Showing 27001 words to 30000 words out of 279257 words

Chapter 10 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34636



5??5?2? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?

Hello Habibaties =?
?>?p?
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy


5???5???5???5??? 9??


Hurriya na shiga falon Hajiya Kaltume ta fara rabon ido ganin yadda kowa yayi jigun, wasu daga yayanta kuma suna amsa waya suna kuka. Gurin da ta tafi wayo ta nufa wato gurin yayanta ta tsaya kusa da shi tana kallonsa har ya gama wayar sannan ta ce.

 Yaya wai garkuwa aka yi da Hajiya?

Kamin ya bata amsa Khairi ta watsa mata harara.

 Tsohuwar munafuka, hala dadi kika ji?

 Dadi dai? Me ye abun jindadi a ciki da har zata ji dadin? Wace irin magana ce wannan?

 Toh Yaya idan ba haka ba, me yasa take tambaya?

 Bata da hakkin sani ne? Ni kuna bani mamaki a gidan nan Wallahi, miye laifi a ciki idan ta tambaya? Karki bata min rai yanzu na fara dukanki

Yasir ya karashe maganar yana nunata da yatsa, sai ta dauke kai domin ta sani sarai zai iya, ba wani jutuwa suke da juna ba. Ya dubi Hurriya dake gefensa tsaye.

 Eh sace ta aka yi, mu ma yanzu Appa ya zo mana da maganar sun ce za a ba su miliyan dari

A take hankalinta ya tashi, tana son ta sake cewa wani abu tana tsoron kar Khairi ko Salma su kwatseta, dan haka ta ja bakinta ta yi shiru tana cigaba da sauran yadda ake ta kiran yan'uwa ana fada musu.

****? ? ?? ****? ? ? ?? ****

A haka sai da Hajiya ta kara sati daya a hannun mutanen nan ita da Hajiya Fatee domin police aka saka a lamarin su kuma suka hana a aika da kudin, suka ce za a gano inda take, sai da Appa ya ga abun na su ba mai yi ba, ga hankalin yaransa da yan'uwan Hajiya Kaltume ya tashi ya nemi sassauci suka rage kadan ga miliyan dari, a sake neman sauki, daker da addu'a da sudin goshi aka samu suka sauko a miliyan goma, bangare Hajiya Fatee ma haka suka karba, Appa ya hada kudinaka rasa wanda zai kai, sai da wani kanen Hajiya Kaltume yayi jihadi yace shi zai tafi kai musu kudin, ranar da zai tafi suka fadi inda zai tsaya a dajin su zo su tafi da shi, haka kuwa aka yi Fadeel ya kawo nasa kudin aka hada da na Appa suka shiga mota aka kaishi har inda suka bukata suka fito suna masa addu'a, su kawo wajen gari suka tsaya. Ba zan wani jima ba suka kira suka ce aje a dauke ta a wata gona dake nan dogon dutse a nan za su aje su. Abun ka da mai nema Yasir da Fadeel da Uncle din Fadeel din suka nufi gurin da moto suna gudu kamar ba za su je su same su a gurin ba. Kamin su isa kowannensu hankalinsa ya tashi kuma zuciyarsa ta cika da zullumi, domin suna tsoron kar su je su tararda gawarta domin sun saba haka wani lokacin sai su ce aje a dauka sai an tafi a tararda mutum a mace.
A bakin titi suka faka motar suka fita suka shiga cikin gonar domin dubawa, Yasir da waya a kunne yana fadawa Appa sun isa gurin Appa kuwa sai gargadi yake masa.

