Showing 6001 words to 9000 words out of 279257 words

Chapter 3 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34644

bakin kofar tana kallon kanenta Hamad dake ta fadawa Amma abun da ta yi masa a makaranta.

 Amma karya yake, karfe 1:30pm aka tashe mu shi ne na ce nasa yaje yayi sallah saboda bus din mu sai 2pm take zuwa ai, shi ne ya taso min fa masi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fa har zai yi dambe da ni gaban yan makaranta har da yan ajinsu fa

Hamad ya juyo ya kalleta a fusace.

 Toh ina ruwanki da ni da zaki ce na tashi na yi sallah, kafiri ne ni ko bana sallah aka ce miki? Salon friends dina su fara tsokana ta suna cewa bana son sallah

 Na ji ba zan sake maka magana ba, amman ni ma karka sake zuwa class dinmu ka ce na ara maka wani abu, ba ruwana da kai karka sake taba min komai kuma safata da ka saka yau ban yafe ba karka sake min taba min komai

Amma ta mike tsaye tana kallonsu kowane zuciyarsa ta kawo kamar abokan gaba.

 Wannan fadan duk na minene wai? Ku kullum baku zaman lafiya? Kai kake binta amman kai da ita babu zaman lafiya, abinci ma ba zaku ci a plate daya ba, magana mai dadi babu tsakaninku kullum sai fada?

Hamad ya ce.

 Ita ce bata ba ni respect ai

 How? Kai ne babba or ni? Ni ce babba ai kai ya kamata ka ba ni respect

 Ni ba zan taba baki respect ba i hate you kuma kika sake min wata maganar banza sai na ballaki

Hamad na kaiwa nan ya juya ya fice rike da jakarsa har yana bankade Hurriya.

 Amma kin ga ko? Imagine

Amma ta dafe kanta ta zauna bakin gadon tana fashewa da kuka.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

A take jikin Hurriya yayi sanyi ta bar jikin kofar ta karasa inda Amma take ta zauna kusa da ita, domin suna yawan samun tsabani da Hamad saboda rashin jituwa dake tsakaninsu su yi fada wani lokacin har dambe suke, Amman Ammansu bata taba kuka ta zubar da hawaye ba akan haka ba sai yau.
[10/18, 5:34 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: https://chat.whatsapp.com/LimnMeG0kWvIfT6JQvVMh1


&A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2ܠ? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?


5???5???5???5??? 3??

 Amma I'm sorry laifin fa duk na Hamad ne shi ba a masa magana ya ji

Amma ta dago da idanuwanta da suka kumbura ta kalleta.

 Ke ai kina ji? Kuma ke ce yayarsa ki daina biye masa mana, ki zauna lafiya da dan'uwanki dan Allah, kullum ina fada muku haka amman baku ji, Hurriya ki daina biye masa kina kallon ba sonku ake a gidan nan ba, a madadin ku so kanku kullum sai rigima da junanku

Amma na magana Hurriya na yawo da idonta akan akwatunan da suke tsaye gefen kofar dakin da bata lura da su ba sai a yanzu.

 Amma kayan miye a akwaitinki?

 Tafiya zan yi

Hurriya ta dubeta da sauri tana kallonta da ya kumbura sosai.

 Amma ina zaki je?

 Gida zan koma gurin Gwaggo

 Saboda me?

Amma ta yi murmushi hawaye na sauko mata.

 Hurriya abincina ya kare a gidan mahaifinku

 Kamar Yaya? Toh ba sai ya kawo wani ba? Amma me ya faru kika yi kuka? Me yasa zaki tafi?

Amma ta rufe ido ta dantse baki.

 Je ki kira Hamad

Hurriya da bata gama fahimtar abun da yake faruwa ba idonta ya cika da hawaye har ya zubo ta kasan gilashin da shi ne rayuwarta. Ta mike tsaye ta fice daga dakin kamin ta isa dakin Hamad ta cire hijabin dake jikinta ta rike a hannu tana tafe tana hawaye har ta isa bakin kofar dakin. Murda kofar dakin ta yi ta tura ta shiga, Hamad dake sanye da short yana kokarin cire safar kafarsa ya kalleta.

 What? Amma ta miki fada ko? That's good next time sai ki sake shiga min hanci

Ya fada azatonsa Amma ta yi mata fada ne sosai, daman haka take sometime idan aka yi mata fada kuka take.

