Showing 123001 words to 126000 words out of 279257 words

Chapter 42 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34660

ta nace sai an koma da ita.

 Kin fadi gaskiya, Tsoho be taba musa ba sai a yanzu ta aka cire masa kowa a zuciyarsa, yau a gaban matarsa nake cewa ba za'ayi ba yace za'ayi Allah mai girma

Hajiya Binta ta sake fada tana hawaye. Hurriya ta bude ido ta kalleta

 Daman na yi tunanin haka Hajiya, saboda kin fadawa Yaya Namra sakon da zata? fada musu, suna ganin kamar kin zafafa sona ne akan na kowa, ita kanta Yaya Namra ta fada min bakar magana, gaba daya a munafuka suke kallona ganin suke kamar zan iya hada ki da Appa ne, Allah kadai ya san fushi da Appa zai yi da ni akan wannan, ni kaina ina tunanin zafafan da Appa yayi ne a kaina ya saka suka raba ni da shi, hawayen nan kuma Hajiya dan Allah ki share su kar wani abu ya sami Appana

 kin yi tunani kuma na yaba da hankalinki, daman ina masa addu'a kuma zan kara, zan dage, ke ma kuma zan cigaba da yi min kuma ba zan zauna haka nan sai na nemi maganin tsari kala kala na baki, daga kuma karki sake wasa da addu'a Allah ya miki albarka

Hajiya Binta ta share hawayenta, tare da bawa zuciyarta.


***?? ***?? ***

A mota babu kalar wutar da Hajiya Kaltume bata hurawa Appa a zuciyata akan Hurriya, har tana fadar Hurriya ta hada shi da Hajiya gashi nan har ta yi fushi gashi kuma ta hana Hurriyar komawa.

 Ni daman abun da nake ta ji ma tsoro kenan, nan gaba kuma ba san me zata kulla ba, yarinya karama ta zama munafuka. Ko yanzu karka yarda ka barta a can idan ba haka ba, Hajiya sai ta tsine maka nan gaba, amman karka sake waiwayar gidan sai idan ta huce

Kwafa kawai Appa yayi be ce komai ba har suka isa gida.

WASHE GARI.

I know littafin nan zai fito, i know zai yi yawo har ya iso gareki. Na fada kuma zan saki repeating Wallahi duk wanda ya karanta min littafi ba tare da ya biya ba, na barshi da mai mafaWar rana da fitowarta. Daga masu sharing har masu karantawa ba tare da biya ba na barku da Allah...!

Misalin karfe goma sha biyu na rana 12:00pm Captain ya shigo gidan, ya bude tsadadiyar motarsa ya fito ipod a kunnesa yana magana cike da gadata, shi alaka dole ga soja, kuma jinin sarauta ga kuma naira, shigar kananan kaya ce a jikinsa kamar yadda ya saba, domin abu ne mai wahala ka ga Captain Da Shadda sai idan wani abun ya taso. With little strong ya hau entrance din ya murda kofar falon Momy ya shiga, hakan nan dai ya ji yau baya ra'ayin yin sallama even though ba fushi yake ko bacin rai ba, haka kuma ba cikin farinciki yake ba, not happy not sad. Kulu na ganinsa ta mike tsaye ta sauri tana kallonsa bakinta da jikinta suna rawa saboda kwarjinsa, abu mai wahala ka yi arba da shi baka ji tsoro da fargaba ba, musamnan idan haduwar farko ce, ba kuma tsoro na wanda zai maka wani abu, kwarjini da yake da shi da murufa ta tsananin mazantaka da zakantaka ya wuce ka lalleshi baka ji kwarjinsa ba, balle kuma ace ka san yadda yake da saurin fushi da tsananin fada kamar gawurtaccen zaki.

 Sannu da zuwa Sannu da zuwa...

 Yauwa sannu ya gida ya aiki?

 Lafiya Kalau Yallabai

Ya dan juyarta da kai yana kokarin yin murmushi

 No ki kira ni da Captain ko Jameel that's my name, amman wani Yallabai Yaya ko ranka da ya dade old fashion ne, bana so. Ina Momy?

 Toh toh na tuba, carpet bari a kirata tana sama

Ya runtse ido saboda yadda ta sauya masa suna saboda rashin iya pronouncing din. Ta haura sama da sauri, sanin kanta ne ba a shiga dakin Momy kai tsaye idan ba ita ta kira mutum ba, musamman masu aiki, dan haka ta fara ya da zango a dakin Namra ta sanar mata domin ita kuma ta sanar da Momy. Sannan ta sauko da saurinta kamar zata fadi.

