Showing 237001 words to 240000 words out of 279257 words

Chapter 80 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34647

ba Wallahi ban yi tunanin rana zata zo irin wannan ina raye ace bana tare da mahaifiyar Hurriya ba

 Haba wacan maganar ai duk ta wuce, sai dai ayi fatan Allah ya tsare gaba

 Amin Bappa

Appa ya kalli dan'uwansa Alhaji Musa, Alhaji Muss na ganin kallon da Appa yayi masa ya fahimci inda ya dosa sai yayi hanzarin cewar.

 Bappa idan da hali ai sai a kira mana ita Iyami, akwai maganar da zamu yi da ita akan sha'anin bikin nan

 Toh babu matsala zan turo ta yanzu

Bappa ya tashi ya fice daga falon da aka gina daga waje domin baki. Cikin gidan Bappa ya shigo ya zauna a kujerar roba dake aje kusa da Amma.

 Mun yi magana da shi na fada masa yadda muka yanke, yayi ta godiya kuma ya kara da bada hakurin abubuwan da suka faru

 A Duk lokacin da ya zo sai ya bada hakuri, shi kam ya fahimci mun hakura mana, gashi ana abubuwa gwanin sha'awa ma

 Ni ma dai shi na gani, daman shi aure ai ya gaji haka, tare da wani dan'uwansa ya zo shi yace suna son ganin Iyami akan maganar Hurriya, na fada masa zan turo shi

Amma ba zata iya cewa ba zata je ba, domin Bappa ne mai fadar ya fada musu zata zo, ta ina zata ki umarnin mahaifinta, sai dai ita kam da za'abi ra'ayin zuciyarta sam bata son kebewa da Alhaji Haruna a yanzu, ba dan ta tsane shi ba, sai dan ta san maganar da zai fada ba zata wuce sake jaddada bada hakuri ba. Amma ta aje turen farin waken dake jikinta ta yunkura ta tashi tsaye ta nufi daki, Babba Hijab ta dauko ta saka ta fito ta saka talkamin ta kofar fita tsakar gidan sai kuma ta juyo kamar zata kira yaranta su tafi tare, sai dai gudun abun da Gwaggo zata ce ya saka ta juya ta cigaba da tafiyar.




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? https://chat.whatsapp.com/ExyBEuiZZ0J1ivlVK5lIOx



Amma na yi sallama Appa ya mike tsaye yana amsawa kunyarta na rufe shi, ba yau ne karon farko da ya ganta bayan rabuwarsu ba amman yau ta fi cika masa ido saboda ya kebe ne daga shi sai ita sai kuma kanensa dake tare da shi a yanzu.

 Hajiya an wuni lafiya

Iyamin da yake ce mata a da yanzu yayi masa nauyin furtawa duk da kasancewar ya girmi Amma nesa ba kusa ba. Amma ta amsa tare da zaunawa ta mikawa Alhaji Musa tasa gaisuwar.

 Lafiya Kalau Iyami ya hakuri? Ya gidan?

 Alhamdulillah, ya wajen su Larai?

 Lafiya Kalau suke, dan Allah Iyami a dai kara hakuri rayuwa sai da hakuri kullum kalubale sabo yake zama

 Babu komai Alhaji Musa an mun saba da jarabawa, Allah dai ya kara mana imani

 Amin amin haka ake so, Alhaji bari na jira a waje

Ya tashi ya fice daga falon Amma ta bishi da kallo tana mamakin yadda yawancin yan'uwa suke goyon bayan hukuncin dan'uwansu a daidai ko kuskure, domin tun da suka rabu da Appa bab da Hajiya Binta babu wanda ya taba takowa a cikin yan'uwnsa da suna duba yaranta ko ita ko ya jajanta mata abun da ya faru, amman yanzu saboda Appa ne yake son zuwa gurinta da kansa gashi Alhaji Musa ya rako shi babu ko kunya ashe da rasuwa Appa yayi haka za su wofintar da Iyalinsa kenan! Bata samu amsar tambayar da ta yi ma kanta ba ta tsinkayo Appa yana fadar.

 Fatar dai duk kuna lafiya

Ta maida kanta kasa ta amsa a takaice.

 Ina Hurriya?

 Tana can dakin Rukkayya kawarta Husna ce ta zo suna can tare

Kallonta kawai yake sai a yau yake ganin ramarta, ta yi rama sosai tun daga lokacin da ta bar gidansa damuwa ta saka ta a gaba ciwo kuma ya rufeta sai ya abun ya zame mata biyu ga tunani ga ibadar ciwo. Sai dai ramar bata karawa Appa komai ba sai tausayinta da kaunarta a ransa.

