Showing 156001 words to 159000 words out of 279257 words

Chapter 53 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34702

gani ai, kuma kin zo nan ne saboda mijinki zai kara aure, gashi kuma ya canja miki, ga danki yana son auren yar kishiyarki da ta fita, kuma kina fargabar kar ciwon da kika aika mata ya karya ta tashi mijinki ya ce zai dawo da ita, sannan kina yawan faduwa har ki ji ciwo a kafa har kika tsoron ko an miki ture ne

Ta daga masa kai.

 Hakkun babu musu a maganarka take

Yayi dariya.

 An fada mana komai ai

 Haka nake so, yanzu so nake a hana ana auren yar iskar yarinyar, kuma a hana mijina aure, sannan a dauke hankalinsa daga gurin kowa sai ni, idan da hali ma wannan matar da take tare da shi abokiyar zamana ita ma a koreta, sannan bana son mijina ya dawo da Iyami, kuma ciwon kafar nan ba turo min aka yi? Ni har tsoron faduwar nake ji kar naje na fada a inda be kamata ba kafar ta cire ko ta karye na shiga uku

 Duk za'ayi Hajiya, amman sai kin daure kuma kin shirya domin ni bana aiki da wasa, ciwon kafarki kuma babu wani ture babu aljannu babu komai, daga Allah ne

 Toh Alhamdulillah yanzu hankali ya dan kwanta, kuma daman ni ai haka nake so, yanzu miye abun yi?

Ya aje madubin dake jikinsa gefe daya ya dubeta.

 Ina mai tabbatar miki da wani abu, tabbas mijinki zai dawo da abokiyar zamanki da kike tsoron ya dawo da ita, matukar baki tashi tsaye ba

Hajiya Kaltume ta dora hannu a kai tana jin wani karin tashin hankali na kusantota.

 Shiyasa na zo gurinka ai, dan Allah a hana ya maido da ita

 Za'a iya hakan ne kadai idan zaki iya daukar nauyin jini, amman muddin matar nan tana raye babu makawa sai ta dawo gidanki

 Dan masani me kake nufi kenan?

 Ni matsala ta bana boyo kuma duk abun da na gani ina fadawa mutum gaskiya, amman ina aiki na gaskiya, abun da ya fi kawai mu yi ma matar nan halbin kasko domin matukar tana raye Wallahi ina mai tabbatar miki mijinki sai ya sake zaman aure da ita

 Dan masani babu wata hanyar sai kisa? Kar abun yayi min yawa?

Yayi dariya.

 Ashe baki shirya kenan kika zo, baki shirya mallakar mijinki ba, kuma baki shirya hana kishiyarki dawawa ba, gaskiya ban ga wata mafita a nan ba bayan wannan, domin madubin nan baya kara kuma ya nuna min akwai sauran zama a tsakaninsu

Hajiya Kaltume ta yi shiru na wasu dakiku sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

 To maganar mallakar Alhaji fa? Da kuma hana dana aure

 Za a yi miki na mallaka zaki mallake Alhaji ki koma kamar uwarsa, karki damu da wannan amman fa zaki zuba kudi

 Kamar nawa Malam?

 A kalla za a kashe 50k

Ta yi murmushi 50k abu ne mai sauki idan dai zata samu biyan bukata.

 50k ma matsala ba ne, zan bada fiye da haka ma, amman a duba idan akwai wani aiki mai sauki da ba sai kisa ba sai ayi

 Bari kiji na fada miki, matar nan ma tana nan ta fara tashi domin wanda kika saka yayi miki aikin nan ya fara karya aikin, tabbas kuwa zata dawo cikin gidanki, kuma dawowarta yana nufin fitarki

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, fita ta kuma? Ai ni shi ne tashin hankalina, ta zauna ma ya na kare balle ita tana ciki ni ina waje?

Gaba daya sai hankalinta ya tashi ta ji wani gumi na keto mata.

