Showing 18001 words to 21000 words out of 279257 words

Chapter 7 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34637

wadaci mutum daya ta juyo ta zauna ta a hankali tana kallon Appanta dake jan kofar dakin. Gam... Kofar na amsawa gabanta ya yanke ya fadi, gaba daya sai ta ji kamar wata duniyar aka kawo ta, sai ta ji kamar wani gidan da bata san kowa ba kuma bata da gatan kowa a ciki aka kawota. Rabon da ta shiga bangaren Momy ma an dade, babu ruwanta da bangare sai da dalili ita ma Momy bata shiga nasu bangaren ita ta ware kanta dabam a gidan. Dayan dakin dake kusa da na Hurriya Appa ya budewa Hamad

 Nan zai mana Hamad?

Ya daga kai sannan ya saka kai ya shige dakin da kansa ya turo kofar dakin ba tare da ya jira mahaifinsa ya rufe masa ba. Appa ya sauke ajiyar zuciya ya juya ya sauka, Namra da Musib suka hada ido suna mamakin yadda Appa ya shigo da Hurriya be ma bari ta zo da kanta ba.

 Musib ina Miwan?

 Ya fita da magariba nan Appa

 Namra da Musib dan Allah a zauna lafiya, yaran nan kanenku ne, jini daya ne ku da su, bana son na ji wani tashin hankali ko fada, Hamad dai kun riga kun san halinsa ba sai an fada muku ba, duk wani abun da zai yi ku kawar da ido ni kaina da nake mahaifinsa hakuri nake da shi, Hurriya kuma kun san babu ruwanta da fita dan Allah a zauna lafiya

Nasiha yake musu amman zuciyarsa cike take da kunci da damuwa narar misaltuwa. Appa ya amsa cike da ladabi

 In Shaa Allahu Appa

Ya dan motsa kansa kadan alamar gamsuwa sannan ya nufi kofar fita.

 Sai da safe Appa mu kwana lafiya

 Allah yasa

Ya amsa sannan ya fice. Yana sakin kofar falon Musib yayi kwafa ya mike tsaye ya nufi stairs Namra ta bi bayansa, ita ta shige dakin Momy Musib kuma ya nufi dakin da zuciyarsa ta raya nasa Hurriyya na ciki. Ya tura kofar dakin kamar abun arziki ya tsaya daga bakin kofa yana kallonta idonta shar da hawaye.

 Yar gatan Appa, da kansa ya riko hannunsa ya kawo ki, kuma saboda ke yayi ta fada da Momy

Uffan Hurriya bata ce masa ba, har ya gaji da tsayuwa ya bar mata kofar a bude yayi tafiyarsa. Runtse ido ta yi tana jin wani sabon kuka na zo mata, ta dawo a rakube gurin ta ta san cewar zata sha azaba da wahalar zama, da ma ace bangaren Hajiya Kaltume aka ajeta ko ba komai zata samu sauki ta wani bangaren saboda Yasir, amman a na bangaren ta san babu mai sonta, gaba daya sai ta ji ta zama wata marainiya ashe ba sai da rashin uwa da uba ake maraici ba. Musib na barin kofar dakin Hurriya ya nufi dakin Hamad ya tura, kwance ya hango shi saman gadon ya baya kofar baya, kuma budewar da Musib yayi be saka Hamad juyo dan ya duba ko waye ba. Wani mugun kallo da tsana irin ta yan uba Musib ya jefi kanensa da shi, sannan ya bar kofar dakin shi ma be rufe masa ba, Hamad na jin alamar an tafi ya juyo ya sauko saman gadon ya iso gurin kofar ya rufe ta da karfi ya saka key, Musib da be jima da barin bakin kofar ba ya juyo ya kalli kofar jin yadda aka bugata da karfi.

 Zaka sha wahala yaro

Yayi kwafa ya nufi dakin Momy sai wani huci yake kamar mace, daman shi ne mai kishin da matan ubansa a gidan sai dai yana boye abun a zuciyarsa, yadda yake jin kiyayyar Iyami da Hajiya Kaltume ko Momynsa bata jin kiyayyarsu haka domin ita sai idan kishin ya motsa mata ne take kula su ko kula wani abu da ya shafesu.

Daren sai ya zamewa Hamad da Hurriya dabam, sanin cewar rabuwa mahaifiyarsu ta yi da mahaifinsu ya hana Hurriya rutsawa har safe, sai ta raya daren da kuka Hamad kuma bayan ya gama nasa fushin bachi ya sace shi. Ta bangaren Appa ma yadda ya ga rana haka ya ga dare, kwanan Hajiya Kaltume ta bangaren be kuranye masa damuwarsa ba, sai ma ya kasa kwantar daga karshe ya koma falo ya zauna ya kunna Tv sai dai kuma babu mafitarsa a cikin kallon kamar yadda babu shi a cikin bacci sai ma karin damuwa, me yasa ya aikata shi ne abun da ya tsaya masa a rai yake ta tambayar kansa, idan kuma ya tuna da abun da yake ji idan tana gidan sai ya ga kamar yin haka shi ne daidai.