 Bappa ya fada min hukuncin da kika yanke, zan iya sanin dalilin da ya saka kika cire kanki

Tambaya yake kamar mai lallaba yaro.

 Babu komai daman ai abun da ya shafi Wan fari ko ?ar fari wasu ne suke shiga gaba su yi ba mu da muka haifeta ba, ni dai al'adar mu ta Fulani da Malam Bahaushe haka na sani

 Haka ne amman yanzu wannan ai duk ya kau Hajiyata, da dai za'ayi tafiyar nan dake zan fi jindadi

 Ba saboda kanmu zamu yi ba ai, ba dan jindadinmu ba, saboda yara zamu yi wanda su ne silar da ya saka na zauna a nan saboda Bappa ya fada min cewar kana son magana da ni akan Hurriya

Appa yayi murmushi ya san halin kayansa ko a lokacin da take gidansa idan ta yi fushi bata iya ba.

 Hajiyata kenan, yanzu miye laifi idan na kiraki mun gaisa? Na san ba zaki fito ba ne sai da dabara shiyasa shi Alhaji Musa yayi haka, amman gaisuwa ce kawai

 Toh na gode

Ta yunkura zata mike tsaye sai ya saka hannunsa aljihu ya dauko daurin kudi ya tashi a inda yake zaune ya isa gabanta ya aje kudin.

 Ki shigarwa Bappa da wannan

 Aa Bappa...

Be bari ta karasa ba ya tare numfashinta.

 Ba na ki bane, balle ki ce ba zaki karba ba, na Bappa ne dan haka karki saka kanki a ciki idai ba kina jin wani abu a game da ni ba, Hajiyata a bar komai ya wuce mana, baki san iya damuwar sa faruwar abun nan ya haifar min ba, yadda Hurriya da yaran nan ma suke kallona wani abu ne da na kasa sauke nauyin da a yanzu nake jinsa, ban tana tunanin zamu kai ga aurar Huriyya ba ma tare da juna ba, amman haka aka rubuta mana dole haka din ne zai kasance

 Komai ya wuce Alhaji, babu amfanin ka yi ta nanata hakuri a duk lokacin da ka zo, ni na riga da na watsar da komai, daman shi aure ai kowa ya san Allah ya hallata saki a cikinsa, Hurriya ma da ka batawa gashi yanzu kana ta gyarawa yaran ma kanana ma yanzu kana jansu a jiki ai komai ya wuce

 Fata ma nake nan da wani lokaci kankane su koma gida tare da ni

 Na san kana da son yara Alhaji amman dai zaman a zai fi a kusa da ni ko Gwaggo

 A can din ma ai kusa da ke ne ke zaki rike kayanki Hajiyata har ma da wasu yayan idan Allah kaddara mana sai mu samu

Amma na jin hakan ta fahimci gurin da Appa ya tafi ita bata je can ba, har a kasan zuciyarta ta san ta yafewa Appa kuma ta kawar da komai, amman zancen komawa gida a yanzu ko nan gaba ba abu ne da take da buri ba, domin ta dandana bata ji da dadi ba.

 Bari na shiga ciki

Ta duka ta dauki kudin.

 Hajiyata baki ce komai ba, ko da yake ya kamata na bari a gama Hidimar Hurriya amman gajin hakuri da nadama sun hana yin haka, Wallahi yanzu ina da buri mai yawa na son kyautata miki fiye da baya, ina son a saka ki alfahari da ni a matsayina na uban yayanki Hajiyata

 Wai ina ka bar Iyamin ne nikam Alhaji?

Appa yayi murmushi ya aje numfashi cikin hikima da kwarewa ta magidanci mai Iyali.

 Yayi min nauyi a yanzu, wata kila dai zan iya fada a gaba, wata kila kuma zan cigaba da fadar Hajiyar ne har zuwa bayan dawowarki Ummara ke da Gwaggo da Bappa

Ya saka hannunaa aljihu ya ciro wasu takardu ya mika mata, Amma ta kurawa takardun ido gabanta na faduwa, tana tuna wacan ranar da ya mallaka mata takardun gidan da bata ci amfaninsa ba kuma takardar rabuwarsu.

 Ki karba mana Hajiya, dan Allah karki ce zaki maida wannan, shaidan kadai yake maida hannun kyauta, kuma ba naki ne ke kadai ba har da na iyayenmu, ina son bayan an gama hidimar bikin Hurriya ke da Hurriya ku tafi yi ma Allah ibada

 Wannan duk an minene Alhaji? Na siye ne da iyayen ko miye?

