Showing 105001 words to 108000 words out of 279257 words

Chapter 36 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34662

kasa ta ce.

 Malam ina ganin kamata yayi ka koma dakin baki dake waje, idan dare ya kara yi zan zo da kaina, daman saboda gudun dana ko masu aikin gidan su ganka ne, kuma yanzu na samu mafitar hakan tun da har na yi ma dana karyar kai dan'uwana ne

 Hajiya ai duk yadda kika ce haka za'ayi, rufin asirin na ki ne ba nawa ba

Ya mike tsaye.

 Sai ki min jagora zuwa dakin bakin, ni ma hankalina zai fi kwanciya da haka

Komawa ta yi ta zauna yayinda yake tsaye yana jiran ta wuce gaba ta nuna masa dakin, sai ta dafe kanta tana jin kamar ta fashe da kuka, abun duniya duk ua isheta, idan tace zata bar cikin,tonuwar asirinta ne gashi har ya fara tasowa dan lokacin data dauka bata mayar masa da amsar ta aminci ko akasin haka ba.


HURRIYA POV.

Kallo daya ta yi ma Appa ta san ba lafiya ba, domin fuskarsa a hade take kamar be taba dariya ba.

 Appa barka da dare

Appa ya duba duban dake kara bayyana bacin ransa.

 Karata kika kao Hurriya?

Ta nuna kamta.

 Ni...

Hajiya Kaltume ta yi karaf ta ce.

 Aa ba ke ba shi.. Tun da kin raina mutane

Hurriya ta kalli Hajiya Kaltume da sauri domin kalamanta suna kara rudata ne kawai.

 Tafiya kike gida gida kina fadar na ki na saka ki makaranta?

Ta fiddo ido kamar za su fasa gilashin dake fuskarta su fito.

 Ni Appa Wallahi ban yi haka ba, ya za'ayi na yi haka?

 Toh waya je ya fada? Da Magariba nan Alhaji Garba ya same ni da zancen yana neman izini yana son ya nema miki makaranta, na gaza ne Hurriya?

Tana jin Alhaji Garba ta san makocinsu ne kuma mahaifin kawarta Husna. A take idonta ya cika da kwalla.

 Wallahi Appa, ban ce ka gaza ba, ban fada mata cewar ka ce ba zaka saka ni makaranta ba, ni ban yi magana da Babanta ko mamanta ba, Appa Wallahi ban kai kararka gurin kowa ba

Appa ya zaburo mata kamar zai kai mata duka.

 Idan baki fada ta ina suka ji cewar baki zuwa makaranta? Har zai same ni da zancen wai yana son ya sakaki makaranta baya bukatar sisina umarni kawai yake so, idan ba kin je ki fadi wani abun ba ta ina zai sameni da wannan maganar? Dukan sauran yaran babu wanda yayi wannan sai ke Hurriya?

Hajiya Kaltume ta tabe baki.

 Ai ita dai Hurriya kamar tafiyar Iyami take jira, duk ta bi ta lalace abubuwa take marasa kan gado, Allah ya tsaremu karki kwaso mana abun magana nan gaba

Cikin kuka Hurriya ta girgiza kai.

 Appa ka ce ka san halina, ba zan aikata maka irin wannan ba, ni dai na san na yi hira da Husna kawai akan karatuna, kuma ban ce mata ka kasa sakani makaranta ba, Wallahi Appa ban fada ba

 Kullum ana fada min abubuwan da kike yi Hurriya, yaron nan ma da na rabaki da shi baki ji ba, an fada min har kyauta yake kawo miki, kuma yana zuwa kina fita hira da shi, yanzu kuma abun ya fara tsallakawa makota, to sai ki tashi ki tafi can gidan kawar ta ki ya hada ke da ita ya rike, makaranta kuma ba zan saka ki ba, ke da karatu har abada, sai dai ki ganina gurin wasu, sannan ban yarda kowa ya saka ki, sai na gani idan da karfi zaki yi karatu, babu wanda zai saka ki makaranta da yawun bakina, idan ke zaki saka kanki Bismillahi

Hurriya ta tashi da sauri ta isa har gurin da Appa yake zaune ta rike kafarsa tana kuka.