 Na fadawa Namra zata fada mata yanzu

 Na gode

Ta fice da sauri tana amsawa da babu komai, ai aikinta ne. Namra ce ta fara sauko da far'a jin cewar dan'uwanta ya dawo kamin Momy ta biyo bayansa tana masa lale marhabun.

 Yau kuma an sake ziyararmu, sannu da zuwa dana

Sai a lokacin ya zauna yana murmushi da murna arba da yar'uwar mahaifinsa kuma mace mai tsakanin kaunarsa fiye da kowa a familynsu.

 Momy ya gida

 Lafiya kalau, yanzu ka dauki wata bakar dabi'a da ba zaka fada min yaushe zaka zo ba sai dai na gane ka kawai ko? Balle na shirya maka wani abu

 Ni kaina bana sanin zan biyo ta nan sai dai na biyo kawai, kuma idan ina ra'ayin wani abu ai zan iya kira na fada miki

 Captain sannu da zuwa

Namra ta fada sannan ta nufi kitchen.

 Ya aikin? Yanzu ka dawo nan kenan? Yaushe ka dawo kasar wai?

 Just two days ba, shi ne suka sake kawo ni nan na yi wata biyu zuwa uku sannan na koma gida

 Kaduna za a maida kai kenan?

 Yeah na dade ina yawo, so yanzu fitar da na yi waje da kuma sa hannun Daddy, za a bar ni Kaduna na zauna a nan, amman idan aikin ya taso na wasu garuruwa zan tafi mu yi, akwai aikin da ban karasa ba nan Gusau kuma kin san tana ta kokarin a magance matsalar tsaron nan shiyasa aka dage sai na dawo

 Maa Shaa Allah, Allah ya taimaka gashi nan ka yi Fresh ka kara samun lafiya

Yayi murmushi tare da kallon Namra data aje masa abun tabawa a mini center table dake gefen kujerar daya zauna.

 Maganar aure dai shi ke nan ka watsar da ita Captain

 Zan yi aure Momy dolena

 To na tsorata da lamarinka fa, wacan ma ana daf da daura aure komai ya lalace kuma tun daga lokacin baka sake gabatar mana da kowa ba

 Bata min rai ta yi da yawa, taya ana daf da daura aurena zaki yi chat da wani saurayi har ya daukeki ku fita, ni fa ina da mugun kishi da zai iya sakawa na kashe mutum, bana iya daukar irin wadannan abubuwan, idan ina son mace ko kallonta bana son ayi

Ya aje ayar maganar tare da daukar lemun da Namra ta aje masa ta sha. Momy ta yi murmushi.

 Toh Allah ya bada ta gari, yasa kamin ka bar garin nan ka samu wanda kake so, kuma ya rage maka wannan fushi idan ba haka ba zaka yi wahalar zaman aure

 Amin

Ya amsa yana dauke fuskarsa da murmushi tare da shan lemun a hankali. Namra ma ta yi murmushi tana taba wayar hannunta kamin ya dago ta kalleshi.

 Yauwa Captain wai a ina ka san Salim?

Ya juyo ya kalleta.

 Salim Sarauta, abokina ne sosai tun a jami'a muke tare, ke ina kika san shi?

Ya daga kafada tana dan zare ido kadan kamar wanda ta rasa abun cewa.

 A hanya muka hadu, ya nuna yana so na daga baya kuma ya koma gurin Hurriya, shiyasa na kai shi gidan ma har ka ganshi, amman ban san me ka fada masa ba na ga yanayinsa ya canja kuma har yau be sake kirana ba

Captain yayi murmushi kasaita murmushin dake kara masa kyauta da haiba

 Ban fada masa komai ba, maybe dai ita ta bata masa rai, na je karbar abu ne na gansu tare, amman karki sake kai shi gurinta, haka yake duk garin da yaje sai yayi budurwa, musamman idan ya ga mai kyau ce just like your sister....

 Hum himm

Ya dan kalli Momy kamin ta sake kallonsa dan amsa masa tambayarta.

 Ina yarinyar take ta dawo?

Momy zata yi magana Namra ta yi karaf ta tari numfashinta ta ce.

 Eh tana dakinta

Ya maida dubansa gurin Momy fukarsa shimfide da murmushi yayi mata godiya.

