Showing 222001 words to 225000 words out of 279257 words

Chapter 75 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34678

46

Bayan kwana biyu....

After ya yanke kiran da ya shigo daga Ethiopia, cikin rashinya sauko da kafafuwansa ya sauko daga kan gadon cikin rashin kuzari, ya saka bedroom slipper dinsa ya nufi kofar falon ya bude ya fita. Downstairs ya sauko ya nufi falon kakarsa Hajiya Nene ya zauna a kusa da kakarsa yana gaisheta. Sai ta kai hannu ta taba jikinsa ta amsa.

 Lafiya Kalau Jamal ya karfin jikin?

 Alhamdulillah

Ya kalli Ammynsa dake zaune sanye da doguwar rigar abaya kanta babu dankwali.

 Ammy ina kwana?

 Lafiya Kalau, ka ci abinci?

 No zan ci anjima

 Haka ka sabawa kanka da wannan dabi'ar baka son cin abinci? Saboda ka daga min hankali ne?

Ya kasa daga ido ya kalleta.

 You fake it ko Captain? Tun ranar da mahaifinka ya bar garin nan baka sake sakin jikin ba, abinci ma baka son ci

Ko bata fada masa kai tsaye ba ya fahimci abun da take nufi.

 Ammy an faking ciwo ne? Bana yin komai saboda na daga miki hankali. Tashin hankalin tashin hankalina ne

Ya kalli wayar hannunsa ya mike tsaye.

 Bari na amsa wannan kiran

Ya fice daga falon. Ammy ta bishi da kallo

 Da gangan yake wannan abun

 Da gaske ba shi da lafiya, na taba jikinsa yanzu da zafi sosai, ki kalli idanuwansa ki gani yaddda suka sauya alamar zazzafi yana damunsa sosai kuma ya rame sukuninsa duk ya sauya, Turai karki zama irin sukunan mana masu kishi da matan yayansu

Ammy ta juyo ta kalli In-law dinta.

 Ba kishi nake da yarinyar ba, Allah ya tsare ni ba zan taba zama daya daga cikin irin wadannan iyayen ba, kawai ba ma the same team ne, ke ma kuma kina goya masa akan abun da kowa ya san ba daidai ba ne a gidan

 Miye ba daidai ba? Goyo masa akan abun da addinin be haramta ba? Ko kuma son abun da danki yake so? Ke ce ba daidai ba, tun a ranar da aka daura auren yaron nan baki bar shi ya fita ko'ina ba, kin tsare shi a gida kamar mace gashi nan kin haifar masa da damuwa

 Idan ya fita ma babu inda zai je, already yayi received email daga gurin aikinsu sun aminta sun ba shi sati biyu ya huta, to me zai fita yayi a waje?

 Namiji ne shi fa, yana da abokai yana da guraren zuwa da yawa yarinyar nan ma tun da aka daura aurensu ba ki barshi yaje ya ganta ba, Turai duk wanda zai so anki yana bayanki ne, domin ke kika haife shi ke ya kamata ace kin fishi son abun da yake so, ba shi kanwa ko yayar da zai ti shawara da ita akan Matsalar rayuwarsa ke ce uwa da ke zai yi shawara a komai, yanzu kuma kin juya masa baya kika kokarin cilasta masa ya zaba tsakanin rayuwa da mutuwa

 Hajiya abun da yarinyar nan ta yi yayi tsauri da yawa, ko da kuma bata aikata ba ni bana sonta bata cikin irin jerin matan da nake son Captain

 Saboda dake za'a daura musu aure ko ba da Captain kuma ke zaki zauna da su ba Captain ba, ko a gidan karuwai ya dauko ta tun da har ya nuna yana sonta ya kamata ki so ta kema, balle kuma har igiyar aure ta shiga tsakaninsu ai zance ya kare, tarewar ki a nan ba zai hana Jamal ya gana da matarsa ko ta tare a gidansa ba, na san duk saboda shi ne kika aminta ki bi mijinki

Ammy ta bata fuska sosai tana jin ta wani bangaren kamar bata kyautawa danta ba, sai dai ita ma kuma ba su kyauta mata ba, sam bata son Hurriya a matsayin suruka.

 Ba gori nake miki ba, amman lokacin da Aliyu ya gabatar mana ke a matsayin matar da zai aura, ba mu ce masa fa wanda muke so, sai kuma karba muna murna da addu'ar alheri, mu dai muradin mu ya auri wanda yake so ba wanda mu muke so ba, so da yawa mu kan ki abu ya zame mana alheri, kuma mu so abu ya zame mana sheri

 Gorin dai kike min Hajiya

Ta fada a ransa a zahiri kuma sai ta mike tsaye ta dauki hijabinta dake gefen kujera ta saka ta fice daga falon. Sama da haura zuwa dakin da Captain yake, tana tura kofar dakin ta ji karar unkurin aman da yake daga bandakin dake bude, tsantsar soyayya da kulawa irin na uwa sai ta karasa gurin da sauri hankalinta a tashe.