 Appa ba ni da gata a duniyar nan sai Allah sai kai, na karbi laifina dan Allah ka yi hakuri

 O tooo kin aikata kenan, daman na san kin yi ai, domin babu wanda zai fitar da sirrin gidan nan sai ke, kullum kina can gurin wannan Husnar ana zagina da yayana ana fadar cin amanarki matan ubanki suke, Momy ma da take rike dake bata tsira ba, balle kuma ni da kika maida abokiyar gabarki, ban da rashin hankali da tunani irin naki ta ina zaki zauna kina zagin ubanki da kawarki har mahaifinta yayi tsaurin ido ya tinkari Alhaji da wannan maganar

Hajiya Kaltume ta fada, Hurriya ta girgiza kai da sauri, amman ta kasa magana. Kalamanta sai suka kara tunzara Appa ransa ya kara baci.

 Na fada miki, ki hada komai baki ki koma can gidansu ki zauna

Hajiya Kaltume ta daga masa hannu.

 aa Alhaji ba za'ayi haka ba, ai sai ka kasa su kara zaginka kuma, mu ma kuma ace muna gani aka koreta, daman dai ta bata maka suna a unguwar nan, kai ne dai baka sani ba saboda sai yau Alhaji Garba ya same ka da wannan maganar, amman zance kala kala ni na ji, Nafisa ma ta ji, kawai dai muna shakkar fada maka ne saboda baka yarda da komai aka fada maka na Hurriya, duk da haka dai ba zan ce ka koreta ba domin bata gidan da ya fi wannan

Hurriya ta kalleta tana kuka.

 Haba Hajiya ki ji tsoron Allah ki rika fadar gaskiya, bana zuwa ko'ina sai gidansu Husna ita ma ba kullum ba, Wallahi ban taba zaunawa wani guri na zagi Appana ba...

Hajiya Kaltume ta rufe baki.

 Laa ke ni da nake miki yaki saboda kar ya koreki, shi ne zaki dubi idona ki ce na ji tsoron Allah na fadi gaskiya, to da can tsoronki nake ji ne? Alhaji ka ji min wata magana?

Appa ya mike tsaye yana kokarin fisge kafarsa, domin ransa a matukar bace yake, Hurriya kuma ta kara rike kafar har sai da ya dago fuskarta ya dauketa da mari.

 Ba zaki sake min kafa ba, ki tafi can gurin wanda kika dauka ubanki ki zauna a gidansa, kuma daga yau sai yau ban yafe miki ba idan kika sake furta wata kalma marar dadi akan Hajiya

 Ba zan saka bakina ba, kar ki rufe ni da duka

Hurriya ta fashe da sabon kuka mai tsuma zuciya ta kwanta a gurin tana ta bawa Appa hakuri amman be saurare ba ya yayi ficewarsa.

 Toh sai ki tashi ki koma gidansu kawar taki da kuke munafurcin tare, daman Allah kadai ya san zagin da kuka min, uwarta ma ai yar gidan Iyami ce kin ga zata fi jindadin rike ki

Hurriya ta dago ta hade hannayenta.

 Dan Allah ki yi hakuri, ki bawa Appa hakuri Wallahi ban kai kararku ko'ina ba, kuma ban zauna na zageku da kowa ba

 Yanzu dai ki tashi ga kofa can ki fice min daga daki, kuma idan ba kina son fushin Appanki ya karu ba ne zai fi miki kyau ki bar gidan, idan ma gurin kawar zaki koma sai ki koma, idan kuma kina son kara janyowa kanki wata matsalar ne ga fili ga doki

Ta karasa tana nuna mata kofa. Hurriya ta mike tsaye ta fice daga dakin tana kuka sosai, downstairs ta sauko ta a nan ta hadu da Khairy dake zaune ta hade rai.

 Yaya Khairy dan Allah ki bawa Appa hakuri, dan Allah Wallahi ban kai kararsa ko'ina ba

Khairy ta fisge hannunta.

 Wannan ya zama karon na karshe da Fadeel zai ce ki dauko masa wani ki dauko, banza mai zubin karuwai ko wane namiji sai kin san yadda kika yi kika ja hankalinsa gareki

Ta tashi daga gurin ta nufi hanyar stairs, Hurriya ta bita da kallo hawaye dake mata zuba suna kokarin katsewa, ita kuma yanzu kishi take da ita ko minene? Beside ita da uwarta su suka shirya mata duk wani kulle kulle a gidan. Juyawa ta yi ta fuskanci kofa ta fara takawa har ta fice, bangarensu Namra ta nufa, ko da ta shiga falon babu hawaye a idonta dan haka babu mai sanin ta yi kuka sai idan an kalli idonta da kyau. Ba tare da ta tsaya kula da kowa na falon ba ta nufi stairs sai Momy ta kirata.