 Thank You Momy, ko wace mace ta fi daraja da martaba a gidan iyayenta ko mijinta, kuma a matsayinki na uwa daman haka ya kamata ki yi

Ya dubansa gurin tsadaden agogon hannunsa sannan ya mike tsaye.

 Ya kamata na tafi kar na bata lokaci

Momy dake mamaki yadda Namra ta yi masa karya ta ce.

 Nan da nan, baka wani dadewa

 Yanayin aikin ne a haka, wai Musib har yanzu ba su dawo ba?

 Suna da daf da dawowa, muna waya da su ai

 Good

Ya nufi kofar fita falon, Momyda Namra suka mike tsaye domin yi masa rakiya. Yana bude kofar da zimmar fita Hurriya ta dake rike da kofar tana murdawa da zimmar shigowa, dayan hannunta kuma yana rike da luggage ta sake naushin kirjinsa da kanta daidai saitin zuciyarsa, a karo na biyu by mistake. A take daga hannun sama saitin fuskarta. Kamin hannun ya kai fuskarta ta yi saurin lumshe idanuwanta dake cike da yalwatacce gashin ido ga kuma na gira da ya kara masa kyau a sama, ta dauke numfashinta tana jiran jin tafin hannunsa a fuskarta.

 Yarinyar bata da hankali komai a haukace take yinsa

Kalaman Momy da kuma jin shiru babu mari babu alamarsa a fuskarta ya saka ta bude ido a hankali pink lips dinta suna motsawa kamar zata ce wani abu. Hannu ta gani a tsaye saitin fuskarta ba tare da ya kai hannun a fuskarta ya mareta, kuma be sauke hannun ba, haka zalika be dauke idonsa daga kallonta ba, kamar yadda fuskarsa take daure saboda abun da ta yi masa. Da sauri ta duke kasa ta ratsa gefenta ta shige falon har Luggage dinsa na dukan kafarsa, abun da ya kara bata masa rai. A lokacin ne ta tuna cewar shi ne mutumen da ya taba marinta.

 Yi hakuri

Ya ta fada tana kara matsawa baya da sauri domin jin take kamar zai iya rikota yayi mata hukunci ne, gashi babu Hamad mai rama mata. Ya sauke hannu ya juyo sai dai ba ita ya kalla ba, Namra ya kalla.

 Why do you lie?

Ta dan yi baya kadan ta rasa yadda zata wanke kanta, Momy ta kalleta sannan ta kalli Captain ta already ya fice har yana kokarin rufe kofar. Sannan ta juyo ta watsawa Hurriya harara

 Kin dawo ko? To shiga ciki ki zauna, gida kam na ubanki ne amman ikonsa nawa ne domin bangarena ne

Hurriya ta sauke kanta ta juya tare da taja kayanta ta haye sama. After ta shige Momy ta kalli Namra ta ce.

 Me yasa kika yi haka? Namra ki daina yin abun da zai saka Captain ya tsaneki fa

Ta dan cize baki cikin yanayin damuwa ta ce.

 Ban dauka zata shigo yanzu

 Ki kiyaye next, domin ni ban ki kum fahimci junanku ba har ya kai ku ga aure, ko ranar da ya bar gidan nan sai da muka yi magana da Ammy, akan ke da shi, amman saboda lura da hankalinku baya kan juna ya saka ba ma son matsawa, kuma ko da babu irin wannan be kamata kina haka ba be careful...

 I will...

Ta amsa tare da kallon kofar kamar mai tunani, tare da saka hannunta tana taba wuyanta. Momy kuma ta nufi upstairs cikin matukar bacin rai.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar? MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne? cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai? shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5??

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?

5??5??5? ?5?? 2? 3?

Tana tsaka da cire tufafinta a luggage Momy ta turo kofar dakin ta tsaya daga wajr tana kallonta.

 Mun ga sakon da Hajiya da ta aiko mana akanki, kuma mun gode ke ma kuma zaki ga irin nawa sakon, mahaifinki yayi gaskiya gidansa ni da ke duk muna karkashin ikonsa, amman nan bangarena ne ina da nawa rules and regulations, dole kuma ki kiyaye domin ba bangaren Iyami ba ne

Hurriya ta sauke kanta ba tare da ta cewa Momy komai ba, ganin haka ya saka Momy ta bar kofar a bude ta nufi nata dakin. Ajiyar zuciya Hurriya ta sauke ta dafa goshinta.

