Showing 114001 words to 117000 words out of 279257 words

Chapter 39 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34692

chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp.
5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5??


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


5??5??5? ?5?? 2? 0?


 A haka Captain yake cewa na bada hakuri na dawo da ita, be san halin yarinyar nan ba makira ce

Namra ta ce.

 Ni ma sai yanzu nake gane halinta Momy, kuma na yarda ita taje ta yo munafurcin a gidan su Husna wata kila tana yin haka ne saboda a tausaya mata

 Bata daukarwa kanta hanya mai bullewa ba kuwa, kuma ni ba zan bada Appanku hakuri akan dawowarta ba, ni ko kaunar ganinta ma bana yi a yanzu

 Ni ma shi ne, gata da fuskar tausayi da iya makirci, ban san me ta fadawa Captain na har yake son a dawo da ita, ko cewa ta yi mu muka koreta kuma? Har da wani cewa idan na sake kai Salim gidan sai na ci ubana, waya sani ko cewa ta yi na kawo mata dan'iska kuma

Momy ta sauke ajiyar zuciya.

 Shiyasa tun farko ban so zaunawarta a bangarena ba, saboda bana son ganin dan kowa a nan sai nawa, gashi nan kuma ta zo tana neman hanani zaman lafiya

Namra ta cige baki, gaba daya yau Hurriya ta yi ruining din day dinta, daman jiya ta gama sanin Salim ba ita yake so ba, yau kuma ta hada mahaifiyarta da Hajiya, ga kuma Captain da ta saka ya zage ta kuma ya zargeta da abun da bata san kuskure a cikin aikata shi ba.

 Wai yaushe ma ya dawo?

Namra ta sake tambaya.

 Ni kaina ban sani ba shekaranjiya ma na yi waya da Hajiya Turai amman bata fada min Captain zai zo, amman dai da alama yau ya shigo garin nan, duk dai zuwan nasa ba sani ake ba

 To yanzu ya zaki ce masa?

 Cewa zan yi na yi magana da mahaifinta yace be yarda ta dawo ba, ban da ma daukarwa rai ya cusa kansa a wannan rigimar

 Kika san abun da ta fada masa

 To ina ta san shi ma yaushe rabonsa da gidan nan

 Zata iya ganeshi ai, kin san ya taba marinta, tawun motarsa ma da aka fasa kika ce Hajiya ce ba Hajiya bace ita ta zuga Hamad ya zo ya fasa masa tawun mota

Momy ta watsa mata wani kallo

 Ke tsaya... Kina nufin tayun da aka taba fashewa na Captain Hamad ne?

 Wallahi shi ne

 Oh yara dai sun zame mana masifa

Namra ta tabe baki tare da duba wayarta sannan ta tashi tsaye ta nufi stairs, kamar wanda ta yi mantuwa sai ta dawo ta nufi kofa.

 Ina zaki je?

 Sakon Hajiya Binta zan isarwa Hajiya

 Dawo kyaleta idan ta matsu ta fada mata da kanta ai tana da wayarta ta kira wayarta ta fada mata mana

 Momy kara na isar mata ai, kar ni ma na yi laifin gurin Hajiya kin san bata hada Hurriya da kowa ba a gidan a nan

Momy ta dauke kai ba tare da tace komai ba, wanda ke nuna alamar ta aminta Namra ta tafi kenan sai dai ba dan ranta ya zo haka ba. Namra ya fice tana juya yawarta a hannun har lokacin sake saken yadda Hurriya ta shirya komai take, me ta fadawa Captain kuma me ya sa ran Salim ya bace shi ya fi tsaya mata a rai, har ta yi kamar ta kira shi sai kuma ta fasa ganin shi ma kamar baya son ta sani, kuma ita Yaya ce be kamata ta shige masa ba. Sai da ta kalli Khairy dake ta fito falon sannan ta dauke kai ta shiga, daman ita da Khairy yanzu babu mai yi na wani magana tun a lokacin da sa'insa ta shiga tsakaninsu saboda iyayensu. Sai da Namra ta shige sannan Khairy ta dauke idonta daga kofar falon Hajiya ta nufi gate, tana ficewa a karamin gate ta nufi babban masu gadin suka bude mata ta fita. Tafiya mai nisa ta yi sannan ta isa gaban wata mota, sai da ta fara kwankwasawa ya sauke gilashin sannan ta bude ta shiga baya ta zauna.

 Yarinyar nan fa bata nan amman baka yarda ba

 Ba zaki iya fitowa da ita ba shi ne kawai

 Wallahi bata nan, Appamu ya koreta ta koma gidan Kakarmu da zama

Ya juyo ya kalleta.

