Showing 63001 words to 66000 words out of 279257 words

Chapter 22 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34676

zancen Momy ya ce ta fita wani abu, bayan kuma ya gama yaga fuskarta cewar ko primary bata yi ba. Alhalin kuma gaskiya ya fada haka ta yi rayuwa rayuwar kauye ba arabi ba boko sai talla kamin ya aurota.

 Alhaji na ga dai kai ma ba kasuwanci ka karanta ba, amman kake kasuwancin nan gashi nan kuma yanzu ka koma dam bokon har turanci kana ji

Appa ya cire gilashin idonsa yana dariya.

 Kaltume ni fa na yi boko kuma na yi zurfi kawai dai rayuwa ce ta yi tsanani kuma kasuwancin ya fi tsaya min a rai shiyasa na watsar, na fara kasuwanci kuma da yake arzikin a nan yake kin ga a yan bokon ne a karkashina, amman ke Kaltume da ko sunaki ba zaki iya dubutawa ba Allah cutarki za ayi

 Ga yayana zasu min komai

 Matan dai ai kin san aure za su yi, Yasir kuma abu ne mai wahala ya rike kasuwanci domin na lura hankalinsa ya fi karkarta a bangaren aiki, bayan nan ma kasuwancin Crude oil yana bukatar kudi mai yawa sai mutum ya tsaya da kafarsa

 Zan dan hada abun da yake hannuna na ga zai kai nawa, sai ka kara min da wani haba Alhaji ina matar Alhaji Haruna Mai Yadi ai wannan kasuwancin ba zai gagara ba

Tana maganar har da wani daga masa gira kamar wata tsohuwar kasuwa. Appa dai yayi murmushi ya girgiza kai. Sai da aka kira sallah azahar sannan ya fita gidan ita kuma ta fito daga bangarensa ta nufo nata tana tunanin yadda zata zama daya daga cikin attijiran matan jihar Zamfara idan ta fara kasuwancin, bayan kasancewarta matar Alhaji Haruna Mai Yadi, so take ta mamaye ko'ina ta sha gaban Momy a yanzu, ta yadda ita kanta Momy sai ta yarda Hajiya Kaltume ta fita komai. Ta shigo falonta cikin yanayi na farinciki da jindadi ta tararda duka yaranta suna zaune falon suna hira ban da Ruma da tun da ta dawo ta ware kanta daban take rayuwarta ita kadai ba tare da sauran yan'uwanta ba, haka ma ba ta sake kusantar mahaifiyarta ba, a baya kuma ba haka take ba ita ce yar autar Hajiya Kaltume kuma ita ce shagwababbiyar yar rikon jakar Hajiya.

 Hirar me kuke yi?

 Yadda zamu tashin garin nan idan Allah ya nuna mana bikin Maama

Hajiya Kaltume ta yi murmushi.

 Gaskiya ne, za ayi biki na ban mamaki daman wasu daga cikin abokan mahaifinku ba su san ma ya taba aurar ba

Maama ta saka dariya

 Hajiya wake maganar auren Sapna auren kauye kuma tun kamin Appa yayi suna, aurena dai za'ayi aure na ji da fada da zai tashi hankali media ya zama topic of discussion a Gusau

Hajiya Kaltume ta yi murmushi kamin ta bi kowa da kallon.

 Toh Allah ya nuna mana, shi ma angon na ki na lura ai dan son riya ne

 Wallahi haka yake, yace aurensa na farko auren hadi ne shi kuma baya son matar aka masa dole shiyasa be wani bada jiki ba, amman aurena ko hmmmm

Duk suka dariya. Khairi ta ce

 Yaya Maama yana sonki Wallahi da alama kan waccan matar tasa zata sha wahala a hannunki

 Kar ma ki ji yadda yake zaginta ni har tausayi take ba ni

 Ba a tausayin mata ai Maama raba kanki, kina shiga gidan nan idan ta samu sa'arki waje za ayi da ke, wai ina Ruma?

Hajiya ta karasa tana tambayarsu yar autarta domin ta zagaye falon da kallo bata ga Ruma ba. Salma ta ce.

 Hajiya kin san Ruma tana dakinta fa, yanzu ta mai da kanta aljanna bata son mutane ko kadan

 Oh ni wannan yarinyar

Hajiya ta nufi hanyar stairs, sai da ta yi kamar ta shiga dakinta sai kuma ta nufi dakin Ruma ta tura kofar dakin ta leka, zaune ta hangowa akan studied table dinta tana rike da wani textbook tana karantawa.

