Showing 165001 words to 168000 words out of 279257 words

Chapter 56 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34661

mutuwa? Ni kawar Salma ce ba makiyiyarta ba

 Kawarta ba zata ce zata auri ubanta ba, mugun kwadayi da dogon buri ya saka zaki auri ubanta tsohon da ya isa haihuwarki, kin ji kunya yarinyar kin ji kunya rayuwarki zata lalace nan gaba, na rantse da Allah sai kin wulakanta

Fada sosai Hajiya Kaltume take yi, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ana riketa ana rufe mata baki amman ta kasa daina saboda zafin mutuwar yarta da take ji, ga kuma silar komai a gabanta tana gani ita tana raye. Hajiya Fatee dake waje ta taso ta shigo cikin dakin ta ita da mutanen dake waje ciki har da Hajiya Binta. A fusace Maryam ta mike tsaye cikin masifa ta ce

 Miye laifina dan na zo gaisuwar yarki? Tun daga garin Naija na taso na zo garin nan saboda gaisuwar Salma, akan wane dalili zaki tara min mutane, to bari jiki na fada miki kanki kika tonawa asiri, domin wanda be san mijinki zai kara aure ba yau ya sani, kin kunyata kanki da mijinki

Tana aje aya Maama ta dauke ta mari, ta kai hannu zata rama Khairy ta rike suka fara dukanta, cikin karfin hali ta fara ramawa ita da cousin dinta aka hau rabasu daker aka kwaci Maryam hannun Maama da Khairy. Hajiya Binta ta dakawa Hajiya Kaltume tsawa

 Wai ke kan kanki farau aure? Wane irin mugun kishi ne yake damunki? Kina babba amman baki san ki tsawatarwa yayanki ba sai dai ki bude musu kofa?

 Hajiya Karki kara min bacin rai, daman kullum goyon bayan dakinki kike baki tana ganin farina ba, ai ni ba wani abun na yi miki ba amman kika dauki tsana da kiyayar duniya kika dora min, ko wani abun na tare miki?

 Magana kike ta rashin hankali da tunani Kaltume, ashe mutuwar Salma bata isheki ishara ba? Girma kike kina cin kasa? Jiya ma danki sai da ya kuka min akan abun da kika yi ma Rukayya, yaro yana son yarinya amman kina neman shiga tsakaninsu saboda bakin kishi da ba zai haifar miki da komai ba? Yanzu kuma kin zo gaban mutane kina kunyata mijinki akan abun da baki da tabbaci? Kuma ko da kina da tabbaci ya kamata ki ci mutuncin yarinyar da ta dauko kafa daga nesa ta zo miki gaisuwa? Kim kunyata kanki kin kunyata mijinki. Shiyasa kullum nake yabon Iyami kun fita shekaru amman ta fi ku hankali, wannan abun da kike yi hauka ne?

 Hauka ne Hajiya, idan kina da magani sai ki ba ni, na gaji da abun da kike min, ba ba ku san me nake ji a zuciyata ba, ba kussn yadda yata ta rasa rayuwarta kun saka ni gaba kuna kunna min wata wutar, na yi kishin kishin halak ne, ni na auri Haruna tun ba shi da komai har ya zama komai, ni nasan fadi tashin da muka yi na rayuwa

Hajiya Binta ta nunata da tsaya rai a bace.

 Karya kike ki fada min wannan, tun kamin a haifeki na ke kula da dana, ni na san fadi tashinsa ba ke ba, ke kullun kara hauka kike ba hankali ba yayanki ma gasu nan kin fara koya musu irin tarbiyarki

Hajiya Kaltume zata sake yin magana wata yayarta ta rufe mata baki, tana bawa Hajiya Binta hakuri.

 Babba babba ne ko yayane, dan Allah Hajiya ki yi hakuri, wani lokacin Kaltume bata iya rike halshe, kar idonki ya rufe Hajiya ayi babu dadi a nan?

 Babu dadi na nawa kuma? Ita da yarta ta mutu idonta be bude ta yi hankali ta natsu ba? Me ye bata fada min ba? Ai wannan yar bata da albarka sam...

Hajiya Kaltume ta mike tsaye ta daki kirjinta dake mata zafi da ciwo a lokaci daya tana kuka mai karfi ta ce

 Ba yar albarka ba ce ni Hajiya Binta, ki aura masa yar albarka ki kawo, ni kuma ki saka bindiga ki halbeni ni da yayana

Hajiya Binta ta kashe ido tana kallon surukar dake mata rashin albarka ta ce.

