Showing 48001 words to 51000 words out of 279257 words

Chapter 17 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34665

na Hamad

Ta dora hannu akai ta fadi a gurin ta fashe da kuka mai karfi.








______________________

Masu karatu shin suwaye wadannan mutanen da suka dauki Hamad?
Me suke so? Za su dawo da shi ko kuma yaya?
Anya Hajiya Kaltume da Hajiya Fatee za su nasara akan kudurinsu?
Wai ni kam me Afrah ta yi ma Hajiya Fatee ne ta tsane ta har take neman raba aurenta da danta? Anya ana samun uwar mijin dake neman raba auren danta ta hanyar asiri?
Anya asirin da Hajiya Kaltume ta saka aka yi ma Iyami akan karta sake aure zai yi kuwa? Amma zata dawo gidan mijinta Appa ko kuma wani auren zata yi ko kuma dai ba zata auru ba kamar yadda Hajiya Kaltume take fata?
Waye wannan Captain din?
Waye Wannan Fadeel din?
Anya Momy zata daina halinta na kyamar Iyami da yayanta kuwa?
Akwai tsabtataciyar Soyayya a cikin littafin mai taba zuciya ta zauna a ruhi, ku dai kun san ba mu fara komai ba. Kuma da yardar Allah ba zan ba ku kunya ba. =??


Duk amsoshin wannan tambayar tana nan ?umshe a cikin littafi na biyu da zamu fara ranar Litanin mai zuwa In Sha Allah. Sai dai shi Book two din ba free ba ne na kudi akan 500 only.

If you want subscribe biya 500 to

2451879008
Zenith Bank
Hadiza Abubakar

Sai ku turo shaidar biyan ta wannan number 08036126660

?an Nijar kuma za su turo katin Zain ko Orange na 500 ta wannan number 08036126660.

Za ku iya bibiyar Litfafin nan a Arewabooks ga wadanda basa ra'ayin karantawa a Whatsapp. A username dina @khadeejacandy ko kuma ku yi searching book din Hurriya.

Sai mun hada ku a Paid Group Real Masoya masu Patronizing dina a ko da yaushe.>?p?
Ku huta lafiya, Allah ya bawa masu niyar siya kudin biya. >?2?

Huriyya book 2

5??5?(?5?(?5?$? 5??5?0?5?(?

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?

Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660

5??5??5? ?5?? 1??


Kamin direban ya isa gida duk wanda ke cikin motar ya dauka Hurriya shudewa zata yi, saboda kukan da take yana yin sama da nufashinta kamar nunfashin zai fice daga jikinta gaba daya. Namra ce take rike da ita tana kuka tana bata hakuri.

 Yi Hakuri Hurriya In Sha Allah zai dawo lafiya Allah zai tsare su

Hurriya bata iya furta komai, gashin idon nata ya rufe gaba daya saboda kukan hawayen ya hanata ganin dishe-dishe ma da take gani idan babu gilashi a idonta. Direban na fakawa Salma da Khairi suka fita suna kuka suka nufi bangaren Hajiya Kaltume suna kuka, Namra kuma ta tsaya ta riko Hurriya suka fito.

 Bana ganin komai Yaya Namra idon ya rufe gaba daya... Karki bar ni nan dan Allah tsoro nake ji... Kira min Yaya Yasir ko ki kaini gurin Amma ko ki kira min Appa na dan Allah

Tana maganar muryarta na rawa saboda numfashim da ya sarke ta. Ta san a gurin dayan su ne kadai zata yi kukanta ta more kuma ta fada musu abun da ya faruwa. Kowane a ko ?a idan abun farinciki ko kishiyarsa ya same shi guduwa yake gurin uwarsa, sai dai ita a yau bata da wannan gatan, ba dan mahaifiyarta bata raye ba sai dan bata tare da ubanta, bata taba sanin zafin rashin Amma a gidan ba sai yau, ko wane a yana bukatar uwa a kusa da shi balle kuma ita da take da lalaurar ido. Dukawa ta yi a gurin ta dora duka hannayenta biyu a kai ta kwalla ihu da kukam muryarta tana kuka har sai da duk wanda ke harabar gidan hankalinsa ya dawo kanta.

