Showing 120001 words to 123000 words out of 279257 words

Chapter 41 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34684

dai ta yi kuka, saboda bata iya magana, tana da abubuwa da yawa a zuciyarta da take son ta tambayi Hurriya amman babu baki, ita kuma Hurriya bata yarda ta yi hirar gidansu da ita, domin ba abubuwa masu dadi ne zata fada ba, ko da Gwaggo ta tambaye ta, ba zata fada ba sai dai tace tana zaune kalau. Cikin wani yanayi na tausayi da kauna da soyayya irin ta uwa zuwa ga yarta Amma ta mika hannunta dake rawa ta kama hannun Hurriya idonta na cika da hawaye..

 Minene Amma? Bana cikin damuwa a yanzu, Appa ya maida ni gurin Hajiya Binta, kin san yadda take so na ai, ita tace min na shirya na zo nan na wuni, saboda na kwana biyu ban zo ba, ashe zan zo na farar da farinciki ne, gashi na ganki Amma kina cin abinci

Tana maganar tana sharewa mahaifiyarta hawaye a idonta. Twins din Amma suka zo da gudu suka kwanta jikinta suna ta son yin fitina, da Amma ta kallesu sai ta ga sun hadu su uku babu daya, da Hamad yana raye da yanzu yayanta sun cika hudu cif.

 Hurriya yau ji take kamar ta cinye Amma saboda murna?

Hurriya ta saka dariya tana kallon Rukayya dake taje kanta.

 Mama Rukayya da kun fada min Amma ta fara motsa hannunta da sai na saci hanya na zo

 Shiyasa ai ba a fada miki ba, ki saci hanya ki zo nan wannan Kalwar ta hada ki da Appanki, kin ga wannan mai fuskar yan wuta kiris ya rage ta shigeta, na tsani kamar nan kamar mutuwata

 Yanzu ai bana gidanta na koma gidan Hajiya, kin ga zan samu sauki, Hajiya bata hana ni zuwa ko'ina balle ma kuma idan nan ne

 To ya aka yi kika koma wai?

 Ita ta rarrashi Appa kuma ya yarda

 Wata kila ta ga wahalar da kike sha a gidan ta miki yawa ne

Hurriya dai ta yi murmushi bata sake cewa komai ba, domin bata son a zafafa a maganar. Bayan sun yi Sallah la'asar ta fito tsakar gidan ta zauna tare da Amma, twins kuma suna ta wasansu kamin ta su fado kanta saboda tsokarnasu da take, sai aka jone ita da su aka rasa waye karami, ita da kurciyarta bata gama fita jikinta ko kuma su da a yanzu suke tasowa. Ana daf da fara kiran Sallah Magariba, Hurriya ta shiga ta dauko hijabinta da jakarta domin sun yi da Hajiya Binta zata wuni a nan ammam ba zata kai dare ba.

 Gwaggo zan tafi, Hajiya ta ce kar na yi dare

 Toh kin koshi dai ko? Idan kuma kina son dan'waken ki tafi da shi

 Aa na koshi a bawa yan biyu a ciki

Sai suka saka dariya yana mulmula kan katuwar tabarmar da Gwaggo ta shimfida. Hurriya ta kai kasa tare da kai bakinta a goshin Amma ta sumbanci, goshinta ta sumbanci gefen fuskarta dama da hagu.

 Ina sonki Ammana Allah ya baki lafiya

Amma ta yi murmushi tana binta da kallon da raunataccin idanuwanta. Gwaggo ta kalli Rukayya dake hankalinta ke kan waya ta ce

 Ba zaki rakata ba? Ke dai kullum kina nan a waya, sai ta saka ki hauka idan baki yi hankali ba

Rukkaya ta kyalkyale da dariya.

 Gwaggo littafi ne nake karantawa na Khadeeja Candy, mai suna Mairo wai an bata apple ta ce a kara mata gorar binni, wai yan binnni gorabar taushi ne da ita

 Kyaje can ta shirmenki, kullum ai cikin karatun littafi kike, tashi ki karata ta samu Napep

Rukayya ta mike tsaye har lokacin dariya take, sai da ta shiga ta aje wayar ta sako hijabinta sannan ta fito tana gyara talkamin kafarta.