 Allah ka kara min hakura zama a gidan nan, kowa da kallar tsanar da yake min

Ta sake aje numfashi mai karfi sannan ta cigaba da cire tufafin ta jera a closet ta aje luggage din gefe ta cire hijab dinta ta saka talkaminta ta fito daga dakin. Ko da ta sauko babu kowa a falon kai tsaye ta nufi kofa ta bude ta fita. By this time ta san cewa mahaifinta baya a gidan sai idan wani abu ya dawo da shi ko kuma ya hana shi fita, dan haka Hajiya Kaltume uwargida, nan ma sai da ya ki bacin ranta da take ganin za a cusa mata, ta bawa zuciyarta hakuri ta danne duk wani abu da zata ji tun gabanin su fada mata, sannan ta tura kofar ta shiga. Sukan na su falon a cike yake suna ta murnar dawowar Salma, sai dai ganin Hurriya ya saka sun tsaya cak suna kallonta kamar irin wanda aka jefo daga sama daga gabansu.

 Hurriya

Hajiya Kaltume ta fada da mamakinta karara a fuskarta.

 Na'am Hajiya ina wuni, Yaya Khairy Yayana, ina wuni yaya Salma sannu da zuwa

Salma ta amsa tana kokarin boye munafurcinta a cikinta.

 Lfy kalau

Yasir kuma ya ce.

 Lafiya Kalau kanwata, na jidadin da kika dawo, Hajiya kin yi abun da ya dace

Hajiya Kaltume ta yi murmushi, wani abun da ya bawa kowa dake falon mamaki ciki har da Hajiya Kaltume da ita kanta Hurriya shi ne tashin da Khairy ta yi ta koma kusa da ita ta rumgumeta tana far'a.

 Alhamdulillah, Allah ya kawar da bacin rana na jidadin da kika dawo, I'm so happy

Hurriya ta kalleta har tana rasa abun furtawa, mamaki ya lake mata a zuciya.

 Ina taje ne ake ta murnar dawowarta?

 Abubuwa da yawa suka faru Salma sai kin zauna zaki sha labari

Khairy ta amsa bayan ta saki Hurriya.

 Ni ma fa ina da labarin da zan baku, kuma dukansu sai mamaki ya kama ku

 Mamaki zai wuce ki ce kin samu wanda kike so zaku yi aure soon bla bla bla ni ma aurar da ni Hajiya take kokarin yi fa, ga Fadeel kin san shi ai dan Hajiya Fatee

A yanzu ma Khairy ce ke amsawa Salma tana dorawa da zancen auren dake ci mata rai. Da mamaki Salma ta kalli Hajiya ta ce.

 Da gaske Hajiya? Fadeel ba yana da mata ba?

Hajiya ta daga mata kai.

 Yana da mata amman kirkinsa ne ya saka nake son ba shi auren saboda ya nuna yana son Khairy

Yasir ya mike tsaye daman shi ba gwani ne na sauraren irin wadannan maganganun na mata ba, dan haka ya kalli Hurriya.

 Muje waje Hurriya ina son magana dake

Hurriya ta juya ta nufi kofa, tana gaba daya bayanta, sai da suka fice sannan Salma ta kalli Hajiya Kaltume ta ce.

 Har yanzu yaya ganin mutuncin yarinyar yake yi?

Khairy ta tabe baki.

 Hmmm me za'a fasa kwanan baya saboda yarinyar nan ya lalata min birthday

 Amman hugging dinta kika yi yanzu fa, kina murna dawowarta

 Toh ai Salma idan baka iya kama barawo ba sai barawo ya kama ka, kara ina haka idan ba haka ba wani abun na samunta nan gaba za a iya cewa ni ce

 Nikam i can't fake love, shiyasa wannan kawar tawa ma na ja mata kunne

 Wace kawa wai?

Salma ta gyara zama tana kara fitar da sauti saboda labarta musu abun da ta kumso.

 Hmmm Appa be fada muku zai kara aure ba?

Sai a nan Hajiya Kaltume ta yi murmushi mai sauti ta ce.

 Ya ma isa Salma? Duk bayan wahalar da muka sha, ga tarin tashin hankali da munafurci da ba mu gama fuskantarsa ba saboda Nafisa da Iyami? A yanzu kuma da ya kamata ace ina da ikon gida ya tunkare da zancen aure? Haba wa..... Ba dai shi ba sai idan wani kuma ko kuma idan na mutu

 Hajiya wannan fa ba wasa ba ne, abu ne da na gani da idona, and she's my friend muna daf da kare

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login