 Idan kin kwana da aure yau Kaltume na kwana a mace...! Sai na nuna miki ruwan nono ya fi karfin wulakantawar

Hajiya Binta ta kalli Maryam da ke tsaye gefe daya tana karewa Khairy da Maama kallon daukar fansa ta ce.

 Wuce mu tafi yarinya...

Maryam ta juya ta fice tare da Cousin dinta, Khairy da Maama kuma suna jin kamar su rufe Hajiya Binta da duka babu hali, Ruma ce kadai ke rusar kuka saboda abun da ke faruwa baya mata dadi sam. Hajiya Fatee da wasu yan'uwan Hajiya Kaltume suka bita suna bawa Hajiya Binta hakuri amman ba ta sauraresu ba ta fice. Yayarta ce ta dawo dakin tana fadar.

 To yanzu me ye amfanin haka? Jiya kin ci mutuncin yarinya yau kin ci ta wannan yarinyar kuma abun be tsaya iya kansu ba sai da ya kai ga uwar miji? Haba Kaltume, mutuwa tana saka mutane natsuwa amman ke kamar ana turaki?

 Anty Hauwa ki bar ni da bakincikin da yake cikin raina, ni na san me nake ciki, ni na san irin halin da nake ciki

Ta fashe da kuka mai karfi. Maama da Khairy ma sai da suka yi kuka saboda ganin mahaifiyarsu na kuka, daman kuma zafin mutuwar yar'uwarsu be isa barin zuciyarsu ba. Sai bayan Sallah La'asar lokacin mutane sun dan fara ragewa, daman wasu sai dai su zo su yi gaisuwa su tafi, Appa ya aiko ya aiko kiran Hajiya Kaltume tare da Khairy da Maama da Ruma, suna jin haka suka san ba dalilin kiran, Hajiya Kaltume gabanta ko faduwa baya yi saboda zuciyarta ta riga da dake, yadda abubuwa suka riccabe mata bata fargabar faruwar komai a yanzu. Can cikin uwar dakin Appa suka shiga, Appa yana zaune kana ganin fuskarka kasan ransa a nace yake. A kasa Maama da Khairy har Ruma suka zauna, Hajiya Kaltume ta zauna a kujerar sofa daya dake dakin idonta a kumbure ga wani ja da suka yi tsabar kuka da bakinciki da suka rumgume.

 Akan wani dalili yarinya zata zo tun daga nesa ki ci mutuncinta ke da yayanki?

 Me yasa zata zo? Ba abun kunya ba ne dubi kamar kai ace zaka auri kawar yarka? Wato Hajiya ta zo ta tsara maka maka komai, so ake a hada min zafi ta ko'ina kamar ni na haifowa duniya bakin duhu

Ta fara kuka da karfi. Appa ya maida dubansa gurin Khairy da Maama.

 An fada min abun da kuka yi, kuma abun da kuka yi ba kowa kuka yi ma sai ni, ni kuka ciwa mutunci ni kuka wulakanta, sannan kun bar magana a bakin kowa, yar'uwarku ta mutu yau kwana daya amman wuni na buyu amman kuna dukan kawarta saboda ta zo gaisuwa, jiya ma ance kun yi ma Rukayya saboda rashin hankali da kikanci irin naku, to daga sai yau ko kare na kawo kuka tsallaka shi sai na yi muku abun da ba ku taba mafarkin ba, idan ita uwarku kishi take ku me kuke yi? Kar wanda ta sake tunkarata da wata bukata tata na yanke, du wata dawaniniya da nake da ku daga yau ta kare, idan har baku san darajata ba babu amfanin cigaba da yi muku komai, ke Maama ki tattara ki koma gidan mijinki zaman gaisuwa na kashe daga yau, domin gobe ban san abun da za su sake yi ba, ke kuma Khairy ki sani nan da kwanaki kadan zan aurar dake, ke tafi can gidan mijin ki yi hankali

 Appa....

Khairy zata yi magana ya daka mata tsawa.

 Shut up ku tashi ku ba ni guri

Suka tashi jiki na rawa suka fice daga dakin suna kuka. A lokacin ne Appa ya kalli Hajiya Kaltume ya ce.

 Ke kuma ki yi zaman ?a?anki, kin ci mutuncina kin ci mutuncin kanki, kin ci mutuncin yayanki duk haka be miki ba sai da kika tsallaka kika ci mutuncin Hajiyata, matar da ta yi silar zuwana duniya, matar da ta rumgume tun bana iya tsayawa da kafafuwana, to kin kai karshe, ko da ace Hajiya bata ba ni umarnin aikata abun da na aikata a yanzu ba, zan aikata a karan kaina jin abun da kika yi mata Hallayenki sun isheni Kaltume, kin kawo min nan

Ya kama makogaronsa da hannuna yana nunawa.