 Saboda me?

 Mumafurci ta yi shi kuma da ya ji ya koreta

 Munafurcin me ye?

 Ba abu ne da ya shafe ka ba, magana ce ta cikin gida, ni dai yanzu mu kare abun da zamu yi ina son na koma kar Yayana ya dawo ya nemi ni bana cikin gida

Ya daga kafadunsa.

 Kin san abun da ya kawo ni ai

 Ni ba zan iya maka magani ba Adam, kullum kana damuna da maganar yarinyar nan, ni fa ina da damuwa baka san abun da yake damuna ba

 Duk wata damuwa taki mai sauki ce saboda na san ba zata wuce ta kudi ba, amman ni kin san kudi ba za su magance matsala ta da yarinyar nan ba saboda kin bata komai

Cikin matukar damuwa da gundira da dora mata laifi da yake ta ce.

 Yanzu me kake so na yi? Ni ban bata ka ba Adam, kuma ba a saka soyayya da karfi ai da ka sakawa kanka ko?

 So nake ki gyara, ki gyara duk wani abu da na bata yarinyar nan ta dawo tana kula ni

 Ban san yadda zan yi haka ba Adam, kuma kai kanka ka san ba auren yarinyar zaka yi ba, ita kuma tana da wahalar sha'ani ba irin mu ba ce

 Ta ina kika karanta cewar ba aurenta zan yi ba? Ina aka rubuta hakan a goshina? Kin gani ko ke kika kara bata abubuwa

 Kai baka san yadda zaka yi ta so ka ba ne Adam, kai ba namiji ba ne, ka dame ni da zancen yarinyar kamar ita kadai ce mace a garin nan

 Ba ita kadai ba ce, amman ita nake so yanzu kuma kin san yadda zuciya ke hana mutum zaman lafiya idan be bata abun da take so ba

 Adam akwai matan da suka fi Hurriya kyau a duniyar nan, kuma babu wanda zaka ce kana so bata amsa maka ba, ita Hurriyar nan fa makauniya ce, bata gani sai da gilashi

 Ko gurguwa ce haka nake sonta...

Ya mika hannunsa a front seat daga kasa ya dauko wata ledar ta mika mata.

 Kudi ba matsala ba ce, zan iya biyanki ko nawa ni dai ina son ki ja hankalin yarinyar ya dawo gareni, kin san yadda nake daga hankali idan ina son abu

Ta mika hannu ta karba ta bude kudi da ba zata iya fadar adadinsu a yanzu, kudi ne mai yawan gaske kuma bata yi mamaki ba, daman cikin familynsu ya fi kowa wasa da kudi, wannan ya saka yan mata da yawa suke lake masa. Ta daga kai ta kalleshi

 Adam.. Me Hurriya take da shi da ya fi na sauran matan duniyar nan?

 Tana da kyau, tana da jiki da sifar da nake so a jikin mace, kuma babu ruwanta da magana ina son mace haka, and zan iya nuna ta a ko'ina as my girlfriend kowa ya gani ya san ya zabo mai kyau

 Ba zan iya sakawa Hurriya ta so ka ba Adam, ko da kuwa duniyar nan da abun da yake cikinta ka mallaka min, ba zan iya cusa soyayyarka a zuciyarta ba saboda tana da wahalar sha'ani kuma tana da tsoro, kuma ta riga ta san waye kai, ko dan gudun gargadin da Appa yayi nata da kuma Yaya Yasir dole ta guje maka

Ya jinginar da kansa yana busar da numfashi.

 But zan iya maka taimakonka ta wata hanyar idan hakan zai wadatarta kuma idan hakan zai saka ka daina dora min laifi

Ya juyo ya kalleta.

 Wane irin taimako? Ni bana da burin da ya wuce yarinyar nan ta so, abun da kika kasa fahimta shi ne yarinyar tana da karfin jini jan hankalin mutum, kuma idan ta shiga zuciyarsa tana da wuyar mantawa abun daga jini ne, baki san iya yadda na yi kokarin cire yarinyar a zuciyata ba amman sai kara shiga take har mafarkinta nake Khairy

 Ba zaka ki wannan shawarar tawa ba, amman ba yanzu za mu yi maganar ba sai idan na shiga gida sai mu yi waya

 Zamu iya maganar a yanzu ai, zai fi saboda gani ga ki

 Yayana zai iya dawowa ya nemi ne, idan kuma ya gano ina nan zamu shiga matsala daga ni har kai

 Ki fada min a nan zai fi

 Matsala ta da kai kenan Adam, ba ka daukar shawara kuma baka yi ma mutum izuri, kanka kawai ka sani ni ina kokarin ganin na cireka a matsala kai kuma kana son jefani, ba abu ne na tashin hankalin ba na ce ka bari na tafi gida idan na natsu sai mu yi magana kamin lokaci ma wata kila na kara samun mafita

Ba dan ransa ya so ba ya sauke ajiyar zuciya ya daga mata kai.

