Showing 60001 words to 63000 words out of 279257 words

Chapter 21 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34626

amince su tafi ba dan wannan babban dalili ba ba zai taba yarda dayansu ya sake takawa gidan ba, domin be manta cin mutunci da kuma wulakancin da Appa yayi masa ba. Gwaggo da kanta ta fita makota ta samo direban da zai tukasu a motar Amma domin bata iya tuka mota yanzu ita kuma ba iyawa ta yi ba, haka ma Rukayya balle kuma Hurriya da bata gama girma ba ma. Gwaggo da Amma suka shiga baya, Hurriya ta shiga gaba aka bar Rukayya tsaron gida, ba su isa gidan ba sai da suka biya suka dauko Hindu domin dazun kamin ta bar gidan ta fadawa Amma idan aka dauko Hamad a fada mata.

 Alhamdulillah Allah ya kawo mana su lafiya

Shi ne abun da Gwaggo da Hindu ke Fada, direban da ya dauko su kuma yana kara basu labarin yadda aka sace wani shi ma suka karbi kudi mai yawa.

 Kasar ce ta lalace Allah ka kawo mana sauki

Amma ta amsa addu'ar da Hindu ta yi da Ameen daman bata cewa komai sai murmushi take tana ta daukin arba da anta. Sai da ta isa gidan sai kuma ta soma tambayar kanta me yasa ta zo? Wani bakinciki ya rufeta ta kasa shiga bangarenta da babu komai ta tsaya, kuma ta ki yarda ta shiga bangaren Hajiya Kaltume daga ita har Gwaggo a babbar harabar gidan da direba ya faka motarsa a nan suka tsaya suna jiran isowar su Hamad.



**** **** ****

 Iyami kuma?

Namra ta daga kai.

 Me ta zo yi?

 Tarbon su Hamad mana Momy, kin manta yau za su dawo? Ya Yasir ma sun tafi gurin dauko su

 Au haka ne fa, kin san badan da babu ruwanka dadin kallo gareshi, ni na manta ma

 Toh ina take

 Tana can babbar haraba tsaye ita da wadanda suka zo har da Gwaggo da Hurriya

Momy ta dan yi jimm kamin ta girgiza kai.

 Wallahi har ta bani tausayi, ta yi going though alot shekarar nan, ga ciki ga saki ga sace a, da dai Appanku zai tausaya mata ya dawo da ita, ta rike yayanta ni na huta ma, daman bana son rikon yayan wasu, dan na san yanzu Alhaji zai ce su dawo gidan nan da zarar sun dawo kuwa ba su da gurin zama sai bangarenna.

 Ni tausayi suke ba ni

 To sarkin tausayi je ki ce su shigo cikin falon nan mana su zauna

Namra ta wara ido with surprise.

 Su shigo Momy? Ko bakar mana kike min?

 Toh ya za'ayi, ai da anyi haihu kuma zance ya kare, ba dan tana da yaya a gidan ba ai ba zata zo ba, da zarar an haihu ai kuma shi ke nan sai hakuri, kuma dai an girma kishi na miye ina zan tsaya kishi da karamar yarinya kamar Iyami? Level dina kuma ba zai taba haduwa da nata ba, har abada dukansu na fi karfinsu sai dai ta kara da Kaltume bakar akuya

Namra ta tashi da kuzarinta ta fice daga dakin ta sauri ta sauko downstairs ta bude kofar falon ta fita. Sai da ta fara gaishe su bayan ta isa gurin da suke a lokacin Amma har ta kai zaune a cikin mota domin bata yarda ta zauna ko da a kujerun baki da ake ajewa a gidan ba.

 Amma Momy ta ci ku shigo ciki ku zauna kamin su iso

Amma ta kalli Namra tana murmushi.

 Ki ce mun gode zamu tsaya a nan

 Ai tun da ita tace mu shiga, mu shiga kawai zai fi mana tsayuwa a nan

Hindu na rufe baki, masu gadi suka bude gate motar da aka je dauko su Hamad da ita ta kunno kai cikin gidan, gaba daya sai hankali ya koma can Hajiya Kaltume, Salma, Maama Khairi suka fito daga bangaren Hajiya Kaltume da gudunsu har Hajiyar da jiki ya hana ta walawa yadda take so, Namra ta shiga bangarensu da gudu kiran Momy. Appa ma ya fito da waya a kunne sai dai fuskarsa babu annuri ko kadan, ba irin da wanda ransa ya bace ba, rashin annuri ne irin na wanda ya rasa wani abu fuskarsa ma gaba daya launinta ya canja. Amma ta fito daga cikin motar ta nufi motar da Yasir ya sauko yana hawaye Ruma kuma na rutsar kuka.

