Showing 15001 words to 18000 words out of 279257 words

Chapter 6 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34638

duk daya yanzu

 Alhaji, dan Allah na ci wannan alfarma dan Allah ko dan yaran nan, mahaifiyarsu ma tunaninsu sai ya isheta kuma kai yanzu baka lura Hamad fushi yake da kai ba?

 Fushi me?

 Ka kore mahaifiyarsu mana

 Ba kin cw bata fada musu ba?

 Eh amman ka san shi ya yafi yar'uwarsa wayo, ba mamaki ya gane, ita kanta Hurriya idan ta fahimta ba zata jidadi ba

Appa ya sauke ajiyar zuciya.

 Ba zan iya ba ne Kaltume, gobe za a zo da motoci akwaishe mata kayanta

 Subhanallahi Alhaji har saki nawa ka yi mata ne?

 Daya

 Amman za akwashe kaya da wuri haka? Wai me yayi zafi ne shi ba wuta ba? Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Ta fashe da kuka ta mike tsaye ta fice daga dakin tana rusar kuka kamar gaske. Appa ya busar da iskar bakinsa shi kansa ya san it's too early ace an kwashe kayan Amma a gidan daga sakinta, sai dai kiran da Bappa yake masa yake son amfani da damar ya nuna musu babu sauran zama tsakaninsada Amma, domin ya kasa amsa wayarsu tun jiya saboda be san abun da zai fada musu ba. Kai ya gigirza sannan ya tashi tsaye ya fice daga part dinsa zuwa part din Hajiya Nafisa wato Momy.


HURRIYA POV.

Hurriya na shiga bangaren Hajiya Kaltume ta samu Umm Khairi zaune a dinning tana cin nata abincin daren, da a bangaren mahaifiyarta ne sai da ta bude ta zuba amman a nan dole ta tsaya a zuba mata ko kuma a bata izinin zubawa.

 Yaya Khairi Hajiya ta ce na zuba abinci

 Gashi nan ai dauki plate ki zuba mai isarki

Hurriya ta dauki plate ta bude manya warmers din ta ta dauki mulmular tuwon da aka nade a leda ta raba uku ta zuba daya a plate ta rufe ta bude dayan ta zuba miyar kubewa anye ta saka nama da man shanu sannan ta rufe ta ja kujera har ta zauna ta tuna bata wanke hannu ba ta tashi ta shiga bandakin dake falon ta wanke hannunta ta dawo ta zauna ta fara cin tuwon, sai da ta yi nisa da cin abincin sannan Khairi ta kalleta.

 Hurriya

Hurriya ta dago a hankali ta kalli yayarta Khairi wadda ta kira sunanta.

 Na'am?

 Me Appa yace miki da ya aiko a kira ki?

 Tambayarmu yayi ina muke son zama

 Toh ina kika zaba?

 Ni dai na ce gurin Gwaggo ko Hajiya, amman yace aa sai dai gurin Momy

Khairi ta yi fuskar tausayi.

 Allah sarki, Wallahi na tausaya muku babu dadi rayuwa gidan babu uwa a gida, da ma dai Appa zai yi hakuri da ya dawo da Amma, Hurriya na ga Appa yana jin maganarki why not ki roke shi ya dawo da Amma idan ma wani laifin ta yi masa ya yafe mata

Hurriya ta yi mata wani kallo na rashim fahimtar inda zancenta ya dosa.

 Amman zata dawo idan ta haihu ai

 Toh Allah yasa ya maida ita, wata kila akwai gyara ai Wallahi duk ban jidadi ba dazun har da kukana

Hurriya na jin haka sai kwakwalwarta ta dauka sarai ta gane karatun Khairi a take wani irin tashin hankali ya same ta, idonta dake cikin farin gilashi suka cika da hawaye ta kasa hade lomar tuwon dake bakinta. Slowly ta mike tsaye taja kujera baya ta fara tafiya zuciyarta na buga kamar zata fasa kirjinta ta fito, tana fita falon ta watsa da gudu bangarensu da karfi ta tura kofar falon Amma ta shiga. Hamad na kwance kan kujera yana kallon remote a hannunsa.

