Showing 153001 words to 156000 words out of 279257 words

Chapter 52 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34675

ba?

Yayi shiru na wasu mintuna sannan ya amsa mata.

 Na taba bata kyautar gilashi a gabanki bata karba kin tuna? Kanenta ya hanata karba saboda ya fi ni iya fitina

Ta yi murmushin karfin hali.
 Hamad din ne ya fika fitina? Anya akwai wanda ya fika fitina Captain

 Yep ai shi yaro ne yake da wannan fitinar, yayarsa ce fa amman tsoronsa take

 Kai ma ai kowa tsoronka yake saboda fitinarka Captain, gaskiya bana jin akwai wanda ya fi ka saurin fusata, fadar bakar magana, da kuma fitina

Ya tsaya ya dubeta.
 Ashe haka kuke kallona, zan baku mamaki wata rana

 Babu wannan ranar ai

 Deal

 Deal

Ta amsa tana dariya, sai ya lumashe ido ya bude ya girgiza kai.

 Ki wuce da kulolin Momy, kuma ki fada mata na gode sosai

Tana jin haka ta san ya sallame ta kenan, that's means yana bukatar ta tashi ta tafi.

 Okay

Ta mike tsaye ta nufi gurin da kulolin suke ta dauki wadanda zata iya ta fara kaiwa a mota sannan ta dawo ta dauki sauran.

 Zaka shigo anjima?

 No maybe gobe shi ma maybe

 Okay sai anjima, a sha aikin lafiya

 Thank you Sis, be a good girl please

 I will.... See you soon

Ta ja kofar ta rufe masa, tare da rakiyar wani sojan ta fita gurin zancen gilashin da ya bawa Hurriya ya tsaya mata a rai, kuma yana kokarin gushe mata duk wani farinciki da take ji na sakata neman turare da yayi. Amman what if shi ba da wata manufa yayi ba? Balle ma yadda yake da halinsa anya zai iya da tafiya da Hurriya?

 Yarinyar nan tana da shegen kyau zata iya jan hankalinsa kamar yadda ta ja hankalin Salim, gashi har yana fadar wai ta yi sa'a yana iya controlling kansa

Ta amsawa kanta da kanta tana juya sitiyarin motar, zuciyarta na raya mata karya da gaskiya deep down inside her ta san she feels jealous why zai bata gilashi bayan ta ki farko few years back, and why ma zai ce ta kawo masa abinci?

 Saboda kin tafi siyo masa turare Namra, shi ma abun alfahari ne zai saka turaren da kika siya masa so wannan ma ba wani abun daga hankali ba ne

Ta bawa kanta amsa a daidai lokacin da masu gadin gidan suka bude mata gate. Misalin karfe 8:30pm Hurriya na dakinta kwance ta soma jin kara kamar ana jifan gilashin windows dinta, bata saka ran wani zai yi haka, wannan ya sska bata damu ta tashi ta duba ba, har sai da ta ji jifan yayi yawa, sannan ta sauka daga kan gadon ta nufi windows, curtains din ta fara dagewa ta leka waje mutum ya hango sanye da kananan kaya komai fari, ta bude window tana kallon Captain dake kasa, sai ya jefar da dutsen dake hannunsa ya dago dayan hannunsa dake rike da karamin bokitin roba ya nuna mata sannan ya aje a kasa, ya nufi hanyar da kofar falon Momy yake, ta nan kam ba zaka iya hango wanda zai fito ko ya shiga falon na Momy ba. Kamar yadda wanda ke tsaye a bakin kofar baya iya ganin wanda ke sama har sai ya fito daga gurin. A bude ta bar window ta juyo da sauri ta bude karamin teburinta dake gurin ta dauko takardar da pen ta yi rubutu a jiki da girma yadda zai gani sannan ta nade takardar a hannunta ta nufi kofar fita ta bude ta sauka falon. Ko da wasa be kalli inda take ba yana ta magana da Momy dake tambayarta ya aiki.

 Aiki kam akwai shi kwana biyu nan, yanzu haka a gajiye nake i need to rest gobe ma da wuri zamu fara

 Namra ta fada min ta same ka kana ta aiki dazun, daman kuna haka ne

 Yeah idan ana karshen shekara da kuma canjin duty ana samun irin haka, lafiya kalau

Ya karashe tare da amsa gaisuwar da Hurriya take masa, sai a lokacin ya kalleta ya dauke idonsa.