 Ina Hamad? Ina Hamad?

Amma ta tambaya domin yaronta ne kadai bata ga ya fito daga cikin motar ba. Aka rasa mai ce mata komai har ta isa gurin ta tsaya tana kallonsu murmushin dake fuskarta na kokarin gushewa.

 Yasir ina Hamad? Dan Allah ku amsa min...!

 Amma sun kashe shi, sun kashe Hamad...!!!!!!

Ruma ta fada da karfi tana kuka. Momy ta dora hannu saman kai tana fadin Innalillahi. Amma kuma ta yi baya baya kamar mai tafiyar baya sai Hindu ta rike ta, runtse ido ta yi ta kai hannunta ta dafa cikinta dake zillo ta durkusa a kasan guiwoyinta ta dafa kasa. Hajiya Kaltume ma kuka take ta nufi yarta ta rika hannunta da niyar rumgume sai Ruma ta buge hannun Hajiya Kaltume ta nufi mahaifinta tana kuka ta rumgume shi yana hawaye, kusan kowa a gurin sai da yayi hawaye.

 Su ba mu gawarsa mana to mu gani, idan da gaske ya mutu su ba mu gawarsa mu gani Wallahi be mutu ba, boye shi suka yi Hamad yana nan da ransa

Hurriya ce take maganar tana kuka, Gwaggo ta rikota ta rumgume tana kuka.


Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?

5??5?(?5?(?5?$? 5??5?0?5?(?

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya kin daukar kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660


5??5??5? ?5?? 5??

Hurriya first lost her sight a jikin Gwaggon, before ta yi going blank aka kwasheta ita da Amma sai Asibiti. Amma aka wuce da ita dakin haihuwa Hurriya kuma aka kaita Emergency. After 49hours of labor Amma ta haihu tagwayenta biyu duka maza. A madadin ta yi murnar ta haihu ta samu yan biyu sai murnar ta koma mata ciki saboda tunanin Hamad bata da wani kuka sai na Hamad. The following day aka sallamo ta daga asibitin bayan sun mata dinki kuma sun dorata akan maganin da zata rika sha na hawan jini sannan suka hana ta wankan ruwan zafi domin jinin nata ya hau sosai irin hawan da ba dan Allah ya kawo sauki ba, da abu ne mai wahala ta fita lafiya.

Har lokacin Hurriya tana asibitin Hajiya Binta na jinyar tare da taimakon Rukayya, kwananta biyu bata san inda kanta yake ba a asibitin, kamin ta farfado sai kuma ta zama so weak sai da ta sha drip da manyan allurar sannan ta samu sauki, the following day ita ma aka sallame ta two days after an sallami Amma. Wani abun da ya bawa kowa mamaki ciki har da Momy kuma ya daurewa Amma da Hajiya Binta kai shi ne, kin lekawar Alhaji Haruna a asibiti ko gida da sunan duba Amma ko kuma duba yaran da ta haifa masa, yan'uwansa na nesa da na kusa duk sun je duba twins din kuma sun je duba Hurriya wasu ma ba su samu labarin abun da ya faru ba sai a da suka je barkar twins. Sai dai Appa be bar rashin zuwa duba yaran da kowa ke musu lale da zuwa duniya, ya hana shi kyautata musu ba, duk wata hidima ta ya kamata uba yayi ma yayansa Appa yayi tun daga kan tufafin mai jego Amma har na jaririnsa, sai dai Amma bata yi taron suna ba, duk kuwa da kasancewar ba ayi taron gaisuwa a gidanta ba, an yi zaman makoki a gidan Appa kuma an masa sallatul ga'if wato sallar da ake yi ma gawar da bata kusa. Ta ko'ina Appa ya karbi gaisuwar mutane ana ta jajanta masa. All those days, hour's Hurriya a daki take rayuwa, domin bata son ganin kowa, idan zata yi alwala sai ta shiga bathroom ta yi idan ta yi sallah ta kwanta, bata son ayi mata gaisuwar Hamad, bata fitowa idan mutane suka tambayi ina take, idan kuma aka shigo sai ta rufe kunnuwanta bata sauraren kowa, she's the only one da ta kasa yardar Hamad ya mutu, ranar sunan yaran ma sai da ta saka kowa kuka, domin ihu take ta yi me yasa Amma ta sakawa little one din Hamad yayan kuma Hamid.