Washe gari da wuri Hajiya Kaltume ta tashi, daman duk ranar girkinta da wuri take tashi ta shirya masa abun karyawa, kasancewar bata da mai aiki tun bayan da ta dauki Iyami aiki ta aure mata miji bata sake yarda ko mai sharar gida ta sake dauka ba, sai dai ta yi komai da kanta ba kamar Momy ba da masu aiki ne suke mata komai sai dai ta ci idan kuma ranar girkinta ne sai dai ta dauki na Appa ta kai masa.
Ko da bakwai ta yi ta gama hada masa ruwan zafin tea da gasa masa bread dan ya fada mata tea kawai zai sha baya son cin komai. Yana shan tea yana hamma saboda bachi da ya gagareshi da dare da alama yana neman fansa a yanzu da safiya.

 Wai dazun ina barin bangarenka Hajiya Fatee ta kira ni

Ya dan juyo kadan yana kalleta alamar ina saurarenki.

 Wai danta Fadeel ya samu tsabani da matarsa shi ne take son na zo

 Allah ya kyauta...

Yadda ya amsa mata ya karantar da ita izinin zuwa ne, daman kuma ta san ba zai hanata ba.

 Ameen zaman auren ne na su, zaman lafiya ta gagar??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a Allah ya shirya tsakaninsu

Appa dai be sake cewa komai ba, har ya shaye tea ya aje cup be taba bread ba. Hakan kuma be yi ma Hajiya dadi ba domin ta san damuwar ba zata wuce ta ?a?an Iyami ba ko kuma ta Iyamin ma gaba daya. Ta dauke cup din ta fita ba tare da ta fada masa yanzu ta tafi ba da safen nan. Ta isa bangarenta rike da cup din. A dinning din da duka matansa suke fara cin karo da shi a kowane falo idan suka fito daga bangarensa ta aje cup din sannan ta nufi dakinta, tana shiga ta raba jikinta da tufafin da ta saka da safen nan ta daura tawul ta shiga bathroom, a gaggauce ta yi wanka gudun kar ta yi latti sanin cewar inda za su je kaune dake gaba daji baya daji. Ko da ta fito ta samu Khairi zaune akan gadonta fuska a kumbure musamman bakinta.

 Subhanallahi haka Yasir ya fasa miki baki saboda yar iskar yarinyar nan?

 Ba laifin Ya Yasir ba ne Hajiya, laifin Appa ne yana mugun son yarinyar nan, ya fi kaunarta da duka sauran ?a?ansa, dubi yadda ransa ya bace saboda na fada mata gaskiya bayan kuma gaskiyar ce

 Hmmm ai ni ganin nake kamar ba banza uwar yaran nan ta bar Alhaji ba, ita kanta ai ba a banza ta aure min miji ba, yanzu kuma saboda yaran nan Allah kadai ya san ran mutun nawa zai Sace a gidan nan

 Wallahi sai na rama komai ta dade

 Toh ki rama dai ta sigar lalama, in ba haka ba Alhaji ko Yasir su ci ubanki kin san jira kawai suke

Ta tashi ta fice dakin tana wani zakuWa ita ga balagaggiya. Hajiya ta shirya cikin koriyar Atamfa ta saka farin mayafi ta sauki jakarta mai kala daya da gyalen da kuma talkaminta ta saka sannan ta dauki wayarta ta kira daya daga cikin drivers din gidan ta sanar masa fitarta. Gurin da take aje kudi ta bude ta dauko kudi mai yawa ta zuba a jakarta sannan ta rufe ta rataya jakar ta fito rike da wayarta sai kamshi take zubawa irin na manyan matan masu kudi kuma masu miji da ikon gida.

 Hajiya fita zaki yi?

Maama ta tambaya.

 Eh wani guri zamu je da Hajiya Fatee

 Allah ya tsare, Hajiya kin ga yadda Ya Yasir ya fasa bakin Khairi

 Na gani, ku ma sai kun yi taka tsantsan ai, ni ba dan ubansu daya ba ai sai na tsora ta na ce aurenta yake son yi

 Lallai ya fi sonta da mu ma

 Hmmm Allah dai ya kyauta, ki tashi sauran yan 'uwanki kar su yi latti makaranta, ni na fita

Daga haka ta fice daga falon Maama na yi nata Allah ya tsare. Ko da ta fito direban har ya tashi motar ya juyata tana fuskantar gate domin ya san uwargidan Alhaji Haruna Mai Yadi bata daukar raini. Tana shiga motar be tsaya da ita ko'ina ba sai gidan aminiyarta Hajiya Fatee, yana aje ta ya juya a can ma ba su bata lokaci ba, Hajiya Fatee ta kira direban dake kai su kauyen ta sanar masa sun shirya, ba su yarda su tafi da motarsu ba saboda tsoron masu kidnapping da kuma tonon asiri, sai dai su dauki shatar motar kasuwa ta zo ta dauke su har gidan Hajiya Fatee ta kaisu inda za su je, kasancewarsa mijin Hajiya Fateen ya dade da rasuwa ita kadai ce a katon gidan sai yan matanta biyu da kuma masu aiki da danta Fadeel ya zuba mata.