 Ke...!

Ta juyo ta kalli Hajiya Kaltume. Sai ta shigo cikin dakin ta maida kofa ta rufe ta nufeta tana fadin

 Wai ke wani sabon iskanci kika kirkira yanzu da rainin wayo? Sai ki ware kanki dabam kina rayuwa kamar wata mayya?

A take idonta ya cika da ruwan hawaye.

 Bana son gidan nan Hajiya, na fada miki ina son na koma gurin Hajiya Binta da zama ko Anty Farisa

 Babu inda zaki je, babu gidan uban da zaki zauna idan ba zaki iya rayuwa a nan ba sai ki hadaye zuciya ki mutu

Hajiya ta fada cikin bacin rai sannan ta juya daf da zata kai hannu ta bude kofar dakin Ruma ta mike tsaye ta ce.

 Har yanzu Hajiya gani nake kamar ba ke bace, na san baki son Amma amman kisan kai Hajiya kisan kai? Baki ga yadda suka fasa masa kai ba, ko'ina jini yake, still kuma suka karbi kudin nan gurin Appa, Hajiya mamaki nake yadda zuciyarki zata iya aikata haka, kullum sai na yi mafarkin Hamad abun da na gani ya kasa fita a idona ni kam ina ma ba ke ce uwata ba...

Hajiya Kaltume ta juyo a fusace ta nufo Ruma gadangadan, tana isa gurin da Ruma take tsaye tana hawaye Hajiya Kaltume ta dauke ta da mari ta rufe ta da duka.

 Yaushe wuyanki yayi tsauri haka har bakinki ya iya furta kalamai irin haka? Dan ubanki fuskata kika gani tare da mutanen ko kuma gurin kika gan ni?

Cikin kuka Ruma ta soma bata amsa.

 Amman sun yi magana dake lokacin da suka dauko mu, Hamad ma ya ji muryarki shiyasa kika ce a kashe shi

Hajiya Kaltume ta yi saurin rufewa Ruma baki tana juyata ta kalli kofar dakin, sannan ta juyo ta kalli Ruma tana kuka.

 Wallahi ban ce a kashe shi ba, Yaushe zan ce a kashe shi? Wallahi ban ce a kashe shi ba, kuma Wallahi idan wani ya ji maganar nan Ummu Rumana sai kin yi bakincikin zuwa duniya

Hajiya Kaltume ta sake ta fice daga dakin da sauri tana share hawayenta, da hakki ta isa nata dakin ta zauna bakin gado kamar wadda ta yi gasar tsere hakki ne na mai jin tsoro da fargaba faruwa wani ba, ba na wanda yayi wani aiki ba. Da sauri ta lalabi wayarta ta kira macen da ke share mata kukanta...

 Hajiya Fatee ke kadai kike?

 Ni kadai nake Hajiya Kaltume Lafiya?

Hajiya Kaltume ta fashe da kuka tana fada mata abun da Ruma ta yi mata.

 Ah toh ita kuma duk saboda wa kike abun?

 Ita wannan bata gani ai, da ma Khairi ce ita ce mai irin zuciyata, kuma ni Wallahi ban dauki yaron nan dan a kashe shi ba, kaddara ce kawai ni ba ma shi na so a dauka ba, yar makauniyar na so a dauka, amman abu ya zo a haka

 To yanzu me ye abun yi?

 Abun yi kawai a rufe mata baki, domin na lura tona min asiri zata yi, tun da ta dawo gaba daya ta bi ta canja, sai zancen barin gidan take nan gaba kadan zata iya cewa zata fadawa wani idan abu ya cika

 Lallai da maganarki, haka ya kamata, daman ita bata san kan duniya ba shekara goma sha bakwai miye ta sani, ai da gaskiyarki da baki saka ta a lamurranki duk da shige miki da take da sabon da kuka yi, wannan ai sai ta fadawa duniya mun je gurin kaza da kaza

 Ina zan yarda? Ai duk yarana bana zuwa da ko daya, sai dai na fada musu

 Haka ya kamata gaskiya ki kirashi ki fada masa komai idan akwai yadda za ayi a danne bakinta nan dan kar ta fada

 Zan kira shi, daman ban gama fita bakincikin Iyami ba yanzu kuma ita zata tsirar min wani sabon shafi

 Wallahi kuwa shegiyar dagar ta sake jefo masa yan biyu haihu kamar karya kuma duk maza, ta dai rantsa sai ta ci gadon Alhaji daman shi ne take ta yi ma wannan haife haifen, ai Wallahi an rage mugun iri ma, yaron nan ba fadar kike yana damunku

