Showing 252001 words to 255000 words out of 279257 words

Chapter 85 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34715

ya tauna dabinon da su suka jika mata lebe, ya saka mata a baki sannan ya lashe hannunsa, ya sake tauna wani har yayi taushi sannan ya dago fuskarta ya hade bakinsu suka ci dabino a tare. Kamin ya cire bakinsa ya kalli fuskarta yatsansa ya saka ya matsa hancinta har sai ta ta fara masa kukan shagwaba.

 Da zafi

 Uhmmm wannan kawai tukuna ma

Ya tsakani idonta yana murmushi, kamin ya tashi ya dauko musu abun tabawa, sai da ya fara ciyar da ita ta koshi sannan ya ci, daga bisani ya kawar da komai ya dauki Amaryarsa cak sai kan gado. Wardrobe ya dauko musu kayan bachi, sai da ya saka nasa sannan ya fara kokarin rabata da lifayar dake jikinta.

 Ke me yake zuciyarki? Hummm me kike tunani?

Ya rada mata a kunnen kamin ya dago ya kalli fuskarta. Sai ta yi shiru domin bata da abun fada, tun da ba wani abu yayi mata ko yace mata ba.

 Kayan bachi zan saka miki

Ta kanne kafada.

 Aa da wannan zan kwanta

 Hey don't try to act smart here

Ta fara rare masa kuka a hankali, sai yayi murmushi yaje kayan bachin ya zauna kusa da ita ya rumgumeta. A dole ya hakura ya kyaleta ta yi b??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????achi da lifayar har safe.



HAJIYA KALTUME POV.

 Kin ba ni kunya Khairy ban yi zaton zaki iya haka a gaban mutane ba, idan ma neman yafiyarta zaki yi ai sai ki yi daga ke sai ita a cikin mutane ba, yanzu ai ta ji dadi ita da Iyami sai su ce gashi nan kina kuka kina neman yafiyarta

 Hajiya wanda aka yada video shi a duniya kamar ni da yana da sauran jin kunya ne? Ni fa yanzu rayuwata ta kare, da ina tunanin auren Fadeel zai rufe abubuwa da yawa akaina kuma ya saka ni jin sanyi amman haka ya gagara, shi ma ya juya min baya

Ruma ta kalli Hajiya cike da damuwa ta ce.

 Hakan da ta yi ba laifi ba ne Hajiya, idan ba irin yau ba yaushe zata roki yafiyarta?

Hajiya Kaltume ta ja tsaki, bakinciki ya zame mata kashi kashi. Khairy ta mike tsaye tana kuka ta haura sama ta shiga dakinta sai ta kife akan gado ta fashe da kuka.

 Ka cutar da ni Adam.. Ka gama da rayuwata ka ruguza shiri ka tarwatsa duniyata wayyo Allah na...

Kuka take sosai tana jin kamar ace adam din yana kusa da ita ta kashe shi ko ta rage zafi, can kuma ta dago ta nufi wayarta ta dauka ta kama number Adam ta aika masa da sako.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326

Yana jin kamshi ya doso bakin kofar falon da yake zaune yayi saurin rufe idonsa, yana murmushi, sai da muryar Gwaggo dake rangwado sallama ta karya hanzarinta. A dole ya bude ido daya.

 Haba dai ina zumudin fara ganin Matata sai kawai na yi arba da fuskar tsohuwa...

Gwaggo ta yi dariya tana mamakinsa.

 Kai daga na maka abun arziki na kawo maka ita na rabaka da jira shi ne zaka watsa min kasa a ido? Daman ai ni ce uwar gidan ba ita ba

 Aa ni yarinya na aura ba tsohuwa ba

Gwaggo ta girgiza kai. Ta matso da Hurriya ta gabanta.

 To gata yaran zamani marasa kunya

Shi dai be ce mata komai ba sai kallon Hurriya yake, har Gwaggo ta fice daga dakin. A inda yake kyautata zaton gabas ne ya maida gaba ya duka kasa yayi sujadar godiya sannan ya dago ya daga kansa sama yana kallon Hurriya dake tsaye gefensa.

 Fatabarakkallahu ahsanal halikin... Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya mallaka min Hurriya a matsayin mata

Ya mike tsaye ya fuskance ya kama hannayenta masu taushi yana murzawa a hankali.

 My Angel rabin rayuwar Captain Jamal Aliyu Turaki, macen dake harba wuta a zuciyar Captain, macen da zuciya takw muradi rayuwata take tsoron rasawa

Ya hade goshinsa da nata yana kallon kwayar idon da ta rufe duk kuwa da kasancewar bata iya ganin komai ba dan komai ba sai dan tsananin kunyar Captain da take ji a yanzu. Shi ma rufe idon yayi suna ta musayar Numfashi, slowly ya saki hannunta ya saka hannayensa ya zagaye kwankwasonta.