 Da gaske baka da lafiya ashe

Ta taba wuyansa zuwa kansa ta ji shi da zafi sosai, da kanta ta kunna lap ta wanke masa baki kamar wani karamin yaro.

 Mu je asibiti yanzu

 Zan iya kira likita ya zo gida ya duba ni

 Aa asibiti zamu tafi

Ta cikin tsananin razani da tsoron kar wani abu ya samu danta. Sakinsa ta yi ta fice daga bandaki da sauri. Tawul ya dauka ya goge fuskarsa idonsa har wani ja suka yi alamar jikinsa ya saki saboda Fever, haka ya fito bandakin yana jin aman kamar be gama yi ba, kofar bandakin ya rike yana jin yawun bakinsa na tsinkewa. Sai ga Ammy ta shigo tare da Momy Ikilima

 Mu tafi ga direba can a waje

 Ammy ba wani ciwo ba ne da zaka daga hankalinki ba

 Ban taba baka umarni ka aikata a take ba tare da ka yi min musu ba, haka last time na ce maka zamu tafi England a duba lafiyarka baka yarda

Ammy kamar zata fashe da kuka take maganar. Ganin haka ya saka shi nufar gurin da ya aje wayarsa ya nufi wayar ya dauka.

 Mu tafi

Gaba ta saka shi, kamar wanda zai gudu sannan ta bi bayansa ita da kanwar mijin nata.

 Zan iya tuki ba ni key

Ya mikama Direban hannu, direban ya kalli Ammy. Sai ta girgiza masa kai.

 Ka bari ya kai mu ina zaka iya tuki yadda jikinka yake da zafi nan

 Ammy ciwon nan be kai yadda kike tunani ba, zan iya tukin nan da kaina

Ya rufe baki yana karkata dubansa ga motar Salim da ya faka kusa da wata motar gidan. Captain ya bude motar zai shiga Salim yayi hanzarin bude tasa motar ya fito.

 Captain...

Be amsa shi ba kuma be fasa shiga motar ba. Ammy ta kalli Salim din ta kalli anta.

 Salim ne

 Na san shi ne Ammy mu tafi

Salim na isowa gurin ya gaishe da Ammy da yar kunyarsa kunshe a aljihu.

 Lafiya Kalau Salim

 Fita zaku yi?

 Eh Captain za mu kai asibiti

 Ba shi da lafiya ne?

 Eh

Salim ya kalli Captain din da baya son kallon gurin da Salim din yake tsaye ya mika masa hannu.

 Hi

Captain ya kalli hannunsa ya kalli fuskarsa, sai ya amsa masa ba tare da ya mika masa hannun ba.

 Hi

 Come on mu bar abun da ya faru ya wuce mana, ba yara ba ne mu, mun samu rashin fahimta kuma mun hau dokin zuciya, amman ba zan bari wannan abun ya lalata alakarmu ba, we're friends for more than 15yrs now wannan dan karamin abun ba zai bata alakarmu ba, na san na yi ba daidai ba a wani gurin kai ma kuma ka zafafa I'm sorry

Salim ya sake mika masa hannunsa a karo na biyu, sai dai wannan karon na neman kawarda fadan dake tsakaninsu ne, ba irin na dazun ba da yake na gaisuwa. Wannan karon ma sai da Captain ya dade yana kallonsa hannunsa sannan ya mika masa nashi hannun ba tare da yace komai ba. Ammy ta yi murmushi.

 Ko ku fa, amman ace mace zata shiga tsakaninku kamar ba maza ba? Ban jidadin abun da ya faru ba kuma daman ina da kudirin na shirya tsakaninku

Still Captain be ce komai ba, Ammy ta bude baya ta shiga tare da Momy Ikilima dake yaba yadda Salim ya fi karfin shaidan ya kawar da girma kai ya kawo kansa. Direban ya ja motarsu zuwa asibiti Salim kuma ya shiga motarsa ya bi bayansu. Sai da aka fara diban jininsa aka auna bayan likitan yayi masa tambayoyi sannan ya ba shi gado domin har yanzu akwai gajiya a tare da shi kuma yanayin jikinsa ya tsananta sosai. A take aka saka masa drip Ammy ta tare a dakin tareda Salim hankalinta a tashe ta fita dakin tana sanar da Daddy. Momy Ikilima kuma ta koma gida dare da direba domin sanar musu halin da ake ciki da kuma dauko wasu abubuwa da ake bukata. Sai dakin ya zama daga Salim sai Captain da idonsa yake rufe hannunsa kuma yake sanye da cannula.

