Showing 258001 words to 261000 words out of 279257 words

Chapter 87 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34699

Allah

Ya sumbanci gefen fuskarta yana kallonta wani irin sonta da son kwanciyar hankalinta ke fisgarsa. Be bar gidan ba sai da mutane suka fara zuwa daga yan'uwansa da na Appa da na Amma musamman wadanda ba garin suke ba.

CAPTAIN POV.

Ammy ta aje tea cup din dake hannunta tana kallon danta.

 To waye kuma da wannan aiki?

 Za mu gane,? kuma ko waye sai ya dandana kudarsa

 Ko yar'uwarta ce?

 Bana tunanin haka, saboda asirinta ya tonu, kuma bana jin Adam ne domin? ya fada cewar ba shi ba ne ko a yanzu!

 Ko ma dai waye ya kamata a hukunta shi a yanzu, domin ya wuce gona da iri kuma ba kai kadai ne da fadan ba har da na mu domin idan hotunan suka sake yaduwa har da mu za a taba

 Mutum daya nake zargi.

 Waye

 Bana son fada, amman gaskiya zata yi halinta, and if i find out shi din ne, zan masa ba dadi

 Zan yi magana da aka daddynka san fada masa a zafafa bincike ta bangarensa ma ko zamu samu wani abu, and ka kula da gidanka domin? wanda zai iya yi ma Iyalinka haka zai iya neman rayuwarka ko ta matarka ko ma ya sake yin wani abun da zai zubar da kimarka, gashi yarinyar ba gani take ba be ma kamata a barta ita kadai a gidan ba

 Na barta ne just for today and tomorrow saboda masu zuwa, amman bayan nan idan zan fita nan zan kawo ta sai idan na dawo sai na dauke ta mu wuce

 A madadin haka ka rika kaita a gidansu mana ko kuma ka dauki mai kula da ita tun da ka ji ka gani zaka iya

Ya dan yi murmushi.

 Nan din ma gidansu ne ai saboda gidanmu ne, Ammy kina son yarinyar nan fa ki daina boyewa

 Au boyewa nake ma?

 Idan ba shi ba, miye na danka mata key mota? Duk soyayya ta dake fa baki taba siye min mota ba, amman ita gashi kin siya mata sabuwa, sannan kika bada kayan bikonta

 To ya zan yi? Na yi abun da ya kamata uwa ta yi ne, ba ni da wani zabin ne

Yayi dariya sosai yana kallon mahaifiyarsa cike da farinciki.

 Ni dai tarewar ne a haka be min dadi ba, da dai ka hakura har idon ya bude da abun ya fi armashi gaskiya

 A yanzu din ma babu abun da ya ragu Ammy, ina farinciki da matata kuma ba wai bana son duba idonta din ne a yanzu ba, akwai planning din da nake, ina son nan da two years....

 What...! Baka da hankali ashe..!

Ya dan bata fuska.

 Ammy ni?

 Taya zaka auro yar mutane ka ajeta har nan da two yrs sannan a duba idonta? Wane irin plan ne wannan? Hummm uhmm you better not, karka kuskura gwada wannan, iyayenta ba za su yarda ba ai

 Karkashin ikona take yanzu

 Haka ake aure a garinku? Dan tana karkashin ikonka iyayenta ba za su yi mata abun da ya dace ba, gaskiya be kyauta ka ajeta a haka har two yrs ba ai sai ta wahala kara dai a gwada idan ma ba a dace ba ansa ba a dace ba ne amman ba wai haka nan kawai ba

Yayi murmushi ya taso daga inda yake zaune ya zauna kusa da uwarsa.

 Kin gani ko Ammy kina son yarinyar nan Wallahi gashi kin damu da ita...

 Ni shawara ce kawai nake baka, idan ta ni ne ka barta har sai nan da shekara goma ma babu abun da ya dame ni

Side hug yayi mata yana dariya.

 Ammyna i love you s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?o much...

Ta yi murmushi kadan tana tabe baki.

 Ka ji da shi, ku yaran zamani sai dai abi yadda kuke so ba yadda iyaye suke so ba

Ya sake yin dariya ya mike tsaye ya fice daga dakin, haka ya fito harabar gidan ya gaisa da mutane cousin dinsa mata suna ta tsokanarsa. Sai da ya shiga motarsa sannan ya kira Nafi'u ya aika masa da wata number.

