Showing 78001 words to 81000 words out of 279257 words

Chapter 27 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34709

da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
page 11

Misalin tara da rabi Hurriya na zaune dakinta ta ji an kwankwasa kofa, tana jin haka ta san wanda be saba shigowa dakin ba ne domin Momy ko Namra basa kwankwasa mata kofa balle kuma Miwan da Musib da basa gidan ma. Ta tashi da saurinta ta nufi kofar ta bude sai ta yi arba da Ruma.

 Appa na kiranki

 Ni

Ta nuna kanta, Ruma ta daga mata kai.

 Eh

Ta juya ta bar kofar ta fara sauka kasa, Hurriya bata tsaya komai ba ta bi bayanta tana sanye da kayan bachi kanta sanye da hular saka. Ruma na gaba Hurriya na bayanta tana jin kamar ta tambaye ta me ya faru kuma dai bata tambaya ba. Cikin tsoro da fargaba ta shiga falon na Hajiya Kaltume gabanta na faduwa. Hankalinta be kara tashi ba sai da ta yi arba da fuskar mahaifinta dake hade babu annuri a tare da shi, bata yarda ta karasa cikin falon ba ta tsaya daga jikin kofa cike da ladabi ta ce

 Appa ga ni

 Okay tasowa zan yi na iskoki can kenan? Ni zan same ki a inda kike na yi magana da ke ko?

 Aa Appa ka yi hakuri dan Allah

Ta taso ta karaso kusa da shi, ba duka take tsoro ba domin be taba dukanta ba, fadansa take tsoro tun daga lokacin da ya canja mata sai ya zame mata abun tsoro bata ma son zuwa kusa da shi sai da dalili domin ta lura baya bukatar ganinta.

 Appa gani

Ta durkusa gabansa tana kallonsa ta cikin gilashin idonta, Yasir na tsaye gefen Hajiya Kaltume dake zaune kusa da Appa, Khairi kuma na zaune a dayar kujerar tana shafa man zafi.

 Miye wannan?

Appa ya nuna mata video karin kudin da aka yi mata. Sai ta saka hannu biyu ta karba tana kallo jikinta na rawa kamar yadda bakinta ma yake rawa domin bata san me zata ce ba.

 Wace ce a nan?

 Ni ce Appa

Ta amsa da sauri.

 Waye wannan da yake miki liki

 Ban san shi ba Appa Wallahi

Tana rufe baki Hajiya Kaltume ta kai mata duka a bakin da mugun karfi.

 Baki san shi ba zai zo yana zuba miki dollars haka?

Apoa ya kalli Hajiya cikin yanayi na rashin jindadin kai hannu da ta yi ta daki Hurriya.

 Ba sai kin dake ta ba, magana ma ta isa a yanzu shata nata line zan yi

 Ai idan ba a dake ta ba, ba zata san Annabi ya faku ba, karya da munafurci babu kalar wanda bata iya ba, ka duba yadda ta zuga Yasir ya fasawa Khairi jiki

Appa ya daka mata tsawa da ta saka ta fashe da kuka ta ja baya tana girgiza kai.

 Waye wannan mutumen na ce?

 Ban san shi ba Appa Wallahi ni ma yau na fara ganinsa?

 Karya take yi Wallahi Alhaji bata san shi ba

Hajiya ta kai kafa ta halba mata wani shuri, kamin ta janye da sauri saboda ciwon da kafar take mata har yanzu.

 Karya take munafuka baki san shi ba zai zuba miki kudi haka kuma kina zaune gashi har sunanki ake fada

Yasir dai yana tsaye sai kallo yake baya son yayi magana Hajiya Kaltume ta rufe shi da fada, bayan kuma ga wanda ya kamata a rufe da fada nan wato Khairi.

 Ku dai duk abun da zai zubar min da mutunci ko kima a idon duniya shi kuke kokarin aikatawa? Ko soyayya zaki yi me zaki yi da mashayi? Kaltume ta fada min yaron nan yayi kaurin suna gurin iskanci da shaye shaye

Hurriya ta saka hannu ta rufe bakinta, ta san duk wani abu da zata fada ba zai wanke ta ba, ita kan da ta sani ma ba zata tafi bikin ba.

 Sannan kuma ka ja mata kunne akan munafurci abun da take ba shi da kyau, kina hada yan'uwa fada kina sa a ciya daya mutumci a cikin mutane

Sai a lokacin Yasir ya saka baki.