 Hamad wai Appa sakin Amma yayi? Wai rabuwa suka yi? Yaya Khairi ta fada min

Tana maganar yana kuka even though bata gama tabbatarwa ba. Hamad ya tashi zaune yana kallonta.

 Ai ke ce mahaukaciya shiyasa baki gane ba

A nan Huriyya ta samu damar fashewa da kuka mai karfi, ta juya da sauri ta nufi bangaren mahaifinta.



*** *** ***

 Ah Ah Alhaji ina ce Kaltume ce Babba a gidan nan? Me zai hana su zauna a bangarenta?

Appa ya mike tsaye.

 A nan nake son su zauna, kuma nan za su zauna ko kin yarda ko baki yarda ba, domin ke da su duk a karkashin ikona kuka kuma a gidana

 Aa Alhaji gaskiya ban ci ?ashi ba ba zan ci aman tsoka ba! Har ina? Yara da girmansu da komai a kawo min su? Da wani abun arziki ne ai matarka take tarewa ta karbe sai a yanzu da yake wahala ce za a kawo min

Appa ya nuna kansa.

 ?a?ane wahala Nafisa? Ke dai har abada ba zaki taba zama matar kirki, har abada mai hali be taba fasa halinsa ba, kowa yana girma yana kara hankali da hali na gari amman ban da ke

 Daman ni ban taba haske a idonka ba, masu haske Iyami ce da Kaltume, ka san ni ka san halina ni bana son a shiga sabgata ina bangarena babu ruwana da kowa, akan me yanzu za a dauko yayar sarauniyar gida mace da ta hana ka ganin martaba a kawo min

Alhaji Haruna ya nuna ta da yatsansa.

 Sau daya tak bakinki ya sake furta wata magana marar dadi akan Iyami da yayanta sai mugun saba miki, ni na zabi su zauna a nan kuma a nan din za su zauna, idan baki son zama da ?a?ana jinina ?ofar gidan a bude take..!

Momy ta aje numfashi da karfi.

 Bismillah ga dakuna nan su zabi wanda suke so su zauna, gidan naka ne yaya naka ne ni ma taka ce Allah ya ba mu hakurin zama

Fuuuu! Appa ya fice daga falon nata cikin mugun bacin rai. Namra da Musib suka bishi da kallo su kansu sun manta when last su ga mahaifinsu a cikin bacin rai irin wannan sai yau.

 Tsakani da Allah takurawa ce dawowarsu a nan, musamman ma dan iska yaron nan Hamad ni ubansa zan ci Wallahi

Cewar Musib yana jin haushin hukuncin da mahaifinsu ya yanke. Bakinciki ya hana Momy sake cewa komai ta kai hannu ta dauki sarkar zinarinta dake kan aje a hannun kujera ta mike tsaye ta nufi upstairs, kamin ta isa dakinta ma wani aiki ne saboda izza da isa kamar wadda bata son taka kasa haka take tafiya.

Bakin gadonta ta zauna ta rike da sarkar sai cika take tana batsewa, ita dai ta san tana daga kafa akan kishi da matan Alhaji Haruna domin ganin take babu sa'arta a cikinsu Hajiya Kaltume dai yar talakawa ce arzikin na Alhaji Haruna Mai Yadi ne, Iyami ma haka rufin asirinsu na Alhaji Haruna ne domin har gidan da iyayenta suke ciki a yanzu shi ya siya musu shi yake dauke da nauyinsu.