 Yasir ku kula da kyau, zai iya yiyuwa dabara suka muku saboda idan kun shiga gurin su sace ku

 Aka yi mana Addu'a Appa In Shaa Allah babu abun da zai faru, fatanmu dai a samu Hajiya da rai

Yana rufe baki ya ji muryar Fadeel yana fadin ya karaso nan gasu a nan, da sauri Yasir ya katse wayar ya nufi gurin, Hajiya Fatee ce da Hajiya Kaltume daure jikin itace, kansu babu ko dankwali sai wani zane atamfa kala daya da suka yafa kamar wasu yan kauye sun yi yaushi kai kace allayahun da yayi sati ne a daure, fuska ta yi burun-burun kana ganin kasan an dade ba a sadu da ruwa ba, baki ya bushe idanuwa sun kode kamar wadanda suka kusa kusantar rame. Hajiya na ganin Yasir ta fashe da kuka, Hajiya Fatee kuma ta fara zubar da hawaye.

 Alhamdulillah Alhamdulillah

Shi ne abun da sukr ta fada bayan sun kwance su.

 Ku yi sauri muje kar su biyo sawunmu, Sannu Hajiya

Fadeel ya fada yana kallon mahaifiyarsa cike da tausayawa.

 Bana iya tafiya Fadeel bana iya komai

Tana maganar tana nishi hawaye na mata zuba, Hajiya Kaltume kam kuka take riri domin da yanzu da aka sako su da kuma lokacin da aka kama su duk yayi mata kamar mafarki, ita kadai ta an bakar azabar da suka sha. Duk yadda Yasir ya so su yi sauri hakan be samu ba saboda Hajiyoyin duk basa iya sauri tafiyar ma sai daker gashi jikin ba kadan ba balle yayansu su ce za su taimaka musu, a haka dai suka isa gurin motar, Hajiya Fatee ita ce mai tafiya kamar mai tatata, Hajiya Kaltume ce mai dan kuzari shi ma ba wani da yawa ba sai na karfin hali. Hankalin kowa be kwanta ba sai da suka isa gida, domin kin amincewa suka yi da maganar Appa da kuma na yaransu cewar a tafi da su asibiti a duba lafiyarsu, Hajiya fatee ce ta fara nuna karfiya sannan Hajiya Kaltume ta rufa mata baya. Daga gidansu Yasir Fadeel ya dauki mahaifiyarsa ya fice da ita zuwa family house dinsu bayan ta yi wanka, sai dai ta kasa saka komai a baki duk kuwa da irin lallabata da Fadeel yake. Be isa gida ba Yasir ya kira wayarsa yana fada masa wai sun kira sun ce shi ma wanda aka aika yana da mai da alama za a samu wani abu dan haka sun rike shi sai an bada miliyan 20.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, mutanen nan ba su da imani ko kadan, kai yaushe aka gama wannan kuma ace sun kama wani? Wai anya ana son mu cigaba da rayuwa a kasar nan kuwa? Wannan wane irin bala'i ne?

Haka yayi ta fada, Hajiya fatee tsabar tsoro ji take kamar ta rufe masa baki, domin ta ga tashin hankali da bata taba mafarki ba.

 Ka rufawa kanka asiri da zagin mutanen nan, ba au da imani ko kadan, su hanyar da imani ya bi ma ba su santa ba

Fadeel ya juyo ya kalleta a daidai lokacin da ya faka motarsa a harabar gidan, yan'uwa da abokan arziki suka fito da gudu suka yo gurin motar domin taron Hajiya Fatee ciki har da Afrah da Hajiya Fatee take zagi wato matar Fadeel da kuma yaranta masu aure.

 Wallahi Hajiya Kaltume ce taja min, ita na raka a kauyen

 Toh me kuka je yi kauyen?

Bata samu amsa masa ba sakamakon bude gambun motar da aka yi ana murna da zuwanta, daman kuma tana neman dalili da zai hanata yi masa wani bayani dan bata shirya tonawa kawarta asiri ba. Ta bangaren Hajiya Kaltume after ta samu ganawa da mutane ta huta zuwa dare danta Yasir ya dauketa zuwa asibiti kamar yadda mijinta ya umarta. Sun dubata suka mata duk wani gwaje gwajen da ya dace sannan suka bata maganin zafi domin kafarta na ciwo sosai saboda tafiya, sai kuma na ciwon jiki da ciwon kai da na ido saboda kukan da suka sha har kammaninta sun sauya.

