Showing 129001 words to 132000 words out of 279257 words

Chapter 44 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34668

halinsa ne ke dai yanzu ba kin mallake shi ba ai duk wanda ta ji zata iya kawai ta zo


 Aa, ina tunanin na gama da komai sai kuma wannan ya taso, na bar shi yayi aure ya kwaso mana wata ita ma ta zo ta hana mu zaman lafiya? Kuma tace zata zuba nata yaya? Ai kara ma Iyami da wannan yarinyar da take karama sa'ar Salma fa kuma kawarta, ni ban gama yarda ba shiyasa hankali yake kwantawa wani bangare, kuma na kira Malam wayarsa bata shiga ba, sai dai kuma ina mamaki idan har gaskiya me yasa Malam be fada min ba? Bayan kuma yace duka aikin da yayi yana bibiyarsa duk lokaci? Ko dai ya kwance kullin ne shiyasa har haka take shirin faruwa

 Hajiya ki kwantar da hankalinki, idan ma ya kwance aiki wata kila akwai abun da yake bukata ne kamar yadda yayi min, sai ki ba shi karki zo ganin yadda yake min aiki a yanzu, ko jiya sai da ya bani maganin da zan saka a nama yanka tara na bawa Fadeel ya ci, kuma tun kwanan baya da ya fara min aikin nan Wallahi na fara ganin gaske, domin yanzu gidana yake cin abincin dare, na safe kawai yake ci a can shi ma kuma na san ya kusa dainawa, ga maganar auren nan har zumudi yake a yanzu ba kamar da ba

 Idan kuwa haka ne, ai babu adalci a ciki, bayan ya fada min yanzu babu kowa a zuciyar mijina sai ni, sai kuma ace ya kwance aiki, idan ma wani abun yake so sai ya fada kai tsaye ba sai ya kwance ba

 Ina ganin zai fi kyau ku yi magana da shi ki ji koma minene, ni kam Wallahi sai sam barka, yanzu har jinsa nake kamar wani dan'uwana

 Zan yi magana da shi

 Okay, kamin ki manta minene size Khairy

 Hajiya zan saka ta turo miki daga baya, yanzu kam bana iya gane komai

 Kar fa ki saka kanki a damuwa, komai zai warware

 Ina fatar haka...

Ta sauke wayar da tunanina kala kala a ranta.




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini d????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
a Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar? MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne? cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai? shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 24
Tun da Hurriya ta shige dakinta bata fito ba, har Magariba, bata son Momy tace ta mata wani abun ba daidai ba dan haka ta kebance kanta a dakinta, da dare ma bata ci abincin dare ba saboda bata fito ba, ta inda ta samu sa'a abincin da ta ci na rana be yi saurin narkewa ba, dan haka bata kwana da yunwar rashin cin abincin dare ba. Da asubar fari ta farka ta yi sallah sannan ta dora da karatun kur'ane har sai da rana ta fito sannan ta yi azakar ta hau gadonta ta koma bachi.

Tara da rabi ta sake farkawa, a kasale ta sauka saman gadon ta shiga bandaki ta wanke bakinta ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin bakar atamfa mai ratsin blue. Ta dora dankwalin a kan gado ta zauna gaban madubi ta gyara gashin kanta ta yi farkin dinsa a baya, sannan ta shafa hoto kadan abun da ba al'adarta mai ma dan ya zame mata dole ne take shafawa, amman a yau da yake ranar jumma'a ce ta ji tana bukatar yin kwalliya. Ta dauki turare ta mai kamshi ta fesa, sannan ta dauki man baki zata shafa sai ta tuna karyawa zata yi, hakan ya saka ta mayar ta aje ta koma saman gadonta ta kwanta tana duba agogo dakin dake nuna karfe goma daidai. Sai dai duk da haka bata son fita ta karya a yanzu ba dan bata jin yunwa ba sai dan bata son tsaba dokar Momy, sanin kanta ne Momy bata karyawa da wuri idan ta? fita ta taba abun da Momy ta aje ba tare da Momy ta ci ba bata san iya hukuncin da zai biyo baya, dan haka ta kara minti talatin akai sannan ta fito kanta a sake babu dankwali gashin kanta sai sheki yake. Masu aikin Momy kawai ta samu a falon dayar na kallo dayar kuma na saka turaren wuta.

 Dan Allah Momy ta gama breakfast dinta?