 Ina Namra?

 Tana bangaren mahaifinta ko a kira ta?

 No, ni ma wucewa zan yi

 Yanzu? Na dauka abincin dare zaka ci

 No na ci abinci Wallahi, har fa na shiga gida na tuna ban siye abu ba dole na fito, shiyasa na biyo nan

Hurriya ta fice daga falon har da hadawa da sauri ta nufi gurin da ya aje mata karamin bokitin, sai da ta fara daga bokitin ta cire karamin tawul din dake sama sai ta yi arba da bakar leda da kuma fara har ta yi kamar zata bude wata zuciyar ta raya mata Momy ko Namra za su iya tararda ita a gurin dan haka ta aje masa takadar da ta rubuto tun a dakinta ta dauki bokitin ta juyo ta dawo cikin falon a daidai lokacin da Captain ya mike tsaye. Momy na ganinta ta fara masifa

 Kin fa san bana son tsautsauniya, miye haka

 Abun da na shanya dazun ne

Ta amsa da sauri tana wucewa, Captain ya kalleta irin kallon nan na ashe ita ma ta iya karya, ita dai bata juyo ba har ta shige dakinta. Har bakin kofar falo Momy ta rakoshi kamar yadda ta saba, shi kuma ya gangara ya fara sauka yana duban gurin ya hango takarda a aje, kai tsaye ya nufi gurin ya dauki takardar Momy na can tsaye kofar falon tana son sai ta ga wucewarsa sannan ta koma ciki.

 Ba zan iya amfani da wannan gilashin ba, saboda Hamad ya hanani karba, idan ina amfani da shi zan ji kamar na aikata laifi ne, yana tuna min da dan'uwana dan Allah ka ba ni nawa please

Shi ne rubuce a jikin takardar, kansa ya daga sama ya kalli window dake bude amman be ganta ba, daman ai ba zata bari ya ganta ba saboda ta san ta aje masa sako.

 Wani abun ne?

Momy ta tambaya.

 Aa takardar dana fito da ita ce dazun ta fadi

Sannan ya juya ya nufi motarsa.

 Momy da kin koma ciki akwai aikin da zan karasa a mota kamin na tafi

 Toh shikenan Captain Allah ya tsare hanya sai da safe

 Sai da safe Momy

Ya bude motar ya shiga ciki ya zauna ita kuma ta koma ciki, a lokacin ne Hurriya ta samu dagowa ta leko window kadan ta yi saurin labewa tana lekonsa ya dade a cikin motar sannan ya fito ya aje mata takardar a daidai inda ta aje masa, sannan ya koma cikin motarsa yayi mata key ya juyata ya bar gidan, sai ta ga fitarsa sannan ta fito dakin da sauri ta sauko falon, samun falon babu kowa ya saka ta ji kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha, sub sub sub ta fice kamar wanda zata yi sata ta dauko takardar bata tsaya dubawa a can ba ya dawo falon tana hadawa da gudu, domin yanzu idan Momy ta tambaye me take yi ma yawo bata san me zata ce ba, da sauri ta shige dakinta ta rufe kofar ta nufi window dinta ta rufe ta saki curtains din sannan ta zauna ta duba takardar, ganin rubutun dake jikin takardar wanda ta ba shi ne ya saka ta mamaki, ta juya baya me zata gani zanen bindiga ne pistol da karamin harsashe, (Albarushi) a jiki. Wani irin faduwa gabanta yayi sai ta ji kamar bindigar ce ya aje mata ba zane ba, daga saka kuma hannunsa ne. Ta aje takadarda tana jin kamar ta yi kuka, ta janyo sabon bikitin ta cire tawul din ciki ta dauko ledodi, leda ta farko ice cream ne da youghurt ga wata madara mai sanyi, leda ta biyu kuma cake ne da gas meat. Sai gata ta sauko kasa ta zauna ta bude gas meat din tana hadeye yawu, ta manta when last ta ci gas meat not because of babu kudin siye a gidansu, sai dan babu wanda yake damuwa ya siya mata wani abun da take so, kuma mahaifiyarta bata gidan balle ta fada mata tana son kaza da kaza. Har ta fara ci ta tuna wani abu ta yi saurin tashi ta sakawa kofar dakinta key ta dawo ta zauna ta bude Fresh milk din mai sanyi ta sha, sanyin ya ratsata har ciki zuciyarta, sai gata tana murmushi daman bakin Hurriya ya san dadi.