Kuma Iyami ba sa'arta bace a shekaru, kuma ta fi Hajiya Kaltume zama makaskanciya a idonta domin ita ga aiki ta zo yi a gidan ta aure Alhaji Haruna, ba dan ma da kaddarar aure ta hana ba kuma yara sun shiga tsakani ba wata kila da ba zata iya hakurin sharing miji daya da yar aikin gida ba, kallon da take yi ma Amma bata da ajin da zata yi kishi da ita sai idan abun ya motsa.
Ita dai abun da ta fi tsana shi ne a shiga sabgarta, idan ta shiga sha'aninta na masu arziki har mantawa take da Hajiya Kaltume da Amma, a yanzu kuma kawo mata Hurriya da Hamad da Appa ya dage sai shi ne abun bacin ranta a yanzu, domin da su zauna a gurinta kara ya dawo da uwarsu ta rainin abunta, sam sam Momy bata son yayan kowa idan ba nata ba, bata mutanta kowa sai masu kumbar susa, idan baka da arziki har ganin take kamar baka cika mutum ba.
[10/18, 5:34 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: https://chat.whatsapp.com/GJ9hOtbWbfDKmq8NrKsDIG


&A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2ܠ? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?


5???5???5???5??? 6??

Da tunanin Amma Appa ya dawo apartment dinsa, tsansar biyayyarta da yadda take gujewa bacin ransa da nuna kulawa akan duk wani abu da ya shafe shi. Ya tabbatar da ita ce ba sai ya bukaci a bawa Hurriya abinci ba, matukar ta san uwar yaran bata gidan zata yi kokarin kwatantan kyautata musu kuma ta ja su a jiki, haka ma da ita ce ya zo mata da zancen dawowa ?a?an abokiyar zamanta a bangarenta zata yi marhabun ta karba da hannu biyu ko da kuwa bata son haka ba zata nuna har ya gani ba, duk wani abu da Amma ta san Appa yana son kokarin raya shi kaunar abun take ba ta bata masa rai ba.
Hannayensa hade a bayansa yake tafiyar fuskarsa a yanutse zuciyarsa a hargitse yana jin kamar ya fashe da kuka gaba daya ya rasa me ke samunsa ya rabu da matarsa rabuwar ta haifar masa da rashin kwanciyar hankali da bacin rai, zamanta a gidan kuma masifa ce a gidansa masifar da be san ta micece ba domin shi dai ya san matarsa bata masa laifi ba, be san dalilin da ya saka ya tsane ta ba. Kukan Hurriya ne abun da ya fara masa maraba da zuwa a lokacin da ya kunna kai cikin falonsa, kuka take sosai irin kukan nan da ya hana gilashin idonta tsaya saboda hawayen da ke cika shi, ta rike gilashin a hannu lipa dinta da jikinta sai rawa suke, dishe-dishe ta ga alamar shigowar mutum bata bukatar saka gilashi domin tantance waya shiga, ta san tsayinsa da yanayin tafiyarsa ta haddace komai. Shi ya taho da sauri ita ma ta nufo inda yake da sauri tana rike da gilashin dayan hannunta kuma yana lalabensa.

 Appa. ..apa... Appa... Appa wai ka rabu da Amma?... Sakin Amma ka yi?

 A gurin wa kika ji wannan maganar Hurriya? Waya fada miki haka cikin daren nan?

 Yaya Khairi.... Appa da gaske? Appa why? Yanzu mu kadai ne zamu rasa uwa a nan Appa! Me Amma ta yi?

Tambaya take tana wani irin kuka numfashi na fitar mata da karfi kamar ranta zai fita. Idon Appa ya cika da hawaye

 Bata yi komai ba Hurriya, be kamata ki shiga cikin magana irin wannan ba, zauna a nan ina zuwa

Ya nufi kujera da ita ya zaunar da ita, ya juya ya fita gaba daya abubuwa sun rike masa har ji yake wani abu na juya masa cikin kai, kamar za a haukata shi haka yake ji. Bangaren Hajiya Kaltume ya nufa tun a tsakar falon ya fara kiran Khairi rai a matukar bace daman ciwon sakin Amma da ya kama shi, ga bacin ran da Momy ta saka masa yanzu kuma Khairi ta kara masa wani ta hanyar batawa Hurriya. Umm Khairi ta fito daga dakin Hajiya tare da Maama Umm Ruman na biye da su a baya, Umm Salma da Yasir kuma suka fito a nasu dakuna duk suka sauko kasa.

