Showing 12001 words to 15000 words out of 279257 words

Chapter 5 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34643

marayu duk daya a yanzu

Hajiya Kaltume ta kai zaune saman gadonta farinciki a mamaye ta, domin dazun hasashe take yanzu kuma gaskiyarce zaharan Hajiya Binta zata fada mata.

 Hajiya ban fahimce ba

 Ai kin san komai Tsoho ba zai rasa fada muku ba

 Wallahi be fada mana komai, wata kila dai ita Nafisa ya fada mata, amman ni ban san komai ba

 Dazun ya zo nan ya fada min cewar sheidan yayi nasara akansa ya sallami Iyami, sai dai saukin abun saki daya yayi mata, kuma be sallame ta ba sai da ya damka mata gidansa dake samaru area kuma ya bata kyautar naira miliyan ashiri, duk da haka dai ina kyautata zaton zata dawo dakinta kamin lokacin ke da Nafisa duk ina son ja muku kunne akan yaran nan

Hajiya Kaltume bata san lokacin data mike tsaye ba ta daki kirjinta da karfi.

 Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un... Amman Alhaji yayi kuskure abun da ba ayi da kurciya tun can da ba za'ayi yanzu bayan ga yara

 Ni dai na kira na ja muku kunne ne kawai, domin na san ko na nemi ya bani yaran ba zai aminta ba saboda yana son yayansa kamar yadda yake son uwarsu, Allah ya tabbatar mana da alheri

Hajiya Binta na kaiwa nan ta katse kiran. Wani irin bille baki Hajiya Kaltume tayi ta kube shi.

 Munafurcin banza da wofi, wato ga Kaltume makiyiyar Iyami da yayanta har da wani kira ki bani amanar yara, ko mutuwa ta yi ai ba zan karbi amanar yayanta ba balle tana da rai, idan kin isa ki saka ya dawo da ita mu gani, har kina fada min yana son yayansa kamar yadda yake son matarsa tsabar kin raina ni

Duk wani farinciki da walwala dake zuciyarta da fuskarta ya gushe tun daga lokacin da ta ji cewar sakin aya aka yi ma Iyami kuma an bata kyautar kudi da gida.

 Wallahi Iyami kin cuce ni, ko a haka dai kin ci ribar mijina, kin haihu da shi dan ki ci gado, kuma yanzu ya sake ki ya dauki gida da miliyan ashirin ya baki, waya taba yi ma kyautar gida a cikinmu matansa, sai dai ko wace ta siya da kudinta

Password din wayar ta cire ta duba kiran dake kasam na surukarta Hajiya Binta ta taba na Hajiya Fatee. Kamin ta amsa duk ta kagu har ta fara saba da marwa a dakin.

 Assalamu Alaikum Kaltume

 Hajiya Fatee zama be gan ni, tsugune bata kare ba, Saki daya Alhaji yayi ma Iyami, kuma wani abun da ya fi ko wane bakin ciki kudi ya dauka ya bata har naira miliyan ashiri

 Million ashiri?

 Ai ba nan haushin yake ba, ya bata kyautar gidansa dake samaru, yanzu uwarsa ta kira tana fada min har wani gargadi take min saboda ya ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?san gatan jikokinta, kin san ba jikokin da take so irinsu, kuma tun da saki daya ne zata iya buga kafa a kasa tace sai ya maida uwarsu

 Tsab kuwa wannan shegiyar tsohuwar zata iya, saboda ba sonki take ba

 Ina fa, kuma ba ba zancen dawowarta kina ganin zan yarda Iyami ta bar gidan mijina kuma ta yi arziki da dukiyar mijina? Wallahi bata isa ba ai yadda ta ci amanata haka ni ma zan nuna mata ruwa ba sa'an kwando ba ne, sai an koya ma Iyami hankali, dan haka ki shirya tafiya gobe goben nan nake son mu tafi ba sai wata rana ba, kar mu sake ayi mana sakiya, domin ita ma zata iya shiga nata malaman ta janyo hankalinsa

 Maganarki haka take Kaltume, karki damu zan kira shi tun yau na fada masa gobe zamu zo, amman fa ki zo da wuri saboda kin san dajin nan babu an mutum ga halin da ake ciki kara mu yi tafiyar safe kar mu yi mugun gamo

 In Sha Allah karfe 8am a gidanki zata yi min, sai na zo

Daga haka suka yi sallama, Hajiya Kaltume tana kwafa tana jinjina lamarin.