 Shikenan, amman zan fada miki gaskiya idan kika ci wannan kudin ban samu abun da nake so ba

Ya tsaya tare da busar da iskar bakinsa.

 Ba zan duba abotar mu ba, kuma kar yi mamakim duk abin da zan miki

 Hakan ma ba zata faru ba

 Okay

Ta bude motar ta fita sannan ta miko hannu ta dauki kudin, be bar gurin ba sai da ta shige cikin gida. Sai da Khairy ta nemi guri ta boye kudin a Garden saboda tana tsoron Hajiya ko Yayanta ya ganta da kudi mai yawa haka a leda, tsayawa ta yi ta natsu sannan ta dawo ta nufi kofar falon.

Ruma na zaune tana kallon Hajiya Kaltume dake ta zuba ruwan bala'i na sakon da Namra ta isar na Hajiya Binta, ji take kamar ace mahaifiyar mijin nata tana kusa da ita ta amsa mata daidai da abun da ta aiko aka fada mata.

 Wato ta koma can zata fara hada mu da Hajiya ko? Ita dai Iyami ta kawo mana bala'i kawai a cikin gidan nan ta hana mu zama lafiya, na kashe maciji amman ban tare kai ba shi ne a nan, yar guda guda ta zame mana fitina a gida

Ruma ta kalli Hajiya Kaltume cikin yanayin bakinciki har idonta na cika da kwalla ta ce.

 Haba Hajiya yanzu kuma me ye laifin Hurriya a nan, fadan da Hajiya Binta take yi saboda abun da kuke mata ne, kuma gaskiya ta fada, da ni ce ko Khairy ba zako bari wani na tafi ba, ita ma Momy da Namra ce ba zata bari ta tafi ba, amman kalli yadda Appa ya koreta kamar wata bare, Hajiya komai sai kin dorawa Amma laifi matar nan bata lafiya magana ma wannan bata iya, shin ya kuke son Hurriya ta yi? Ta rasa dan'uwa mahaifiyarta babu lafiya yanzu kuma Appa ya koreta kuma still ita kike dorawa laifi

Hajiya Kaltume dake jin kamar ya janyo Ruma ta rufe da duka ta shiga fada a tsawa.

 Da uwarta bata zo ta aurar min miji ba duk zamu san da wannan matsalar ne? Da yanzu za a haifi Hurriya har ta fara hada munafurci ne? Da take kwance bata da lafiya ni na saka mata ne? Mugun bakin kwadayinta ne ya ja mata

 Momy ma Appa take aure, amman baki mata masifa kamar yadda kike yi ma Amma, Amma tana son mu tana nuna mana kulawa tsabanin Momy da ko bangarenta bata son mu shiga, kuma idan har suna da laifi to duk laifinsu daya ne domin Appa suka aura

 Ke yarinya ki iya bakinki, idan baki san gari ba saurari daka, banbancin Iyami da Nafisa ai a bayyane yake, Nafisa a can ya ganta ya auro, Iyami kuma sai da ta gama cin duduniyata ta san sirrin gidana da na mijina sannan ta kulla min gadar zare ta zubar da ni a kasa, ke ba zaki gane abun da ake ji ba, saboda ke yarinya ce baki san me duniya take ciki ba sai nan gaba

 Ko da hakan ta kasance a gareni, ba zan tsaneta kamar yadda kika tsani Amma da Hurriya ba, da ina ganin kamar ke ce mao gaskiya amman daga lokacin da aka kashe Hamad, sai tunani ya canja wane irin tsana ce zata saka a kashe rai? Idan Amma tana da laifi Hamad fa? Me ya aikata? Yaron nan yana kuka yana kiran sunan Appa da mahaifiyarsa suka fitar da shi, kansa na jini yana ihu yana fadar ayi hakuri yana rike kansa dake jini yana kiran sunan Hurriya daga karshe ma sunana ya koma yana kira, Hajiya na kasa manta wannan duk lokacin da na kalleki wannan abun nake gani, amman ni cewa kika kar a taba ni saboda ina yarki wace irin zuciyata ce wannan?

Hajiya Kaltume na mikewa tsaye Khairy na turo kofar falon ta shigo da sallama. Hajiya ta yi saurin kallon kofar idonta kamar za su fado saboda razana.