Misalin karfe tara da rabi na safe suka kama hanyar kauyen gidan zalla dake cikin local government din Kwatarkwashi. Suna tafe suna hira Hajiya Fatee na kara fada mata yadda matar danta Afrah ke son mulkar mata a ta saka shi ya manta da ita. Idan ta kai aya sai Hajiya Kaltume ta dauko nata zancen na abun da ya faru tsakaninta da Alhaji a jiya. Sanar da shi da suka yi cewar suna nan tafe ya saukaka musu wucewa kai tsaye dakin da yake gabatar da tsiface-tsifacensa. Sai da ya fara yi musu maraba da zuwa sannan Hajiya Kaltume ta ciro kudi 300k ta aje masa tana masa godiya.

 Aiki yayi Malam, dan haka na zo da kaina na kawo maka goronka, kuma na yi maka godiya

Malamin da hakoransa ke daskare da jan goro ya yi dariyar jindadi da farinciki ya jinjina kai.

 Hajiya ai na fada miki, indai muka yi aiki ba a dawo mana da shi, kuma kar tunanin kin yi kin yi baki dace ba yasa ki karaya a gurinmu, idan kin ji ana malam anjima da nisa ba ma gobe da nisa ba to kika zo nan kakarki ta yanke saka kawai

 Na gani ai Malam Wallahi na gode, domin shekara da shekaru ina neman yadda matar nan zata bar min mijina amman abu ya garara sai an yi kamar za a rabu sai kuma ka ga ba rabuwar bace, sai yanzu Allah ya kawo karshen abun, sai dai ko yanzu ni ina jin tsoro domin na lura ya shiga damuwa matuka gaya saboda sakinta da yayi, ina jin kar ya ce zai dawo da ita domin saki daya yayi mata

 Ina ko alama! Karki damu Hajiya, idan har mutum zai mutu ya dawo to kishiyarki zata dawo gidan, ai farraqu muka musu ita tana gabam yana yamma har abada ba zama a tsakaninsu

Wani kalar dadi ya lullube Hajiya Kaltume.

 Haka nake so, kuma ina son a koya mata hankali so nake ka yi mata wani aikin da ba zata sake aure ba har abada, tun da ta zabi kishi da ni to ko bayan ta bar gidan mijina sai ta dandana bakincikin da nadanar auren Alhaji da ta yi, sannan be sake ta sai da ya damka mata kudi har miliyan asirin, Malam ina son a lalata duniyar da ya bata, har da gidan da ya mallaka mata idan akwai yadda za'ayi a ruguza gidan ko ma ya karbe abunsa, kuma a daureta ko kare kar ya sake sha'awarta balle har ta yi aure

 Wato so kike a lalata duniyar da ya bata, ba wadda ya bata kawai ba, har tata duniyar da ta mallaka za a iya lalatawa idan kina so

 Aiko idan ka yi min haka, ina mai tabbatar maka aikin Hajji bana da kai za'ayi, kuma zan maka kyautar kudi har naira miliyan daya

Malamin ya sake yin dariya yana gyara babbar rigarsa.

 Hajiya na miki alkawari akaifa kishiyarki ba zata sake amfana da ita ba, ba duniyarta ko ta mijinki da ya bata ba, har dukiyar wani idan ya dauka ya bata ba zata taba amfanarta ba, ita da aure ko sai lahira idan ana yi, kuma yadda ba a mutuwa a dawo haka ba zata sake dawowa a gidan mijinki ba

 Alhamdulillah

Hajiya Kaltume ta fada tana daga hannu sama ta yi ma Allah godiya, sannan ta kalli Hajiya Fatee suka taba suna dariya. Daga bisani Hajiya Fatee ta kora masa da nata bayanin.

 Malam nima da tawa mtsalar na zo yau, suruka ce ta saka ni a gaba, ta mallake min an yaki ya kara aure kuma baya jin maganar kowa sai ta matarsa, ga kudi yana da shi amman ko kyauta zai yi sai abun da ta so yake bayarwa, ni so nake a raba su ya sake ta saki uku idan da dama

Malamin ya amsa mata da kai.

 Ya sunanta, ya kuma sunan anki?