 Wane breakfast kuma Hurriya breakfast tun yaushe har an wanke komai, na rana ma kadan ya rage a gama

Hurriya ta ji babu dadi.

 Dan Allah Inna Shatu idan kuka gama abinci ku rika zuba min nawa dabam, ba sai an hade da na gida ba

 Toh Hurriya

 Yauwa na gode

Ta nufi hanyar Kitchen kamin ta karasa ta ji muryar Namra a stairs tana kiranta.

 Me zaki yi a Kitchen Hurriya?

 Tea zan hada

 Saboda jindadi ko saboda me?

 Ban samu breakfast ba, shi ne zan hada tea

 To ki jira abincin rana ya kusa karasawa ai, idan yayi sai ki ci, kin san baki karya ba kika je kika kwanta kina ta bachi any how

Namra ta karasa tare da isowa daidai gurin da Hurriya take tsaye. Hurriya ta sauke kanta ta juya domin barin kofar kitchen din.

 By the way Momy tace karki sake shigar mata kitchen idan kina bukatar wani abu ki yi magana, ba wai ki shiga Kitchen haka kawai dan jindadi ki ce zaki hada tea ba

Hurriya ta juyo ta kalleta ta cikin gilashinta duba mai kyau.

 Amman Yaya Namra nan gidan ubana ne, ina da iko da komai kamar yadda kike da shi, me yasa kuke kyarata ne? Me na yi muku?

Mamaki ya saka Namra rike baki.

 Ni kike fadawa wannan maganar?

 To ya kuke son na yi ne? Na zuba abinci a jiya Momy tace kar na sake zuba abinci idan bata ci ba, yau ina jin yunwa amman haka na wuni a daki saboda kar na fito na tararda bata gama karyawa ba, yanzu kuma na fito Inna Shatu tace an wanke komai, yanzu kuma zan hada tea ki ce ba haka ba, ko dan saboda jindadi zan iya hada tea Yaya Namra balle kuma ban karya ba

Tana maganar hawaye na sauko mata. Inna Shatu ta aje kaskon wutar dake hannunta tana fadin.

 Abun be kai haka ba, tafi dakinki bari na hada miko tea din, ai da magana kika min sai na hada miki ma ba sai kin shiga ba

A take Namra ta tsaka rantsuwa.

 Wallahi tallahi ba zata sha tea din nan ba, ke har kin isa? Ki fada min magana? Ina yayarki? Okay yanzu da kika dawo wani sabon rashin kunyar ne kike dawo da shi ko? Har kina wani tutuyar gidan ubanki, uban da baya sonki? Uban da be damu dake ba, uban da ke da banza duk daya a gurinsa?

 Kamin nan na yi gatan da wata ya a gidan nan bata yi ba, mahaifina ya so ni fiye da kowa a gidan nan, rayuwa ce ta sauya saboda bata tafiyarwa kowa a yadda ta saba ba, kamar yadda bata tafi min a yadda na taso ba? Sai aka sauya min da wata kaddarar mai daci, kuma hakan ba yana nufin zan tabbata a ciki ba, kar wannan ya zama abun gori a gurinki Yaya Namra, domin ke ma baki san a ina rayuwa zata kai ki ba, babu wanda ya san gobensa, kamar yadda ni ma ban san ya GOBENA zata kasance ba, dukanmu muna tafiya ne akan RAI BIYU ran farinciki da kishiyarsa, a WANI GARI? rayuwa kaddara zata sauke mu na gaba? Babu wanda ya sani, na sani ni a yanzu tawa kaddara baka ce kamar BAKAR WASIKA, amman ba zan dauwama a haka ba...

Bata daina kuka ba kuma bakinta be yi burki ba har sai da ta fashe kurjin dake mata ruwa a zuciya, sannan ta juya ta nufi stairs, har ta shige dakinta Namra bata gama mamakin inda ta samo baki haka ba.

 Amman zata aikata tun da ta iya munafurci zata iya aikata wannan ma ba mamaki, tab aiko kin dauko tuwa dafa kanki

Ta shiga Kitchen ta dauko plantain, har ta yi aikin soyawa ta gama bata daina mamakin yadda Hurriya ta fada mata magana kao tsaye ba.