IYAMI POV.


 Ban san me ya hana shi daukar wayata ba, kunyar abun da ya aikata yake ji ko kuma rainin wayo ne da raina talaka

Gwaggo ta kalli Bappa dake maganar ta girgiza kai.

 Alhaji Haruna ba shi da dabi'ar raina talaka, domin be taba mana haka ba wata kila dai yana jin kunyar abun da ya aikata ne, wata kila kuma baya son ka yi masa magana komawarta ne

Iyami ta kalli Bappa cikin karfin hali ta ce.

 Bappa da dai zaka kyale shi da ka kyauta min, domin na yi ta tambayarsa ko na masa wani laifin ne, amman ya ce ban masa komai ba, kawai dai bana jin natsuwar zaman aure da ni ne a yanzu

 Tun da can be san da wannan ba sai yanzu? Kuma be tashi sakinki sai yanzu da ciki wata shida?

 Ba saki yayi mata na wulakanci ba, ya kyautata mata daidai gwargwadon yadda ake son kyautatawa a saki da zaman aure, kuma aure rai ne da shi ko babu komai idan lokacin rabuwa yayi dole sai an rabu, mu dan bashi lokaci har ya dawo hayyacinsa ni na tabbatar Alhaji Haruna yana son Iyami akwai dai abun da aka yi

Wannan karon Gwaggo ce take maganar. Bappa ya mike tsaye yana ja tsaki.

 Akwai yadda aka yi na me? Ku yi komai ba za su bar shi ga Allah ba sai kun ci wani abu, yanzu zaki iya cewa asiri aka yi masa, kar ma ki kawo wannan maganar, ni na fita


 Toh Allah ya dawo da kai lafiya

 Ameen

Ya fice yana sake gwada kiran number Alhaji Haruna Mai Yadi. Fitarsa da kamar minti uku Hindu ta shigo dakin tana sallama, Gwaggo ta amsa mata. A bakin kofar dakin ta saki jakar hannunta tana kallon amiyarta.

 Iyami da gaske Alhaji ya sake ki?

Iyami na kallonta sai hawaye suka zubo mata, Gwaggo na ganin haka ta mike tsaye ta fice daga dakin domin bawa kawaye damar tattaunawa.





________________

Masu karatu kuna ganin Alhaji Haruna ya yi ma kansa mai kyau kuwa? Ya Hurriya zata ji idan ta san cewar Appa sakin Ammanta ya yi?
[10/18, 5:34 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: https://chat.whatsapp.com/GJ9hOtbWbfDKmq8NrKsDIG


&A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2ܠ? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?


5???5???5???5??? 5??

 Akwai matukar mamaki ace duk son da Appan Hurriya yake miki ya sake ki, saki fa Iyami?

Amma ta saka hannu biyu ta share hawayen fuskarta.

 Ni ma dai ganin nake kamar ba sakin ba ne, saboda ban saka ran ba mutuwa ce zata raba ba, har yanzu tunani nake ko dai boye min yayi? Wata kila na masa wani laifi ban sani ba

 Bayan kin ce ya fada miki baki masa komai ba?