 Amman kana ganin idan an aikata aikin zai yiyu?

 Me zai hana? Saboda hasarin halbin kasko idan be sameta zai iya fadawa akan jininta shakiki kamar danta ko yarta

Hajiya Kaltume ta taba hannu biyu.

 Shikenan ma daman yarta ta isheni a duniyar nan, a aikata mata kawai ka ga aikata mata zai saka su ji tsoro su hana Yasir Rukayya, kuma zan huta nima hankali ya kwanta, amman ina lafiya idan aka ce zata dawo kuma ni na fita

 Idan aka yi haka babu ita babu mijinki har abada

 Toh yanzu yaushe za'ayi aikin

 A yanzu ma idan kika bada kudi, sai a dauko kayan hadi a kira aljannu, cikin dare za'ayi halbi kin ga ruwan da yake cikin kaskoncan? A cikinsa za a halba idan aka gabatar da aiki aka yi halbi da dare kamin safe sako ya isar mata, amman fa tabbas idan be sameta ba zai fada akan yarta balle ma ita muke fatan ya samu

 Akan samu irin haka ne, ayi ma mutum aiki kuma ya zama be fada kansa ba?

 Ban taba samun irin haka ba, gaskiya wani lokacin ma akan fada ma mutum biyu da uwa da jininta, kawai ina tabbatar miki karfin aikin ne

 Zan biya kudin, zan bada 200k gaba daya, ina son a hana dana aure kuma a janyo hankalin mijina a gareni sannan kuma a hana shi aure wacan yarinyar da yake hasashen aure a yi musu farraqu

Dan masani na jin 200k ya ji ransa yayi wasai kudin wata gona da wani gidan kauye har da fili ma.

 Hajiya ni ko ina tabbatar miki, kuma na miki alkawari tsakanin yau zuwa gobe zaki tashi da labari mai dadi akan kishiyarki, na mallaka kuma akwai aikin da zan hana sai ki aiko ko kuma ki zo da kanki jibi ki karba, da zarar ya ci an gama da shi, a game da auren da zai kara kuma wannan ni an san aikin da zan yi, mai irin sunan yarinyar ma ba zai sake sha'awa ba

Hajiya Kaltume ta yi murmushi ya jinjina kai

 Haka nake so, so nake na mallake komai a gidan nan, ya zama be ganin kowa sai ni da Yayana, Hurriya ma ina son a cire masa ita a rai kwatakwata

Ta saka hannunta a jaka ta dauko 200k ta aje masa.

 Idan bukata ta biya zan baka ninkin wannan, ni dai burina ayi aiki yayi

 Aiki kam ya gama, tashi ki yi tafiyarki

 Na Gode dan masani

Ta mike tsaye tana jin kamar an yaye mata damuwarta gaba daya, tunanin kar ta daukarwa kanta hakki da yawa duk ya kau saboda ta ji ance zata fiya Iyami ta dawo. Bata bar garin ba sai da ta sake komawa gidansu Kulu ta yi musu alheri kowa ta bishi da 1k sannan ta shiga motarta direbanta ya kama hanya, suna mata addu'a bayan sun gama murna da jindadin kyautar da ta yi musu. Ta isa gida cikin farinciki kamar wata wanda ta aikin jihadi, tana shiga bangarenta ta yi wanka ta yi sallah sannan ta fito ta shiga Kitchen da taimakon Salma da Khairy suka gama girkin dare, sannan ta koma dakinta su kuma zauna a falo. Bayan gama sallah magariba ne yar yayarta ta shigo gidan daman ta kan zo jefi jefi idan an yi hutu. Hajiya Kaltume ta yi murna da zuwanta sosai daman suka sha hira a dakin kamin ta shiga da kayanta a dakin Khairy. Misalin karfe tara daidai Hajiya ta dauki abinci mijinta ta shiga bangarensada kanta ta kai masa, so take ta dawo da al'adarta ta kai masa abinci da kanta saboda ta samu damar tsare shi kuma ta tabbatar ya ci abincin idan ya saka maganin da bokanta dan masani zai bata. Sai dai gaba daya ya lura da yanayinta be sauko ba daga tsabanin da suka samu jiya, har yanzu fuska a daure take kuma tun bayan da ta gaishe shi ya amsa be sake ce mata komai ba, ita kuma bata yi yunkurin wani abu ba, har sai da ya fara cin abinci, sannan ta dawo gabansa ta zauna ta zuba masa ruwa.