 So nake ka yi min hacking din account din da yake jikin number nan, ka duba duk wani abu da ke cikin chat din maybe zamu samu wani abu da muke nema, ka yi duk yadda zak iya ka duba komai na account din

 Okay ranka ya dade

****? ?? ****? ?? ****

A WEEK da bikin auren Hurriya Amma da Gwaggo suka tafi Ummara tafiyarsu da kwana biyu Momy ta tafi tare da babbar ?ar Appa wato Sapna Momy kuma ta biyawa yarta Namra suka tafi tare duk kuwa da kasancewar ta taba zuwa ba sau daya ko biyu ba. Hakan kuma ba karamin taba ran Hajiya Kaltume yayi ba, a nan ta fara shige shigenta ko zata samu kamin Momy da Amma su dawo Appa ya daura aure da ita kuma ya juyawa Momy da Amma baya, amman yi take kamar tana shuka dusa, ga ciwon kafa ya sakata gaba amman ta kasa tsayawa ta maida hankali gurin neman lafiyarta kokarinta na yadda zata koma karkashin inuwar mijinta ne a yanzu.? Bata da wani buri da ya wuce wannan kuma duk inda zata saka kafa ta gabatar da bukatarta za su karbi kudinta su ce za a mata aiki mai kyau kuma Appa zai juyo ya nemata haka ma aurensa da Amma ba za a maida ba. Babu abun da ke daga mata hankali a ciwon kafarta nan kamar yadda idan an bincika ake ce mata babu wani rauni ko wani ciwo a gurin amman kuma ita tana jin azabar ciwon da ko tafiya bata iya yi daidai yanzu. Tana shan wahala sosai gurin hawa da saukowa a stairs har bata son yin ko daya sai idan ya zame mata dole. Yau ma kamar kullum ta sauko tana ta wai wai wai da kafar har ta zauna. Yasir yayi saurin yanke wayar da yake ganin Hajiya ya aje wayar gefe ya maida hankalinsa gurin tv.

 Me kake ayi nan? Yau baka da aiki ne?

 Ina da aiki sosai ma Hajiya, gyaran gidan da Appa yace za'ayi ne mutanen nake jira su iso

Wani kallo Hajiya Kaltume ta yi masa na rashin zato balle tsammani.

 Gyaran gida za'ayi? Ba mu da labari

 Ni ma ban sani ba, kawai ya kira ni yace min na jira kar na fita da wuri so that idan sun zo na nuna musu lungu da sako na gidan

 Ikon Allah to gyaran gida na minene? Na ga dai ko auren Hurriya ba'ayi gyaran gidan nan ba, baka fada min shi yasa aka gyara gidansu Iyami ba? Amman ba a gyara nan ba, to yanzu kuma gyara me za'ayi

 Wallahi ban sani ba Hajiya, kin san ba komai ne Appa yake shawara da ni ko ya sanar min ba, amman dai ko minene ai zamu ji

Hajiya Kaltume ta sauke wani dogon numfashi tana jin wani sabo na tukare mata a kahon zuciya.

 Ya kafar taki?

 Da sauki

Ta amsa irin amsawar dake nuna hankalinta baya gurinsa.

 Da dai kin daure kin fita a duba kafar nan kar abu ya zame miki babba fa, Appa ma na ji yana zancen yana son fita a duba lafiyarsa shi da yake lafiya ma kenan balle ke da ciwon kafa ya matsawa ya kamata a bincika ko minene

 Zan yi Yasir akwai abun da yake gabana yanzu, ina son na gama da shi ne tukuna

 Minene Hajiya?

 Be shafe ka ba

Ta mike tsaye cikin jan kafa da dingishi ta sake haurawa sama ta shiga dakinta zuciyarta har rawa take kamar zata fado. Ta zauna bakin gadonta ta rasa me zata yi kuka ba mafita ba ne, to miye mafita, yanzu tana ji tana gani Amma zata dawo gidan nan?? Ko kuma dai sabon aure Appa zai daura.

 Na shiga uku na lalace..

Ta fashe da kuka. Ta lalabo wayarta ta kira Number sabuwar kawarta Hajiya Larai dake ke karata gurin masu magani a yanzu.

 Subhanallahi Hajiya kamar fa kuka kike yi..

 Ba dole na yi kuka ba, ciwo ya dame ni ga kuma auren nan Alhaji jin sa zai yi ko kuma ya maida iyami abun duniya ya isheni Hajiya Larai, kullum sai ramewa nake ga ciwo ga bakinciki

 Komai zai warware Hajiya Kaltume karki damu kanki, kin ga duka malaman nan da na kaiki gurinsu sun iya aiki babu wasa babu kama hannun yaro kuma tun da aka yi musu biya mai kyau ki saka ido zaki ga yadda komai zai tafi daidai

 To ai abun ne kullum shiru Hajiya Larai abu sai kara gaba yake, yanzu fa har Alhaji ya saka ayi masa gyaran gida, ni dai ina tunanin ko zan bo ta bangaren Hajiya Binta ne idan na je yi mata barka da dawo na bata hakuri ko abubuwa za su daidaita, wani abun fa dole sai ana saka baki

 Karki kuskura zubar da kimarki Hajiya Kaltume da yardar Allah sai Alhaji ya zo yana kuka yana neman yafiyarki

 Toh Allah yasa, da wacan Malamin ne da ya rasu da yanzu aiki ya fara amman su babu wani motsi har yanzu

 Gaggawa aikin shaidan ne ki saka hakuri sa sannu zaki ga aiki yayi, kuma yanzu ma idan mun gama wayar nan zan sake shiryawa na tafi gurin Malam na gangare na sake masa bayani

 To sai na ji ki Allah ya taimake mu

 Amin

Ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya.