 Finally... ?

Ya rada tare da sumbantar saman fatar bakinta. Ya dago hananyensa yayi sama dasu ya kwantar da ita a kirjinsa dake cike da babbar riga.

 Ina da wata babbar kyau da zan miki, na zabi na fada miki a yau ne saboda yau din nan rana ce ta musamman a garemu amman ba zan baki kyautar ba sai nan da wani dan lokaci kankane, kuma karki tambaye ni minene zaki gani idan lokacin yayi, wannan kyautar ita ce cikar farincikinki a tare da ni

Ta yi shiru ya labe a jikinta fitinannen kamshin dake tashi a jikinsa yana ratsa hancinta ya rikita lissafin kwakwalwarta.

 My Precious Pearl

Ya furta mata yana kwanto da kansa kusa da saitin kunnensa. Ta kara lafewa a jikinsa tana jin kamar ta fi ko wace mace sa'arta dacen mijin aure a yanzu.

 Yaya...

 Uhmmm

Ya amsa can kasan makoshinsa yana jan numfashi, ruwan turaren da ta yi wanka da su kamshi na rikita masa lissafi.

 Kar wani ya shigo

Rumgume ta ya yi yana lilo ya daga kansa sama idonsa suka cika da kwalla. yana shakar kamshin dake jikinta.

 Ai ni halalinki ne Hurriya, daga ranar da aka daura mana aure aka musanya komai bawa ya zama halalinki kuma na ki, naki kuma ya zama nawa, yau kin saka ni shiga wani yanayi da ban taba jin kaina a ciki ba

Wani shauki na angonci da farinciki yake jin kansa a ciki, tun da aka daura auren be taba jin nauyin ya hau kansa ba sai a yau. Dagota yayi daga jikinsa ya daga mayafinta ya sauke shi a bayanta yana kallonta. So now Hurriya dake tsaye a gabansa matarsa ce.

 My dream Girl, i never knew you're the one waiting for me, Allah ya bar min ke i see the future in you... My soul my heart my blood line my joy...

Ya sumbanci goshinsa irin sumbantar da sai da yawun da ya jika goshinsa ya saka tsigar jikinta tashi, ya sumbanci gefen fuskaerta hagu da dama sannan ya kwantar da kansa a wuyanta hancinsa ya shakar kamshin dake tashi a gurin, har lumshe ido yake yana jan numfashi.

 Ranar yau kamar mafarki baka ji haka ba?

Ya bude idon ya kama fuskarta yana yawo da idonsa, ya sumbancin hancinta.

 Na ji, abun dai kamar wasa ace ni din ango ne, kuma angon ma na Hurriya...

Ta bude idon tana kallon numfashinsa ke fita, sai ya hade goshinsu yana goga mata hancinsa a hankali.

 Bana jin akwai wata macen da ta yi dacen, ango a yau kamar ni, ka kawar da duk wani abu da ka ji, ka runtse ido daga komai ka tsaya ka dage sai ni, ban taba hasahen wannan ba, farkon da ka fara dukana ina maka kallon azzalumin mutum ne marar imani da tausayi ashe ban fahimce ka ba, kai zaka canja rayuwata...

Yayi murmushi mai sauti.

 To ba dole ba, tun haduwarmu ta farko da kika buge kirjina kika guda zuciyata kika shiga ciki kika zauna abunki,? ban san kina ciki ba sai daga baya and i have faith in what i see, a karo a biyu ma haka kika daki kirjina kika kusa kika shiga da karfin tsiya kika yaki duk wata mace dake shirin shiga ciki kika zauna

 I think i meet a angel in person, ka zama hasken rayuwata ba

Ya saka hannunsa yaja lips dinta da sha man lebe a hankali yana kallonsa cike da fitina.