 Wayyo Amma ma, Amma..... Amma... Amma... Ke..... Amma na

Namra ta yi saurin rika hannunta tana kuka.

 Hurriya ba gani nan ba, ta zo muje ciki Momy tana nan ai

Ta fisge hannunta, sanin kanta ne daga Momy har Hajiya Kaltume babu wanda ta isa ta jingina a cikinsa ta yi kuka, domin ba su dauke ta kamar sauran ?a?ansu ba.

 Kira min Yayana kira Yayana

Namra na cira kafa da zimmar tafiya kiran Yasir sai ta hangoshi ya fito da saurinsa ya nufo inda yake.

 Hurriya

Hurriya na jin muryarsa ta mike tsaye da sauri ta fara lalaben inda zata ganshi.

 Yayana Yayana Yayana

Kusan duk wanda ke tsaye yana kallonta sai da ya tausaya mata, domin lalurar rashin gani babbar matsala ce. (Alhamdulillah da kyautar Allah, if you can read this ku gode Allah, ba zabinku ba ne, kyautar Allah ce, and don't forget littafin na kudi ne idan kika karanta baki biya ba, ko kika min sharing na barki da Allah)

Yasir na isowa ya rika hannunta dake ta rawa take da fatar bakinta.

 Yayana dan Allah ka kai ni gurin Amma... Dan Allah..

Without second thought yaja hannunta ya karbi key hannun dayan direban da ya aje Hajiya Kaltume few minutes before the incident happen. Ya bude motar Namra bata kara jin tausayinta ba sai da ta ga yadda take lalaben motar zata shiga, Yaisr ya taimaka mata ya saka ta a back seat sannan ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya murza key ya juya motar cikin tashin hankali, ba dan yana namiji ba da tuni shi ma ya fashe da kukan kamar yadda kanensa da mahaifiyarsa suke kukan. Shiru Hurriya ta yi a cikin motar domin bata ganin komai sai duhu zucuyarta kuma ta cika fa tsoron abun da ya faru. A harabar gate din gidan Yasir ya faka motar sannan ya budr ya fito da Hurriya. Sai da ya daga gate din gidan sai kuma ya ji ba zai iya shiga ciki ba domin ba zai iya zama mutum ya farko da ya labartawa Amma labarin an sace danta ba, ya san idan ya shiga gidan ta ga yarta a wannan halin sai ta tambaye shi shi kuma ba zai iya mata karya ba. Haka kuma ba zai iya barin Hurriya ta shiga cikin gidan ita kadai ba a wannan yanayin.

 Hurriya ko dai ki hakura mu koma? Ba zan iya shiga cikin gidan nan ba, bana son na daga hankalin Amma a yanzu

Tana jin haka sai ta saka dayan hannunta ta kwance hannunsa dake rike da nata.

 Tafi zan.... Iya... Shiga... Daga... Nan

Be san bata gani gaba daya ba, a zatonsa tana gani dishe-dishe kamar da, dan haka be musa mata ba ya bude mata gate ta lalaba ta shiga, ya maida kofar ya rufe sannan ya koma cikin motar ya fice daga unguwar. Hannu Hurriya ta mika tana lalaba hanya, tare da amfani da zuciyarta tana ayyana yadda hanyar take a lokacin da take gani.

 Ke Hurriya...

Ta ji muryar Rukayya sai wani sanyi ya ziyarceta. Ta karaso kusa da ita ta rika hannunta.

 Waya kawo ki? Mun ji an bude kofar gate ba mu ga an shigo ba shiyasa na fito na duba

 Yaya Yasir ne ya kawo ni, ya tafi Mama Rukayya kai ni gurin Amma na

 Me ya same ki Hurriya?

