Showing 210001 words to 213000 words out of 279257 words

Chapter 71 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34633

da Hurriya, Wallahi ba zan yarda ta fi yayana more rayuwa ba, bayan duk abun da uwarta ta yi min? Ta aure min miji ta zo ta yi miki a gidana yanzu kuma ta tafi yarta zata taka nairar da ta fi ta ubanta, yar mai aiki? Uwarta ta mallake min miji ta yi yadda take so ita kuma yanzu ta take mu koma karkashin inuwar ta muna daga kai mu nunata?

 Ke ni fa wani abun ma mamaki yake ba ni, anya zuri'arsu suna barin namiji a banza kuwa? Idan yaron be da hankali kuma iyayensa sai suka yarda? Ko da ba yaron kwarai ba ne?

 Captain ne fa na Soja, Nafisa ma jinsa take ballw iyayensa, kuma ko bayan haka idan ta aure shi ai ta take, nan gaba sai a fara lissafi da ita a cikin yara kanana masu arziki, Hajiya Fatee bana son Iyami bana son zuri'arta dan haka bana fatan wani abun farinciki ya same su

 To yanzu me ye abun yi?

 Abun yi ki shirya gobe a gidanki zan yi karin kumallo, mu kama hanyar kauyen nan muje mu samu malamin nan da kanmu, idan be fara aiki ba ya tada idan kuma ya riga da ya fara a kara fetur hayaki ya baibaiye ko'ina a rikita Iyami da iyalinta a karkato da hankalin mijina gareni

 Amman fa ina tsoron kauyen nan Hajiya Kaltume kin san fa irin wahalar da muka sha wacan karon, mussamman ma ni da kanana yara suka haikewa har da guziri na yo, ko dai aika zamu yi?

 Wannan zuwa da kai ne ya fi aike, yadda hankalina yake a tashe idan ban je garin nan na yi magana da Malam ba na hura masa wuta ba zan samu salama ba, duk wani tsoro ya kau min a yanzu, ai sawun giwa ya zarce na rakumi, idan ma ba zaki je ba, ni zan shirya ma tafi

 Aa ba zan bari ki tafe ke kadai ba, idan kin zo zamu tafi tare

 Sai na shigo

Ya katse wayar tana daga zanenta ta duba fitsarin da ke bin kafarta har lokacin mararta ta kasa rike su.

 Dole, wannan tashin hankali da me yayi kama? Ina ga Iyami ta dawo gidan nan kuma yarta ta auri mai kudi? Goma ta hadu da ashiri, rayuwa ta samu kenan

Ta jefar da wayar akan gado.

 Ba zan taba bari ba, ba za a mareni a tsinka min jaka ba... 




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
43

Hajiya Binta ya jinjina kai tana kara girmama labarin Allah, a duk lokacin da ake son mutun ya kunyata idan Allah yana tare da bawa ba a taba ganin abun da ake bukata, kariyace da sakamako mai kyau tare da kyau da kariya mai yawa daga Allah zuwa ga bayinsa da suka rike shi kuma suka dogara a gareshi.

 Duk wanda ya aikata wannan abun ya aikata ne saboda ya ci mutuncin Hurriya ya ci namu, ashe be sani ba yana kara kusance da mata da alheri ne

Appa yayi murmushi a yayin da yake zaune a kasa rike da sarka ya kalli Yasir dake gefensa ya mika masa sarka.

 Budewa Hajiya ta gani

Yasir ya karba ya mike tsaye ya bude mata sarka, Hajiya Binta ta saka hannu ta karba idonta na cika da hawaye.

 Allah na gode maka da ka nuna min wannan ranar, Allah ka sakawa wannan auren Albarka, kuma ka nuna min na sauran yaran

 Amin Hajiya Amin

Appa ya amsa da kansa, fadar irin farinciki da yake ciki a yanzu bata lokaci ne, farinciki da yake a yanzu ya fi wanda ya samu kansa a lokacin da aka haifo masa ita.

 Be kamata mu zauna ba Tsoho tafiya zamu yi mu sanar gidan mahaifiyarta da kuma ita yarinyar halin da ake ciki

 Haka ne... 

A nan kam sai yanayin Appa ya canja, ya sauke kai kasa damuwa na bayyana a fuskarsa. Yasir ya aje sarkar zinarin dake hannunsa ya mike tsaye ya fice daga dakin yana taba wayarsa. Appa ya bishi da kallo har ya fice sannan ya juyo da kansa ta inda Hajiya Binta take zaune ya ce.