 Hindu namiji na sakinka haka nan? Ai na ga sai da dalili

 Dalili daya ne Iyami sa'ar da matansa suke nema sun samu, kin mata a cikin manyan mata kuma tsofin mata kike zaune? Matan da sun kusa sa'ar gwaggo? Wace ce warinki a cikinsu? Iyami babu kalar kazafi da kage da ba su miki ba duk dan saboda ki bar gidan amman burinsu be cika ba sai a yau, maganin ma na san sun gwada Allah dai ne be ba su sa'a ba sai yau

 Hindu Waallahi ina son mijina, mijina kuma yana so na amman yau komai ya kare

Amma ta fashe da kuka.

 Har sai kin fada? Ai kowa ya san yadda kuke zaune ya san mijinki yana sonki kuma ke ma kina sonsa, sakin ma da zai miki Iyami na musamman yayi wane namiji ne zai saki mace ya dauki dukiya ya danka mata? Ai sai zababbu cikin mata, kuma ko yanzu karki yanke kauna In Shaa Allah zaki koma dakinki ki cigaba da addu'a nima kuma zan taya ki kuma ki saka ayi miki a islamiyayo nima kuma zan zaka ayi miki

Kasa cewa komai Amma ta yi sai kuka take kukan da da zaka iya rantsewa mutuwa aka yi mata, idan ta tuna da sakinta Appan Hurriya yayi sai ta ji zuciyarta ta narke ta rasa me ke mata dadi a duniyar nan da ace mutuwa yayi sai ta dangana amman tunawa cewar yana raye kuma shi da kansa ya zabi rabuwa da ita ya fi komai daga mata hankali.

 Toh wai a can kika bar su Hurriya?

 Ya ce zai rike su

Ta amsa mata cikin kuka. Hindu bata wani dade a gidan ba ta mata sallama ta fita domin komawa nata gidam ta dora girki. Haka ta wuni a daki idan Gwaggo da jikokinta suka shigo sai ta boye fuskarta ta danne kukanta har sai idan ta kadaita ita kadai, tunanin yaranta ya tsaya mata a rai, tana ta auna lokacin dawowarsu makaranta da kuma irin abubuwan da suke idan sun dawo, da dare yayi sai ta kasa bacci domin wannan ne daren farko da zata kauna a gidansu tun bayan aurenta shekara goma sha shida. Ko biki ake a gidan ko wata hidima Appa baya barin ta kwana ko da kuwa ba girkinta. Daren sai ya zame mata wani dare na dabam da bacci ya gagara kusantar idonta ma balle har ya sace ta, kukan ma sai ta neme shi ta rasa wata zuciyar nata raya mata hanyoyin da zata bi ta shirya da mijinta sai ta saka zaren idan ta karshe sai ga ba hanya ce mai bullewa ba, dare ne da yayi mata tsawo fiye da sauran dararen da suka gabata, karfe biyu da rabi ta doro alwala ta fara raya daren da sallah nafila a haka aka kira sallah asuba akan idonta.


HURRIYA POV.

Da murna ta shigo dakin Appanta ta zauna kusa da shi a kasa kamar yadda ta saba, sai ya kai hannu ya shafa kanta zuwa bayanta yana murmushi irin murmushin nan dake dauke da so da kauna da kuma farincikin abun da idanuwa suka yi arba da su.

 Hurriya toh yaya?

 Lafiya kalau Appa, ka dawo lafiya?

 Lafiya Kalau, ina can gurin aiki zuciya na nan tare da ku sai tunaninku nake Ina Hamad

 Shi ya ce ba zai zo ba?

Ta amsa tana kai hannu ta gyara gilashin idonta. Hajiya Kaltume dake zaune kan carpet ta yi murmushi, irin murmushin nan da ya zame mata dole ne, domin ta kasa hadeye maganar da Appa yayi cewa yana gurin aiki zuciyarsa na gurin yayansa ta ce.

 Hamad ai ba zai zo ba, dazun ma dukanta yayi ya fasa mata gilashi sai da Yasir ya shiga tsakaninsu

Appa ya kalli Hurriya cikin yanayin damuwa.

 Me ya hada ku?

