Showing 198001 words to 201000 words out of 279257 words

Chapter 67 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34655

sake tambaya domin tabbatarwa.

 Yayarta ce, mahaifinsu daya a gurin Birthday Khairy muka hadu da Hurriya, saboda Khairy ce friend dita

 To me yasa ka hadawa hotunan? Bayan ka samu abun da kake so a gurin Khairy? Akan me zaka cutar da Hurriya meye nata a ciki?

 Ba ni na yada hotunan ba Wallahi, ban san waye ya yada ba, wata kila Khairy ce saboda ta ji haushi abun da muka yi mata, ta ce min sai ta dauki fansa, wata kila ita da yada hotunan

 Me yasa ka amsa cewar tare kake da Hurriya? Why? Idan ma an yada me ye ribarka na amsawa

Ya kasa magana sai wayyo wayyo yake yana kuka. Captain ya kama hannun ya murza.

 Ba tambayarka nake ba?

 Wayyo....wayyo.... Wayyoooo..... Na yi hakan ne saboda kar nawa sunan na bace ni kadai, dan Allah ka sa a maida ni gida dan Allah

 Za a maid kai, na samu abun da nake so ai ka saukakawa kanka, amman still zaka fuskanci hukunci...

Captain ya tsayar da video ya mike tsaye ya fice daga dakin da Adam ke ta ihu yana neman ceto.

 Ku bar shi a nan DSS za su zo su dauke shi, ku babu hannunku a ciki, ko a office kar wanda ya amsa cewar kun je dauko yaron nan

 Yes Sir

Ya sara masa, sauran soldera din da suke waje mota biyu duka suka sara masa, sannan ya bude masa motarsa ya shiga ya rufe motar ya sake sara masa. Captain ya cire plane mode din ya shiga contact dinsa ya nemo wata number ya kira, after sun gaisa ya ce

 Mubarrak akwai wata yarinya da aka batawa suna, kuma abun ne da ku ya kamata ace kun yi Handel a yanzu, Lawyer na zai shigar da kara a gurinku cikin dare nan, please ina son ka tashi yaranka a location din da zan turo maka yanzu su dauki yaron, already na saka an dauko shi daga asibiti na san be kamata na yi haka ba amman na kasa hakuri ne

 Me yaron ya aikata....

Captain ya labarwa abokinsa abun da ya faru a takaice, sannan ya dora da cewar.

 Already babansa ya kai case din kotu saboda na karya masa hannu, na zubar masa da hakora so now i want you to cover me up...

 Karka damu I know my job, ka turo Lawyer ka ya saka kara a gurin mu yanzu nan

 Thank you

Yana sauke wayar ya kira Lawyer sa Barrister Hauwa Zamau. Yana tukin motar yana fada mata abun da ya faru har ya isa gida.

 To a matsayin wa zamu shigar da karar?

Yayi shiru yana kallon harabar gidan kakan nasa.

 A matsayin wanda zata aura, ina neman hakkin cin zafinta da yayi, abu ne kika sani duk wanda ya yi ta adi ko kuma ya buga hotuna ko bidiyon tsiraici na mutum a yanar gizo ba tare da izinin mutum ba, to lallai irin wannan mutumin ya aikata laifi, and can be punished for Cyberstalking under S.24 of Cybercrimes (Prohibition, Prevention, etc.) Act 2015 of Nigeria or any law being in force in Nigeria..

 Amman a yadda ka fada min ya amsa maka cewar ba shi ya yada hotunan ba

 Wannan zai zo daga baya, a iya yanzu shi kadai muka sani da hotunan dan haka shi muke zargi, shiyasa muka shigar da karr gurin DSS saboda fadada bincike

 Good point, i hope iyayenta ba za su ba mu matsala ba

 I will fix that later... Ki aiko min da account number dinki yanzu nan

 An gama ranka ya dade

Ya katse kiran ya sauke wayarsa. Gallary dinsa ya shiga ya kama hoton Hurriya da ya dauka a dakinta ya duba.

 Mai tsada... Kin rike mutumcinki gashi abun da suke shirya miki ya koma kansu, ashe kaddarar mai yawa ce Allah ya takaita a haka, pretty girl with golden Heart...

Magana yake da hotonta dake cikin wayar yana murmushi kamar ance masa tana saurarensa, kaunarta ta karu a zuciyarsa, a yanzu ya kara tabbatarwa ita din tabbas mai tsada ce...
Sai da ya turawa Barrister alert mai kauri tare da Nafi'u sannan ya fito motar, sai a lokacin ya lura bakin motoci dake gidan, kamin yayi wani motsi kira ya shigo wayarsa wannan karon Daddysa ne ya kira, ya amsa kiran da girmama da ladabi.