 I'm so sorry akan abun da ya faru, gaskiya ta bayyana yanzu kuma za a yadawa duniya cewar Hurriya bata aikata ba

 Matsalata da kai ba akan Hurriya ta aikata ko bata aikata ba ne, so please sunanta ya fita daga bakinka, matsalar sa muka samu saboda na karya hannun Adam ne so mu yi magana akan haka kawai

Salim yayi ya dan tabe baki.

 That's right... Adam yayi abun da kake bukata an turawa mahaifinka video kai ma kuma na turo maka ka duba whatsapp dinka

Captain ya bude idonsa ya kai hannunsa na hagu ya ciro wayarsa ya bude whatsapp dinsa, suna ganin Salim ya fara budewa kamin ya sauke video kiran Daddy ya shigo wayarsa ta whatsapp video.

 Daddy

 Hi Jamal... Yanzu Ammynka take fada an baka gado a asibiti, haka ne... 

 Eh amman da sauki ba yadda take daga hankalinta ba ne...

Salim ya juya ya fice daga dakin, yana rufe kofar dakin Ammy na kawowa bakin kofar dakin, ganin Salim sai ta fasa shiga ciki.

 Ina son magana da kai Salim

 Okay Ammy, zamu iya yi a nan ko sai mun tsada

 Idan muka matsa zai fi

Ya fara takawa ita ma ta taka sai suka jera suna tafiya.

 Amman ina son na sake yaba maka ne akan kokarin da ka y na kawar da komai a ranka, kuma ka bawa Captain hakuri duk da kasancewar ta wani bangaren ka fi shi gaskiya, na jidadin haka domin idan baka yi ba na san Captain ba zai taba iya aikata abun da ka aikata ba, ka san halin abokinka

Salim yayi murmushi.

 Nasan halin kayana Ammy ba sai kin fada min ba, shiyasa ai na bada hakurin da kaina, ni kuma na fahimci ban kyauta ba ta wani bangaren and be kamata na bar yarinyar kamar Hurriya ta raba ni da Captain

 Good na jidadin dawowarka sosai, daman ina neman wanda zai taya ni fadan nan domin ni kadai nake yakin nan a gidana, Engr yana goyon bayan Captain yan'uwansa kuma basa son fada masa gaskiya saboda Engr, yau ma Hajiya Nene fada ta yi min tana ganin kamar kishi nake da yarinyar nan ni kuma ba kishi nake da ita ba i just can't find any reason da zai saka na so ta, i know da cousin dinka aka aikata abun nan amman ko da ba gaskiya ba ne ai wannan abun ba zai shafe a idon duniya ba

Ya tsaya daga tafiyar da yake.

 Why are you telling me this Ammy?

 Bari na tambaye ka tsakaninka da Allah... Shin zaka iya auren yarinyar nan a lokacin nan?

 Ba zan iya ba, ko a gaba balle a yanzu na jinjinawa Captain yayi kokari kuma yayi jihadin da ba kowa sai iya ba

 To me yasa ba zaka taya ni fada masa gaskiya ba? Ka lurar da shi ta wani gurin da kurakurai suke mana

 Idan na yi hakan zai bata alakarmu da shi ne akwai, ba zai fahimta ba kuma sai yi tunanin na zo ne saboda na daga masa hankali na hana shi zaman lafiya da Hurriya ko sonta yadda ya dace

 Cikin Hikima zaka yi Salim, wannan taimako a gareni da kuma shi kansa abokinka, Wallahi bana son auren

 Amman an riga an daura ai Ammy meyasa baki hana ba kamin a daura

 Babu wanda ya sanar min da cewar za'a daura, mahaifinsa ya shigo gida ne kamar haka ya sanar mana sun je jaje kuma yin nemi aurenta an ba su har an daura, yarinyar da bata gani ma amman idonsa ya rufe ya rantsa sai ya zauna da ita

Salim ya sauke ajiyar zuciya ya saka hannayensa aljihu.

 Yarinyar nan bata cancanci Captain ba ko kadan ko da kuwa bata aikata ba, ya kamata ya lura da yadda duniya take kallonta a yanzu, amman kin san Captain ba a masa daidai, kawai dai mu saka masa ido zai fi

 Kai ma dai ba zaka iya ba kenan...! Babu wanda yake iya fahimtata

Ta cige baki tana kallon wani ward din dake facing dinsu, Salim ma gurin yake kallo sai dai kowa da kalar tunaninsa. After Salim ya fice Captain ya tashi zaune

 Ina fatan dai ba wata matsala ta ja rashin lafiyarka ba?

 Aa rashin lafiya ne kawai babu wata matsala Daddy

 Ma Sha Allah, daman ina da niyar kira na maka albishir sai kuma Ammynka ta sanar da ni ciwonka a take tawun giwa ya take na rakumi

 Akan Adam ne?