 Ji take ta yi sa'a da ni, saboda ya girma kuma Salim ya nuna yana sona ya koma gurinta, sai take jin ita ma ta kai mace.. To yarinya da sauran kuma na gode Allah da zai musanya min da ni, domin da ace CIWON SO ya kama ni na wannan Salim din da Allah kadai ya san yadda zata kalleni ma

 Wacece ke da ya kamata ki maida hankali ki yo ki gama, kina nan kina shiririta ko? Kuma kin fi kowa sanin halin Captain zai iya fushi yace ba zai ci ba, balle ma ya fada min da bako zai zo gidan nan

Momy ta tambaya tana tsaye kofar kitchen din, mundayen zinarin dake wuyan hannunta suna amo. Namta ta juyo ta kalleta.

 Bako kuma?

 Haka yace amman be fada min ko waye ba

Namra ta dan kalli gafe tana tunawa da maganarsu da Salim a jiya, and if she guess it right Salim ne bakon kenan, domin Captain ya fada mata alakarsa da shi.

 Uhmmmm wahalalle

 Wa...?

A tsawace Momy ta tambaya tana mata wani kallo sakaka. And that's was the moment da ta yi realize bata fayyace ko waye ba.

 Wani tunanin nake yi dabam ba Momy ba Captain ba, na isa? Haba ko hauka nake ai ba zan fara ce masa haka ba

 Good

Sai a lokacin Momy ta numfasa kamin ta bi miyar da Inna Shatu ke zubawa a karamin kula.

 Wa kike zubawa miya Shatu? Ko kun fara satar nin har da abinci kuma?

 Subhanallahi, Wallahi ban taba ba, Hurriya ce idan zan zuba abinci na zuba mata? nata dabam

 Saboda me?

 Toh Hajiya yanzu kuma ni na ce wani abu? Sai dai ki tambaye ta

 Karki sake raba abincin mu da ita, salon da saka mana wani abu a abinci ko kuma saboda ita ta fi wani neda za a ware mata abinci, ban da ma rainin wayo idan Hurriya ta fada miki abu sai ki yi? Waya dauke ku aiki? Babu sisin mahaifinta a cikin biyan masu aikin gidana, juye miyar nan tun wuri

 Toh Hajiya

Ta juye miyar ta aje kular ta fice. Anan ne Namra take bata labarin abun da ya faru tsakaninta da Hurriya.

HURRIYA POV.

Yadda ta yi spending Night and Morning dinta a dakinta haka ta zauna a dakinta har la'asar, saboda tana gudun ta sake fitowa ta sake yin arba da wani abun bakinciki, kukan kan ta sha shi kamar shi ne last hope dinta. Ta rumgume yunwa, bakiniki kuma yayi mata rumfa a zuciya, bata ji zata iya fita ba har sai da yunwa ta yi ta kawo mata farmaki ta hana ta shakat ta hana ta zaman lafiya balle kwanciyar gado lafiya.

Sai da ta hada da karfin hali sannan ta iya Sallah la'asar saboda jikin nata babu kwari ko kadan, tana sallamewa ta dauko kur'ane ta karanta suratul Kahafi ta yi addu'a ta maida kur'anen a muhallinsa sannan ta dawo gaban madubi ta zauna tana kallon kanta, fuskarta har ta yi rama saboda azumin dole da ya kamata tun jiya har yau da yamma.

Siraran hawayen da suka zubo mata ta share sannan ta dauko hoto ta shafa a fuskarsa saboda boye abokin rayuwarta wato kuka, sannan ta ta shafa man lebe kadan, ta tashi ta dauko dankwalinta ta daura daidai yadda zai tsaya akanta ta karya karin dankwalin da kyau irin daurin Zarah Buhari, ta sako gashin kanta data daure ya sauko a gadon bayanta hakan kuma ba karamin karawa daurin nata kyau yayi ba, ta gyara gilashinta, ba dan komai ta yi haka ba sai dan karawa kanta courage, and tana jin she deserves to live a happy life kamar sauran sa'aninta balle kuma a yau da yake rana ta musamman wato jumma'ah even though zuciyarta na cike da damuwa da kunci, kuma kwalliyarta zata boye kukan da ta yi. Bata saka talkamin da suka saba sakawa idan za su saka kasa ba a haka ta nufi kofar dakinta ta bude idonta cike da tsoron arba da Momy ko Namra, ba dan tana jin yunwa sosai ba ba zata sauko ba sai dai bata da wani zabi da ya wuce ta bawa cikinta da jikinta abun da suke bukata.