 Tukuna dai... Yanzu din ne zan sama hasken rayuwa kuma sanyin idanuwanki Hurriya

Ya hade bakinsu na wasu dakikun da suka suka kusa hada mintuna daya. Yadda jikinta yake rawa ya kara tabbatar masa da ita din sabo shiga ce da bata saba da irin abubuwan nan ba.
Sai da ya ji alamar shigowa mutana sannan ya natsu ya kyaleta, ba tare da ya dauke ido akanta domin kallonta ne kadai abun da ke kwantar masa da hankali a yanzu, daren ma ya karaga yayi matarsa ta kasance a gefensa. An yi hotuna kamar za a kure camera duk wani hoton da aka dauka da Captain idan Hurriya tana ciki zaka tarar yana satar kallonta ne ko ma yana kallonta gaba daya. A nan ya samu gaisawa da wasu daga cikin yan'uwan Amma aka gabatar da shi a gurinsu suka ganshi shi ma ya gansu sai yaba halinsa da hakittarsa suke suna fadar shi da Hurriya sun dace da juna.
A can gidansu ma hotunan aka sha kala kala daman amsu dauka hoton ba daya ba ne, abinci ma sai kalar wanda kake ra'ayi zaka ci, abu daya ne ya rage armashin bikin shi ne rawa da ba ayi ba, domin babu kamu babu dinner abun da mutane da yawa suka saka ran za'ayi amman ba'ayi ba, saboda lalurar dake tare da Hurriya ta ido, idan aka ce za'ayi zata wahala kuma mutane da yawa za su gane Amaryar makauniya ce.
Da yawa sun zo daga dangin Appa saboda ya sanar musu da kanshi, hakan ya nuna yana son zuwansu bikin kenan, ciki har da Sapna da wasu daga cikin yayanta, amman daga bangaren Hajiya Kaltume har Momy babu su babu yayansu haka kuma babu a wani na su da ya zo. Amma ba ta yi mamaki ba daman ta san ba za su zo yarta ba, balle kuma abun alheri ya sameta kamar wannan na aurar Hurriya da mutumen da kowa ke yaba halinsa da na Iyayensa.

Misalin karfe takwas na dare aka jera manyan motoci na alfarma a kofar gidan Bappa kai kana ganin motocin da manyan matan da suka zo bikon amarya ka san amaryar mai tsada ce. Bappa ne ya fara yi mata nasiha sannan Gwaggo Hindu ma ta yi mata Amma kam sai ta kasa cewa komai sai kuka take tana fada Hurriya ji take kamar ?ar zata tafi ta barta ne tafoya ta har abada, ita kanta Hurriya bata iya rike kanta kuka take.

 Ki yafe min Amma ki yafe min

Shi ne abun da take ta fada ta rike Amma da karfi daker aka banbare hannunta, kusan ta saka mutane da yawa kuka, 3M Nene wato kakar ango ta bada a yi bikon Amaryar sai kuma akwati daya na manyan laces da atamfa da turare da Ammy ta hada na bikon Amarya, haka suka aje kayan sannan suka dauki Hurriya. Husna na rike da hannun kawarta har gaban mota sannan iyeye suka shiga tare da Hurriya Suna ta zauna daga gaba aka ja motocin sai gidan Appanta. A babban falonsa aka shiga da Hurriya aka zauna da ita tana sanye da lifaya an rufe kanta da fuskarta.

 Maraba Maraba Maraba

Shi ne abun da Appa yake ta fada har ya zauna yana kallon inda yarsa take zaune a natse.

 Ki ji tsoro Allah Hurriya akan dukan lamurranki, ki bi biyaya ga mijinki domin shi ne abokin rayuwarki a yanzu kuma shi ne jigonki, ki bi shi sau da kafa neman aljannarki ya tashi daga karkashin kafafuwanmu ya koma gurin mijinki, ki yi koyi da mahaifiyarki mace ce mai tsananin biyayya agareki kuma mai son abun da nake so, indai kin bi halin mahaifiyarki mijinki ba zai taba kuka dake ba

Hurriya ta mike tsaye ta matsa kusa da inda take jin muryar mahaifinta sai wata daga cikin kanen Appa ta kamata ta zaunar da ita gaban Appanta. Hurriya ta rike kafafuwansa tana kuka.

 Na gode Appa, da yardar Allah ba zan saka ku ji kunya ba, Appa ka yafe min dan Allah

 Na yafe miki Hurriya baki min komai ba, ke yar albarka ce.

Shigowar Yasir ne ya hana kwalla dake idon Appa zubowa domin ya shigo da zolaya ne.

 Wayo take Appa dan ta samu a yafe mata, ai ba mutuwa zaki yi ba aure ne dan haka ki daina wani rokon gafara, ko Appa ya yafe idan ban saka baki ba ba ta yi ba

Duk suka yi dariya har Hurriya da ta daga kai tana jin kamar ace zata iya ganin yayan nata mai tsananin nuna kauna a agare tun kurciya har girmanta. Yasir ya daga mayafinta ya dubi fuskarta.

 Kanwata, yau zaki tafi ki barmu ko? Rayuwarki zata koma wani gida tare da wasu Iyali da ba mu ba, Allah ya baku zama lafiya, kuma zan jaddawa angon nan cewar kanwata mai zurfin ciki ce ko da tana cikin damuwa bata fada dan haka ya rika kula

Hurriya ta kwanto jikinsa tana kuka.