 Ka ga video ne?

 Aa zan sauke kenan ka kira ni, amman Salim ya fada min Adam din ya aikata abun da ake bukarta ya aikata

 Ya aikata yayi kamar yadda muke bukata, mahaifinsa ya turo min da video, domin ya kara kira bayan ya tafi gurin mahaifin yarinyar be yi nasara saboda na yi waya da shi na fada masa duk irin magiyar da za su masa kar ya aminta da su, sai kuma ya dawo ni ma yana rokona sai dai ban bashi wata amsa ba bayan wanda ka bashi, kuma na tabbatar masa a jibi Monday za a shiga kotu, sai gashi yau ya turo min da video

 Na jidadin hakan Daddy thank you very much, da goyon bayanka ne na samu wannan nasarar, zan yada video, na san hakan zai wanke yarinyar nan ko da ba gaba daya ba, zata yi farinciki idan ta ji i wish ni zan fada sanar mata ma saboda na mata wannan alkawarin

Daddy yayi murmushi.

 Yaron ma abun tausayi, kaddarori ne kawai da rashin tunani irin na yaran yanzu, jiya ma na yi waya da Hajiya nake tambayarta zuwa yaushe ne ya kamata ace Hurriya ta tare saboda damuwa a yanzu matsalar idonta ne, ina son ta dawo karkashin ikonmu ne gaba daya sai a nema mata maganin hakan zai fi armashi da ace tana gidansu za'a nema, sai dai Hajiya tace min mu daga kafa zuwa nan da kwana biyu zata tafi ita da Hajiyar Maru sai su yi maganar tarewar domin abun ne da ya danganci mata, kuma na bata sako ta fadawa iyayenta mu dai yarinya muka aura ita muke so, ba dan mun raina arzikin ubanta ba, amman ba ma bukatar komai daga garesu zamu zuba komai daga nan garin da zata zauna har zuwa inda aiki zai kaika

 You're best Dad ever samun irinka Daddy sai an tona, Hurriya ta yi sa'ar samunka a matsayin suruki

 Akan kawo mana neman taimakon auren wasu ma mu yi balle kuma naka? Jamal ba dan kana son yarinyar nan ba no a kashin kaina yarinyar ta ba ni tausayi na halin rayuwar data samu kanta, ina tunanin idan da ace yata ce ya zan ji, yarinya karama an bata mata rayuwa da suna akan abun da bata aikata ba

 Akwai matukar tausayi Daddy, amman Ammy ta kasa gane haka

 Zata gane Son.. Zata gane.. Matsalar da aka samu Ammynka mace ce mai matukar son riya da alfahari ba irin wannan auren take son ayi ba, kuma su mata suna da wannan dabi'ar da rike abu balle kuma bata son yarinyar, dole sai ka yi hakuri with time zata fahimceka..

 Ina fatan haka

 Bari na barka ka huta, zan aikawa mahaifinta da video yanzu, na san ba zai masa dadin kallo ba, amman ya kamata ya san gaskiya kuma ya san matakin da zai dauka ko dan nan gaba, amman da zaka hakura da yadawar wata kila zai fi, ya zai ji idan aka ce yarsa ce ta aikatawa yarsa haka?

 Daddy idan video be fita ba taya za a wanke Hurriya? Cikin alkawarin da na yi mata na fada mata cewar sai na yada wanda yayi mata wannan abun fiye da yadda aka yada hotunanta

 All the best... Get well soon

 Thank you Daddy

Ya fita daga video call din ya sauke video da Salim ya turo masa yana kalla, a take ya ji kamar an yaye masa ciwon dake damunsa saboda farincikin yadda Adam ya bada labarin komai a video kamar yadda ya fadawa Captain da iyayensa banbancin wacan video da wannan, wannan video shi ya dora shi da kansa a shafinsa na tiktok kuma yana sanye da tufafi na kamala har da hula kamar mutumen arziki. Bayan ya gama kallo ya jira Ammy a wayar sai ta amsa tana shigo dakin domin tana daf da kofar dakin ne a lokacin da ya kira wayarta.

 Lafiya? Allah yasa ba jikin ba ne

Ta karaso gurinsa da sauri. Captain dake jin kamar yau ce ranar angoncinsa ya mikawa Ammy wayar yana dariya.

 Ba shi ba ne, duba wannan ki gani

Ta karbi wayar ta kunna video ta kalla, sai ta tabe baki ta zauna.

 Still dai ba zai goge hoton tsiraicin Hurriya da yake idanuwan mutane ba, kuma hakan ba zai hana ace kasan yarinyar nan da aka yada hotunan ta da wani saurayi ba? To Captain take auren yaron Engr A A

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login