 Mu tafi yar gidan Gwaggo, ke ko kishinki bata yi sai fada take min ban raka kishiyarta ba

 To idan ma ba yar wuta ba, wace kishiyar ce zata yi kishi da Hurriya baiwar Allah, kifi musulmin nama

Hurriya ta yi dariya, ita kanta Gwaggo dake maganar dariyar ta yi, kamin ta raka da addu'a, Amma kuma ta bita da kallo tana dan murmushi kadan. Tare suka isa da Rukayya har titi suna tafe suna hira, Rukayya sai tambayarta take wai halin Hajiya Kaltume na nan ko ta daina.

 Me zata daina kuwa Mama Rukayya ni dai arzikina, daya bana gidan yanzu duk wani abun da zata fada ko ta yi ba zai shafe ni ba

 Wallahi kin huta, ai kara da Hajiya Binta ta dauke ki, kika rabu da wannan bakar kalwal mai bakar zuciya

Hurriya ta kalleta tana murmushi.

 Amman dai Mama Rukayya wasa kike so? Hajiya fa mahaifiyar Yaya Yasir ce

 And so what? Ke baki ga yadda ta maida Amma ba? Ta mallake Appanku baya jin maganar kowa sai nata? Ni fa da zan samu sa'arta sai na dauko fansar duk abun da ta yi mana, saboda tana tsaye nan a makoshi?

 Toh kuma ki yi Yaya da Yaya Yasir?

 Wai ke ina ruwanki da Yasir din ne? Ke fa wata rana kamar munafuka haka kike

Hurriya bata san lokacin da dariya ta subuce mata ba.

 Mama Rukayya ke dai yi a hankali, dan kin san Yayana fa, shi yake zane mu idan muka yi laifi

 To ni sai ya dake ni? Ke yarinya kama kanki, ai ko kirana yayi ban daga ba sai kin ga yadda hankalinsa yake tashi, idan kuma ya zo ya karbi wayata ko ya gan ni da wani ya fara kishi kenan, ni Rukayya i no dey carry last, haba ni ba halin Amma ne da ni ba, kowa ya ce min kule chasss zan ce masa

A karo na barkatai Hurriya ta yi murmushi, ta tsayar da mai napep ta shiga bayan ta fada masa unguwar da zai kaita.

 Toh Allah ya tsare, damo sarkin hakuri

 Amin Mama Rukayya na gode

Mai napep yaja suka dauki hanya. A bakin gate ya sauke ta ta ba shi kudinsa sannan ta shiga cikin gidan, tana yin arba da daya daga cikin motocin da mahaifinta ya fi yawan hawa gabanta ya yanke ya fadi, tun a nan ta fara rage tafiyarta, hakalimlnta be tashin ba sai da ta kunna kai cikin falon ta yi arba da Hajiya Kaltume da Appanta, Hajiya Binta kuma tana zaune saman kujera.





Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar? MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne? cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai? shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5??


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


5??5??5? ?5?? 2? 2?



 Hurriya an dawo

Far'ar da Hurriya ta gani a fuskar Hajiya Kaltume lokacin da take fadar haka ya fi daga mata hankali fiye da ganinsu da ta yi a gidan. Cikin rashin kuzari da faduwar gaba ta karasa kusa da Hajiya Binta ta zauna a kasa, sannan ta mikawa Appa gaisuwa.

 Lafiya Kalau

Ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Kaltume na murmushi tana kallon Hurriya irin murmushi na murnar ganinta, bayan kuma a kasan zuciyarta ba haka ba ne.

 Hajiya Ina wuni?

 Lafiya Kalau mutan aljanna, an dawo? Tun dazun muke nan ai, Hajiya ta ce kin tafi duba Iyami ya jikin nata

 Tana jin sauki?

 Sosai?

 Eh

 Maa Shaa Allah...

Ta kasa cewa Allah ya bata lafiya, saboda hausawa suna cewa addu'ar fatan alheri ta makiyi karbabbiya ce, wai idan yayi maka sai an karba. Hurriya ta juya a hankali ta kalli Hajiya Binta dake zaune fuska ba yabo ba fallasa.

 Hurriya an dawo?

 Eh Hajiya sannu da gida

 Sannu dai yar Albarka, kin yi Sallah?

 Aa ina tahowa ne aka yi kira

 To tashi ki shiga ciki ki yi Sallah ki

Hajiya Kaltume ta ce

 Ai da ta bari sai mun tafi sai ta yi sallah a can

 Babu inda Hurriya zata tafi, ai na fada miki tun da ya koreta ta dawo nan kenan idan kika ga ta bar gidan nan to bana raye ne

A take Hajiya Kaltume ta saka kukan munafurci.