 Su dai iyaye na kyautatawa ne, ina ta tunanin abun da zan yi musu na kyautatawa sai na ga babu abun da ya dace kamar wannan, ke kuma bana bukatar siyenki ai, yara sun riga sun bude min hanya, ko ayi dan ni ba ayi dan yara, rokon yafiyar da nake ma kawai ina son na kankare zunubi na ya yake gurinki kuma ya goge bakin fentin da zuciyarki ta yi min, domin bana son wata rana idan mun koma ki kalleni a matsayin Appan Hurriya kamar yadda kike kira a baya ki tuna cewar na yi miki wani abu ba daidai ba, amman komawa kam wajib ce ko ki yarda ko karki yarda umarni ne zan yi kuma dole ki bi

Amma bata san lokacin da hawaye suka zubo idonta ba murmushi kuma ya cika fuskarsa, yau Appa rayuwa yake aiwatar a gabanta irin yadda suka saba a baya kamin abubuwa su chabe musu.

 Allah ya saka maka da aljanna ya rabaka da Hajiya Lafiya ya yafe zunubanka ita kadai ce godiyar da zan iya maka a yanzu

 Godiyar kenan, a daura auren ma idan tafi Ummara kina dawowa ki tare a dakinki idan ma baki bukatar zama a wannan gidan ni zan iya gina miki sabo da irin samfurin da kike so Hajiyata

Amma ta rausayar da kai cikin yanayi na farinciki da damuwa domin a tsorace take har gobe.

 Ya Salam Alhaji...

 Ahhh to Hajiya a free zan baki kujerar Ummara ki tafi ki dawo ki auri wani? Saboda ga Alhaji Haruna Mai Yadi Shashasha ko hmm?

Dariya da kanta ta yi mazauni a hakoran Amma har sautinta ya fito tare da hawaye. Farin cikin da ya kwana biyu be ziyarci zuciyar Appa ba ne ya ziyarce a yanzu saboda ganin murmushin amaryarsa uwar yarsa Hurriya abar kaunarsa mai yawan biyayya a gareshi.

 Haba ko ke fa, ni na san ban saba cewa eh ki ce a'a ba yana daga cikin abun da nake yabonki da shi a kullum idan na tashi fada ko tuna, dan Allah karki fara a yanzu, ba halin kirki ba ne, wannan kafewar ma ban san inda kika aro ba, domin ba halinki ba ne baturiyata

Amma ta saka hannu biyu ta karbi takardun ta koma ta zauna speechless tana kallonsu. Appa kuma ya ciro wayarsa dake ringing ya amsar wayar yana mamaki kiran da ya kwana biyu be shigo wayarsa ba sai yau.

 Wa'alaikussalam

 Na'am Alhaji Hafeezu

Appa yayi shiru na dan lokaci sannan ya ce.

 Aa ina wani guri mai muhimmanci amman dai yanzu zan tafi gida, mu hadu a can

Ya katse wayar ya saka aljihun gaban rigarsa da babbar riga ta tare sannan ya kalli Amma ya ce.

 Hajiya zan tafi gida yanzu, daya daga cikin iyayen maneman auren Khairy ne ya kira ni a waya, ya ce yana bukatar ganin a zai same ni ni kuma na fada masa mu hadu a gida zai fi, tun da ga Alhaji Musa ma a tare da ni sai mu ji ko minene

 Allah yasa mu ji alheri

 Amin, kuma dan Allah ki fadawa Bappa ba sai ayi min godiya ba, kar ya kira ni na ki dagawa yayi zaton wani abu, Wallahi godiyar ce bana bukata, kuma ina jiran kiranki idan an saka ranar tafiyar kar lokaci ta matse

 In Shaa Allahu

Amma ta amsa da murmushi, shi ma murmushin yayi.

 Na gode uwar biyu

Ya fada sannan ya fice ransa fes buk'atarsa ta biya, hakarsa ta cin na ruwa. Daga gidansu Amma kai tsaye gidansa ya nufa tare da Alhaji Musa yana bawa Alhaji Musa labarin irin biyayyar da Iyami take masa wanda abu ne da duk wanda yake kusa da shi ya sani. Yayi mamakin tarardar mutanen da ba zai iya kiransu da baki ba a gidan domin shi da su suna kusan zama surukai ne a matsayinsu na iyayen Fadeel. Tun a waje Appa ya gaisa da su sannan yayi musu iso suka shigo cikin falonsa suka zauna tare da shi, ganin yanayin fuskarsu dake dauke da damuwa ya saka Appa be yi wata hubbasa gurin ganin an kawo musu wani abun tabawa ba, domin alamu ya nuna ba farinciki ne ya kawo su ba, sai kishiyarsa.