 Ni ba ita ta fada min Khairi tana wani abu a gurin ba, daukarwa kawai naje yi sai kuma na yi decide na shiga ciki, kuma idan ma Hurriya tana da laifi to laifin Khairi ne, domin ita ta shirya biki kuma Appa da ka ga irin shigar da ta yi da irin mutanen da ta tara a gurin sai ranka ya bace

Hajiya Kaltume ta watsa masa harara.

 Ita Khairi da ka raina ba, ita meye laifinta? Birthday kawai ta yi fa, kuma ina ce Hurriya ce silar kowa ya fara yin birthday a gidan nan amman ba ayi mata fada ba sai Khairi

Appa ya mike tsaye.

 Ban shigo nan dan ku rufe ni da ka ce na ce ba, and Hurriya ina jan kunnenki idan wani abu makamancin wannan ya sake faruwa sai na baki mamaki

Yana kaiwa nan ya fisge wayarsa da Hajiya Kaltume ta tura masa video ya fice daga falon. Hurriya ban da aikin kuka babu abun da take yi, ta rasa ta ina zata fara wanke kanta.

 Munafuka sahibar kuka, ki yi ta rerawa mutane kuka saboda a tausaya miki a kyale ki ko? To yanzu dai kin ji abun da Alhaji ya fada idan zaki kama kanki gurin yan iskan samarin nan ki kama, idan kuma ba zaki yi ba yi, ga ki ga guri duniya ce

 Wallahi Hajiya ban san shi ba, ni ban taba ganinsa ba

Ba dan Yasir na tsaye gurin ba da babu abun da zai hana Khairi saka baki, sai dai tana tsoron ta yi magana ya sake rufeta da duka. Dan haka ta ja bakinta ta yi shiru sai kallonsu take, Hajiya Kaltume kuma ta rufe Hurriya da fata ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, sai balbale Hurriya take da bala'i ta ko'ina kamar ita ce ta aikata abun da Khairi ta aikata. Sallama aka yi sai suka dago baga dayansu suka kalli kofar amman aka rasa wanda zai amsawa Rukayya sai Yasir dake kokarin sakin fuska.

 Rukayya

 Na'am Yasir ya gd

 Lafiya kalau

Hurriyya ta tashi da sauri ta nufi kanwar mahaifiyarta ta rumgume ta da sauri tana kuka.

 Mama Rukayya kara da kika zo

 Idan ta zo magani zata miki? Idan dai zaki canja hali ki canja domin hanyar da kika daukarwa kanki yanzu ba mai daurewa ba ce

Hajiya Kaltume tana fada tana tabe baki, Rukayya da ke rumgume da Hurriya ta kalli Hajiya ta ce.

 Ba zan mata magani ba, amman Allah zai mata

Yasir yayi sauri cire hannayensa aljihu.

 Rukky Please aa karki fara abun da ba halin ba

Ta kalli Yasir sai kuma ta dauke kai ta rika hannun Hurriya suka fice daga falon, Hajiya ta bita da harara da maganganun kala kala.

 A dare kamar wannan yarinya budurwa ace bata gidansu, kuma ta shigo nan tana neman fada min magana ita marar tarbiya

 Haba Hajiya Rukayya tana da tarbiya Wallahi dan Allah ki daina fadar haka, kuma baki san abun da ya kawota ba, be kamata ku samu tsabani da ita ba, ni zaku haifar da matsala

Yana magana fuskarsa a raunace kamar zai yi kuka. Sannan ya bi bayansu yana jin Hajiya na jan tsaki.

A waje Hurriya sai rantsuwa take yi ma Rukayya na cewar bata san yaron ba, amman saboda shi Appa ya rufeta da fada.

 To miyasa ba zaki bude baki yi magana ba, idan kina irin wannan zaman sai kin cutar da kanki, ba zaki bude baki ki yi magana ba sai ki zauna kina kuka, ko da kina da gaskiya a rashin gaskiyar za a baki

 Basa bari na yi magana kuma idan na fada basa yarda

 Amman duk abun da ba halinki ba ai an san ba halinki ba ne

 Toh sarkin masifa me kike karanta mata?

Rukayya ta juyo ta kalli Yasir da isowarsa kenan gurin, shi ma kansa yau sai ya bata haushi saboda abun da mahaifiyarsa ta yi. Bata ce masa komai ba ta kalli Hurriya

 Daman na fito daga gidan Anty Hauwa ne na ce mai napep ya biyo ta nan zan duba ki

Hurriya ta rike hannunta tana jin kamar ta bita amman ba hali.