 Hello Daddy

 Jamal kai ka aika aka dauki yaron nan daga asibiti?

 Wane yaro?

 Dan gidan Bashir Sarauta

 Cewa suka yi na dauka?

 Ka amsa min kawai ka dauke shi ko aa? Me ya fitar da gidan?

 Na dauke shi, amman na yi covering case din yana hannun DSS yanzu

 Why? Fadan nan ba naka ne kai kadai ba so ka cire hannunka a ciki ka bar ni da mahaifin yaron nan, ka zo gida yanzu nan

Daddy ya katse wayar a take. Captain ya karasa ya shiga cikin falon, ga mamakinsa sai ya samu Salim a falon tare da wasu mata biyu, sau daya ya kalli gurin da Salim yakw zaune ya dauke kai zai wuce gurin Ammynsa dake tsaye tana kallonsa da waya a hannunta.

 Jamal.... Ina Adam...?

Captain ya juyo ya kalleshi.

 Jamal....? How dare you call your boss like that?

 Ba a office muke ba, baka da wannan ikon a nan, ina Adam?

 Na dafa shi an cinye ka san ni maye ne

 Kai ka aika da boys aka dauko yaron nan ina ka kai shi?

 Taya ka san ni na aika aka dauko shi? Ka gan ni a gurin ne?

 Mahaifiyarsa ta fada min yadda komai ya faru? Taya zaka aikata hakan Jamal? Ina hankalinka ya tafi?

Captain ya taka ta isa inda yake tsaye, cikin wani irin isa da izza Captain ya ce.

 Bari na kira headquarter na fada musu Salim Sarauta ya shigo har cikin gidanmu ba tare da uniform ba, yana tukumar ogansa da sace wani wanda ban san da wanzuwarsa a kasar nan ba, kuma ka kira sunana kai tsaye with full of disrespectful, and you know yadda wannan abun zai taba aikinka

Captain ya kara matsawa kusa da shi sosai.

 Ka san yadda Power take da karfi a Familymu, zan yi duk yadda zan iya na ga an cire uniform a jikinka, lastly ka san yadda bad ending yake karewa korarren ko da karami ne balle kai, and you know i can do it, so respect yourself....

 YES SIR...

Salim ya amsa masa dan dole yana kamewa guri daya, sannan ya hade yawu ya juya ya kalli matar da hankalinta yake a tashe ya ce.

 Mu tafi Anty Nabila

 Mu tafi? Bayan ba mu san inda yaro yake ba? An zo an dauki yaro cikin asibitin yana cikin tsananin ciwo sannan ka ce min mu yafi? Mu koma mu yi me?

Cikin kuka matar take magana, sai dayar dake gafenta ya amsa waya sannan ta kama hannunta

 Mu tafi Anty Nabila

Sai da suka wuce sannan Salim ya kalli Captain ya juya ya fice daga falon cikin tsananin takaici.





Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
40

 Ban zan iya fadar wata rana da ka samu matsala da abokinka ba sai yau, duk wannan akan yarinyar da bata kai ta kawo ba ne? Kana kokarin fita hayyacinka, duk wasu abubuw ada ba dabi'unka ba su kake aro ka yafe yanzu! Idan idonka ya rufe ni nawa be rufe ba, ba zan taba karbar yarinyar da duniya ta gama ganin tsiraicin a matsayin suruka ba...

Be ji zai iya musu da mahaifiyarsa ba, saboda haka ya karasa gurin da take tsaye ya kama hannayenta ya sumbanta yana murmushi.

 Zaki so ta Ammy saboda kina son farincikina, kuma a yanzu farincikina yana tare da yarinyar nan, ba ni da wani buri a yanzu da ya wuce na ga na tsamota daga kogin da aka jefata

 Wai me yarinyar take da shi ne da babu a sauran mata?

 Na so wasu matan kamin ita Ammy kin tuna? Har an min baiko da wasu, duka baki ce komai ba ga wannan? Wanda ta fisu komai?

 Babu wani abun da ta fi su sai tallata tsiraici

 The more da kike zaginta the more da nake jin kaunarta na karuwa a zuciya, zagin da kike mata ya kara bude min hanyar son taimaka mata

Kallon rashin fahimtar inda anta ya dosa Ammy take masa, cikin bacin rai da daga muryar ta ce.