 Wallahi ya addabi kowa, kuma ni ba shi na ce a dauka ba, iya yar macijiyar na ce a dauka, su kuma sai suka bata aikin suka kira wayata a gabansu yaro ya ji ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?muryata, shi ne duk sila ni kaina kullum tunanin yaron nan nake nake Wallahi abun ya hana ni sukuni sam

 Allah dai ya rufe asiri kar wannan yar autar taki ta janyo mana jagwal

 Ameen, ai maganinta zan yi

Daga haka suka yi sallama, babu bata lokaci Hajiya Kaltume ta lalabo number Malaminta a wayar ta kira shi domin kai masa kukanta, daman kiran Hajiya Fatee da ta yi na neman jin shawarar abun da zata ce ne domin bata yanke hukunci sai ta shawarci aminiyarta.


Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
5??5?(?5?(?5?$? 5??5?0?5?(?

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660


5??5??5? ?5?? 6??

The following week Appa ya aika mota dauko Hurriya, a lokacin ne hankalin Amma ya tashi sosai daman babu irin magiyar da bata yi ma Hajiya Binta ba a lokacin da ta zo mata da sakon cewar Appa zai aiko da mota a dauki Hurriya next week, Hajiya Binta ma ta yi iya kokarinta amman be saurareta ba, saboda ba zai iya tsabawa abun da Hajiya Kaltume take so a yanzu ba, ita kadai zata ba shi shawara ya dauka bayan ita baya sauraren kowa ciki har da mahaifiyarsa da kuma Momy da bata ma gane kansa yanzu, sai dai bata cika damuwa da al'amurransa ba domin ta bussinees dinta take da harka da manyan mutane. Son ta mallaki gida ko ta mallake Alhaji Haruna baya gabanta domin jin take kamar ma ta kusa gogawa da shi a arziki. Hurriya kamar zata shide haka aka fito da ita daga gidan ita kuka Amma kuka Gwaggo kuka Rukayya kuka tana rikon Amma amma na rike ta kamar wadanda za a raba rabuwa ta har abada. Ita dai bata son komawa gidan saboda babu dan'uwanta mai tare mata fada a cikin haka kuma babu mahaifiyarta, kuma a yadda ta fahimta ba zata sha da dadi kamar da ba a hannun Appa yanzu. Amma kuma tana jin kamar za a kara mata kewa ne domin babu Hamad a kusa da ita a yanzu Hurriyar take gani tana jin sanyi yanzu kuma za a dauke ta. Har aka iso gida da ita kuka take sosai kamar na mutuwa, gaba daya ta bi ta rike ce da direban yayi parking ta rasa ina zata shiga bangaren Hajiya Kaltume ko Momy gurin da dakinta yake a yanzu, ko kuma bangaren mahaifiyarta da babu kowa a cikin, kamar wata bakuwa haka ta rika kallon gidan.

 Hurriya

Ta dago da sauri ta kalli Dattijon direban da ya kawo ta, jikinta na rawa.

 Ki yi hakuri ki yi da addu'a babu abun da yake daurewa

Tana kokarin amsa masa da kai sai ta kasa, daman shi kam baki ba zata iya furta komai ba.

 Ina zaki je? Gurin Momy ko gurin Hajiya Kaltume?

Sai kawai ta fashe masa da kuka.

 Ko kuma gurin Alhaji zaki je? Yana nan ciki daman yace ba zai fita ba sai kin dawo

Ta daga kai da sauri, sai ya kama hannunta suka isa bangaren mahaifinta sai da suka isa daf da kofar falonsa sannan ya saki hannunta.

 Ki shiga ciki

Ta daga masa kai, sai da ya wuce sannan ta kwankwasa kofar part din kamar wata bakuwa bayan ba haka ta saba ba, idan zata shiga bangaren Appanta sai dai ta tura ta shiga da murnarta tana rangada sallama. Sai da ta yi knocked sau uku sannan ta tura kofar falon ta shiga, sanyin ac ya fara yi mata maraba da zuwa, kaminnta juyo muryar mahaifinta a dayan falon da alama waya yake, babu komai a hannunta sai carbin Amma da ta dauko, tufafinta ma sai daga baya za a dauko mata ko kuma ta yi using wadanda suke gidan na bangaren Momy. Hawaye na sauko mata kamar ba gobe haka ta shiga karamin falon tana ta son ta bude baki ta yi sallama amman ta kasa. Appa na ganinta a take annurin dake fuskarsa ya gushe kamar wanda yayi arba da bakin maciji, a take ya yanke wayar da yake ya mike tsaye ya nufota yana fada.