 Ina jin kunyar hada ido da mahaifiyar yarinyar Hajiya, abun da na yi mata ban kyau ba, be kamata na aikata hakan ba, ban san me yasa na sake ta ba, kuma na kasa samun dalilin har yanzu da muke maganar nan dake, Iyami bata min komai ba face biyayya da kyautatawa, amman na saka mata da mafi munin sakamako na juya mata baya na wulakanta yaran da ta haifa min

Ya shigar da lips dinsa duka biyu a bakinsa ya rufe dantse bakin zuciyarsa na ?una da abun da bakinsa yake furtawa.

 Alhamdulillah, ganin ka gane kuskure ni a gurina abun farinciki ne, babu daren da bana addu'ar Allah ya baka ikon gane gaskiya, domin abun da ka aikata kamar baka aikata shi cikin hayyacinka ba

 Ban san me ya rufe min ido na aikata haka ba, ina jin nauyin iyayenta da ita kanta Iyamin a yanzu

 Ka kawar da komai a ranka, daman shi aure ya gaji haka, a tsaba kuma a shirya ko a yanzu dare be maka ba, lokaci be kure ba zaka iya gyara inda ka yi kuskure ka share inda ka bata, kar wannan jin nauyin ya hanaka sanar da yarka Hurriya cewar ka bada aurenta a yau, kai da kanka nake son ka fada mata wannan

Ya amsa mata da kai sannan ya mike tsaye yana hade rigarsa.

 Zamu jiraki a waje Hajiya sai ki shirya mu tafi

 Toh...

A waje suka jira Hajiya ta fito tana rike da sadakin jikarta, ta shiga baya Appa da Yasir kuma suka shiga gaba. A motar Hajiya sai godiya take yi ma Allah na yadda ya kawo auren Hurriya a kusa kuma da mutumen da ba ayi tsammani ba, Appa kuma fargaba da kunya na lullube shi a yayin da Yasir yake kara kusanta gidansu Gwaggo.

 Ni na manta ban tambaya ba, yaron dai yana da kirki ko? Murna da farinciki sun mantar da ni wannan

 Ba shi matsala Hajiya na san shi, yana da kirki kuma babu wanda zai fadi sherinsa, Hurriya ta yi dacen miji fatan mu dai Allah ya bata lafiya kuma ya basu zaman lafiya

Hajiya Binta farinciki sai ya kara ninkuwa, ta kara yi ma Allah godiya.




HURRIYA POV.

 Wannan jaraba da kuke ta fadawa Allah ya yaye muku, idan wannan ya wuce sai kuma wani ya zo, ke kin tashi baki ya bude ita kuma ido ya rufe

Gwaggo ta kalli Hindu wanda ke kallon Hurriya tana lalaben gini har ta iso gurin da Amma take zaune tare da Gwaggo da kawar Amma wato Hindu ta zauna.

 Abun da Allah yayi annabi sai ceto, likitocin sun ce wai damuwarce ta taba mata ido, amman ni ban yarda ba na fi zaton wani aikin ne aka yi mata idon ya rufe gaba daya, gashi an yada hotunanta kin ga shikenan an gama da rayuwarta, ba ido balle ta yi karatu ta gina kanta kuma babu wanda zai aureta a haka

Hindu ta rafka uban tagumi.

 Oh Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, wannan mugun kishi da me yayi kama? To ko ita ma za mu nema mata taimakon a gurin da aka nemawa Amma? Tun da gashi dai mun fara ganin haske

Amma ta kama Hurriya ta kwantar da ita a cinyarta hawaye na sauko mata.

 Mun dai ga haske Hindu, Wallahi ban dauka zan iya kara yin magana ba, na dauka kalmaina sun kare a duniyar nan, ina kallon abu na zan iya cewa a bani ba, ina da maganganu da yawa a bakina amman ba zan iya furta ko daya ba, bana iya motsa jiki bana iya komai, amman ki duba yanzu magana fa nake yi, bana jin karfi a jikina sosai amman Alhamdulillah na gode Allah

 Shi ma duk zai bari da yardar Allah, lafiya daman da rarafe take shiga a jiki har a tashi tsaye, ciwo ne yake jefar da mutum farat daya

Cewar Hindu. Kamin su daga kansu gaba daya su kalli kofar gidan, Hajiya Binta ce ta shigo Appa yana bayanta sai Yasir a bayan Appa.

 Sallamu Alaikum

Gwaggo da Hindu suka amsa mata, Amma kuma ta sauke kai kasa tana nadamar kallon Appa da ta yi kamar wanda ta yi arba da bakin maciji.