BAYAN KWANA BIYU....

Hajiya Kaltume ce zaune kan kujera Maama na matsa mata kafafuwan da har yanzu ba su daina mata zafi ba, domin bata taba gwada yin tafiyar da ta yi daga inda yan fashin dajin suka kamata ba zuwa sansaninsu, ko a lokacin da take da kurciya balle yanzu da girma ya fara kamata. Momy ce ta yi sallama ta shigo falon tana sanye da wada tsadadiyar shadda yar mali sai sheki take kamar an watsa mata ruwa, kana kallon shaddar ka san ranar ta fara sakata, wuyanta na cike da sarkar zinarin da ba ko wace matar mai kudi ce zata iya sakawa ba, gamshin da take ma na dabam ne domin Momy bata yarda ta siye turaren irin wanda Hajiya Kaltume ko Iyami za su iya siye ba ko da kuwa kudin da take da shi zai kare. Idan kana neman dake ji da kansu asalin ji da kai da nuna isa idan ka yi arba da Momy ka kai karshen aya. Maama ce ta amsa mata sallamar tana hada baki da Khairi dake fitowa daga kitchen rike da bowl din kankana. Hajiya Kaltume tun da ta kalli kofar falon ta ga Momy ce bata sake sha'awar kallon gurin ba. Tsaye Momy ta yi kusa da kujerar da Hajiya Kaltume take zaune abun ka da matan da tsibbo ya waya kuma suka wayance shi sai Hajiya Kaltume ta zame kafafuwanta daga hannun Maama ta matsa daga inda Momy take tsaye, jiki be bata banza ta kawo Momy bangaren ba, tunani take wani abun ta zo yi mata.

 Kaltume ashe an dawo

Momy ta fada cikin izza tana Kiranta da Kaltume kai tsaye kamar yadda ta saba, tun zuwanta gidan taba taba kiranta da Hajiya ba balle kuma Yaya kamar yadda wasu matan suke yi idan za su kira uwargida ko da kuwa da sunan yaranta ne.

 Eh Allah ya nufa Nafisa

Hajiya Kaltume ta amsa kamar an mata dole tana wani kashe ido. Momy ta tabe baki kamar wadda ta manta a falon Hajiya Kaltume take idan ma Hajiya bata ganinta kuma yaranta suna kallonta, amman tsabar raina uwarsu da ta yi da kuma rashin tsoron anyi an ce ya saka ta yin haka.

 Toh Allah kyauta gaba

Maama da Khairi ne suka sam da Ameen, sukan tsoronta ya dade da cika musu ciki ba kamar mahaifiyarsu da take jin zata iya karawa da ita ba. Momy ta juya ta fara takawa kamar wanda bata son tafiya, haka yanayin ya ke tun tashi, sai dai lamarin ya samu promotion ne a lokacin da ta auri Alhaji Haruna Mai Yadi, saboda ta nunawa Hajiya Kaltume da Iyami ita yar sarauta ce kuma yar masu kudi ba Kamarsu.

 Mtsssss

Hajiya Kaltume taja guntun tsaki tana bin bayanta da harara.

 Wallahi matar nan ta raina min hankali, wato na fahimci so ta yi na mutu gaba daya idan ba haka ba ace ma samu na kubuto hannun azzaluman mutanen nan da ba su san Allah ba, amman bata shigo ta min barka da dawowa sai yau da aka kwana biyu?