 Dan haka na iyankance alakata da ke a yau Kaltume, NA SAKE KI SAKI DAYA....


Hajiya Kaltume ta sauko daga kam kujera tana taba kirjinta.

 Ka sake ke ni Alhaji? Ni Kaltume yau ni ka saka? Ehhhhhhh ehhhhhhh ehhhhhhh hmmmmmmmm

Ta dora hannu akai tana dukan kanta kamar wata bayarabe.

 Ehhhooooooooo ehhhhwoooooooo hoooooo ni niiiiiiii hmmmmm kilkilkil ni aka saka? Lallai wani bakincikin sai namiji, bani bakin cikin sai namiji, yata ta mutu kuma ka sake ni, namiji dan kunama Haruna mai siyar da yadi ka ji kunya ka yi abun kunya, yau kam na tabbatar Binta bata kaunata yau na tabbatar da waye kai Haruna mai yadi, Mai yadi Haruna, tun baka da taro da sisi nake tare da kai, tun aka siyar da yadin uku da sisin kwabo, tun kana siyar da yadin mutuwa yadin likkafani nake tare da kai Haruna, yau ni ka saka saboda zaka auri yarinya sa'ar yarka? Lallai namiji ba dan goyo ba ne, namiji dan kunama, duk macen da ta ce namiji uba ne sai ta kwana marainiya

Babu kalar gorin da bata yi ba Appa ba, dan Alhaji ma da take masa alkunya yau bata saka ba saboda bakar zuciyarta ta mutanen farko ta tashi, halin na mata masu bakin kishi da bakar zuciya ya motsa, tana murzar kafa a kasa tana kuka tana ihu arzikinsa daya dakinsa ba mai daukar magana ba ne sai an bude. Appa ya mike tsaye sai ta matsa da jan jiki ta riko rigarsa tana zuba masa rashin mutuncin.

 Ka tsaya mana mai abun kunya, saboda kana takama da arziki, arzikinka na banza, saboda kana takamar kana da kudi sai ka aure yar aiki yanzu kuma zaka auro kawar yarka, kuma duk a ni Kaltume bakincikin zai kare, ni zaka nunawa bakinciki? Allah ya saka ka auro mai farar kafa, idan arzikin ya kare sai ka ga zata zauna da kai ko kuma sai Hajiya Kaltume mai zuciyar karfe? Wallahi sai ka yi nadamar sakin da Binta ta saka ka yi min yau Haruna mai yadi

Appa ya buge hannunta ya fisge rigarsa.

 Albakarcin fadin sunan uwata da kika sake yi da kuma addu'ar da kika yi, na kara miki saki daya, dazun saki daya na yi miki yanzu kuma na kara miki daya, Kaltume NA SAKE KI SAKI BIYU

Hajiya Kaltume ta fadi kwance kasa tana burzar da yawu tana ware hannaye sama kamar wata mai aljannu.

 Shi ke nan na mutun yau an dandana min bakinciki a namiji yau an dandana bakinciki, so ake na mutu gaba daya

Appa ya kabe mata rigarsa ya fice daga dakin yana jin kamar ya kara mata wani sakin, daman abun haka yake idan mace ta yi magani duk ranar da abun ya karye namiji zai tsaneta irin tsanar da be taba yi ba. Ficewa yayi daga bangare gaba daya domin baya son sauraren kalamanta da kukanta dake kara masa bacin rai, kuma baya son hankalin mutanen dake waje ya kai garesu. Yana tafiya hannayensa a baya yana tuna lokacin da ya saki Iyami, yarinya a cikin matansa amman bata yi wannan haukan da cin mutuncin da Kaltume ta yi masa da uwarsa ba, yana tuna lokacin da ya bata takardar sakinta a rubuce ta karba, har ta yi masa addu'ar Allah yasa hakan shi ne mafi alheri kuma ya ba shi ikom kula da Hurriya da Hamad. A yanzu yake tambayar kansa me yasa ya saketa? Why? Me ta yi masa? Me yasa ya rabu da matarsa abar kaunarsa? Har ya isa bangaren na Momy be samu amsar tambayarsa ba. Cikin yanayin damuwa da ya kasa boyuwa a fuskarsa ya murda kofar dakin ya tura ya shiga, ba zai iya fadar abun da ya kawo shi bangaren ba, kawai dai ya baro na shi bangaren ne saboda Hajiya Kaltume, ba zai iya barin gidan a yanzu da ake amsar gaisuwar yarsa ba, sai dai arba da tawayensa dake wasa a falon Momy suna mata tsalla akan kujeru Hurriya na kokarin hanasu sannan na fahimci kewar yaran da ya kasa zuwa ganinsu ya kasa karbarsu ya rumgume su a lokacin da aka haife su ce take kiransa.