 Yana da kirki wannan Captain din, even though ya mareni, amma kowa yana da good and bad side right? But me yasa yake min dole? Har da bazarana da bindiga, ni dai ba zan sake yi masa magana ba maybe next time zai iya dora min ita a kai, aiko zan iya suma ma

Ta kai naman a bakinta tana taunawa dadin naman har kwakwalwarta yake kaiwa ziyara.

 Tsorata musulmi dai haramun ne

Ta fada tana turo baki. (Ni ko na ce Hurriya manya amman ba shi kayan dadi halak ne ko =??) sai ta ci naman ta koshi sannan ta rufe sauran tana jin kamar ace ita ma tana da karamin freezer kamar Yayarta Namra da yanzu sai ta saka komai a ciki ta aje. Cake din ta janyo ta bude ta gutsuri kadan ta ci, da dadin yayi mata yawa sai a tsikaro mata wani tunanin, ta tashi da sauri ta dauko takardar da yayi mata zanen bindiga ta bude gurin ajiyarta ta dauko karamin katin da wani ya bata a lokacin da aka dauke Hamad ta dauko ta hada su guri daya tana duba yanayin rubutun sa hannun hannun da handwriting din duk kala daya ne.

 Laa shi ne mutumen da ya ba ni abun nan?

Ta fada tana tuna lokacin da ta shigo falon har ta tambaye shi waye ya ce mata soja ne, ta ce yayi mata alkwarin zai taimaka ya dawo mata da dan'uwanta kuma yayi mata, mamaki ya kara cikata, har tana jin kamar ace tana da wani abokin tattaunawa ta fada masa. Da mamaki ta kwanta kamin tunanin dan'uwanta ya biyo baya, ita dai kam ta san ta yi marmarin dan'uwanta sosai, fadan da suke be hana su yin hira ko gulmar wani a tare da juna, shi zai daketa amman idan wani ya taba ta sai inda karfinsa ya kare da yana nan a yanzu ta san wasu abubuwa za su zo mata da sauki. Hawayen da ya zubo mata ne ya share ta sauko saman gadon ta nufi kofar dakin ta bude ta sauka kasa, a falo ta hadu da Namra tana cin abincin dare, ta kalli abinci ta dauke kai domin a koshe take but da ace bata ci ba babu wanda zai ce Hurriya sauko ki ci abincin, kuma idan ta zo cin zai iya zame mata matsala ace ta yi wani abu ba daidai ba. Ficewa ta yi tana daga kai ta kalli hadarin dake haduwa a sama iska ya kadawa kamar zai taso. Bangaren Hajiya Kaltume ta nufa ta shiga falon, sai da ta fara gaishe da Khairy da wata Cousin dinta ta bangaren Hajiya Kaltume da ta zo gidan, sannan ta gaishe da Salma dake playing game da Ruma.

 Kamar kin san ina nemanki, daman na ce akwai birthday wata friend dinmu da za ayi gobe zaki je?

Khairy ta fada cikin far'a. Sai Hurriya ta bata red card.

 Aa

 Why? Ki rika fita cikin mutane mana kina hutawa kina bude ido ya fi miki zama kullum a gida kuma ba school kike zuwa ba

 Ni dai na fi son zama a gida, bana jin fita gobe

 To jibi zaki je? Za a yi wani jibi ma, kuma wannan ma ina jin kamar tace zata daga zuwa jibi

Hurriya ta kalleta tana mamakin yadda take son cilasta mata fita a gobe ko jibi.

 Aa Yaya Khairy idan kika ga na fita gidan nan to wani babban abu ne ya fitar da ni, kamar duniya ko ciwo ko aika, amman ba fita haka nan kawai dan na shakata ba

 Toh.... Kika gane? Aiko zaki takura yarinyar kara ma ki sake jikinki ki yi yawa, shiyasa ko kawaye baki da idan an tashi aurenki ban san ya zaki yi ba, ke gaba daya baki son shiga cikin mutane kamar wata kura

 Ina jin dadin yin haka, na saba ne. Yayana yana ciki gurinsa na zo

Daga karshe ta tambayi abun da ya fi mata muhimmancin bayan ta bata amsa, daman saboda ta yi magana da shi ta zo bangaren.

 Eh yana dakinsa

Ta nufi stairs Khairy ta bita da harara tana yatsina fuska.