 Haba Hajiya yanzu duk hakurin da muka yi ta baki baki hakura ba, ita dai Hurriya na san bata da matsalar komai kuma ko yanzu zata so komawa gidan ubanta domin babu kamar gidan uba a duniyar nan

 Nan da take ai daji ne, da bata da alaka da kowa, ke ni kar nake ganinki, halinki babu wanda ban sani ba Kaltume, tun kina da kurciyarki har yanzu da kika yi yaya, saboda na aika muku da shi ne kika taso mijinki gaba kuka ta so wai azo a kalailaye ni da dadin baki a tafi da Hurriya ku karasa kasheta a can ko?

 Wallahi ba manufata kenan ba, ni taya zan ce na kashe rai balle kuma Hurriya haba Hajiyaba zan iya aikata haka ba, kawai maganar da kika fada mana ne, na lura da haka ya kamata na yi kasancewa uwa, a wacan lokacin idona ya rufe ne ni da Alhaji shiyasa har ya koreta, ni kuma na kasa dakatar da abin amman na bashi hakuri Hajiya, ita kanta da zata fadi gaskiya ta sani

Cikin kuka Hajiya Kaltume take maganar da hawaye shabe shabe a fuskarta. Kukanta ya bata ran Appa har yayi sanadin da ya watsawa Hurriya wani kallo daya saka ta sauke idonta kasa da sauri.

 Hajiya, ki yi hakuri haka ba zai sake faruwa ba

 Ba fa zata koma ba, daman can ni bana son zamanta a gidan nan, ba za a kula da ita ba yadda ya dace, gashi ba iya magana take ba fa ma Hamad ne shi ne mai iya magana da fadar abun da aka yi har ma ya rama, amman ita ba zata fadi komai ba, ko a lokacin da aka ce taje ta yi gulmarka a wani guri ai be kamata ka yarda ba, domin idan akwai wanda ya san halin Hurriya ciki da waje a duniyar nan kai ne, yadda ta shaku da kai bata shaku da mahaifiyarta haka ba

Appa ya sauke kansa kasa har lokacin hakuri yake badawa yana neman yafiyar Hajiya.

 Ni na yafe maka amman tabbas da baka zo ba kam, ina nan rike da wannan abun a raina kuma ba zai maka dadi ba saboda ni uwa ce, ko ban fada ba idan raina ya bace zaka iya gani a al'amurranka ko a jikinka ma

 Toh a yafe min Hajiya hakan ba zai sake faruwa ba, kuma dan Allah ki bar mu mu tafi da Hurriya

 Ba za a tafi da Hurriya ba, idan ka ga ta bar gidan nan to a dayan biyu ko dai ta yi aure ko kuma na mutu

Hajiya ta sake fashewa da kuka, ita kanta Hurriya ta tsorata da yadda Hajiya take son komawarta a gidan har da hawayenta. Cikin kukan Hajiya Kaltume ta kalli Hurriya data kasa tashi a gurin da take zaune ta ce.

 Subhanallahi, ki yi hakuri dan Allah, kuma ki sak baki Hajiya ta hakura ita ma, wannan maida magana baya da ake ba shi da dadi, takas mahaifinki ya zo saboda ya tafi da ke, dan Allah ki yi hakuri Hurriya

Hajiya Binta ta yamutse baki.

 Hurriya bata da ikon kanta, ikonta yana gurin mahaifinta da mahaifiyarta sai kuma ni, dan haka ki daina saka Hurriya a cikin maganar nan

Hajiya na fadar haka Appa yayi karaf ya kalli Hurriya ya ce.

 To idan haka ne, Hurriya ina baki umarni a matsayina na mahaifinki ki koma gida cikin yan'uwanki, idan ba haka ba zaki yi mamakin abun da zai biyo baya...

Appa na gama fadar hakan ya kalli Hajiya Kaltume ya ce.

 Tashi mu tafi

Sannan ya mike tsaye, Hurriya ma ta mike tsaye da sauri, cikin karfin hali na tsufa Hajiya Binta ma ta mike tsaye ta rike hannun Hurriya.

 Hurriya ba zata koma ba, gaba daya ka canja tsoho ta ya zan yi umarni kuma ka yi kokarin karya wannan umarni? Anya kana cikin hayyacin Tsoho?''

Ya kada kansa kasa.