 Maa Shaa Allahu, Iyami ce a waje? Haka nake so lafiya ta samu

 Alhamdulillah, Rukkaya dauko tabarma ki kawo ma baki

Gwaggo ta amsa tana bawa Rukkaya umarni. Appa ya kasa daga ido ya kalli kowa kamar wanda ya aikata abun kunya. Rukkaya ta fito rike da tabarmar ta shimfida kusa da wanda Amma take zaune. Hajiya ta fara zaunawa sannan Appa Yasir, daman haka tarbiyar take, sai iyayen sun fara zama ake zama, idan kuma suna zaune ba ka tsaya a kansu ba sai dai rankwafa ko na zauna a kasa.

 Jama'a ina kwananku ko wuni zan ce domin dai yanzu ai 12pm ta yi

 Lafiya Kalau Hajiya ya gidan

Gwaggo ta amsa ba yabo ba fallasa. Appa ma ya mikawa Gwaggo gaisuwa, ba dan yana a gaban Hajiya Binta ba da kuma tunanin dalilin zuwansa wata kila da ba zata amsa gaisuwar Appa ba.

 Lafiya Kalau

Amma ta daga kai ta kalli Rukayya dake zaune ta ce.

 Dauko min hijabina Rukayya

A rude Appa ya dago kai ya kalli Amma, Hajiya Binta ma ta kalleta Yasir ma kallonta, dukansu sun yi turus suna mamakin jin furuci ya fito daga bakinta.

 Iyami kina iya magana yanzu?

 Allah ya nufa Hajiya

Amma ta guntun murmushi tana amsawa Hajiya Binta dake rike da baki.

 Allah da iko kake, kai Alhamdulillah yau farinciki ya mana yawa

 Amma....

Yasir ya kirata sai ta kalleshi ta yi murmushi ta amsa.

 Na'am Yasir

 Alhamdulillahi

Wannan karon Appa ne ya jaddada godiyarsa ga Allah yana kallon Amma, irin kallon da ya dauki shekaru be yi mata ba, nadama da damuwa bayyane a fuskarsa karara. Rukkayya ta kawo Hijab ta mikawa Amma, sai Amman ta karba ta saka domin tana ganin Appa da Yasir ba muharramanta ba ne a yanzu.

 Hurriya ta so mahaifinki na son magana da ke

Hurriya ta amsa kiran da Hajiya Binta ta yi mata ta tashi zaune, sai ta lalaba ta matsa gurin da Hajiya take ta zauna, Appa ya kai hannayensa ya kama nata hannayen ya juyo da ita ta fuskance sai ta nade kafafuwanta irin zaman da musulunci ya koya mana yayin da zamu ci abinci, wato ta nade kafafuwanta tana fuskantar mahaifinta.
A lokacin da Appa ya kalli yarsa sai tausayinta da kaunarta da kuma kunyarta a lokaci daya mamayeshi. Ya sauke ajiyar zuciya sau uku sai a hudu ya samu damar hada kalmomin da zai gamsar da yarsa da su ya hada guri daya ya fara magana.

 Hurriya na san kin san cewar ni mahaifinki ne, a cikin abubuwan da Allah ya dora min nauyinsu akwai ciyar da ke da shayar da ke da tufatar da ke da halak, idan kuma kin kai munzali Annabi yace na zaba miki mijin na kwarai wanda na yarda da addinsa da dabi'arsa kuma mai abun yi. Ban sani ba ko na kokarta a tarbiyarki, wata kila na yi jarumta a ciyar da ke da tufatarwa, ba zan gane hakan ba sai ranar alkiyama, a cikin kokarin sauke nauyin da Allah ya dora min, na aiwatar da wani a yau. Yake ?ata yau kina zaune a gabana ne a matsayin matar wani, wanda cin ki da sha da tufatarwarki za su koma a kansa, a yau kin shiga sahun manyan mata, a yau kin tashi daga budurwar kin zama matar aure, daga yau ladarki zata riSanyya har zuwa lokacin da za ki bar duniya, neman aljannarki a yau ya sauka daga kan kafata ya koma karkashin kafar mijinki.... A yau na aurar da ke Hurriya...

Ta daga kanta ta kalli gurin da take kyautata zaton fuskar Appa take, bata iya ganin komai saboda rashin masoya biyu, wato idanuwa, amman a haka zuciyarta take ayyana mata yadda fuskar mahaifinta take. Bata ganin komai sai duhu, sai dai makanta bata hana idanuwanta suke zubar da hawayen da tun da Appa ya fara magana suke mata zuba. Appa ya dauki sarkar dake gaban Hajiya Binta ya dora a cinyoyin Hurriya.