 Amma da baki saka Hamad din ba, Wallahi Hamad be mutu ba, karya suke yi Amma dan Allah ki cire, ki saka masa wani sunan ba Hamad ba

Tana kuka tana rokon Amma a canjawa jaririn suna, Amma ta aje Little Hamad ta kama Hurriya ta rumgume.

 Hurriya dole mu karbi wannan gaskiyar, tana da daci amman dole ne mu karbi kaddara, duk yadda kike son Hamad na fi ki sonsa domin ni na yi nakudarsa na haife shi, una jin fiye da yadda kike ji

 To me yasa kika sama Amma? Why? Why?

Amma ta girgita da karfi tana kuka.

 Saboda ya mutu Hurriya, baki daya Allah ya karba ya bamu biyu ba? Toh sai mu gode masa, yadda ya so haka yake aikatawa, Hamad ya tafi tafiya ta har abada ya kamata ki karbi wannan, wannan shekarar haka ta zo mana

Hurriya ta saki jikinta sai ta lankwasa ta yi baya Amma ta sake ta ta fadi kasan carpet din. Ita kam ta kasa yarda dan'uwanta ya tafi ya barta, fadan da suke yawan yi yake damunta a yanzu, why take ramawa idan yayi mata abun? Ko wane motsi yana tuna mata da dan'uwanta ne, bata taba sanin tana kaunarsa ba sai a yanzu da baya kusa da ita, ina ma ita aka dauka ba shi ba haka take yawan ayyana a ranta. Kusan kowa a gidan sai da yayi kuka kuma aka kasa wanda zai rarrasheta sai Yayanta Yasir, domin shi kadai ya fahimci manufarta kuma ya mara mata baya cewar Hamad be mutu ba, domin karbar gaskiyar cewar ya mutum shi ne ?arya a zuciyarta.


****?? ****? ?? ****? ? ****

 Hajiya ki yi ha?uri dan Allah, bana son ina musa miki akan abubuwa, amman yaran nan da Iyami ta haifa nawa ne, idan ina bu?atar ganinsu ba sai na jira wani ya ba ni shawara ba, ayukan ne sun min yawa a yanzu amman da zarar na samu lokaci zan je na duba su, idan suka yi ?wari ma aka yayensu Wauko su zan yi na dawo da su gidana domin zuciyata ta fi amintuwa da haka

Hajiya Binta ta kalleshi tana mamakin yadda yake ita bude baki ya musa mata a duk lokacin da ta yi masa maganar zuwa duba Twins din da Amma ta haifa.

 Tsoho me yake damunka? Wani lokaci ne baka da shi akan iyalinka?

 Hajiya kin san kasuwanci ba daya ba, kuma idan ina son ganin yaran nan ni zan je da kai na, ina cw dai na sauke duk wani hakki na uba?

 Toh baka bukatar ganinsu kenan? Haka kake nufi? Toh ni da nake bukatar ganinsu zan tafi, ko miye ya rufe maka ido ka kasa taka kafarka gidan Iyami Allah ya yaye maka shi tsoho, yau sati daya da haifa maka yan biyu kyautar Allah amman ka kasa taka kafarka ka duba yayanka

 A gaishe su, Hajiya zan leko in Shaa Allah, kuma idan kin tafi ki fada mata next week Hurriya zata dawo zan aiko da mota a dauke ta saboda makaranta

Yana maganar yana mikewa tsaye abun da be saba yi ba, ko magana Hajiya Binta take masa baya iya daga kai ya kalleta tsabar biyaya amman a yanzu duk ya canja mata, abun da be yi mata da kurciya ba a yanzu da girma ya kama shi yake canjawa. Baki saki Hajiya Binta ta fi danta da kallo har ya fice sannan ta girgiza kai hawaye na cika idonta.