 Toh Allah dai ya sa lafiya, irin wannan ziyara da rana tsana ba tare da wani abu ba

Wanda ake kira da Alhaji Hafeezu ya yi gyaran murya ya kalli Appa cikin kyautata ladabi ya ce.

 Alhaji la??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fiya amman ba lau ba, wato maganar ce da nauyi shiyasa na ce zamu sameka a inda kake ban so mun zo nan gida ba sai dan ka bukaci hakan, domin ka yi mana karamci da hallacin da be dace ace mun furta wata magana makamancinyar wannan ba a gidanka

Appa yayi murmushi mai cike da takaici.

 Karka damu Alhaji Hafeezu daman na saka tsammanin faruwar hakan, tun a lokacin da abubuwa masara dadi suka faru a gidana, na shiryawa fuskarta ko wane kalar kalubale, kuma na san zancenku ba zai wuce ku ce Fadeel ya janye daga zancen neman auren Khairy ba?

Sai duk suka kallo juna ganin yadda yayi saurin harbo jirginsu. Appa ya sake fadada murmushinsa.

 Karku ji komai, yayi abun da ya dace kowa yana son auren yar kwarai, kuma ita kanta Khairy ba wai bata da tarbiya ba ne, kaddara ce dai irin wanda ta saba fadawa bawa, shi kuma yayi abun da yake ji ya natsu da shi ne, babu ta inda zai zama mai laifi a gurin kowa, ni din nan ma mai shiga gaba ne a nema masa aure idan ya samu wata yar da yake so

Appa ne mai magana Alhaji Musa kuma ya fara fada yana ganin kamar hakan be dace ba, Fadeel din be rumgumi kaddara ba.

 Kayya dai assha dai..! Ba haka aka so, amman yara ne basa jin shawara kuma basa jin maganar manya na su hangen dabam yake, ya same mu sa zancen ne kuma yace shi ya janye, mu kuma muka ta inda aka hau ice ta nan ake sauka, da ace ya janye jikinsa kuma baka ji wani bayani daga garemu ba kamar hakan be dace ba, a matsayinmu na iyaye

Appa ya sauke ajiyar zuciya daman ya san za arina, sai dai kuma jin albishirin be masa dadi ba, ko kadan domin yana neman mai kwashe masa Khairy ne a yanzu da shi kansa baya sha'awar ganinta.

 Yaro yana da gaskiyarsa kowa yana aikata abun da yake jin natsuwa da shi ne, a addini ma ance ka bar abun da kake kwankwato zuwa ga wanda baka yi, ba wani abu ba ne

 Mun gode Alhaji mun gode da Fahimta

Alhaji Musa zai sake magana Appa ya dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu. Suka tashi suka fice cikin kunyar sakon da suka isar.

 Alhaji be kamata ka yi haka ba, taya zasu same ka har gida da wannan maganar?

 Sun yi abun da ya dace Alhaji Musa, haka ake son iyayen na gari su kasance sun warware ne saboda su suka nema masa aure, to da ace anyi tsammanin shi zai aureta ko kuma mu ji shiru a kara tun wuri su sanar mana, kuma yana da gaskiyarsa babu namiji da zai son auren mace kamar Khairy saboda abubuwan da aka fada ta yi ma yar'uwarta ta jini, balle kuma ga maganar Fyade ta shigo ciki kuma ka san yadda society mu suke daukar abun da girma

Cikin takaici da Allah wadai Alhaji Musa da ya kasance kane ga Alhaji Haruna ya ce.

 Ummu Khairy bata kyautawa kanta ba, bata kyauta ba ban jidadi ba ta bata maka suna ta lalata rayuwarta ina amfani haka

 Idan ma akwai amfani a yanzu ta gani idan ma babu kuma ta gani, Allah ya shirya mana zuria

 Amin, yaran ne yanzu hankalinsu da tunaninsu sai ka rasa ina yake zuwa, ita na Hurriya saboda bata aikata ba ne Allah ya dubeta ya kawo mata wannan yaron ban da haka ai da sun zame maka su biyu abun babu dadi

 Ko su goma suka zama zan iya dauka Alhaji, yadda kaddara ta rubuta ai haka za a wanke a sha, Allah baya aje kayansa ga wanda ba zai iya dauka ba,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login