 Yayana yayan da ya fi na kowa

 Ina alfahari da ke kanwata

Appa da kansa ya bukaci a shiga da ita gurin yan'uwanta ta yi musu bankwana, haka kuwa aka yi bangaren Hajiya Kaltume aka fara shiga da ita, aka zaunar da ita a falon, Hajiya Kaltume ta fito ta tsaya daga sama bata sauko ba saboda bakinciki, daga inda take tsaye ta yi Allah sanya alheri. Khairy kam saukowa ta yi tana kuka sosai kamar ranta zai fita ta yi rama kamar ba ita ba, da kanta ta zauna a gaban Hurriya ta kira sunanta da muryar kuka sai Hurriya ta kasa amsawa.

 Ki yafe min dan Allah... Na san na cutar da ke amman ki daure ki duba hakkin jinin dakw tsakaninmu ki yi hakuri ki yafe min dan Allah...

Rukayya Allah Allah kawai take kar Hurriya tace ya yafe mata, domin ta san halin yarta da sanyin hali. Hajiya Kaltume dake tsaye can sama kuma tana jin kamar ta sauko ta lakadawa Khairy shegen duka akan wannan abun kunyar da ta yi mata. Ruma ma ta roki yafiyarta tana kuka ta rumgumeta, daga bangaren Hajiya Kaltume aka wuce da ita bangaren Momy, a falo aka samu Momy tare da Namra suna zaune da Miwan. Hurriya ta zauna kasa tana neman yafiyarki tana kuka.

 Babu wanda zai ce kin masa wani abu da saninki Hurriya, halinki mai kyau ne, ni na yafe miki haka Allah ya kaddara haka ya so, Allah ya ba ku zaman lafiya

Shi ne abun da Momy ta fada tana hawaye, domin a yanzu ta yarda babu sarki sai Allah babu yadda zata yi da abun da Allah ya kaddara faruwarsa. Daga gidan Appa aka wuce da ita family house din mijinta ta gaisa da su Nene da Hajiyar Maru, kanen Mahaifin Captain da kanenen mahaifiyarsa da wasu daga cikin danginsa, babban akwaiti aka bude mata kowa ya kawo nasa kyautar a zuba wasu tufafi wasu kudi. Da aka kawo a gurin Ammy sai ta kama hannun Hurriya ta saka mata key mota.

 Barka da zuwa Turaki Family yarinya, ba dan Captain yana ana ba, amman tabbas kin yi dacen miji fatan ba zaki ba shi kunya ba

A take falon ya dauki ihu kowa na murna da mamakin Ammy ta yi ma Hurriya kyautar mota, a sabuwar motar aka saka Hurriya da masu kaita gidan mijinta suka kama hanya zuwa gidan Captain. Kusan rabin unguwar Gidan dawa sai da suka san da Amarya a unguwar saboda manyan motocin da suka rika ratsa titin suna shiga cikin unguwar. Wani mamaken gidan da za a iya karamin gida hudu a ciki aka shiga da Hurriya, har gaban babbar kofar falon aka faka motar, kan wani jan carpet da aka shimfida na musamman domin Amarya Hurriya ta sauko da kafafuwanta tana lullube da fuskarta aka shiga da ita gidanta mai cike da kamshi ga gua na tashi ta ko'ina.. Dakin da aka ware a matsayin na Captain a ciki dakuna biyar da Appa ya cika mata da kayan daki aka zaunar da ita akan gadon na alfarma, kan lallausan zanen gadon da aka siya mata gurin Khadeeja Candy. Iyaye suka sake yi mata nasiha sannan suka tafi, aka barta da Husna sai yan matan Amarya. Ba dauki dagon lokaci ba aka shigo da ango yana sanye da shaddarsa fara mai matukar kyau. Kana ganinsa ka ga ango baki baya rufuwa fuska dauke da annuri. Kusa da matarsa kuma uwargidansa ya zauna abokansa na zolayarsa shi dai be ce komai ba sai murmushi yake. Su ma abokansa da yan'uwa suka yi ta su nasihar sannan su Husna suka kara da taku suna dariya domin babu mai aure a cikinsu.

 Ba sai kun fada mana ba, angonta ya ta jadda mana amaryar mai tsada ce, dan haka ba mu bukatar tayawa zamu bada abun da ba a isa a mayar mana ba... Ko wace mota da zata yan matan amarya akwai jakar kawayen amarya a cewa kowa jaka tana dauke da kyauta da kuma kudi na siyen bakin amarya

Hakan da Cousin din Captain ya fada va karamin faranta ran amarya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login