 Wai Alhaji yanzu saboda dan tsabanin da muka samu jiya shi ne kake ta wannan fushin? Yaushe rabon da ka yi fushi da ni haka?

Yayi kamar be ji ta ba ya cigaba da cin abincinsa.

 Ayi hakuri ranka ya dade a gafarci Kaltume, ban san abun zai zama haka ba, idan aure ne ayi ta yi kai zaka zauna da su ba ni ba, ita m Iyami Allah ya bata lafiya ka dawo da ita ta rike yaranta

 Ameen

Ya amsa ba tare da ya kalleta ba, sai ta ji kamar ta dauki murfin kular da yake cin abinci ta buga masa a kai saboda bakincikin amsawa da yayi da amin. Sai dai tuna abun da ta taka ya saka ta yi murmushi ta kawar da duk wani bacin rai daga zuciyarta... Sai da ya gama cin abinci ya sha ruwa sannan Namra ta kwankwasa kofar karamin falon nasa.

 Waye?

Hajiya ya tambaya tana harara kofar a zatonta ma yar makiyiyarta ce.

 Shigo

Appa ya amsa mata da kansa yana gyara, ta turo kofar falon ta shigo, ganin Hajiya Kaltume ya saka ta ji babu dadi domin tana son magana da Appanta private ne. Ta zauna kusa Hajiya Kaltume dake kallonta tana raya abubuwan da za su faru nan da yan kwanaki kadan idan ta mallake mijinta.

 Appa barka da dare

 Barka dai Namra, ya kike?

 Lafiya Kalau Appa

Sai ta yi shiru.

 Akwai wata matsala ne?

Ta dan kalli Hajiya Kaltume ta kalli Appa.

 Daman ina son magana da kai ne, amman zan bari sai da safe sai mu yi maganar kamin ka fita

 Privacy kike so?

Ta daga kai. Appa ya kalli Hajiya Kaltume kai tsaye yace.

 Kaltume mu shiga bedroom mu bar miki nan ko kuma ke zaki shiga

Hajiya Kaltume ta dubi Appa da mamaki sai dai bata ce komai ba ta yi murmushi.

 Aa bari ni na shiga, Namra a kebe lafiya

Ta yunkura ta tashi tsaye ta nufi bedroom din Appa ta shiga ta rufe dakin, a nan ta samu damar yin kwafa ta cize baki.

 Nan da dan lokaci komai zai canja, ke ma idan baki yi hankali ba sai kin fi Hurriya shiga matsala ke da uwarki duk sai kun zama abun tausayi

Ta zauna kan sofa tana matsa kafarta dake dake gwada son yi mata ciwo kamar jiya.

 Wai ni Alhaji zai cewa na ba shi guri zai yi magana da Namra, da dane ko fadar haka da ta yi ai sai yayi mata fada, amman ba komai duk a tafin hannuna zaku dawo sai na juya ku kamar waina

Sai da Appa ya gama maganar da zai yi da yarsa sannan ya shigo dakin cikin wani yanayi na rashin yabo da fallasa ya zauna bakin gadonsa yana kasa wayar hannunsa, kamin ya dago ya kalli Hajiya Kaltume ya ce.

 Tun shekaranjiya nake wani tunani

 Kamar na me Alhaji?

Ya sauke ajiyar zuciya.

