Showing 201001 words to 204000 words out of 279257 words

Chapter 68 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34690

ne kana da full hujja

 Okay, Daddy amman idan ka tafi please ka lurar da shi wasu abubuwan na rayuwa, na tafi asibitin ban ga yarinyar ba kuma na tafi gurin Momy tace min yarinyar tana gurin mahaifiyarta, ina tunanin korarta yayi gashi bata gani kuma mahaifiyarta bata da lafiya bakinciki sai yayi mata yawa

Daddy ya ji tausayin Hurriya ya kama shi.

 Amman me zai hana a nunawa mahaifinta video nan maybe zai sauko ya yafewa yarsa laifin da bata aikata ba

 Aa bana son nuna masa shi a yanzu, already case din yana hannun DSS idan aka fitar da video lauyoyin Adam zai su iya cewa an masa cin zafi ne an masa da karfi ya fadi abun da ba ayi ba, kuma na yi ikirarin ban dauke shi ba fitar da video zai rushe wacan ikirarin nawa, and Salim zai iya samun kofar shigar da koke a kaina, bana son ya samu wannan damar, amman idan aka je kotun shi da kansa zai sallamo yarinyar ai kuma dole kowa ya san me suka shirya kuma na saka a bincika mutanen da suka yada hotunan kowa zai fadi inda ya samu ai daga nan gaskiya zata fito

 So shari'a biyu za'ayi kenan?

 Yeah... Yarinyar nan mai tsada ce Daddy, su sun shigar da ni saboda na karya ma dansu hannu, mu kuma mun shigar saboda dansu ya ci mutuncin Hurriya, and na yi alkawari kowa sai ya karbi kasonsa sai na kunyata su kamar yadda suka kunyata yarinyar nan

Yana fada yana jaddawa jikinsa na rawa yana matse hannunsa.

 Allah kadai ya san halin da take ciki yanzu, sanadinsu ta rasa idonta gaba daya daman ba lafiya ta wadace ta ba

Daddy dai sai kallonsa yake da yanayin.

 Zan tare da mutane a gobe zan jajanta masa abun da ya faru kuma na fada masa matakin da ka dauka, idan ya ba mu hadin kai shi ke nan idan kuma be aminta ba dole mu yi aje case din

 Daddy please ba zamu aje case din ba, na mata alkawari ko da ba zan aureta ba be kamata na kasa cika alkwarin da na yi mata ba

Daddy be sake cewa komai ba, ya ciro wayarsa dake aljihu yayi yana tabawa. Can ya dago ya kalli Captain yana murmushi.

 Lawyer na ne ya aiko min sako, wai Bashir Sarauta yace ba a janye case din a gobe, wata kila yana tunanin saboda an kai case din dukan da ka yi masa a kotu ne ya saka ka sake daukeshi

 Ya zo nan ne?

 Ya zo nan amman ban yi magana da shi ba na fada masa be kai wannan matsayin ba a yanzu, da kam ina ganin mutuncinsa amman ban da yanzu, kuma na fada masa idan ya sake zargin a na da daukar yaronsa sai na shigar da kara a kansa

Captain yayi murmushi da be wadaci fuskarsa ba.

 Daddy wannan ai shi ake cewa fin karfi

Daddy ma yayi murmushi mai sauti irin na masu dollars and pounds.

 I have to do the needful kamin na bar garin nan, gobe da yamma zan koma Kaduna ban sani ba ko Ammynka zata bi ni ko kuma zata tsaya jinyar anta ne

Captain yayi murmushin da ya kusan za a iya cewa ya zame masa dole ne kawai, sannan ya mike tsaye yayi ma mahaifinsa sai da safe ya fice.



HAJIYA KALTUME POV.

 Tun jiya da muka yi waya da ke baki sake kirana ba, abun har ya soma ba ni tsoro, da na shirya zuwa gidanki a yau

Hajiya Fatee ta yi murmushi.

 Ai ni dole na zo na same ki Hajiya Kaltume shiyasa da Fadeel na kira cikin na ce ya zo ya kawo ni gidan nan, amman Hajiya gajin hakuri kika yi ne har kika aikata mata haka?

 Ina fa wai ni? Wannan ai can ya fito tsakaninta da dan'iskan saurayinta, wata kila matsala suka samu shiyasa ya watsa hotunan, ai ni ya biya ya hutar da ni wannan kadai ya isa ya hana Hurriya aure, domin babu wanda zai daukarwa yayansa uwa irin wannan? Sai dai a samu dan baro can ko masu gyaran talkama a hada su, idan ma ta samu domin babu mai auren makauniya

 Kuma kika ce ta rantse da kur'ane?