 Kai ni gurin Amma please, bana gani yanzu bana iya ganin komai sai hudu, gaba daya idon ya rufe, na daina gani dishe-dishen ma

 Innalillahi

Rukayya ta fada tare da jan hannunta suka shiga ciki, Amman dake zaune dakin Gwaggo tana kwadon zogale ta aje kwanon zogalen ta yunkura da cikinta wata tara ta mike tsaye da sauri ganin Hurriya da hawaye a fuska kacha-kacha har ya bata gaban hijabinta, gata sanye da uniform din makaranta da bata cire ba kuma babu gilashi a idonta.

 Hurriya me ya same ki?

Kunne da jikin da yayi kewar uwa ne kadai zai iya fahimtar yadda ruhu yake ji idan ya ji ko yayi arba da uwa.

 Amma ina kike?

Ta saki hannun Rukayya ta fara lalaben inda take jin muryar Amma. Amma ta mika hannu ta rikota sai Hurriya ta rumgume ta ta kwanta jikinta tana wani irin kuka da ya saka Amma ta kasa rike kanta ita ta fashe da kuka.

 Me ya faru Hurtiya? Me ya same ki? Waya kawo ki? Me ya samu idon naki ina gilashinki

Har Hurriya ta bude baki ta yi magana, zancen da Yasir yayi a waje ya fado mata a rai. Shi ma kenan ya ce ba zai iya sanar da Amma ba balle kuma ita da take yarta. Kamar an saka allura da zare an dinki bakin Hurriya haka ta zama, ta kasa furta komai kuma ma sai ya koma mata cikin zuciya hawaye kawai take ita yi.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Amma ta furta gabanta na bugawa da karfi. Ta san ba lafiya zata kawo yarta a irin wannan yanayin ba, kuma gashi ta kasa fadar komai sai rumgume ta take kamar zata shige jikinta.

 Hurriya yi a hankali mana, kin san akwai kanenki a jikinta, ko kuma ki zo ni na rumgume ki idan rumgumar kike so

Gwaggo ta fada, sai Hurriya ta girgiza kai tana kara kankame Amma.

 Hurriya dukanki aka yi?

Ta girgiza kai.

 Wani abu aka watsa miki a ido?

Ta girgiza kai.

 Fada kika yi da wani?

Ta girgiza kai.

 Dan Allah ki bude baki ki yi magana mana minene? Ko dai fada kika yi da Hamad? Na san zai iya cewa yayi miki mugun duka saboda bana gidan?

Maganar da Amma ta yi ta Hamad ta saka Hurriya fashewa da sabon kuka.

 Yasir ya kawo ta, ta fa yi magana dazun yanzu ne dai ta kasa cewa komai

 Wata kila fadan ta yi da Hamad shiyasa ta kasa fada tana tsoron kar na yi masa fada ya kara mata

Zuciyar Amma ta fi aminta da fada suka yi da Hamad shi yasa har ta furta hakan, ganin Hurriya ta fashe fa kuka a lokacin da ta ambace shi.

 Kai Hamad yana da matsala Wallahi sai ace baka iya zaman lafiya fa yan'uwarka, ko tausayinta baya ji

Rukayya ta fada. Sai Gwaggo ta ce.

 Kusan duk mabiyi da mabiyi haka ake, ba kowa ke shiri da juna ba

 Amman dai shi nashi yayi yawa

Amma dai ta yi shiru tana ta saurare numfashin Hurriyya dake fita da karfi..



FAMILY HOUSE...

A rikice Appa ya fito motar tun kamin direban sa ya gama fakin, ya nufi hanyar Falon Hajiya Kaltume cikin tashin hankali, hausawa suka ce ba a saka masa rana. Gaba daya kuka suke cikin falon har Namra da ta shigo. Hajiya Kaltume na ganin Appa ta kara mulmulawa a kasa tana dafa kai ta tashi zaune ta koma ta kwanta kamar wata bayarba...