 Allah ka shirya bawan nan naka, Allah ka karya duk wani abu da aka yi masa Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Ta rafka uban tagumi tana kokarim ganin bata bar hawayenta sun zubo ba, domin ta san illar zubar hawayen uwa ga anta. Appa har ya isa gida bw daina ganin laifin Hajiya ba, ganin yake tana kusa masa cikin al'amurran da be kamata ta saka kanta ba, shi dai aka haifawa yara to damuwa kuma na me tun da har be ce ba yayansa ba ne, kuma yayi musu duk wata hidima da ya dace uba yayi ma ?a?ansa. Ba ta inda ya ji sayin kamar ta gurin da Hajiya Kaltume take taba masa ita ma tana dorawa Hajiya Binta laifi, tana bashi gaskiya na kin son zuwan da yake.

 Gaskiya Hajiya ba a haka, ai sai ta saka maka ido ta gani, ina laifin bayan duk wata hidima, kuma yara idan suka yi wayo ai sai ka dawo da su nan gurin Momy ta cigaba da kula da su, tun da tana da masu aiki ba daya ba za su rika musu komai

 Ni ma haka na gani, amman ta kasa fahimtata sai laifina take gani, gaba daya ta rufe ni da fada

 Toh ya ka ayi, sai hakuri ka san bata hada Iyami da kowa ba a gidan nan, duk dai abun da yayi dalili ya raba amman dai Hajiya bata dauki kowa sukarta ba sai Iyami, wai ni yaushe Hurriya zata dawo ne Alhaji

Tana maganar ya aje kofin ruwan dake hannunsa ya amsa mata.

 Next week, na fadawa Hajiya idan ta je ta fadawa Iyami zan aiko da mota a daukota saboda makaranta

Hajiya Kaltume ta dan tabe baki tana shafa zanen atamfar dake jikinta.

 Makaranta ma ai bata jira Alhaji, yanzu kan sai dai a canja mata makaranta a maida ita Government School, ko ba komai ta dan rage kewar Hamad dan na san abun zai yi da damunta, amman idan ta koma wata makarantar sai ta samu sabin kawaye kewar zata dan ragu, kuma ka ga yanzu private school ai duk an yi nisa da karatu sai dai ta Gwafnati ita ce za su karbe ta ko dan lalurarta

Appa yayi shiru kamar mai nazari, idea Hajiya Kaltume na cewa a saka ta wata makarantar ta government be masa ba, sai dai ba zai iya nuna mata haka ba.

 Ko kuma a kaita wata makaranta, amman makaranta government bata cika kyau ba, bayan kuma ga duka yan'uwanta a private suke, kuma kudin biya makaranta ai akwai shi ba babu ba

 Ba shi zaka duba ba, yadda Hurriya take da kokari a makaranta ko'ina zata iya karantu, kuma zata gane kamar sauran yan'uwanta daman kuma ta fi su basira, ni dai gaskiya shawarar da nake baka Alhaji a kaita government schools kuma bana son ka musa min akan haka, kai fa ka san Hurriya kamar ?a take a gurina, yadda ba zan so abun da zai cutar da Ruma ko Khairi ba ita ma ba zan so abun da zai cutar da ita ba

 Shi ke nan, tun da haka kike so, za'ayi, Allah ya tabbatar mana da alheri

Fuskar Hajiya Kaltume ta fadada da murmushi.

 Amin Alhaji na, Allah dai ya kara rufa asiri, ya kara wadata

 Ameen

Ya amsa cikin rashin dadin rai da be isa ya nuna a fili ba. Abun ku da makirar mace haka ta rika jan sa da hira tana tabo bangagori da dama na kasuwanci, sai dai be yarda ya fada mata abubuwan da take son sani ba, sai dai ta fahimci wasu bangarorin da kuma har ta nuna masa sha'awar na son fara kasuwanci. Appa ya saka dariya.

 Kaltume ina zaki iya kasuwanci crude oil? Kina mace? Wannan kuma ai sai mu maza

 Hmmm Alhaji ka manta karin maganar da hausawa suke cewa duk abun da namiji zai iya mace ma zata iya? Ai mata ma kansu ya waye yanzu ana damawa da su sosai akan crude oil a yanzu

 Amman yan boko Kaltume ke da ko primary ba ki yi ba ina ke ina wannan kasuwanci? Da ma dai Nafisa ce tace zata yi ba zan musa mata ba, domin ita tana kasuwanci sosai ta san kan kasuwanci domin shi ta karanta kuma mahaifinta ma kin san waye shi ba sai na fada miki ba, amman ke Kaltume ina ke ina wannan kasuwanci?

A take fuskarta ta canja domin ya tabo mata inda bata so, dauko

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login