 Alhaji Lafiya?

Cewar Hajiya Kaltume da ta riga su saukowa gabanta har faduwa yake.

 Akan wane dalili Umm Khairi zata fadawa Hurriya sakin mahaifiyarta aka yi? Ita mahaifiyar bata fada ba sai ke yar iya? Wannan ba rashin hankali da rashin tarbiya ba ne? Ki shiga cikin maganar iyayenki?

Ya juya gurin Hajiya Kaltume.

 Kin ga abun da kika hanyo ko? Kin maida yaran nan kawayenki da maganar da ya dace da wanda be dace ba duk fada kike a gabansu, har suna jin sun isa sun kai su saka baki a zaman takewar mahaifinsu, sai na koya miki hankali sai na koya miki hankali Ummul Khairi

Jikinta ya dauki rawa domin ta san halin Appansu idan hau yana wuyar saukowa. Yasir ya karbawa Appa.

 Iskanci ne da rainin hankali, ta fi uban kowa baki da bakin iyayi a gidan nan kamar wata babbar mace, yau sai kin fadi wanda ya aike ki

Hajiya Kaltume na jin haka ta yi saurin zunguje Khairi.

 Ba zaki bada hakuri ba yar iskar yarinya? Idan kuma ba haka ba ne sai ki fadi yadda aka yi ai ko?

 Appa Wallahi karya take min, yarinyar nan munafukace sai dai idan labe ta yi, ko kuma so take ta hada min sheri

Tana rufe baki Yasir ya fara dukan bakin nata ya saka hannnunsaya kama lips din ya jan sai da ta ti ihu sannan ya rufe ta da duka gaba daya, Hajiya Kaltume ta fara kokarin kwatar yarta Appa kuma ya fice daga falon ba tare da ya hana Yasir dukan Khairi ba.

 Ai fa an taba yar gata yar gaban goshi yar lasa da halshe, kai dan Allah karka kashe min ?a saboda ?ar wasu da ba zata amfana maka komai ba

Hajiya Kaltume na masifa tana kwatar Khairi dake ta rusar ihu, Maama da Salma sai haushi suke ji saboda ana dukan yar'uwarsu Ruma ce kadai take jin abun da yayarta ta yi bata yi daidai ba.

A bangaren Hurriya Appanta na fita sai ta tsagaita kukanta ta share hawayen da suka ki tsaya mata ta saka gilashin da zai bata ganin kofar fita dakin daidai ta mike tsaye ta fito daga bangaren mahaifinta ta dawo na su bangaren tana tafe tana hawaye har ta isa. Sai ta ta tura kofar falon ta bude sai kuma ta kasa shiga domin jin take kamar Amma ma mutuwa ta yi ba barin gidan ba bata taba sanin haka kewa take ba sai yau da ta yi kewar mahaifiyarta. Kusan da ita da wanda ba shi da lakka a jiki duk daya domin tun a yanayin tafiyarta zaka fahimci zuciyarta ta karaya salulu ta shigo falon ta zauna kan kujera har lokacin Hamad na zaune a inda ta barshi, sai dai a yanzu fuskarsa na nuna danuwar dake zuciyarsa domin ya bata rai sosai ba kamar dazun ba d ya bar abun a cikin zuciyarsa. Fashewa Hurriya ta yi da kuka tana girgiza kai ji take kamar ace mata ba gaske ba ne, da ace ta san sakin Amma Appanta yayi babu abun da zai hana ta binta, da ba zata yarda ta zauna a gidan ba, a yanzu kam ta yarda ita wawuya ce da bata yi saurin ganewa ba, domin tana da saurin yarda idan aka fada mata abu dauka take ko da kuwa ba gaskiya ba ne. Kukanta ne ya saka Hamad hawaye yana ta dantse baki yana boye cikarsa domin zuciyarsa kawowa take kamar wani zaki, amman sai duk da hakan sai ya gagara rike kansa shi ma ya fasa kuka, ita da shi suka zama kamar wadanda aka cewa Amma ta mutu ta bar su.