 Wa'alaikussalam

Ta amsa mata muryarta na yin kamar zata yi rawa. Khairy ta karaso cikin falon tana musu kallon tuhuma domin jiki da fuskar Hajiya Kaltume ya nuna alamar ba lafiya ba, ga Ruma sai kuka take sosai.

 Lafiya?

 Lafiya Kalau

Hajiya ta amsa mata da sauri, Ruma ta tashi tana kuka ta nufi stairs, Khairy ta bita da kallo har ta haye sannan ta kalli Hajiya da hantar cikinta ke kadawa ta ce.

 Me ya faru take kuka?

Abun ka da makiri kuma wanda karya bata yi ma wahala a take Hajiya ta juye abun domin bata son kowa ya ji.

 Munafurcin da Hurriya ta yi ne ya taba ta

 Munafurci?

A tsaye Hajiya Kaltume t????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? a zubewa yarta komai da Namra ta fada har ma da wanda bata fada ba, daman ai ba zata bar miya haka nan ba sai ta kara mata gishi da magi.

 Wallahi kawai ki fadawa Appa shi zai yi maganinta idan ba haka ba, shi ma kansa sai ta hada shi da Hajiya, waya sani ma ko ta zugota ta zo tace ba ta yafe masa ba, ko kuma ta rantse sai ya sake ki, daman tana da haushin barin gidan nan da uwarta ta yi, shiyasa ni gaba daya fa bana kaunar yarinyar nan, ga iya jan hankalin maza na bala'i kamar wata rikakkar karuwa

 Wannan kuma ba banza ba, ai kin san uwarta sai ta wanke ta bata sha, kamar yadda ta sha ta dauke hankalin Alhaji har ya aureta

 Gaskiya ni ma i doubt wannan farin jini da jan hankalin ba banza ba ne, ba zai yuyi ace kowane namiji farar mace mai kyau yake so ba, to mu ayi yaya da mu bakake?

Tana fada tana bata rai kamar ta ci magani.

 Ba farin ne kawai ba, har da asiri

 Daga gani ma ba banza ba, Hajiya tafi ki fadawa Appa ya daukar mata mataki tun wuri

Ta zauna saman kujera tana ta fushi kamar an mata wani abu, kamin ta shiga Gallary wayarta ta kamo hoton Hurriya ta kura ido tana son tantance abun da Adam ya gani a fuskarta da jikinta da ya nace sai ita, ga Fadeel ma ko a jiya da ya zo sai da ya nemi yin magana da ita.
Hajiya Kaltume da har lokacin a tsaye take ta juya ta nufi kofar dake gefen dinning wanda zata sadata da bangaren Appa, zuciyarta fal da tsoro na maganar Ruma, yanzu ba kisan ne abun da ke ranta ba, fallasar asirinta ne abun da yafi damunta, shekara uku amman Ruma ta kasa mantawa ta saka sakewa gaba daya ta canja tun a lokacin da wannan abun ya faru, idan kuma har zata rika sakin baki haka wata rana dole asirinta zai tonu, ita ta san har ga Allah bata ce a kashe Hamad ba, ba saka an dauke shi dan a kashe shi ba, hasalima ba shi aka je dauka ba, Hurriya ta ce a dauka, tsaitsayi ya biyo ta kan Hamad ashe da rabon ya bar mata baya da kura. Bata san ta isa bangaren Appa ba sai da ta ji ta bugi kofar shiga, a nan ta sauke ajiyar zuciya ta rufe ido ta dafe kanta da hannu daya.

_Kai wayyo Allah... Da na sani ban aikata wannan abun ba, da ma ta asiri na bi kamar yadda na yi ma Iyami, duk gajin hakuri ne ya ja min, yanzu ko yaran nan aka kama suka fadi sunana ai na shiga uku sunana zai bace a duniya, yarana su ji kunya musamman ma matan nan_

A ranta take ta sake sake rashin natsuwa da tashin hankali na kara kusantar ta, ta sauke ajiyar zuciya ya kai sau takwas sannan ta sauke hannunta ta murda kofar ta shiga, babu kowa falon dan haka ta nufi karamin falon Appa da ya fi yawan zama. Yana ganinta yayi saurin sauke wayar da yake ya yanke kiran murmushin dake fuskarsa ya bace.

 Hajiya

Ta zauna kusa da shi tana fada.

 Na'am Alhaji a nan ake hutawa, Nafisa bata shigo ba?

 Ina tunanin sai an jima kadan zata shigo

Yayi saurin rejecting kiran dake shigo masa ya saka wayar silent ya aje ta a gafe.

 Toh bari na yi magana ta kamin ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login