 Ina tunanin yaran nan ne da Iyami ta haifa, twins Hamid da little Hamad, tun da aka haifi yaran nan ban taba zuwa dubasu ba a matsayina an ubansu

Hajiya Kaltume ta ji gabanta ya fadi irin faduwar da be taba yi ba, yau Appa ya fadi abun da bata kawo ran faruwar sa a nan kusa ba, lallai a yanzu ta yarda Malamin da yayi mata aikin ya fara karya shi saboda yana son ta ba shi kudi mai yawa ya mallaketa kamar yadda ya mallake Hajiya Fateee da bata ma son a fadi laifinsa. Babu wani abin da zata yi a yanzu da ya wuce ta boye komaia kasan zuciyarta, dan haka ta yi karfin halin murmushin da za a iya cewa ya zame mata na dole ne kawai ta ce.

 Toh Alhaji ai za a iya zuwa ka dubasu ai yaranka ne, ni zan iya raka ma sai mu tafi tare, ba wani abu ba ne

Wannan karon ajiyar zuciyar da Appa ya sauke mai nauyi ce sosai.

 Ina jin nauyin hakan, saboda na juyawa yaran nan baya na ci amanarsu ba tare da sun min komai ba, ina tunanin zan dauko su amman me zan ce idan zan aika a dauko su? Kai....

Ya busar da iskar data cika masa baki sannan ya tattare girarsa guri daya yana jin rashin dadin a abun da yayi ma yaran nasa da suka kasance jininsa.

 To ai ba abin kunya ba ne Alhaji, yaranka ne kuma idan acan baya ka yi kurkure yanzu ai gyara kake kokarin yi, karka dauki wannan a matsayin matsala dan Allah shirya ka je ka duba su ko kuma a dauko maka su

 Ban gama yanke shawara ba tukuna, zan yi tunanin abun da ya kamata na yi

Ya amsa mata sannan ya aje wayar ya hau saman gadon, ita kuma ta juyar da fuskarsa a dayan gefen tana kashe ido wani bakin kishi na cizon zuciyarta, sai a yanzu take jin ta yi daidai ta ya yarda a ayi ma Iyami halbin kasko domin bata san da wane irin zata sake dawowa gidan ta ba idan Appa ya maida ita gidan.
Kamin safiya ta waye Hajiya Kaltume ta matso saboda bokanta ya fada mata cewar idan yayi aikin da dare ya halba mata kamin safe bukata ta biya kuma ita ta yarda da hakan, sai da ta baro bangaren Appa ta dawo bangarenta take cin ciwon rashin karbo number wayar dan masani da bata yi ba, da yanzu sai ta tambaye shi ya samu yin aikin ko be samu ba. Kitchen din ta ta shiga ita da Ruma suna shrya abun karyawa, Khairy da Salma kam ana can wata duniya ana sharar bachi musamman ma Khairy da bata kwantawa sai ta sha abun da zai jefata a bachi mai nisa. Ita ma Ruma bata saba tashi da wuri ba saboda uwarsu bata koya musu tashin da wuri, sai dai yau ta tashi saboda tana da lecture 8 na safe. Suna shirya abun karyawar Hajiya Kaltume na tunanin kalaman da Dan masani yayi mata, kuma yanzu ta fara tabbatar da haka, domin a yanzu ta lura idan ta yarda ta fadi wata maganar akan Iyami Appa zai iya bata nata rai, balle kuma ace ya dawo, wata kila milkin da zata yi a yanzu zai fi an can baya, gashi yanzu ta haifi yara biyu maza ita kuma tana da daya ga son da yake yi ma Hurriya zai dawo, su ma kananan yaran zai fara nuna musu gata, sannan kanwarta ta aure danta dadi kan dadi, ga kuma wani auren da zai kara, above all ita ya saketa.

 Kam uban can kai....Gwuttt

Ta yi kwafa har sai da Ruma ta kalleta.