Ta dan rika skirt dinta ta dage shi kadan saboda ta samu sauka stairs din cikin jindadi, hakan kuwa sai ya bawa kyawawan kafafuwanta kuma farare fes damar bayyana. Tana hango falon da mutane gabanta ya buga da karfi, maza ne biyu da bata ga fuskokinsu ba, sai Momy da Namra dake falon, ganin babu sarki sai Allah ya saka ta cigaba da takawar without making any sound domin babu talkamin a kafarta, hakan kuma sai ya taimaka mata babu wanda ya lura da saukowarta har sai da ya rage sauran taku biyar ta sauka.

Kusan a tare Captain da Salim suka dago suka kalli stairs din dake hagu da inda suke zaune, sai dai sun samu tsabanin aje idonuwansu a mabanbanta muhalli a jikin Hurriya, Salim ya tafi kai tsaye gurin fuskarta, yayinda Captain ya fara sauko idonsa a kan zarazaran yastun kafarta sirara masu matukar kyau zuwa leg dinta slowly ya bi kasanta da kallo zuwa gurin da Salim ya dade da yada zango wato fuskarta, Subhanallahi ba zai ce be taba ganin mata masu kyau ba a duniya but Hurriya is different tana da wani sirritacce kyau mai jam hankali maza zuwa gareta, wato kwarjini yana fisgar zuciyar wanda duk yayi arba da Innocent face dinta, tun daga kan daurin dankwalinta har bakar atamfar dake da ratsin blue, zuwa gashin kanta da ya bayyana, da yadda gilashin idonta ya daidaita a fuskarta, kaf babu abun da bata yi masa kyau ba.

(Mace mai sirhirtaccen kyau ba ana nufin sai mai kyau ba, aa wasu ma ba su suka kyau ba amman Allah yayi musu kwarjinin da maza suke sonsu, balle kuma ayi sa'a kwarjin ya hadu da dan'uwansa kyau, ko kuma kudi, ko farinjini, sai namiji yayi kamar zai haukace akanki yayi ta nan da nan da ke, abu ne mai wahala ko a taron mutane ka ga an wulakanta mace mai kwarjini, ba kuma dole sai mai kudi ba, wani ko talaka ne zaku ganshi da kwarjini, wani kuma an hada masa duka, kudi, kyau, farinjini, kwarjini)

Salim ya mike tsaye yana kallonta.

 Sauko mana Hurriya

Momy da Namra suka dago su ma dan bawa idanuwansu abincin. A take zuciyar Hurriya ta raya mata saboda ita ya zo, ko kuma saboda Yayarta Namra amman yanzu da ya ganta yake kokarin bata shirinsa, ga kuma mutumen dake kuss da shi mutumen nan ne da ta bugewa kirji a jiya har ya so ya mareta, daman kuma ya taba dandana mata zafin hannunsa dan haka bata manta ba, ga kuma Momy da Namra da bata san iya hukuncin da zata karba a gurinsu ba idan wani abun ya faru. Juyawa ta yi da sauri ta koma tana hada taku biyu uku na stairs din duk wani rashin karfi da yunwa sai suka kau a lokacin, a tafiyar da za a iya kiranta da gudu ta haye sama ta shige dakinta ta rufe ta saka key.

***? ? ***? ? ***

 Salim zauna mana

Kamar mai jiran umarnin Captain sai ya koma ya zauna ya maida idonsa a kasa.

 Yarinyar nan fa bata shirya magana da kai ko saurarenka ba, jiya babu yadda ban lallabata ma amman sam bata ba ma saurareni ba balle har ta fahimci me nake fada

Namra ta fada tana kallon yana yanayinsa ya can sauya duk kuwa da irin kokarin da yake na ganin ya boye damuwarsa.

Captain ya kallesa ya fara magana calmly.

 Ita soyayya ba a mata dole, idan bata ra'ayinka karka ce sai ka cusa kanka da karfi a gurinta, kuma ni ban ga wani dalili na son a biyo mace ama lallabata ta so mutum ba, ni dai har ga Allah ban ga yarinyar da zan iya yi ma wannan ba, kuma ba zan taba ganin ta ba har abada, yanzu ma saboda ka fada min da gaske kake yi kuma kana sonta sosai shiyasa har na yarda muka zo tare, amman dan ina da alaka da ita ko ba zan iya saka wani abun ba ko na hanata

 Allah ma ya tsareka da hada alaka da wacan yarinyar

Daga Salim har Captain kallon Momy suka yi sai dai babu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login