***?? ****?? *****
Ya shafa fuskarta sannan ya tsika ci abarba ya kai mata a baki, daker ta dago daga kirjinsa ta bude baki ya saka mata.

 Tauna mana haba Baby, an fada min gida ma fa haka kike yi ba ki wani cin abinci, shiyasa ko kibar amarci da kowa yake yi ke baki yi ba, sai dai ni na yi

 Daman ni bana wani cin abinci

 Ai mantawa na yi na ce Amma ta roka mana ki rika cin abinci tun da Hajiya ta dawo balle na ce da ita

Hurriya ta yi dariyarta mai kayatarwa.

 Har da cin abinci sai an roka

Ya sumbance ta.

 Eh mana, yanzu ma ba mu yi latti ba, cikin week din nan za su dawo kamin su dawo zan fada musu su roka miki cin abinci

 Daman na sha addu'a a gurin Kakata Hajiya Binta tun tana Saudi gurin Ummara har ta dawo addu'a take min, su Amma ma da suke can addu'ar suke ta mana Allah ya tsaremu ya bani lafiyar ido ya sa a yi aikin cikin nasara da sa'a.

 Amin ka ji yar gata, ta ko'ina roka miki ake

Ta dago kamar tana ganinsa.

 Allah yasa kamin mu tafi aikin nan su dawo

Ya kai mata kiss a goshi.

 Da wahala gaskiya, mu da zamu tafi jibi su kuma sao karshen satin nan za su dawo ai

Ta bata fuska.

 Ko ka daga har wani satin please

Ya kwaikwayeta yana jan hancinta har ta turo baki gaba yadda ta yi.

 Ko ka daga har wani satin please

Ta daga hannu zata dokeshi sai ya rike hannu ya matse har sai da ta yi kara sannan ya sake ta yana dariya.

 Ke ba ganin kike ba sai fitina, ka ji min mata haka kika fitini zuciyata kina dukan kirjina har sai da kika shige ciki...

 Ba wani nan kai ne daga ganin yar yarinya kyakkyawa ka cusa kai har da wani ba ni chocolate da gilashi kana saka ni cin abinci dole a office dinka

Ya zaro ido yana dariya.

 Ta nan kika bullo kuma

Ta nauyi cikinsa.

 Yanzu duk sai na rama abun da ka yi min har da marina da kai yi

Ta lalaba fuskarsa ta kai ma kumatunsa cizo har sai da yayi ihu ya rumgumeta yana dariya yana mata chakulkuli.

 Na daina... Na daina...

Ta yi dariya sosai har da su dari.

 Ki biyani chocolate din da kika ci nawa, daman na rubuta duk abun da kashe miki ai ba dan Allah na yi ba

 Ka fadi ko nawa ne, idan Saurayi Captain ya zo zai biyaka, amman fa soja ne kana yin wasa zai harbeka yana da fushi sosai

Yayi dariya ya cigaba da tsakalar cikinta tana ihu da dariya a lokaci daya.


Two days later... Jirginsu ya tashi daga Abuja tafiyar awa hudu da mintuna 40 suka yi sannan suka sauka Addis Ababa babban birnin Ethiopia. A Oasis hotel apartment /Haya Hulet suka sauka Hotel ce mai kyau da aka wadata a abubuwan more rayuwa. Mama Rukayya da ta kasance yar rakiya daga bangaren Hurriya sa kuma Momy Ikilima daga bangaren Captain suka sauka a daki daya, Captain da matarsa kuma suka sauka a daki daya, sai wanda suka zo da shi domin hidima shi ma aka ba shi nasa dakin dabam. Kwana biyu a hotel din Hurriya na tafiya kwararrin likitocin da suke Bethel Hospital, addis Ababa, Landmark General Hospital, Medical center hayat hospital MCM suna duba idon, daga karshe dai aka yanke shawara yi mata aiki a Medical Center Hayat Hospital MCM, saboda kwarewar aikinsu da kuma kyakkyawar alakar dake tsakaminsu da wani na kusa da Hurriya.