 Eyyyy Eyyyy Eyyyy ni Kaltume yau na shiga uku yata, wayyo Umm Ruman, Alhaji ina cikin matsala da bala'i sun sace min yar auta, wai ni mi na yi ma mutane ne ne? Wayyo Allah na

 Haba Hajiya ki yi hakuri mana, idan ke kina haka su kuma yara waye zai rarrashensu? Dan Allah ki tashi

 Alhaji wasu sun tare mota sun tafi da Ruma

 Hamad ma yana can hannunsu ai, ba ita kadai ba, kuma In Shaa Allahu zaku dawo lafiya

 Mutanen nan ba su da imani shi Hamad ai namiji ne, ita kuma mace ce yarinyar yar shawalwala

Appa ya zauna a kujera ya cire hular kansa duk sanyin ac falon gumi ne ke keto masa ta ko'ina. Salma da Khairi suka fara fada masa abun da ya faru suna kuka ba tare da ya tambaya ba, Kamin ya dago ya bi kowa da kallo.

 Ku daina mana kuka tun da ba mutuwa aka yi ba, ku yi ta addu'a, idan ma wani abun suke so ai dole za su kira. Ina Hurriya?

Appa na rufe baki Yasir da shigowar falon kenan ya amsa masa.

 Yanzu na kaita gida?

Appa ya masa wani kallo.

 Gida ina?

 Gurin Amma tana ta kuka ta ce a kaita can, shiyasa na kaita amman ban shiga gidan ba

Appa ya dafe kai cike da takaici kamin ya dago ya kalli Yasir yana jin kamar ya mareshi.

 Ban taba sanin baka da hankali ba, sai yau Yasir ka kaita ta fadawa Iyami abun da ya faru kamar baka san halin da Iyami take ciki ba? Ciki ne fa a jikinta kuma tsohon ciki idan ta fadi ta rikice wani abu ya same ta ko ya samu abun da ke cikinta kai zaka mata magani? Wani irin shashanci ne wannan?

Yasir yayi shiru sai a lokacin shi ma yake ganin abun da yayi na kai Hurriya a irin wannan lokacin be dace ba. Hajiya Kaltume ta fashe da kuka.

 Haba Alhaji wake da Iyami yanzu an dauke min yar shawalwalar yarinyar, mace ce fa, al kara ma Hamad namiji ne

Appa ya tashi ya fice, Yasir ya bi bayansa, daga gidan station suka nufa daman kamin su isa Appa ya kira CP ya fada masa abun da ya faru, suna isa ya saka aka shigar da report kamin yan sanda da suke sashen kidnapping su tafi gidan aka kwaso duka yaran, ana tambayarsu yadda abun ya faru suna fada. Babban cikin su dake tambayar ya kalli Namra da ta kare nata bayanin ya ce.

 Wacece Hurriya? Ina ita Huriyyar take?

 Tana gidansu

 Okay ita ba yar'uwarku ba ce?

Appa yayi gyaran murya dan ya san Namra zata iya wata kwabar.

 Yata ce, ni na haifeta amma yanzu tana gurin mahaifiyarta da ta koma gida haihuwa

 To zamu iya ganin ita Huriyyar? Domin ga dukan alama ita aka zo dauka, ita da Ruma din a yadda na fahimta Hamad din tsautsayi ne ya rutsa da shi, rashin samun Hurriyya sai suka dauke Hamad din, dole akwai tambayoyin da nake son yi mata

 Ni ma na yi wannan tunanin duba da irin labarin da suka ba ni, zan je na zo da ita

Appa ya fada sannan ya kalli Yasir.

 Idan an gama ka maida su gida, ni zan je na taho da Huriyya

 To Appa

Yasir ya amsa cikin ladabi da biyayya, Appa ya ma Officer sallama ya fice. Tare da direbansa suka isa gidan Gwaggo, a waje suka faka motar direban ya fito ya bude masa mota ya fito. A ransa yana son shiga amman jin hake kamar ana tsikara masa allura a zuciya saboda ya doso gurin da Amma take.