 Salamu Alaikum

Yayi sallama muryarsa na isar da rauninsa dake idonsa na arba da yaransa kanana da yayi, sai kuma ya samu kansa da kunyarsu damuwar abun da yayi musu ta yi kamar zata fadar da shi a tsakar falon. Hurriya da Namra suka amsa masa Namra na murmushi Hurriya kuma na faduwar gaba, tana addu'ar Allah yasa ba wani abun aka cewa Appa ta yi ba. Ya zauna kan kujera yana kiran Hamid dake tsalle yana rike da kwalbar lemu.

 Husaini baka tsoron ka fasa kwalbar ka ji ciwo

Hurriya ta kalli mahaifinta da saurin jin da ganin yadda ya nunawa kanenta kulawa, Namra kuma ta dan hararesu ta ce.

 Tun dazun haka yake, idan aka hana shi kuma yace zai turowa mutane kunamu, shiyasa ban ma masa magana ba

Appa yayi murmushi yaran suna nufar gurin da yake kamar wadanda suka saba da shi. Ya kama su ya dora dayan a cinyarsa dayan ma ya dora shi a cinyarsa yana kallonsu.

 Husaini...

Wanda aka kira da Husaini ya nuna kansa yana gyara masa sunan domin ba su saba jin ana kiransu da haka ba.

 Hamid

 Oh Hamid... Haka Hamid.. To ai kai ne Husaini... 

Appa ya fadi hakan ne saboda Hasan da Husaini shi mutanen da suka saba da shi, kuma shi zai fi musu dadin fada.

 Appa Little Hamad shi ne Husani, Hamid Hassan ne

Hurriya ta fada masa domin banbantawa, Appa ya hade wani abu mai karfi na bakincikin rashin sanin yaransa da iya banbance a rashin dalili, yana cewa Hamid Husaini ne saboda shi ne mai karamin jiki, Little Hamad kuma shi ne mai jikin Hamad, a can baya har wasu suke daukar shi ne Yayan Hurriya saboda girman jikinsa.


Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 33

Appa sai kallonsu yake yana shafasu idonsa a raunace kamar mai shirin yin kuka, sai dai be bar hawaye ko alamarsu a idonsa kasancewarsa namiji kuma Uba. Abun da Hurriya ta kasa yi ita kan sai da nata hawayen na farincikin suka zubo, yaran da ba su taba rabar gurin da mahaifinsu yake ba suka ji dumin jikinsa. Yau gasu zaune a cinyarsa yana shafa su. Kusan a lokaci daya kowa ya kalli kofar falon da aka bude har Appa. Captain ne ya shigo cikin shiga ta kananan kaya kamar kullum yana rike da keys dinsa dayan hannunsa kuma yana rike da wani kwali da aka yi rapping. Saitin gurin da Hurriya take tsaye tana share hawaye ya fi maida hankali, kamin ya kalli gurin da Appa yake zaune tare da yaransa yana amsa sallamarsa.

 Sannu da zuwa Captain

Namra ta fada cikin murna da farinciki ganinsa tare da kyakkyawar tarba kamar kullum, Captain ya aje kayan dake hannunsa a mini glass table dake kusa da inda yake tsaye ya karasa gurin Appa ya risina har kasa ya mika masa hannu biyu ya rika hannun Appa daya.

 Barka da yamma Appa

 Barka dai yaro ya aikin?

 Alhamdulillah, ya hakuri Allah yayi mata rahama, mun yi gaisuwa a waje amman ban samu gani ka ba

 Alhamdulillah, Ameen ya Allah. Ba komai Allah ya bada lada

Appa ya amsa kana ya kalli Namra dake gabatar masa da Captain.

 Wannan ne an Yayan Momy Jameel

 Na wayance shi ai, Nafisa tana yawan nuna min hotonsa da labarinta, wannan ne karo na uku da muka gaisa i think

Captain ya amsa da auri.

 Haka ne ranka ya dade

 Allah ya taimaka

 Ameen na gode

Ya amsa yana rankwafawa alamar girmamawa da kunyar da be san ta ina take fito masa ba. Appa ya sauke twins ya mike tsaye ya rika hannunsu ya nufi stairs, sai da ya haura ya shige dakin Momy sannan Captain ya kalli Hurriya da yake zaton ko an kai kararta a gurin Appa ne ya shigo yayi mata fada har take kuka.

 Why are you crying?

Ya tambaya me take yi ma kuka in a sign

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login