 Haka Khairy tace, wata kila kuma wani ne acan waje yake taya mu fadan, kuma shi ma yaron nan ta yi masa wulakanci ba, kuma abun da zai baki mamakin idan ba su saba haduwa ba a ina ya samu hotunanta

Hajiya Fatee ta kyalkyale da dariya ta bawa Hajiya Kaltume hannu suka tabe.

 Ai wannan abun yayi dadi Wallahi ana ganin yarinya kamar ta kirki ashe ita ma yar banza ce

 To kin gani dai gashi Allah ya tona asirinta, ko uwarta ai zaman banza ta so samu gurin Alhaji shi kuma da yake ba dan'iska ba ne sai ya bijiro mata da aure

 Amman ni abun ya ba ni mamaki da kika ce Alhaji be koreta ba, ga irinsu nan da yawa ana kora da ya korata da mun huta ma

 Ni ma abun da yasa na kira na tambaye ki kenan ko dai Malam be fara aikin nan ba har yanzu? Kin ga shiru fa ina zaune a gidan nan amman Alhaji be yi wani unkuri na maida aurensa da ni ba, jiya kuma Khairy ta fada min kuka yayi ta yi yana tsinewa wanda yayi abun nan

 Zai yi wahala ace ba a fara ba, ya kamata dai mu kara hakuri kar mu yi gaggawa, domin tun ranar da aka tura kudin na kira shi na fada masa an tura kudin kuma yace min sun shiga ya gani, har na yace min anjima kadan zai shirya ya tafi gurin Malamin nasa ya kai masa kudin, tun daga ranar ban sake jin wayarsa ba, ko yanzu na kira bata shiga ba

Ta sake gwada kiransa a gaban Hajiya Kaltume aka ce wayar a kashe take.

 Kin ji ko? Ina tunanin ko dai wayar tasa ta fadi ne, har wadda ta hada mu da shi na kirata tace ita ma bata samun wayarsa a yanzu

Da mamaki Hajiya Kaltume ta ce.

 To kuma be siye wata ba? Ni fa jikina ya fara sanyi Hajiya Fatee

 Karki ji komai, ni na yarda da Malamin nan dari bisa dari, mu kara hakuri idan aka kara kwana biyu ba mu ji komai ba ni zan shirya da kaina na tafi kauyen na bincika na ji

 Allah yasa dai yayi mana aikin mai zafi, so nake Alhaji ya zo jiki na rawa ya roki yafiyata kuma ya maida aurensa, sannan a shafe masa Hurriya da uwarta a ransa kuma a hana shi auren nan da zai kara a mallaka min shi na juya shi yadda nake so

 Wannan ai a rubuce yake, daman ya fada miki irin aikin zai yi kuma zaki gani, ke dai ki kwantar da hankalinki ba gashi kin fara gani ba, wata kila aikin ne ma ya saka hotunan nata suka yadu

Hajiya Kaltume ta rike baki tana mamaki da dariya.

 Haka fa.. Kin ga gaba kenan sai kora, kuma da yardar Allah sai Hurriya da uwarta sun koma bara, tun da idon ya rufe ba zan bar Alhaji ya nema mata magani ba kuma ba zan bari ya maida uwarta ba, kin ga rayuwa ta kare musu kenan, daman na fada mata sai na dandana mata bakinciki kuma sai ta gani, ba za a ci amanata a zauna lafiya ba

 Wani abun ma sai nan gaba

Suka bushe da dariya, Hajiya Fatee ta mike tsaye ta dauki hijab dinta ta saka.

 Bari na tafi kar na batawa Fadeel lokaci aiki zai je na ce ya kawo ni na ganki ya maida ni direba na yayi tafiya

Hajiya Kaltume ta mike tsaye ta yi mata rakiya suka sauko kasa suna hirar, bacin rai dake zuciyar Hajiya Kaltume tuni ya yaye saboda kawarta ta karafafa mata guiwa kuma ta kwantar mata da hankali. Ganin Khairy zaune a falon ya ba wa Hajiiya Fatee mamaki

 Ah... Na yi zaton kina waje? Tare da Fadeel muke fa

 Na sani bana jindadi ne shiyasa

Ta amsa a kasalance tana sauke ido kasa kamar munafuka. Hajiya Kaltume ta ce.