 Zan sallami mai napep din sai na sauke ki gida

 Aa na gode yanzu zan tafi

Ta saki hannu Hurriya ta fara tafiya sai ya kirata.

 Rukky

Ta juyo ta kalleshi.

 Na ce zan sallami mai napep zamu sauke ki gida tare da hurriya daga nan ta duba Amma

Bata son tace masa no, kuma ta san Hurriya zata so ganin Amma domin ta dauki lokaci bata saka ta a ido ba, ko da tace zata je sai Appa ya hana saboda Hajiya Kaltume tace zuwan da take tana tafiya ne dan ta fadi karya da gaskiya.

 Tahm

 Hurriya shiga ki dauko Hijabinki

page 12
Ya fada sannan ya nufi gurin motarsa ya ja motar ya iso har gurin da Rukkaya take tsaye, bata shiga motar ba sai da Hurriya ta fito sanye da dogon hijab dinta har kasa, sannan ta bude ta shiga front seat Hurriya ta shiga baya, ya fara driving suka fito gate a nan ya sallami mai Napep din sannan ya ja motar suka kama hanya.

 Rukky please bana son wani abu marar dadi yana shiga tsakaninki da Hajiyata, idan ma ta fada miki wani abu marar dadi ko ta yi miki abun da bw dace ba, ki danne ina son ki dauke ta kamar mahaifiyarki, saboda ni kuma ina tunanin ina da alfarmar da zaki yi haka a gareni

Ta hade yawu can cikin ranta take cewa Allah ya tsare ta Hajiya Kaltume ta zama uwarta.

 In Shaa Allah

Ya kalleta yana murmushi.

 Thank you

Ita ma ta mayar masa da murmushin daga haka be sake cewa komai ba ita ma kuma bata sake cewawa har suka isa gidan. Hurriya ce ta fara budewa ta fita motar Rukayya na kokarin fita Yasir ya shigo ya dakatarda ita.

 Ina zaki je?

Ta masa kallon rashin fahimta.

 Gida mana...

 Ni kuma sai ki bar ni a nan?

Ta yi dariya.

 To ka fito mu shiga gidan bakonka ne?

 Ki dai tsaya mu yi hira ko raina zai saki ni raina ma duk a bace yake

 Waya bata maka rai Hurriya?

 Idan kina son jin labari zauna

Ta yi murmushi sannan ta dawo ta zauna ba tare da ta kalleshi ba.


Hurriya na shiga cikin gidan ta fada dakin Gwaggo da sallama da muryar dake nuna alamar kuka ta yi. Amma na jingine jikin kujera ita kadai a falon tana fuskantar tv dake falon, ta dan karkato kadan ta kalli Hurriya. Hurriya ta isa gurin sai ta kwanta saman jikinta ta fara hawaye, bata son ta fada mata abun da ya faru saboda kar ranta ya bace gashi ba magana take ba balle ta bata shawara.

 Amma na Allah ya baki lafiya, Allah ya tashi kafadunki

Ta cikin Amma ta iya amsawa da ameen ta kwanto da kanta saman kan Hurriya ta rufe ido. Gwaggo ta fito daga dakinta tana mata maraba.

 Yau Hurriya ce a gidan nan kuma da dare, amman dai Alhaji be san kin zo nan ba ko?

Hurriya ta dago hawaye shakaf a fuskarta ta kalli Gwaggo.

 Be sani ba, Ya Yasir na biyo zamu kawo Rukayya ne

 Daman tace sai ta biyo ta ganki, na dauka ma can zata kawana gidan Hauwa, saboda na ga dare yayi sosai

 Tana waje ita da Yaya Yasir, Gwaggo zo

Hurriya ta kama hannunta suka koma cikin dakin, ta zauna bakin gado Gwaggo ma ta zauna daman tana ganin ruwa hawaye a fuskarta ta san akwai abun da ya faru.

 Wani abu aka yi Hurriya?

 Sheri aka yi min Gwaggo.... 

Ta labarta mata abun da ya faru, sannan ta dora da abun da mahaifinta yayi mata recently before birthday Khairi.