 Hajiya lafiya?

 Lafiya kalau je ki taso yan'uwanki su tashi haka mana, wata kila ma ko sallah ba su yi ba

Ta juya ta fice daga kitchen din. Hajiya Kaltume ta bita da kallo tana tunanin zuci.

 Hmmm wato ya sake ni ko? Ai kara ma a kasheta idan aka kasheta iyayenta ma za su yi hankali tun da na gane kwadayi yayi musu yawa har suna son daukar wata yar au aurawa Yasir, zan koya musu hankali

Tana maganar tana wani huci kamar macijiya, sanin mijinta baya karyawa da wuri a weekend days kuma today Saturday ya saka ta shiga dakinta dan ta kishingida, sai dai me tunanin yadda abubuwan suka soma sauyawa mata a lokaci daya ya saka ta kasa bachin na safe, ta dayan bangaren kuma idan ta tuna matakin data fara dauka sai ta ji ranta yayi fari. Kadan kadan bachi ya fara fisgarta saboda bata samun yin na dare ba yadda ta saba saboda tunani ganin take komai kamar mafarki ne.

 Hajiya ni kam na wuce

Ta zabura ta bude idon da sauri sakamakon maganar da Ruma ta yi mata, tana cikin shirinta na na fita ta goya teddy bag dinta a baya.

 Kin yi breakfast?

 Eh na yi

 Khairy sun tashi?

 Na tasheta daker ta tashi ita Kuma Salma na ta tashinta ta ki tashi

 Toh Allah ya kiyaye

 Amin

Taja mata kofar dakin, kamin ta rufe Yasir ya turo kofar dakin ya shigo.

 Hajiya Ina kwana?

 Idan ban kwana ba zaka gan ki, Alhaji Yasir mijin Rukayya

Kalaminta be masa dadi ba ko kadan, fushin da ta yi da yi da shi da safe ma be jidadin haka ba balle kuma yanzu da abun ya biyo har da bakar magana.

 Ayi hakuri Hajiya

 Hakuri daya ne, ka hakura da abun da uwarka bata so, shi ne mafita agareka, idan ba haka ba zaka janyowa kanka abun da ba zaka iya dauka ba

 Toh Hajiya

Ya mike tsaye ya fice daga dakin. Hajiya Kaltume ta taja uban tsaki.

 Idan ban tashi tsaye ba wai sai su kasheni wadannan, gaba daya basa tausayina daga shi har ubansa

Ta juya kwanciyarta, sai kuma ta ji bachin baya mata dadi ta tashi zaune.

 Har neman hanani bachi suke saboda tashin hankali

Ta mike tsaye ta shiga bandaki, sai da ta yi wanka sannan ta fito ta shirya cikin Holland wax ta saka turare ta fito daga dakinta ta shiga dakin Khairy, saman carpet ta sameta zaune da alama sai a lokacin ta yi Sallah.

 Khairy sak yanzu kika yi sallah asuba?

Khairy ta juyo ta kalleta.

 Bachi na yi da yawa shiyasa

 Wallahi ku daina wasa da sallah, duk wani abun da zaka aikata idan Sallah ka yayi kyau to komai zai zo da sauki

 Toh Hajiya zan kiyaye next time

 Haka kike cewa kullum, idan kin yi breakfast ki gyara gidan zan shiga bangaren mahaifinku, ita Salma ta tashi?

 Ban sani ba, tana dakinta

 Ina Jannat?

 Ta sauka kasa tana falo ko dinning

Tana amsawa mahaifiyarta tana hamma domin har lokacin bachin be gama da ita ba. Hajiya ta ja mata kofar ta nufi dakin Salma dake leke da na Khairy ta tura sai ta hangota kwance kan gado, ta baya kofar dakin baya tana fuskarta windows.

 Umm Salma.... Umm Salma..

Haka Hajiya ta yi ta kiranta tana

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login