 Wai ke kam me yake damunki? Tun jiya kike wani laude laude kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki

Sai Hajiya Fatee ta daga hannu tana fadin.

 Wata kila abun yar'uwar ne ya shafeta kin san abun da ya taba gira shi ya kai ga ido har ya taba hanci, idan abun da ta yi karki saka kanki a damuwa kwana nawa ya rage miki ki har gidan ma, kuma wannan ai abun farinciki a gurinku, kowa be lalace ba sai Hurriya na tabbatar da Iyami tana lafiya ace wani ne a cikin yaran Hajiya Kaltume yayi haka farinciki zata yi 

 Kwarai kuwa shiyasa ni ma bana fatan alheri ya same ta sai sheri

Hajiya Fatee ta wuce gaba suka jera da Kaltume har wajen gidan, kamin Fadeel ya juya motarsa suka nufi karamin gate din gidan na bangaren Hajiya Kaltume. Daga inda suke tsaye suka hango shigowar manyan motocin na alfarma har hudu cikin gidan, duka motocin aka nufi bangaren Momy da su.

 To baki kuka yi kuma?

 Ta yi dai ita yar karyar arziki, ita din ma ba barinta zan yi ba Wallahi

 Aifa ki bari aikin Malam ya fara kawai sai wanda kika so zai zauna a gidan nan, ni na manta ban fada miki ba Afrah fa tana gidansu yaran suna gidana shi kanshi jiya gida ya kwana

Hajiya Kaltume ta rike baki.

 Ki ce Allah

 Ba kina wasa da lamarin Malam ba? Hmmmm

Hajiya Kaltume ta jinjina kai tana kara ganin girman Malamin da kwarewar aikinsa, Afrah da ta gagari Hajiya Fatee yau ace Fadeel ya kora Afrah gida. Babu halin yin wata doguwar magana saboda Fadeel ya faka mota a gabansu ya budewa mahaifiyarsa.

 Hajiya Fatee zamu yi waya

Hajiya Fatee bata sake furta wani abu ba saboda Fadeel yana gurin sai dai ta yi murmushi mai sauti ta shiga motar, Fadeel ya ja bayan yayi ma surukarsa to be sallama.




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
41

Da tunani kala kala Momy ta sauko falon Namra na bayanta.

 Yaya yau kai ne a cikin gidana?

Daddy dake zaune akan kujera tare da sauran yan'uwansa yayye da kanne yayi murmushi.

 Nafisa mamakin zuwana kike ne?

 Kwarai kuwa, Yaya tun da aka kawo ni gidan nan sau daya ka taba zuwa gidan nan fa, da Hajiya Turai ce ba zan yi mamaki ba, amman ganinka ya saka ni a fargaba Allah yasa ba Captain ya ce na yi masa wani abu ba?

Alhaji Munzali yayi dariya, Daddy ma dariyar yayi ya ce.

 Saboda ba ni da kunya zai na taso na kawo miki takakka har gida?

Ta yi dariya.

 Namra duk a firgicce take ita ma ta dauka Captain ya turoka, saboda jiya ya zo nan yana neman a kai shi gidansu Hurriya na hana Namra, wata kila hakan ya fusata shi ya kai karata a gurinka

 Hakan da kika yi ai kin yi daidai, Ammy sa ma ta yi masa magana be so ma amman daga karshe dai ya fahimta kuma yace ya hakura

Momy ta zaro ido tana dukan kirjinta.

 Ya hakura yaya? Amman ya kyautawa kansa daman can yarinyar bata dace da shi ba Wallahi, ni daman na san Hajiya Turai ba zata yarda danta ya auri yarinyar nan ba

Daddy ya gyara babbar rigarsa yana kallon Namra dake jera musu abun karyawa.

 So jiya mun yi magana da Captain saboda ya shigar da kara DSS yanzu kuma yana son ya janye karar ne a hannata komai a gurin mahaifinta, ni kuma yau zan koma Kaduna, shiyasa na zo yanzu na san be isa fita ba ina son na yi magana da shi mu kai karshe

 Hakan yayi, ban da Abin Captain na son wahalar da kai miye na wani shigar da kara, yarinyar nan fa makauniya ce ma idon za su bude ba za su bude ba Allah masani amman ya tsoma kansa a damuwarta har da ikirarin aurenta kamar wanda baya cikin hayyacinsa

 Wannan maganar kuma ina tunanin ta wuce Nafisa, ki sallamawa mai gidanki zan yi magana da shi

 Toh Yaya

Ta tashi jikina na rawa ta nufi bangaren Appa, a nan Daddy ya samu gaisawa da Namra yana tambayarta ya karatu.