Ana gobe za ayi mata aikin ta tsora sosai duk kuwa da irin karfafa guiwa da tabbacin da likitocin suka bata cewar za'ayi nasara. Har yanzu zuciyarta bata yarsa 100% idonta zai bude ta samu lafiya kamar kowa ba, ganin tun haihuwa take da ciwo har zuwa yanzu d ta girma.

 Baki yarda da ni ba? Baki yarda za'ayi nasara ba? Baki yarda Allah zai iya warkar dake ba? Baki yarda Allah ya karbi addu'ar da ake ta yi miki ba?

Ta kwantar da kanta a kirjinsa.

 Na yarda, kawai ina tunanin idan ba ba ayi nasara ba, zan tabbata a haka ne har abada

 Za'ayi nasara da yardar Allah

Ya kwantar da ita kan gadon ya fara kissing din wuyanta, tana ta kokarin hana shi amman be saurara mata ba sai da ya raya daren kamar darensu na farko har tana masa kuka a yanzu din ma. Da asuba shi ya taimaka mata ta yi wanka suka yi sallah, ta hau gado da niyar bachi kamin lokacin zuwa asibitinsu yayi, a nan ma be bar Hurriya ta huta ba, sai da ya sake gajiyar da ita har tana masa miya. Misalin karfe daya na rana suka isa asibitin aka wuce da ita dakin da aka ware mata na musamman sannan aka fara yi mata wasu treatment din. Ba a shiga aikin da ita ba sai karfe bakwai na yamma. And the most expensive news is anyi aikin cikin nasara sai dai babu tabbacin ko zata gani daidai ko kuma irin na da ne ko ma idon be bude gaba daya ba sai idan ta bude idon, hakan kuma ba zai samu ba sai nan da sati idan idonta ya warke. Daga ranar da aka yi aikin suka saka mata dokokin na abun da zata ci ko ta sha da irin motsi ko aikin da zata yi. Sun bada damar mayar da ita gida ayi jinyarta kamin ranar da za a bude idon, sai dai Captain ya zabi ta zauna asibitin saboda ta fi samun kula kuma ya san a gida ko a Hotel din da suka sauka zata iya karya dokarsu.

A asibitin Hurriya ta yi jinyar idonta for one week, ranar da za a bude idon ba ita kadai ba har Captain da Rukayya da Iyayensu dake gida da fargaba suka wuni na tsoron rashin nasarar aikin. A hankali aka fara warware daurin dake idonta har aka cire, ita kanta ta ji alamar nasara a tare da aikin domin tana iya jin haske a idonta dake rufe tun kamin ta bude.

 Hurriya can you open your eyes please....

Ta fara motsa ido da take jin kamar ya like mata. Wani likitan an ganin haka ya dauko wani magani ya diga mata a idon dake rufe.

 Open it slowly...

Ta bude idon a hankali, sai dai bata iya daga shi sosai yayi mata kamar na masu shan kwaya (Irin na Ummu Falsak) sai dai tana iya ganin abun da yake gabanta da dishe dishe hakan kuma ya faranta ranta.

 Don't let tears drop

Ta yi kokarin hade kukanta bayan dayan likitan ya bukaci haka. Sai ta sake maida idon ta rufe sannan ta bude a hankali. Fuskar Captain ta fara cin karo da ita kamin ta bi sauran Likitocin hudu da suke dakin da kallo dukansu farar fata ne kamar kasa mijinta babu daya da ta sani.

 Alhamdulillah

Captain ya fada yana durkusawa kasa yana kallonta tsabar farinciki.

 Congratulations

Cewar Likitocin suna tabawa kansu kowa ne na gaisawa da dan'uwansa. Captain ya dago ya rumgume ta yana farinciki.

 Ina gani yanzu ina gani ina gani Alhamdulillah

 Daman na fada miki za'ayi nasara gashi kuma anyi

Hawaye ya sauko mata tason ta share tana tsoron saka hannu a gurin, blink din sa take da idonta ma ganin take kamar idan idon ya rufe ba zai bude ba. Captain ya sumbance ta a gaban Likitocin sannan ya sake ta ya juyo.

 Dukansu sun yi kokari gurin aikin nan Baby Aisha Alhamdulillah, wannan shi ne Dr Camil, sai a Dr Nille....

Haka ya bi yana gabatar mata da Likitocin da suka yi nasarar yi mata aikin Maza uku mace daya tana musu godiya.

 Bayan su akwai wani matashin yaro mai karatun Optometrist.. Wato likitan ido who will perform medical and surgical treatment for eye condition, shi ma ya kamata a gode masa, domin tare da shi aka yi aikin a kokarinsa da yake na koyon aikin kuma duk saboda ke ne, ina da yakini Allah ba zai kunyata shi ba shiyasa na yarda 100%

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login