 Appa ya siyawa kowa sabon kaya na birthday din Yaya Khairi amman ni Hajiya tace kar ya siya min ina da kaya da yawa, na masa magana sai yayi min fada, Gwaggo yanzu Appa baya so na ko kadan idan na matsa kusa da shi sai yayi ta min fada, zaman gidan ba ya min dadi kowa tsarguwata yake

 Ki yi hakuri Hurriya zalinci be taba doreba, kuma komai yana da iyaka wata rana sai labari, ke dai ki yi ta addu'a ki yi ta fadawa Allah matsalarki zai magance miki ita, mu ma muna nan muna yi kuma akwai wani littafi da na siya miki na addu'o'i mantawa na yi ban bawa Rukayya ta kai miki ba

Gwaggo ta tashi ta nufi gurin da ta aje littafin husnul muslim ta dauko ta mika mata.

 Addu'o'i ne da suka zo daga bakin Annabi Muhammad, karki yi wasa da su, domin ba mu san me za a sake jifanke ko mahaifiyarki da shi ba, kuma duk abun da zaki ci ki yi bismillah, sannan kar tsoro ya saka a baki wani abun da aka san an cutarwa ne ki ci ko ki aikata, yanzu girma kike yi ya kamata ace kina kara wayo

Ta share hawayenta

 Na gode Gwaggo

 Ba komai Allah dai ya tsareki, kuma ina kara gargadinki ban da sakaci da addu'a, kin ga rashin daukar addu'a da muhimmanci ne ya jefa Iyami a halin da take yau, sannan kuma zan karbo miki maganin tsari akwai wani mai bada taimako na yi magana da shi ya ce sai an ba shi 150k sannan zai fara yi na Iyami aiki, ya fada mana jefa ce aka yi mata mai hatsarin gaske, kuma idan ba mu yi fa gaske ba zamu rasata

 To yanzu ina za'a samu 150k Gwaggo?

 Ina nan ina ta kokari Hurriya, idan kuma haka bw samu ba dole gidan nan zamu siyar mu nemi karamin wannan mu siya sauran kudin sai mu yi maganin da su domin lafiyarta ta fi mana komai

 Amman idan aka yi zata warke Gwaggo? Kin san ana ta yi amman babu wani sauyi

page 12
 Muna fatan haka, shi dai mutane da dama sun karba kuma an dace, mu ma muna fatar mu dace wannan ciwon nata ya isheni Allah kadai ya san abun da take ji a ranta, ina fatar na ga ta warke kamin na mutu

Cikin kuka Gwaggo ta karaso maganar ita kanta a yanzu bata da wata damuwa da ta wuce ta Iyami. Hurriya ta tashi rike da littafin ta fito sai ta tsaya daga bakin kofar dakin tana kallon Amma dake kallon kofar dakin tun da suka shiga ciki, wasu hawayen ne suka subuce mata sai ta fashe da kuka. Amma ta girgiza mata kai tana jin kamar ta yi mata magana a dama, shigowar Rukayya ne ya saka Hurriya boye fuskarta Gwaggo kuma ta taso ta fito daga dakin tana fada.

 Wane irin abu ne zaki je ki zauna har dare haka Rukayya

Yasir dake bayanta yana sallama yayi saurin tare mata fadan.

 Tun isha'i take nan kofar gida Gwaggo laifina ne ni na tsayar da ita, ayi hakuri dan Allah

Rukayya ta juya ta kalleshi shi kuma yaki yarda au hada ido sai hakikancewa yake yana ba Gwaggo hakuri kamar shi yayi laifin. Ya zauna saman kujerar da Amma take jingine yana mata ya jiki.

 Amma ya jikin?

Ta amsa murmushi kadan alamar jikin Alhamdulillah. Gwaggo kuma ta amsa masa.

 Jikin sai Godiya

 Allah ya kara sauki

Ya kalli Hurriya dake labe jikin curtains din dakin.

 Muje Hurriya kar Appa ya fara neman mu

Hijabin ta janyo ya sauko ya rufe mata fuska sannan ta tako ta iso gurin Amma ta kwanta jikinta ba tare da tace komai ba ta mike tsaye, Amma ta bita da kallo har suka fice. Har sun isa gurin mota ta tuna bata shiga ta duba kanenta ba.

 Yaya dan Allah minti daya zan koma na duba Twins

 Karki dade

 Toh

Ta koma cikin gidan da gudunta ta duba su ta fito ta shiga motar, sai da suka kama hanyar gida sannan Yasir ya kalleta ya ce.

 Hurriya da gaske baki san yaron nan ba?

 Wallahi ban san shi ba Yaya

 To ya aka yi yanzu ya kira ni wai yana neman Hurriya na tambayi sunansa ya ce sunansa Adam Sarauta ina ya samu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login