 Hurriya

Ta juyo sai dai bata daga kai ta kalleta ba.

 Me yasa kika kai karar bakinga gurin mahaifinsu Husna?

 Ko da na fada be zama lallai ku yarda ba, amman ni ban kai karar Appa ba, ban san dalilin mahaifinta na samun Appa da maganar karatuna ba

 Allah kyauta, iya baki dai yana da kyau muma Allah kadai ya san irin zagin da zaki jan mana

Hurriya ta juya ta ta cigaba da tafiyarta, sai da ta isa bakin kofar dakinta sannan hawaye suka zubo mata. Ta murda kofar ta bude ta shiga, sai ta samu kanta tsaye tana fuskantar madubin dake gabanta, wata macen mai kama da ita take gani, mai tsananin rauni da damuwa, cikin zuciyarta take hangowa mai cike da kunci da bakinciki. Takawa ta yi kamar mai koyon tatata ta isa gaban madubin dake dakin tana kallon Innocent face dinta.

 Rarrashi nake so, babu mai yi min, gata nake nema na rasa shi ta ko'ina, rayuwa a gidan da babu uwa akwai wahala ko da tana raye, farinciki neman gagarata yake yi, me na tare musu ne? Wane laifi na aikata wa kowa yake ta tsanata? Dan wannan abun har ya kai Appa ya koreni? Kuma babu wanda zai bashi hakuri?

Magana take da kanta tana kallon kyakkyawar fuskarta dake zube a jikin madubin.

 Ba komai yake bukatar kuka ba Hurriya, wani abun jajircewa yake bukata, ki karfafawa kanki guiwa, ki goyi bayan kanki, sannan kuma ki saurari zuciyarki, idan babu mai kaunarki ki kaunaci kanki, nuna musu zaki iya karki yi kasa a guiwa, wata rana ke uwa ce, irin wannan matsalolin ke zaki magancewa yayanki...

Wani ne ya kamata ace ya tsaya a gafenta ya fada mata wannan, akasin haka zuciyarta ce ke karanta mata karantun da a yanzu ta shirya daukarsa, domin a yanzu ne idonta ya bude zuciyarta kuma take kokarin waraka da rauni. Hannu ta saka ta share hawayenta na dama zuwa hagu, sannan ta yi murmushi ta juya cikin kuzari ta fara hada kayanta. Abubuwan da ta san zata fi bukata ta hada a luggage ta ta dauki Qur'anenta ta fito daga dakin, ta fara saukowa a hankali sai da ta sauko falo sannan ta kalli Momy ta ce.

 Momy zan tafi?

 Ina?

Momy ta duba ta da mamaki.

 Ina?

 Appa ya ce na bar masa gidansa

 Saboda wannan abun?

Hurriya ta yi shiru bata ce komai ba. Momy ta tashi tsaye.

 Ina zuwa, ki bar gidan ki tafi ina?

Ta nufi hanyar da zata sadata da bangaren Appa, kamin ta karasa Hurriya ta ce.

 Momy ko kin tafi ba zai hakura ba, ransa ya bace sosai

Momy ta juyo.

 Daman na san za a rina, yadda Kaltume ta kori uwarki wata rana sai ta koreki a gidan nan, ke ma kuma baki jin magana tun da kin san halin mahaifinki a yanzu ai ya kamata ki kiyaye, miye na zuwa ki yi tseguminsa da kawarki har magana ta dawo kunnensa

Hurriya ta sauke kanta kasa, ita kanta bata san yadda zata warware wannan abun ba, balle kuma su da suke kallonta a munafuka. Namra ta sauko rike da leda ta mikawa Hurriya dake tsaye.

 Gashi Ethiopian ya ce a baki

Hurriya ta kalleta, tana tsammanin zata taya ta jimamin korar da Appa yayi mata ko ta tausayawa mata amman bata ga alamar ko daya a fuskarta ba.

 Ki rike na bar miki

Ta juya ta ja Luggage dinta ta cigaba da tafiyarta, sai da ta fice daga bangaren na Momy sannan ta ci hawaye ya cika idonta duk yadda ta so ta hana su zubowa abun sai ya gagareta, domin bata iko da hawayenta a yanzu hasalima su suke da iko da ita. Har ta isa gate masu gadin suka bude mata suna tambayarta lafiya, bata hararo babban dalilin Appa na korarta a gidan ba. Idan ma mahaifin Husna ya same shi da zancen, be kamata ya koreta saboda wannan ba. Tana tafiya tana karfafawa kanta guiwa hawaye na zubo mata, har ta isa babban titin dake sokoto gusau road, a gurin ta tari napep ta hau zuciyarta bata raya mata zuwa ko'ina ba sai gidan kakarta mai kaunarta Hajiya Binta.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar? MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne? cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai? shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5??