 Bala, ka sallamo Hurriyya

 Toh ranka ya dade

Malam Bala ya wuce cikin gidan, Appa kuma ya jingina da mota, Malam Bala be dade ba ya dawo yana sanar masa Gwaggo tace ya shigo tana son magana da shi. Rasa yayi me zai ce, shi dai be isa ya juya yayi tafiyarsa ba, kuma yana jin kunyar hada ido da iyayenta ita kanta Amma a yanzu kunyarta yake ji. Haka dai ya daure ya danne duk wani abun azabar da yake ji ya shiga cikin gidan, sai da ya hada da addu'a sannan ya samu courage din shiga har cikin falon Gwaggo. Be zauna ba sai da ya risina ya gaishe da ita kamar yadda ya saba, ba dan ta girme shi ba, sai dai ma shi ya girme ta, yana bata girmata ne tun a lokacin da ta zama sukurukarsa a yanzu ma be yada girmanawarba, domin har a yanzu sun din suna da kima da daraja a idonsa.

 Hurriya ta shigo tana ta kuka, amman bata yi magana ba har yanzu ta kasa fadar abun da ya faru, a baki Rukayya muka ji cewar Yasir ne ya kawo ta ma, kuma da kayan makaranta ta shigo, babu gilashi a idonta, yanzu kuma sai ga Malam Bala ya shigo wai kana kiran Hurriya shiyasa na ce ya shigo da kai ciki mu ji abun da ya faru domin mu ma hankalinmu duk a tashe yake

 Gwaggo, ni ma kaina ban san abun da ya faru ba. Shiyasa na kira Hurriyar na ji ta bakinta

 Can gida ba su fada maka komai ba.?

Appa ya ki yarda su hada ido.

 Ba su fada min ba, Hurriya tana kusa?

 Eh tana dakin mahaifiyarta, bari a kirata

Gwaggo ta tashi ta fita. Bata jima ba Iyami ta shigo falo tana sanye da digon Hijab har kasa Hurriya na rike da hannunta. Appa na kallonsa sai gashi ya mike tsaye yana kallon cikin dake jikinta cikin wani yanayi na rashin jindadi.

 Na fada maka babu uwar da zata so yayan wasu kamar nata, yanzu wannan tashin hankali duk na minene? Ba komawa gidanka nake bukata ba kwanciyar hankalin yayana kawai nake bukata a yanzu...

 Iyami zauna

Amma har ta yi kamar ta ce masa ba zata zauna ba, domin niyarta ta kawo Hurriya kuma ta jadda masa amanar yayanta ta koma, sai kuma ta zauna domin bata saba musa masa a komai ba. Sai da ta zauna sannan shi ma ya zauna.

 Ba wani abu aka yi mata ba, ki daina saka kishi da son cusa kiyayyar Kaltume ko Nafisa a zuciyar yayanki, ba dukan Hurriya aka yi ba, ba wata bakar magana aka fada mata ba, babu wanda ya mata komai, ba mutuwa aka yi ba

 To miyasa ta zo tana min kuka? Kuma Yasir da ya kawo ta be shigo gidan ba ya fita?

 Ni ma shi na zo tambayarta

Amma ta kalli Hurriya har lokacin hawaye take sai dai ba kamar dazun ba. Ta kalli Appa

 Ina Hamad...!

Appa ya ji tambayar kamar saukar aradu. Appa ya kalleta ya kasa cewa komai.

 Ina Hamad Appan Hurriya?

 Dan Allah kin kwantar da hankalinki

 Kamar ya na kwantar da hankalina? Miye abun tashin hankali a tambayar Hamad? Ko kuma shi ya aikata wani laifin?

 be aikata laifin komai ba Wallahi, ki ba mu guri zamu yi magana da Hurriya

Amma ta kalli Hurriya kamin ta mike tsaye ya fice daga falon. Appa ya tashi daga inda yake zaune ya koma kusa da Hurriya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login