 Afrah ake kiranta, shi kuma Fadeel

Ya dauko kasa dake cikin farantin katako ya dora a cinyarsa yayi zane zane ya jinjina kai ya dago ya kalli Hajiya Fatee.

 Lallai sai kin tashi tsaye, ta mallaki danki Mallaka bata wasa ba, kuma idan ba ki yi da gaske ba abu ne mai wahala ya sake yin aure ko da kuwa ta mutu

 Ka ji irinta ba, shedaniyar yarinyar na sha wahalar yarinyar da can babu ruwansa da ni ma, sai da na tashi tsaye, dan abun da ubansa ya bar min duk a can ya kare, ba dan Allah yasa nasa gadon yayi albarka kuma ya samu babban aiki ba da yanzu mun kade

 Toh lallai dai gata nan ko yanzu a tsaye take akan danki

 Dan Allah a zaunar da ita, idan da dama ma a kwantar da ita a saka ta bacci ko a sumar da shegiya

Malamin yayi dariya

 Ai tun da kika zo nan komai zai zama tarihi Hajiya, ki bada kudin karan alkamin kawai a saka aiki

Da sauri ta bude jakarta ta dauko kudin da ba zai wuce 30k ba ta aje masa.

 Ga wannan ban zo da kudi mai yawa ba, amman dai a fara saka aiki da wannan idan zan dawo zan ciko jaka da yardar Allah

 Toh shi ke nan ba matala idan na gama aiki na hada abubuwa zan kira na fada muku sai ku zo ku karba ko kuma ku aiko ko kuma ni da kaina na aiko muku

A bisa wannan suka yi masa sallama suka fito suka dawo cikin motar. Direban ya a kama hanya, ba su yi nisa da garin ba suka rage gudu ganin an tsayar da motocin dake gabansu a zatonsu sojoji ne, hankalinsu be tashi ba sai da suka fara jin harbe harbe wasu na ihu.

 Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un Bandits ne

Direban ya fada, da sauri Hajiya Fatee ta kalli Hajiya Kaltume da cikinta ya soma murdawa.

 Mun shiga uku mun lalace, ya zamu yi?

 Shiyasa bana son shigowa dajin nan gari gaba daya ya lalace a yanzu

Cewar Hajiya Kaltume ido na raina fata.

 Kai direba ya zamu yi?

 Hajiya ni ba ku kuka kawo ni nan ba, kuma gashi motoci a bayanmu balle mu juya

Maganar yake yana leken motocin dake bayansu ga karar bindigar sai matsosu take.

 Toh ko dai mu kira Malamin nan mu fada masa

Hajiya Fatee da fitsari ya fara zubo mata ta kalli Hajiya Kaltume.

 Ya mana me? Soja ne shi ko dan sanda?

 Ya turo aljannu su dauke mu mana, Hajiya mutanen nan suka kama mu ai mun shiga uku, kuma na cewa Alhaji me? Daga zuwa sulhun aure!

Cikin tashin hankali Hajiya Fatee ta ce

 Aljannu suka dauke mu ai shikenan mun bar duniya kuma kara ma wadannan da aljannu dan su kai mu za su inda babu kowa su aje, ko su kai mu China aljanni ai ba zai dauke ka ya aje ka nan kusa ba sai wata duniyar

Hajiya Kaltume ta fashe da kuka tana neman agajin Allah.

 Allah ka yafe mana Allah ka dube mu Allah Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, ni har na bata zane

Direba ya bude kofar a hankali ya sulale ya yanki daji cikin ciyayi. Hajiya Kaltume ta saka kalma shada, Hajiya Fatee ta kama mata suka karasa suka kallon juna kowacce na kai hannu ta taba yar'uwarta. domin sun san yadda suka ci suka koshi nan ba za su iya gudu ba ko sa sun gwada hakan.








____________________


Hmmmmm masu karatu kun taba gani ko jin mugun kishi da bakar hassada irinta ta Hajiya Kaltume?
Ni dai Hurriya ta ba ni tausayi domin rayuwa gurin da baka bukatarka yana da wahala, musamman idan babu uwa a kusa.

Ta wani bangaren kuma Iyami tana da laifi daga zuwa aiki sai ki aure mijin mata? Ina laifi ki rumgume talaucinki ki shafawa kanki lafiya, yanzu wa gari ya waya...?

Mu hadu da ku page din gobe, amman kamin nan ina son na ga Comments baza-baza line by line in ji Bature...
[10/18, 5:35 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: &A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2ܠ? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?


5???5???5???5??? 7??

Ana kiran sallah asuba ta sauko daga kan gadon ta nufi kofar dakinta ta bude ta fito, a hankali ta sauko downstairs, tana isa bakin kofar falon bata tsaya komai ba ta kai hannu zata bude kofar.

 Ina zaki je?

Ta juyo da sauri domin bata yi tsammanin wani zai iya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login