Khairi ta mika mata bowl din watermelon din tare da fadar

 Hmmm Hajiya ai da baki dawi ba sai matar nan ta zuba ruwa kasa ta sha

 Ai ni bayan Iyami bana da makiyiya irin Nafisa, kuma ita ma sai ta bar gidan nan da yardar Allah, komai sai ya dawo karkashin ikona sai na bata mamaki, ai Wallahi da ban dawo ba da sai Iyami ta ci ubanta dan sai ta gane kuskurenta, duk saboda ita na sha wannan bakar wahalar, duk dalilinta ne da bata aurar min miji ba da yanzu ban san wadannan yanta'adda da ba su da imani ba, yanzu na fito ga kanen can a daure

 Hajiya ba su da Imani ko?

Maama ta tambaya.

 Ina fa, ai babu imani a tare da su, abinci sa mun ji yunwa suke ba mu, idan dare yayi muna nan cikin hudu sai idan sun haska mu, sun dauremu sai kace awaki, sannan a ciyayi muke bacci, baba kalar kwaron da be cize ni ba, shi kam sauro ya samu abun nema style style yake mana na cizo, kuma duk ranar da aka yi waya ba a samu daidaituwa ba sai sun mana duka, kuma a kafa muka yi tafiyar nan har ciki daji, yara kanana na haife su amman haka suke juya ni kamar waina, Allah dai ya isar min akan Iyami kawai zan ce, kuma kiyayya yanzu na fara, dacan ina boyewa? Wallahi yanzu a fili zan nuna bana sonta bana son yaranta, duk sai na ga bayansu

 Hmmm Hajiya karki ga yadda Hurriya ta shigo falon nan tana ta zumudi ta ji dadi an kama ki har tambaya take

Khairi ta shimfida mata fahimtarta akan Hurriya. Hajiya Kaltume ta cize baki.

 Shegya bakar dagga, daman idan bata yi murna ba ai bata cika yar kishiya ba, aiko sai ta gane shayi ruwa a gidan nan, ke shiga dakin yayanki ki kwaso min gilasan yarinyar nan gaba daya ki boye min su

Kamar mai jiran umarni haka Khairi ta tashi da zafinta da murnarta ta nufi hanyar stairs. Maama ta tashi daga kasan da take zaune ta zauna kan kujera.

 Amman Hajiya Yaya Yasir zai iya gane dauka kika yi fa?

 Ta ina zai gane fada masa zaki yi? Ko ma ya gane ai ba bayarwa zan yi ba, idan ya matsa min har shi ba zan ragawa ba, dan ni mai kaunar mai kaunar Iyami da yayanta ma bana kaunarsa, arzikinta daya ma dawo Wallahi da na mutu can da sai ta gane kurenta, kuma ita da Alhaji har abada

Sosai ta hade fuska tana maganar irin hadewar da ya kara mata muni da bakin fata.

 Hajiya ai ba ita kadai ba, Hajiyar su Appa ma fa bata zo ba sai a waya ta kira, amman Wallahi da Amma ce da tun ranar zata iso gidan

 Hmmm ita ai bata da wata power yanzu, ko ba komai a bakin rame take, kuma babu yadda zata yi da ni, bugu da kari kuma na kore matar da take so, sai na ga uban da zai dawo da ita a gidan nan

Sun dade suna hirar Hajiya Binta da Maama kamin Khairi ta fito daga dakin Yasir da gilasan har uku ta nunawa Hajiya.

 Kin gansu Hajiya cikin closet dinsa ya saka su

 Je ki yi musu mugun boyo idan ma bala'i yayi bala'i ki ce masa ni na dauka da kaina

 Ba sai ance haka ba, kawai kowa yace be shiga dakin ba kuma babu wanda ya dauka

 Shi ke nan, ya ma fi sauki

Khairi ta fada a ganinta shawarar da yayarta Maama ta bada ta fi, sama da ta Hajiya Kaltume. Kamin Khairi ta isa stairs aka dauke wuta, a take hankali Hajiya Kaltume ya tashi domin har yanzu bata gama wartsakewa daga tashin hankali da azabar da ta sha a dajin ba.