 Wannan yarinyar akwai shegen taurin kai

Jannat kalleta.

 To ke dole sai kin tafi da ita? Sai ki kyaleta mana, ni fa bana ma son shiga da kanena cikin kawayena Wallahi

 Ni ma ai dole ce ta saka akwai dalili, if not ta isa ma na tsaya ina lallabata Mtcheeee

Taja wani guntun tsaki. Hurriya da bata san wainar da ake toyawa ba haye sama ta shiga dakin dayanta bayan ta yi knocking bata ji an amsa mata ba. Babu kowa dakin sai dai tana jin motsin ruwa a bandaki tana gane yana ciki dan haka ta nufi gefen gadonsa ta zauna kusa da wayarsa, karanbani ya saka ta dauki wayarsa tana tabawa ta kawo haske amman bata bude ba sai an saka password, kamar zata cinye wayar haka ta kurawa screen din wayar ido tana kallon hoton Mama Rukayya dake jikin screen din ta yi masifar kyau ta sha makeup din zamani.

 Ke me kike yi da wayata?

Ta dago da sauri ta dubi kofar bandakin sai kuma ta yi murmushi.

 Yayana hoton Mama Rukky ne a wayarka

 To ya aka yi?

 Ba ayi komai ba

 Me ya kawo ki dakina? Gulma kika zo yi min?

Ta washe hakora gaba daya ta manta da me kawo ta ma.

 Get out

Ta mike tsaye tana dariya zata fice, sannan ta tuna dalilinta na zuwa ya juyo da ta dawo.

 Yauwa Yayana na tuna abun da ya kawo ni ma

 Minene?

 Gilashina da yake hannunka wanda na baka ajiya, tun da dadewa ka tuna?

 Na tuna, ya aka yi?

 Daya zaka ba ni please

 Why

 Zan saka ne

 Wannan da yake idonki fa?

 Shi ai shi ba wanda Appa ya siya min ba ne

 Waya siya miki

 Ni dai ka ba ni zan yi amfani da daya

 Wallahi ba duba tun a lokacin da aka taba fasa miki gialshin na bincika ko'ina ban ganshi ba, ban san ya aka yi ya bata ba

 Yaya ka sake dubawa idan ka gani ka ba ni

 Okay

 Toh, Yaya yau ka je gurin Mama Rukayya? Ko zaka je?

Ya watsa mata wata kalar harara.

 Hurriya yaushe na fara wasa da ke?

Ta fice da sauri tana dariya, a yanzu kam ta tabbatar Yayanta yana son kanwar mahaifiyarta, idan haka kuma ya kasance zata fi kowa farincikin domin dukansu tana sonsu. Bangaren Momy ta dawo ta shiga dakinta ta yi wanka sannan ta saka kayan bachi ta yi addu'a ta yi karatun suratul milk sannan ta kwanta.

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina mas????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? u fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 30

HAJIYA KALTUME POV.

Kai ta daga sama tana karewa dakin kallo wanda ya kasance na kasa ne ko'ina sai kulli kullin yawu da aka sarkafa, sai mayan allunan karfe da madubai ga kuma ruwa a kasko da karya ga kwalabe ta ko'ina kana shiga gurin zaka fahimci wane irin mutum ne, balle kuma hancin mutum yayi arba da gawurtaccen kamshi turaren aljannu dake tashi har wani juyin kai yake sakawa. Cikin hikima Hajiya Kaltume ta jinjina kai tana jin dadi, ganin take kamar ciwonta ya warke ma gaba daya. Yana shigowa cikin dakin ta gyara zamanta ta matsa baya tana kallonsa.

 Malam an shigo

Ya zauna yana fadin.

 Da dai zaki kirani da Dan masani, ko na gangare zai fi Hajiya

 Toh dan masani, sannu da kokari

 Yauwa sannu dai Hajiya

 Ya gidan ya iyali da komai

 Komai lafiya kalau, Hajiya

Ta dauko katon madubi ya dora a cinyarsa.

 Daman... 

Zata fara bayani ya daga mata hannu, ya dangwalo yawun bakinsa yayi rubutu da shi, sannan ya kalleta ya girgiza kai ya maida idonsa a gurin madubin, ya fi karfin minti ashirin a haka sannan ya dago ya kalleta ya ce.

 Kanwar Kulu ta kawo ki nan ko?

 Eh haka ne, can gidansu na fara zuwa sannan aka kawo ni nan

 Na

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login