Ta zayyana masa abun da ya faru daga karshe ta rufe da fadar Yasir ya shirya su. Appa ya sauke ajiyar zuciya

 Ina ganin yaran nan za su koma gurin bangarenki sa zama Kaltume, saboda a rika saka musu ido, kar wata Hamad ya ji ma yarinyar ciwo, daman ko dan kula da abincin da wasu abubuwan dole su koma can

 Gurina kuma Alhaji? Ni da nake da yan mata cike da daki? Kuma ka san yadda bama jituwa da uwar yarinyar nan yanzu nan Hurriya ko kaya ta taka na cire mata cewa za ayi na cutar da ita, ba zan hana ta zama ba idan haka kake so, amman dai da zaka barta a hannun Nafisa wata kila zamu samun zaman lafiya, daman Nafisa bata da yara da yawa uku ne kawai kuma mazan fita suke Namra ce kawai ka ga ta samu yar'uwa a kusa ko? Amman ni Hajiya ma sai tace na mata ba daidai ba domin ta kira ni tana ja min kunne akan yaran nan

Ko kadan maganar da Hajiya Kaltume ta yi bata yi ma Appa dadi ba, sai yake jin kamar bata son zaman yaransa a gurinta ne, hakan kuma sai ya kara jefashi a cikin damuwar sakin mahaifiyarsu da yayi gashi nan ya koma nema musu gurin zama domin ba zai iya barinsu a katon part din uwarsu su biyu kawai ba babu mai kula da su.

 Hurriya yata ina kike son zama?

Ya tambaya yana kallon fuskarta, Hurriya ta kalli Hajiya Kaltume sannan ta kalli mahaifinta ta ce.

 Gurin Hajiyarka ko Gwaggo

 Ba zan iya bari ku zauna hannun kowa ba matukar ina raye, na fi sonku a kusa da ni na rika yaran wasu ma ta ina zan bada nawa riko? Idam har ba zan iya bari ku zauna gurin Iyami ba to ba zan iya hakurin ku zauna a gurin kowa ba, je ki kira Hamad

Hurriya ta tashi ta fice, Hajiya Kaltume ta bita da kallo Appa kuma ya sauke ajiyar zuciya.

 Yaran nan sun zamar min kamar wasu marayu, Wallahi yau saboda tunanin abubuwan da suka faru na kasa sukuni

 Akwai damuwa kam sosai, na da zaka hakura ka dawo da mahaifiyarsu da duk yafi wannan nema musu gurin zama da kake, idan ma wani laifin ta yi maka ka yafe mata dan Allah ko mu da muka kwana biyu aka saki a yanzu ai sai mun ji dabam balle kuma ita da take da sauran kurciyarta

Appa be ce komai ba bayan sauke kai da yayi kasa, domin baya jin dawowa da ita mafita ne kamar yadda sakin ma ya kasa zame masa mafita domin ko yanzu jin yake kamar akan ?aya yake saboda tunaninta domin yana matukar son matarsa ga kuma tunanin makomar yaranta. Hajiya Kaltume ta tsare mijinta da ido ganin ya noce kai kasa sai zuciyarta ta raya mata zai iya dawowa da ita kenan ganin yadda ya zurfafa a tunani ga kuma son yaranta da yake. Sai a lokacin da Hurriya ta dawo dakin tare da Hamad sannan Hajiya Kaltume ta kawar da kai tana kwafa a zuciyarta, Appa kuma ya dago ya kalli Yayansa. Hurriya ta zauna a inda ta zauna dazun Hamad kuma ya tsaya jikin kofa fuskarsa ba yabo ba fallasa.

 Hamad ka ci abinci?

 Aa

Ya amsawa Appa da kai. A take Alhaji Haruna ya kalli Hajiya Kaltume.

 Ba a basu abinci ba Kaltume?

 Tuwo na girka, ka san Hamad ba ya cin ciwo kuma basa cin abinci da ake girkawa masu aiki

 Idan shi baya ci ita Hurriya bata ci? Haba Kaltume kin san uwar yaran nan bata cikin gidan nan a matsayinki na babba ki kasa kiran yaran nan ki ba su abinci?

