, dayan ne ya rage

 Allah ya taimaka ya sa a ci amfani

 Amin

Ta wuce gaba suna mata Allah ya tsare hanya, Hurriya ta biyota har gurin motarta ta direba ke ja ya kai ta duk inda take son zuwa. Kamin ta shiga motar ta juyo ta kalli Hurriya

 Karki yi wasa da abun da na kawo miki, kuma ki cigaba da hakuri Allah ya miki albarka

 Amin Hajiya, na gode

Ta shiga motar Hurriya ta rufe mata motar tana daga mata hannu har suka fice, sai da ta juyo zata shigo falon sannan gabanta ya fadi.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Ta furta domin faduwar gaba ne da bata saba jin irinsa ba, kuma na zata iya fadar dalilinta na faduwar gaban ba, sai da ta ja dogon Numfashi ta sauke sannan ta shiga falon, kallo daya ta yi ma Momy da Namra ta maida kanta kasa bata sake kallonsu ba har ta haye sama ta shige dakinta.
Namra taja tsaki tana wani hura hanci.

 Gaba daya yarinyar nan ta fita raina, Allah kadai ya san me ta fadawa Hajiya yanzu kin ga tana zuwa bata ko tsaya an kiraki ba ta shige dakinta, ta sauko tana min maganar yaushe zan yi aure wata kila ta fada mata karyar ina mata wani abun shiyasa har take tambayar yaushe zan yi aure

Momy ta tabe baki.

 Komai zata yi, su je su yi ta yi, gida ne dai ba a isa a kore ni ba, ni har wata magana na ji a gurin Hajiya Mardiya

 Wace Hajiya Mardiya?

 Matar Alhaji Shamsu dan masanin tsafe, wai Alhaji zai hada shi da Kaltume tana son ya fara sana'ar crude oil

Namra ta daki kirji.

 What? Hajiyar?

 Ita fa, ni ma nace ko dai ba ita ba tace min ita ce fa, wai har sun fara maganar ma, ita ma mijinta ne ya fada mata

Dariya ta subucewa Namra irin dariyar nan dake dauke da mamaki.

 Hajiya so take sai ta take ki Momy, saboda yanzu daga ke sai ita yanzu, Amma bata nan ganin take kishi ya koma tsakaninku

 Ai ba zai daure ba, ni fa ina da degree a fannin kasuwanci, ita kuma ko primary bata yi ba, kin tana ganin mace da irin wannan kuma tace zata fi ni? Sannan ni arziki na na ubana ne da na gada da kuma nawa da na nema tun yana da rai har bayan ransa, ita kuma yar talakawa ce kamar Iyami, duk arzikin da zata samu ba zai kaiwa ba, domin ita zata samu ne ta karkashin Alhaji ni fa? Kuma kin ga karatun da na Musib ya tafi yi a waje saboda na saka shi cikin ragamar kasuwancina ne, domin idan mu ne yau gobe ba mu ba ne, ita kuma yanzu zata fara kuma dan ta be sha'awar kasuwanci, dana kuma yana da gogewar hakan

 Ita ma Hajiya ina zata iya da kasuwancin Crude oil? Tana mace kuma ita da bata yi karatu ba?

 Ai a duniya yanzu babu kasuwanci dake saurin kawo kudi kamar crude oil shiyasa take son ta fara, amman ina nan dake sai ta koma ko abun da zata daura ya gagareta, ai Iyami ma yanzu ishara ce agareta, ciwon na kwantar da ita ta rasa komai daman can da Alhaji ake tutiya yanzu kuma ba a tare, shiyasa rayuwar talauci bata yi ba Wallahi, ke yanzu kina ganin idan ace Iyami wata shegiyar attajira ce a gidan nan akwai wanda ya isa ya wulakanta mata ya? Kuma kin ga wannan abun da mahaifiyarta akatau a duk lokacin da na kalli yarinyar can ko uwarta na tuna da wannan sai kimarsu ta kara raguwa a idona..

Bata kai zaren zancen ba ta yanke saboda kukan wayarta ta ji, ta juya ta dauki wayarta dake gefe tana ringing, ganin number da ta yi appearing a gaban gilashin wayar ya saka ta yi murmushi

 Captain

Ta yi shiru still tana murmushi kamin ta sake fadar.

 Alhamdulillah, Okay

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login