 Wannan sadakinki ne... An umarci iyaye su bawa yarinya sadakinta domin nata ne... Wannan naki ne Hurriya...

Hurriya ta kasa cewa komai bata jin komai sai _A yau na aurar da ke Hurriya_ haka kalmar ta yi ta maimaita kanta a kunnenta kwakwalwarta na juya kalamin.

 Aure....

Amma ta tambaya domin Mamaki ya hana Gwaggo cewa komai.

 Hajiya ban fahimta ba, wane irin aure kuma? 

 Ki kwantar da hankalinki zaki fahimta

 Ban gane na kwantar da hankalina ba, taya zai shigo cikin gidanmu kai tsaye ya fada mana ya aurar da Hurriya? Saboda ya mayar da mu talakawa? Ni ba ni da hakki akan Hurriya kenan? Wane irin magana ne wannan?

 Kin fini hakki akanta Iyami, Annabi ya ambaci uwa sau uku sannan ya ambaci Uba... Ban aurar da ita yau saboda na wulakanta ki ba, ban aikata hakan da wata manufa ba sai dan ina ganin hakan ne abun da ya cancanci ko wane uba na gari aikata, na aurar da ita ne a inda nake kyautata zaton za mutunta a rike ta amana, Iyami ki yi hakuri tabbas na yi kuskure ban nemi shawararki ba na aurar da Hurriya

 Wa ka aurawa ita? Saboda abun kunyar da ya faru ne ka yanke shawarar aikata haka?

Gwaggo ta tambaya a fusace. Appa ya tausasa murya ya ce.

 Aa Wallahi su suka zo neman aurenta da kansu, sunan yaron Jamal da ne ga Nafisa, dan wajen Alhaji Aliyu Turaki...

Hawaye ya subucewa Amma.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, me ya sa zaka aurar min da ya a inda ba a san darajar mutane ba? Macen da bata son hada hanya da talaka? Zaka dauki Hurriya ka jefa a cikin danginta? Yarinya karama ta kafa fuskantar irin bala'in da na fuskanta a gidanka, da na san haka rayuwa zata zama gaba daya Wallahi da ban aureka ba, amman kaddara ta yi min zanen da ban isa na goge ba

 Subhanallahi Subhanallahi Subhanallahi

Appa ya maimaita har sau uku sannan ya ce.

 Na san ban kyauta miki ba Iyami, amman ki tausasa ko dan yaran nan

Amma ta masa wani kallo na takaici da bakinciki.

 Yara? Wadannan twins din da aka haifa ka kasa zuwa ka tara hannu ka karba? Ko kuma an da aka kama ka ce ba zaka bada kudin fansar sa ba! Sai da na hada komai da na mallaka na bada, sannan Hajiya Kaltume ta baka umarnin biya? Ko kuma Hurriyar da ka juyawa baya?

Appa ya kasa amsawa ya sauke kansa kasa yana mai jin kunya da nauyin abun da ya aikata.

 Bari na fada maka da bakina ka ji, yata bata auru ba, ba zan bada ita a inda za a wulakanta ta ba, abun kunyar da aka yi mata kazafin aikatawa ni zan iya rumgumarsa

Ba tare da Appa ya dago kai ba ya ce.

 Iyami karki furta kalami cikin fushi

 Irin kalamin da ka furta a lokacin da na ke cikin gidanka da cikin yayanka? Irin zuwan da iyayena suka yi ka wulakanta su? Yata ba zata je ko'ina ba Haruna.... Ban amince da wannan auren ba...

Hajiya Binta ta ce.

 Adai hakuri Iyami a daina tuna baya, a bar baya ta wuce

 Haka ne Hajiya, da dan yaran nan ba da be isa ya shigo cikin gidan nan ya zauna a nan yana magana da ni ba

Appa ya share hawayen da suke masa zuba.

 Na cancanci tozarci da wulakanci da rashin mutunci a gurinki Iyami, ban kyauta ba na sani, kuma na karbi hakan

Ya kalli Hurriya dake amayar da ruwan hawaye ya ce.

 Ba zaki ce komai ba Hurriya? Wata kila ban kyauta miki ba, domin ban tsaya na ji ra'ayinki ba

Hurriya ta mika hannayenta ta kama hannayen mahaifinta ta rike.

 Hakika kai uba ne na gari Appa, ba zaka aurar da ni a inda kake tunanin zan wahala ba, ba zaka aurar da ni a inda za a musguna min ba, ko da ban gani a aikace

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login