 Ban yi tunanin ba su ci ba, ranka ya dade ayi hakuri ba za a koma ba In Shaa Allahu

 Hurriya zaki ci tuwo?

Hurriya ta daga kai a hankali daman tuwo is one of her favorite saboda abincin Appanta ne ita kuma duk abun da Appanta yake so tana sonshi, kuma yawan girka shi da Amma take ya saka ta saba da cinsa, domin Alhaji Haruna ba shi da wani abinci da ya fi tuwo duk arzikinsa ya fi son agirka masa tuwo a gidansa domin abun da ya saba da shi tun kamin zuwan arzikin.

 Zan ci tuwo Appa

Ya kalli Hamad da ko a yau ko sannu da zuwa be masa ba kuma be gaishe ba, abun da be saba ba domin duk tsaurin kansa yana gaishe da Appa yana masa sannu da zuwa kamar yadda Amma ta koya masa.

 Kai kuma me kake son ci? Je ka kira Dahiru ko Bello ya kaika Restaurant ka siyo abun da kake so

 Bana son komai

Ya amsa kai tsaye ba tare da ya kalli kowa ba. Appa ya kalleshi da kyau.

 Hamad zo nan

Ya shiga cikin dakin sai ya zauna nesa da Appa kamar wani bakonsa ko wanda be saba da shi ba, bayan kuma a da can ba haka yake masa ba idan yayi nesa da shi to yayi laifi ne, amman idan babu laifi baya zama nesa da mahaifinsa kuma sukan zauna su yi hira da juna ayi wasa da dariya sai dai ba kamar yadda suke yi da Hurriya ba.

 Me aka yi? Waya taba ka?

 Babu ba ayi min komai ba

Hajiya Kaltume ta tabe baki tana murmushi.

 Kai ma dai Alhaji, a gidan nan ba zai taba Hamad ya kwana lafiya? Idan ma an fi karfinshi ai kasan yadda yake yi ma mutane ruwan duwatsu ko kuma ya shammaci mutum yayi masa wata ?etar

Hamad ya dago ya kalli Hajiya Kaltume da irin kallon da ya fi kama da harara, daman can shi ne mai taya Amma kishi wani lokacin, Hurriya kam team babu ruwanmu ce.

 Toh na ga yana ta bata rai ne kuma yace ba zai ci abinci ba?

 Uhm. Hmm

Kawai Hajiya Kaltume ta ce ta cigaba da kallon Appa dake tambayar Hamad ina yake son zama.

 Ina Hurriya zata zauna?

 Gurin Momy

Appa ya amsa masa.

 Nima zan zauna a can

 Toh yayi kyau, amman dai ka saki ranka Hamad ka ji? Kuma ka ci wani abun yaushe rabonka da abinci?

 Na sha zobo da rana

 Zobo ai ba abinci ba ne, zaka sha tea da bread a hada maka?

 Bana son komai Appa bana jin yunwa

 Shikenan zan yi ma Nafisa magana sai ku maida kayanku part dinta

Appa ya fada cikin yanayi na rashin jindadin dansa be saka komai a ciki ba. Hamad ya mike tsaye ya juya. Appa ya bishi da kallo yana fadin.

 Hamad babu ko sai da safe?

 Sai da safe Appa

Ya fada ba tare da juyo ba har ya fice. Hurriya ta mike tsaye domin yunwa ta matsa mata lamba.

 Appa ina tuwon?

Appa take tambaya sai Hajiya Kaltume ta amsa mata.

 Je bangarena ki zuba ki ci, mahaifinki ya rima ci balle ku ci tare

 Toh

Ta nufi kofar fita da saurinta. Sai da ta fice Appa ya kalli Hajiya Kaltume ya ce.

 Dan Allah a rika kula da yaran nan, su da marayu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login