 Zamu wuce Kaduna gobe

 Ban samu amincewa daga gurin aikin mu ba

 I don't care zamu tafi Kaduna gobe idan hutun da ka rubuta ya kare sai ka dawo

Yayi murmushi sannan ya wuce ciki, da kallo Ammy ta bi danta, kiyayyar da take yi ma Hurriya a yanzu ba dan tana talaka ne kawai ba, har dan hotunanta sun fita a duniya ne, taya zaka kalli kazantacciya yarinya irin Hurriya a matsayin matar danta guda daya tilo? Duk shekarun nan da ta dade tana jiran zuwan wannan ranar? Ace daga karshe Hurriya ce? Duk matsayinta a idon duniya da yadda mutane suke kallon mahaifinsa? Wai ina kishin danta ne? Taya ya barar da komai idonsa ya rufe akan yarinyar nan? A yanzu ne take ganin ya dace ta yi wani abu saboda haka ta bi bayansa ta shiga dakin da yake, sai ta same shi yana canja riga.

 Captain... We need to talk

Ya karasa jan rigar kasa ya nufi gefen gadonsa ya zauna yana kallonta. Ta daure ta zauna tana aje numfashi a gurin da ba muhallinsa ba, daga bisani ta saita fushin zuciyarta.

 Magana ce da nake son ka ba ni aron hankalinka kuma ka bude zuciyarka ka karbi abun da nake son fada maka

Ya daga mata kai yana kara tattara hankalinsa gareta.

 Ba zan hana ka taimakawa yarinyar nan ba idan taimaka mata kake son yi, abu mai kyau amman kar hakan ya saka na manta waye kai, Captain ya kamata ka dawo cikin hayyacinka, ka tsaya ka yi tunani mai kyau yarinyar nan bata dace da kai ba, future dinta ya lalace sanadin haka zai iya taba naka rayuwar, taya zaka shiga taron mutane da fuskar yarinyar da duniya ta gama kallon tsiraicinta? Ni ma ta ya zan kalli kawaye na gabatar musu ita a matsayin suruka?

Yayi murmushi yana saka hannunsa na dama cikin kishiyarsa wato na hagu.

 Ammy kina so?

 Wane irin magana ne wannan? Taya zaka tambayi uwa tana son danta musamman uwa irin ni?

 Dan Allah kin amsa min

 Ina sonka irin son da babu uwar dake yi ma danta shi

 Toh dan Allah ki so Hurriya, duk mai so na, kamata yayi ya so abun da nake so, duk wani illarta da zaki ina min a yanzu ba zan gani ba, wata kila sai nan gaba shi ma kuma bana fata

 Ta ya soyayya zata rufe maka ido, ka kasa yin biyaya ga mahaifiyarka Jamal? Akan yarinyar daka hadu da ita da girmanka? Ka bijirewa mahaifiyar fa ta haife ka ta yi wahala da kai? Ko dan saboda kai kadai Allah ya ba ni shiyasa kake min haka?

Ta karashe maganar idonta na cika da kwalla. Ya kalleta da fuskar da babu wasa a cikinta.

 Zan hakura da Hurriya Ammy, matukar hakan shi ne zai faranta ranki, na hakura da ita Ammy, soyayya ta yi kadan ta yi min irin wannan rufin, zan hakura da nawa farinciki

Ta share hawayenta tana murmushi ta dafa shi.

 Allah ya maka albarka, ba zaka gane amfanin abun da na yi maka ba sai nan gaba, yarinyar ba ta dace da kai ba, be kamata ta zo a matsayin surukar mu ba

Ya daga mata kai yana murmushi kadan, sannan ya sauka daga kan gadon ya zauna a kasa ya kama kafarta ya rike.

 Ina rokon alfarmar ki bar ni na karasa aikin da na dauko, na yi ma yarinyar nan alkwarin zan gyara mata komai, shi wannan karki hana ni Ammy

Ta kama hannunaa da sauri cikin farinciki.

 Ba zan hana ka ba, na amince ka taimake ta, matukar ba zaka auro min ita a matsayin mata

 Na gode

Yayi mata godiya ransa babu dadi, domin a iya gaskiyarsa yayi mata alkawarin hakura da Hurriya saboda bata sonta, ba zai zabi farincikinsa sama da na mahaifiyarsa ba, sai dai yayi ma kansa wani alkawari daya zai taimaki Hurriya zai cireta a damuwa kamar yadda ya fada.