 Hajiya ba umarninki nake kokarin karyawa ba, bana son zaman Hurriya a ko'ina sai a gida, sanin kanki ne tun kamin yau kin ce na baki ita ban baki ba, saboda bana son kowa ya rika min da

Hajiya Binta ta masa wani kallo na tsanaki, shi kuma ya ki yarda ya daga kansa ya kalleta sai yawo yake da idon a kasa. Tun tashinsa har girmansa bata ba shi umarni ya tsaba sai a yanzu, ba kuma yanzu ta yau ba, yanzu da girma ya cin masa ita kuma take gangarawa. Ko a lokacin da ya saki Iyami babu yadda bata so ya dawo da ita ba yaki, yanzu kuma saboda Hajiya Kaltume ta sako shi a gaba ya zo a maida Hurriya yake wannan bubutan.

 Kai ma haihuwarka aka yi, kamar yadda ka haifi Hurriya idan baka yi hankali ba, kai ma sai na baka umarnin da idan ka saba ba zaka ga da kyau ba

Hajiya Kaltume ta kama gafen mayafinta tana share hawaye tare da mikewa tsaye domin ta lura ran Appa ya bace kamar yadda na Hajiya Binta ma ya bace har ta fusata.

 Ba za'ayi haka ba, ba ta kai ga haka ba, Alhaji mu tafi, tun da Hajiya na zon zaman Hurriya a nan ka barta ta zauna Allah ya bada hakurin zama

Appa ya kalli Hurriya sai da hantar cikinta ta kada ta fara kokarin zare hannun Hajiya Binta a hannunta, ba kuma dan komai ba sai dan saboda Hajiya Kaltume, sannan ya dan risina ya ce.

 A tashi lafiya Hajiya

Hajiya bata amsa masa ba bata ce masa komai ba har ya fice, kana ita ma Kaltume ta yi ma Hajiya sai da safe ka roki gafararta sannan ta fice. Sai a lokacin Hajiya Binta ta zauna ranta a jagule.

 Hajiya dan Allah ki yi hakuri ki bar na tafi, kar na kawo rudani tsakaninki da Appa, ko kuma Appa yayi fushi da ni kamar yadda ya fada

Hajiya bata kula hawayen Hurriya dake saukowa ba ta daka mata tsawa.

 Ke rufe min baki nemi guri ki zauna babu inda zaki je, gaba daya sun canja masa kwakwalwarsa, idan yace ya yafe ke ni ma sai na yafe ki, idan takamar yana da kudi yana kula da ni, ai ai ba haka ya tashi yana ciyar da ni ba, Allah ke min komai

Hurriya ta duka tana kallon Hajiya bi ta data koma ta zauna.

 Idan kika samu tsabani da Appa saboda ni, zai kara wutar kiyayyata a zuciyarsa ne, kuma zai tsine min domin baya a cikin hayyacinsa a yanzu, da ba ke ma ba zai tsaba umarninki ba, idan kika yi fushi da shi ba zai ga da kyau ba, idan kuma hakan ta faru da shi, ke da mu abun zai shafa, domin ke uwarsa ce babu yadda zaki da danki sai hakuri, mu kuma yayansa har kasa ta hade bamu da wanda ya fi shi, amman matansa za su iya gina kansu har su manta da shi, wuya bata kisa Hajiya, kuma duk yadda suke nufina da sheri Allah zai kareni, ina jin tsoron fushin iyayena akaina, yardar Allah tana tare da yardar iyaye, mahaifiyata bata da lafiya kuma bana kusa da ita, ki fahimta Hajiya su suke su raba ni da Appa, dan Allah karki bari haka ta faru, ki yafe mishi ki sauko daga fushin ki yi hakuri na koma...

Hawaye ya zubo a idon Hajiya Binta, kalaman Hurriya na hankali sun ratsa kwakwalwarta, sai ta saka hannunta biyu da tsufa ya canja musu halittar fata ta rike fuskar Hurriya.

 Ke yata ce ta gari Hurriya, kuma kamar kore kamar kumbonsa, barewabata gudu danta yayi rarrafe, kin fi duka Yaya da Tsoho ya haifa hankali da hangen nesa, karamar yarinya mai kwakwalwar manya, All????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ah ya miki albarka, na barki na barki ki koma gidan ki zauna, zalinci baya dorewa kuma da yardar Allah sai kin fi su albarka, sai sun koma karkashinki sai rayuwarki ta dawo tana burgesu, ki shirya gobe zan saka direba ya kai ki, kuma zan biki da addu'a, zan rika zuwa ina dubaki

Hurriya ta lumshe ido tana kwantar da kanta a hannun Hajiya binta hawayenta na sauka a tafin hannun kakarta. Ita kanta bata son komawarma amman ta lura kamar wani abu suke shirya mata kuma suke son hada mata ita da mahaifinta shiyasa suka har Hajiya Kaltume

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login