 Ai na kare, next week zan tafi service Kaduna In Sha Allah

 Abu yayi kyau, muna da bakuwa kenan

Daddy ya fada sai ta yi murmushi tana jin farinciki jin cewar Captain ya hakura da auren Hurriya. Kamar yayan mahaifiyarta Alhaji Munzali ya san dalilin farincikinta sai ya bijiro mata da makamanciyar maganar.

 Aure fa Namra?

Ta yi shiru ta noce kai kasa, Daddy yayi murmushi ya amsawa Alhaji Munzali yana kare yarsa.

 Za'ayi a daga mana kafa mana Alhaji, komai ai lokaci ne za ayi babu jimawa In Shaa Allah

Yanayin yadda Daddy ya bada amsar sai ta ji kamar yana mata inkiya da auren Captain ne, hakan ya kara fadada farincikinta.

 Alhaji Rufa'i ku taba wani abu mana, kamin nan da wasu shekaru Nafisa ta mana gorin mun shago gidanta ba mu ci komai ba, kasan Nafisa akwai rike abu ga iya gori

Sai duk suka saka dariya har Daddy da yayi maganar. Daddy ya dauki ruwa ya sha ya ci yankan cake daya sauran kuma kowa ya ci abun da yake sha'awa even though ba san da zuwansu ba abun da yake gidan na tabawa ne Namra ta kawo. Appa ne ya shigo dakin yana sanye da Babbar riga irin ta Malam Bahaushe sky blue shaddar dake jikinsa har wani kara take tsabar sabun taka, be zauna ba sai da ya mikawa Alhaji Aliyu Turaki hannu biyu suka gaisa yana masa maraba da zuwa.

 Yau Yaya da kansa a gidanmu

 To kai ma gorin zaka min kenan, daman ance idan zama yayi dadi miji yana daukar dabi'un mata, mata ma tana daukar dabi'un miji

Momy ta yi dariya tana zaunawa, Appa ma dariyar yayi ya mikawa sauran hannu suka gaisa, sannan ya zauna.

 Toh Allah yasa ba laifi muka yi ba

Appa ya fada, sai Daddy ya kalli Alhaji Sadiq ya ce.

 Ka gani ko? Ita ma haka ta ce mana

Sai duk suka saka dariya har Namra, sai suka natsu sannan Daddy ya kalli Namra da Momy ya ce.

 To Nafisa ke da Namra ku ba mu guri zamu yi magana

Momy ta tashi ta wuce sama ranta fes, Namra ma ba laifi ta ji farincikin fasa auren da Captain yayi a yanzu kuma ba zata iya fadar dalili ba. Sai da suka haye sama gaba daya sannan Daddy ya kalli Appa ya ce.

 A cikin mu nan babu mai bukatar gabatar da kansa, musamman ma ni na san ni na baka auren Nafisa da hannuna, domin ni mahaifinmu ya wakilta na bada aurenta a madadinsa

 Haka ne ranka ya dade

Appa ya fada cikin girmama, domin bayan alakar auratayya Appa ya san waye Engr A A Turaki a fannin naira da kasuwanci.

 Toh da farko dai na zo nan ne saboda na jajanta maka abun da ya faru da yarka, ba abu mai dadi ba muna jajanta maka

Appa ya sauke ajiyar zuciya ransa yayi masa babu dadi.

 Wani ne yake kokarin ganin ya mutuncina, domin wannan abun ni aka taba ba wai Hurriya ba, kuma yarinyar nan ta da kur'ane a gaban yan'uwanta a gabana ta ce bata aikata ba, sheri ne kawai na makiya, ba kuma zan bar maganar ba yanzu haka mun yi da Lawyer na zai zo ya same ni yau mu tatauna matakin da ya kamata mu dauka

Daddy yayi murmushi

 Wani suruki da baka san da zamansa ba har ya dauki matakin kai yaron DSS, ya riga ka daukar mataki ina zaton be san ma Hurriya ta yi rantsuwa ba amman yana gaba gaba gurin yarda da cewar bata aikata ba, kusan shi ne silar zuwana nan hankalinsa ya tashi har yana zaton ko ka kore Hurriya ne?

Appa yayi ma Daddy kallon rashin fahimta

 Aa ban koreta ba, Gwaggonta ta tafi da ita zata fi samun kulawa a can saboda bakinciki abun da aka yi mata,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login