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


5??5??5? ?5?? 1?? 8?



Hajiya Binta dake aikin dama shuwaka ta dago ya kalli Hurriya wanda shigowarta kenan da kaya niki niki.

 Subhanallahi Hurriya lafiya

 Appa ya koreni Hajiya

 Kora? Kora fa kika ce Hurriya

Ta daga kai idonta na zubar da hawayen da bata son zubarsu, sai dai kuma bata isa ta hana su zuba ba.

 Me kika masa?

 Kawata ce ta yi

 Kuma a gidan aka rasa wanda zai yi wani abu har kika fito?

 Hajiya Mai Napep yana waje yana jira

Hajiya ta sauke ajiyar zuciya.

 Shiga dakins ki dauko kudi a jaka ki ba shi

Hurriya ta nufi dakin, bata dade ba ta fito rike da one thousand ta fice ta sallami mai Napep din sannan ta dawo ta zauna kusa da Hajiya Binta.

 Hajiya yanzu kowa baya so na gidan nan, ban san me na yi ba, kowa ya tsane ni

Hajiya Binta ta bude robar gishi ta diba kadan ta zuba a cikin shuwakar data dama ta dauka ta sha sannan ta kalli Hurriya ta ce.

 Nasara ce take tare da ke jikata, duk gurin da kika ga tsanani yayi yawa, to wani alherin ne babba zai taho, wata kila nan gaba sai kin zama wata abar kwatance a cikin familynku, duk sai kin fi su daukaka da nasarar rayuwa Hurriya karki ji komai a ranki, kar wannan abun ya dame ki

A lokacin ne wani kukan shagwaba ya rufe Hurriya ta tabe baki tana kallon kakarta abar kaunarta.

 Hajiya ai yace ba zan yi karatu ba, wai ba da yawun bakinsa ba

 Idan yana takamar haihuwarki yayi shi ma ai haihuwarsa aka yi! Kuma wanda ya haife shi yana raye, kina can ma nake miki yaki balle kin dawo gurina? Ba dan yana gidan mahaifinki ba ai da sai na ce haka ya fi, daman na yi nayi ya bar min ku na rike ke da Hamad ya ki, yanzu kuma kin ga ya koreki da kansa

Hurriya ta kwanta jikin Hajiya tana zuba shagwaba kamar ba ita ba.

 Cewa yayi wai na tafi gidansu baban kawata na zauna saboda ...

Hajiya Binta ta girgiza kai cike da takaicin bayan ta gama sauraren dalilin korar da aka yi ma Hurriya.

 Kin yi tunani da baki tafi gidan Iyami a wannan yanayin ba, sai abun ya kara mata yawa a zuciya, idan ma zaki fada mata sai ki ce mata ni na dawo da ke nan gurina

 Shiyasa na taho nan ai

 Kim kyauta daman ina neman abokiyar zama, shi kuma Allah ya warware masa duk wani abu da yake cikin kansa, gaba daya an juye masa hankali ya canja kamar ba shi ba, gidan nan ma sai ya dauki wata uku biyu be zo ba, kiran waya kuma sai idan na kira shi, babu ruwansa da kowa sai Kaltume, gaba daya ta dauke masa hankali sai abun da tace yake yi

 Kuma ni ban ce Babanta yayi masa magana ba fa Hajiya, ni ban yadda aka yi ma Babanta ya ji ba

 Wata kila tana tausaya miki ne, sai ta aika hakan da kyakkyawar niya, shi kuma ya kasa fahimtar abun, daman kowaye zai ji haushi amman be kamata idonsa ya rufe har haka ba, maraicinki ya kamata ya duba, yanzu da baki da ni ko baki da uwa a raye sai dai ki koma wani gurin rabe gurin yan'uwa ko kuma wadanda baki hada komai da su ba?

Ta kara gyara kwanciyarta jikin Hajiya.

 Allah ma yasa ina da ke

Hajiya Binta ta yi murmushin dake kara bayyana tsufanta, ta shafa kan Hurriya.

 Kar Allah ya raba mu har sai na damkaki ga miji mai amana Hurriya

 Ameen

Ta amsa tare da rufe idonta tana dariya.

 Ja'irar yarinya wato har da cewa Amin ko?

Ta saka dariya sosai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login