 Hurriya Hamad

Kusan a tare suka dago suka kalli kofar gefen Dinning din kofar da Appa ke tsaye, kofar cikin falon Amma ce dake basu damar shiga bangaren Appansu. Hurriya ta tashi da sauri ta nufi inda yake tana kuka sosai Hamad kuma ya dauke ido alamar baya son ganin Appa.

 Wannan kuka sai kace an yi mutuwa? Haba karku saka kanku a damuwa tsakanin halshe ra hokora ma ana basawa balle kuma mutum da mutum, dan tsabani muka samu shi ne Amma ta tafi gida, amman da zarar al'amurra sun daidaita zata dawo

Hurriya ta kasa magana sai kuka take, Hamad kuma ya mike tsaye ya share hawayensa ya nufi sama.

 Karka shiga, ba a nan zaku kwana ba, na yi magana da Momynku a can zaku kwana ku zo muje

Be jira cewarsu ba ya kama hannun Hurriya zuciyarsa na masa babu dadi, daman can shu baya son kukan wani ko ganin wani a damuwa balle kuma yaransa, sanin cewar shi ne silar damuwar ya saka shi jin babu dadi gaba daya abubuwan sun zo masa ta yadda be yi zato ba. Ganin Appa ya nufi kofar fita falon tare da Hurriya ya saka Hamad ya bi bayansu, sai da suka fita harabar gidan gaba daya, sannan Appa ya tsaya ya tsayar da yarsa ya daga kanta ta kalleshi.

 Haka zamu shiga bangaren Momynki kina ta kuka Hurriya? Dan Allah ku yi hakuri idan ba so kuke ni ma na yi kukan nan ba, ba ku san abun da yake cikin zuciyata ba, ina cikin wani irin tashin hankali da rudani marar misaltuwa

Kai kawai ta iya daga masa ta saka hannayensa ta share hawayenta tana ta aikin hade kukan dake neman ya gagari tsayawa a iya bakinta da idonta.

 Ammanku ba mutuwa tayi ba, zaku iya zuwa ku ganta a duk lokacin da kuke so, ita zata iya zuwa ta ganku, Hamad na san kai ne mai zuciya ka sakawa kanka hakuri dan Allah ko dan yar'uwarka

Ko saitin gurin da Appa yake tsaye Hamad be kalla ba, yadda ya dauke kai yana kallon wani gurin sai ka rantse da Allah ba da shi Appa yake magana ba, domin a yau kam ba shi da abokin tsana kamar Appansa saboda sanin cewar ya rabu da Amma, ko da kuwa ba zai iya fadar abun da ya faru tsakaninsu ba, hausawa suka ce mai lalabe a duhu balle an haska masa, a banza yayi fushi balle an taba shi. Appa ya dauke kai ya rika hannun Hurriya suka cigaba da tafiyar, da kansa ya shiga falon, be zarce ko ko'ina ba sai Stairs kai tsaye ya nufi dakunan da suke gefen bedroom din Momy kamar yadda suke a kowane bangare, ya san dakin Namra da na Musib da Miwan dan haka be taba dakunansu ba ya nufi wani dakin ba dabam ya tura kofar dakin sannan ya saki hannun Hurriya daki ne dake dauke da furniture na mutum daya domin Appa ya saka an zuba furniture an gyara ko wane daki duk kuwa da kasancewar wasu dakunan babu kowa, ba dan komai ba sai dan irin haka ko kuma idan an yi baki ko ma idan yaransa sun yi sha'awar canja daki daga wani zuwa wani. Hurriya ta daga kafarta ta shiga cikin dakin ta isa bakin gadon da zai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login