 Innalillahi Maama kunna haske, na shiga uku... 

Kamin Maama ta kunna fitilar wayarta Mekano dake aikin bada hasken wuta a gidan ya fara aikinsa, haske ya cika ko'ina. Hajiya Kaltume ta dafa zuciyarta tana sauke gajiya.

 Kai Allah raba musulmi da wahala, har yanzu ji nake kamar ina kusa da dajin nan, shiyasa ko waya bana son karba, mun ga tashin hankali mun ga shiga uku duk saboda bakar Iyami

Hajiya ta karasa tana fashewa da kuka, domin Iyami ta hana ta zaman lafiya ta hana ta rawar gaban hantsi.


*** *** ***

Ta dayan bangaren Iyami tana ta fama da nata, tunanin da damuwa sun hana ta walawa ko da kuwa tsakar gidan ne, ga wani sabon lalurar laulayi da ya same ta bayan dawowarta gidan iyayenta, iyakar kokarinta tana yi na nunawa Gwaggo da Bappa ta karbi kaddara, sai dai a kasan zuciyarta tana fama da tunani domin kuwa tana son mijinta, domin tana zaune lafiya a gidan tana rumgume da yayanta ciwonsu lafiyarsu duk ta sani, ba kamar yanzu da tunanin halin da suke ciki yake hana ta sukuni ba. Gashi a duk lokacin da Hamad ya zo gidan sai ya fada mata abun da aka yi musu, Hurriya ce bata fada saboda bata son tashin hankali Amma kuma tana da zurfin ciki. Gwaggo ma tana iyakar kokarinta na kwantar mata da hankali ganin cikin dake jikinta gudun kar ta jawa kanta wata matsala. Addu'a kuma su dukansu suka dukufa da yinta ta neman Allah ya daidaita tsakaninta da Appa, sai dai ta bar kyau tun ranar haihuwa domin bata damu da yin azkar din neman tsari ba, tana ta tawaya a wannan babin, duk kuwa da ta san tana cikin kishiyoyi irinsu Hajiya Kaltume da Momy.
[10/18, 5:35 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: &A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?

Hello Habibaties =?
?>?p?
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy


5???5???5???5??? 1?? 0??


Washe garin ranar...

Hurriya na cire uniform dinta na makarantar boko ta dauki bakar abaya ta saka, ta bude gurin da take zuba hullunata tun bayan da ta kwaso kayanta daga bangaren Amma ta dawo da su bangaren Momy a dakin da aka bata, ta dauko farar hulla ta saka a kanta. Sannan ta fara gyara dakinta ta kintsa komai, cikin natsuwa ta fito daga dakin ta shiga dakin Hamad da ya watsar nasa uniform din akan gado ta dauka ta aje masa ta gyara masa dakin, daman shi be kula da gyara daki ba ko a lokacin da Amma na gidan balle kuma yanzu da tufafinsa ma sai da Hurriya ta kwaso ta dawo masa da su dakinsa dake bangaren Momy. After ta gyara nasa dakin ta sauka kasa domin dauko abun shara da mopper haka take kullum idan ta dawo take gyara nata dakin da na Hamad domin Momy ta hana masu aikinta share dakin Hamad da Hurriya haka ma ta hana ko cokali suka aje masu aiki su dauka, kamar ya yaran gidan ba haka Momy take treating dinsu, musamman ma Hurriya da bata iya budewa kowa cikinta, Hamad kuma idan ya ci abinci a nan yake bari sai dai Hurriya ta dauke masa, ba kowane rules and regulations na Momy ya sani ba, ko na ya sani ba amfanin da za su masa domin ba bi zai yi ba.

Gurin da ake aje kayan taje ta dauko ta hauro sama a hankali, domin Momy ta jaddada mata bata son jin karar tafiyar kowa a saman, hakan ya saka take kokarin ganin ta kiyaye dokokinta, ta san ba dan komai take

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login