 Ya aka yi? Kin dawo kina ta yi ma mutane kuka mutuwa aka yi? Ni ba dan Kaltume ta matsa ba ai sai ki zauna can a gurin uwar taki

 Appa

Ta furta tana kallonsa gilashin dake mata garkuwa na daf da faduwa. A madadin ya amsa sai yace waye bana son jin muryarsa ba ke ba, a take korata ya saka ta gaba.

 Muje can bangaren Nafisa tafi tafi

Ta tsaya a gurin tana kallonsa kamar hoto har ya iso, ganin ba tafiya zata yi ba ya saka shi fisgar hannunta ya wuce gaba ya hanyota sai kallonsa take har suka isa cikin falon Momy ya sannan ya saki hannunta. Kamin ya ce komai Momy ta aje plate din doyar dake hannunta ta rafka salati.

 Haba Alhaji, ina laifi ka barwa Iyami yarinyar tana ganinta tana jin sanyi? Ni dai tsakani da Allah hankali ya fi kwanciya yarinyar ta zauna a gurin uwarta

Ita ma kamar Appa na jiranta sai ya rufeta da fada.

 A nan nake son ta zauna, a nan zata zauna ke kanki gurin da na ga dama zaki zaun balle kuma ita da take yata, karki sake fada min abun da ya kamata na yi, ba shawararki nake nema ma

Tabe baki ta yi bata sake cewa komai ba har ya fice, sannan ta ce

 Ni ma dan an rasa ya za'ayi da ni ne, na cika na make gurin kuma sai hakuri Wallahi, ni da zai maida Iyami ki koma can gurinta ya fi min kwanciyar hankali, ina zan iya da rikon yayan wasu yayan da idan suka girma suka samu arikin uwarsu za su nema

Hurriya dai tana tsaye a gurin da Appa ya barta ta kasa matsawa ko'ina sai hawaye take. Mahaifinta ya canja mata, ta rasa dan'uwanta kuma ta rasa mahaifiyarta a kusa da ita.

 Lafiya kika tsaya nan kika zuba min ido? Mahaifinki ma baki da amfani a gurinsa yanzu balle kuma ni, wuce ki tafi dakinki tun da an kawo min kaya ya zan yi, Iyami ta haifa mana ta tafi ta bari

Huriyya ta dauke kai da sauri ta fara tafiya, sai kuma Momy ta kirata.

 Hurriya

Ta juyo a hankali ta kalleta ta kasa amsawa har lokacin hawaye take.

 Zo ki zauna yi hakuri kinji

Hurriya ta dawo ta zauna saman kujerar dake dama da Momy.

 Gaskiya dai Alhaji ya ci amanarki Wallahi, ni ai ko da bala'i sai na karbi yayana, ko da yake Iyami ba zata iya ja da Alhaji ba, ta ina talauci zai ja da arziki, amman dai gaskiya be dace ya rabaki da Iyami yanzu ba, ai sai tunanin ya hade miki ga na dan'uwa ki kamu da hawan jini da kurciyarki, kai Kaltume bata da imani, haka fa ta raba Sapna da ubanta, Sapna bata isa ta tako garin nan ta ce zata zo gurin ubanta ba, tana can kauye cikin talauci shi kuma ya kyaleta... Hmmmm

Ta mike tsaye tana kwalawa mai aikinta kira.

 Bilki

Tsohuwar ta fito da gudu daga kitchen, daman haka take da yan aiki idan tana falo sai dai su boya a wani guri bata zama daki daya da su, idan har ka gansu a falo to tana dakinta ne ko kuma ta fita.

 Hajiya ga ni

 A dauke plate din nan kuma ga yar Iyami nan idan zata ci abinci a zuba mata

 Toh Hajiya

Tsohuwar ta dauke plate din sannan ta kalli Hurriya dake zaune.

 Hurriya a zuba miki abinci?

Hurriya ta girgiza kai alamar aa, Momy tabe baki ta dauki wayarta.

 Dan kan masa in ji sure, cikinki ko na wani, kin san dai ba rarrashinki zan yi dan ki daina kuka ko ki ci abinci ba, ina da tausayi da zuciyar imani amman laisa son dan wani kamar nawa kam karya haram babu boye boye ba munafurci, shiyasa ni na fi

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login