 Daddy yana nema na bari na shiga dakinsa

 Yana can bangaren mahaifiyarsa, dazun sau biyu Bashir Sarauta na aiko masa da mutane yana neman ka ba shi dansa

Be ce komai ba ya dauki wayarsa da keys din Nene dake kan gado ya fice daga dakin, gaba daya sai yanayinsa ya sauya, rashin kuzari da walwala sun tattara a fuskarsa da jikinsa. Kamar wanda aka yi ma mutuwa haka ya shiga bangaren kakarsa dake cike da mutane a falon da yaranta da jikokinta cikin ?a?anta har da Daddy dake zaune kusa da ita. Kowa zai iya shaidar Captain baya cikin farinciki domin abun a bayyane yake a fuskarsa balle kuma mahaifinsa da ya fi kowa sonsa.

 Ina makullin motata? Ashe fitina zaka je ka tayar shi ne ka karbi motata?

Nene tana maganar tana kallonsa, sai ya karaso ya mika mata key motar ba tare da yace komai ba, sannan ya nemi gurin ya zauna yana mamakin kansa da ada ne idan aka bata masa rai kadan sai yayi kamar zai tashin kowa balle kuma babban abu kamar wannan, amman a yanzu ya kasa yin komai sai ma sauyin yanayi da ya zo masa.

 Jamal.... Lafiya?

Nene ta tambaya mahaifinsa kuma sai kallonsa yake yana karantar damuwarsa. Captain ya kalli Nene ya kalli kowa dake falon sannan ya mike tsaye

 Ba komai, Daddy ka ce kana son ganina?

Momy Ikilima ta ce.

 Captain akwai wata matsala ne?

Ya girgiza mata kai alamar babu. Daddynsa ya sauke ajiyar zuciya cike da kulawa ya ce

 Shiga ka jirani a falon Hajiyar Maru

Ya amsawa Daddy da kai sannan ya fice daga dakin.

 Baka tambaye shi ina ya kai yaron mutane ba? Kuma na ga yanayinsa kamar da matsala, Allah yasa ba kashe shi suka yi ba, kasan zuciyar Captain fa idan abun ya motsa baya iya rike kansa

 Zan yi magana da shi Hajiya zan ji ko minene

Daddy ya mike tsaye ya fice daga falon, kowa sai mamakin yadda yanayin Captain ya canja. A falon Hajiyar Maru wato step mother dinsa Daddy ya samu Captain zaune ya soke kai kasa yana jiransa.

 Karantawa min abun da ya saka ka cikin damuwa?

Daddy ya tambaya ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????tun kamin ya zauna. Captain ya dago ya kalli Daddy ya fara magana da muryar da ke kara bayyana damuwarsa.

 Ammy ce....

Ya fada masa abun da ya faru tsakaninsu ya kuma jadda masa cewar ya hakura da Hurriya saboda mahaifiyarsa. Daddy yayi murmushi ya kawar da kai kamin ya juyo ya dauko masa zancen daukar Adam da aka yi, a nan ma Captain be boyewa mahaifinsa komai ba, har video da ya dauka na Adam sai da ya nuna masa.

 Samarin yanzu hauka tana damunsu, idan yarinya tace bata sonka sai ka koma bibiyar bayanta kuma? Da alama dai ba son gaskiya yake mata ba shiyasa ya koma bibiyar rayuwarta

 Ni ma haka na ce

Captain ya fada babu kuzari babu nishadi da jindadin da ya shigo da shi. Daddy ya ce.

 Amman Barrister tana da gaskiya, mahaifin yarinyar ba zai kawo matsala ba, ka san wasu iyayen basa son bibiyar irin wannan lamarin

 An abun haushi ma mahaifinta be san ina son yarinyar ba, be san na dauki wannan matakin ba, na shigar da karar ne a matsayin wanda zai aureta ba tare da tunanin wata matsala zata biyo baya ba, amman yanzu ina tunanin zan yi magana da Barrister na fada mata a canja abun

 Saboda me?

 Ammy bata so kuma. Na fada mata na hakura Daddy

 Hakan yana da kyau, amman ka bari mu yi magana da mahaifinta mu sanar masa halin da ake ciki idan ya aminta sai a sauya labarin daga kai zuwa mahaifinta kai tsaye, a matsayin mahaifinta ya shigar da karar ba kai ba, daman hakan zai fi mutuncin saboda kai ba aurenta ka yi ba, da ace kai mijinta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login