 Ba saboda haka ba ne, Amma ta ce na kira ka kuma kuka take yi, ban san abun da aka yi mata ba

Be tsaya ya karasa cire safar daya ba ya sauko da kafar ya biyo bayan Hurriya da tuni ta juya bayan ta isar masa da sakon Amma. Hamad na shiga dakin ya karasa inda take zaune ya zauna bakin gadon babu abun da zuciyarsa take nuna masa sai fadan da suka yi da Hurriya.

 Amma saboda Hurriya ne ko?

Amma ta share hawayenta ta kalleshi, sannan ta kalli Hurriya ta mika mata hannu. Hurriya dake tsaye jikin kofar dakin ta karaso da sauri hawaye na sauko mata ta kasan gilashin dake idonta. Amma ta kama Hamad ta dauki hannu Hurriya ta dora a saman hannun na Hamad.

 Dan Allah ku zauna lafiya, ku so junanku ku kaunaci junanku, kai baka da wata yar'uwa da ta fi Hurriya, Hurriya ke ma baki da wani dan'uwa da ya fi Hamad, wannan yawan fadan da kuke yi ku daina anyi ance da rashin bawa juna girma duk ku aje shi a gafe, musamman ma kai Hamad idan baka canja wannan hallayar ba zaka sha wahala a gidan nan kana kallon yadda kake rayuwa ma yanzu balle kuma idan bana nan

 Amma ina zaki je?

Hurriya ta tambaya daman ta kagu ta ji domin hankalinta yayi matukar tashi akan hawayen da ta gani a idon mahaifiyarta ga kuma tufafinta a shirye. Amma ta kalli Hurriya sai ta rasa ta ina zata fara amsa mata tambayarta, at her age it's too early ta fada mata sakinta mahaifinsu ya yi, ita kanta kalmar tana mata nauyin furtawa a yanzu balle kuma yadda ?a?anta za su ji idan ya sauka a kunnesu har su fahimta.

 Gida zan tafi gurin Gwaggo ba na fada miki ba? Sai na haihu zan dawo, za'a rika kai ku kuna duba ni

 Me yasa ba zaki haihu a nan ba? Kuma kike kuka?

Hamad ya tambaya ya tambaya yana kallon cikin idonta kamar mai kokarin kure karyarta. Amma ta yi murmushi ta share hawayenta.

 Saboda bana jindadi a yanzu, bayan kun fita rashin lafiya ta taso min, kuma ina yawan yin haka a duk lokacin da kuka tafi makaranta, kuma kin fi kowa sanin bana son mai aiki na fi sha'awar na yi komai da kaina, ni da mahaifinku muka yanke shawarar zan koma gida na zauna har sai na haihu na samu lafiya, shiyasa ban tafi ba na jiran har sai kun dawo na sanar da ku, kuma na ja muku kunne dan Allah ku zauna lafiya

Kalaman da Amma ta yi a yanzu sun sanyaya zuciyar Hurriya har ta samu kuzarin cire gilashin idonta ta goge hawayenta ta maida abokin rayuwarta.

 Allah ya baki lafiya Amma, zamu rika zuwa kullum

 Ba kullum ba dai sai a lokutan da mahaifinku ya zaba, kuma ku masa biyayya dan Allah ku zauna lafiya da kowa, ke dai na san baki da rigima Hamad ne mai matsala

Hamad dai be sake cewa komai ba sai kallon mahaifiyarsa yake zuciyarsa na raya masa wani abun na dabam.

 Ku rike karatunku, boko da Islamiya karku saka wasa

 In Shaa Allah Amma zamu zama yara masu kirki

Hurriya ta fada da murmushi a fuskarta. Hamad kam kallonta kawai yake kamar wadda aka cewa mutuwa zata yi anjima.

 Je ka saka tufafinka ku rika min kayan na kai mota

Ya mike tsaye ya fice daga dakin cikin wani yanayi kamar ba shi ba, yadda ya natsu a lokaci daya wani tunani ya zo masa sai ka dauka wani babban saurayi ne.

 Amma wa zai rika ba mu abinci?

 Haka ne na manta ma yau ban girka muku komai ba, sai da ku sarrafa wani abun ku ci, ko kuma ku sha tea, idan mahaifinku ya dawo zai fada muku gurin da zaku karbi abinci, gurin Momy ko Hajiya Kaltume shi zaku tambaya

 Toh Amma Allah ya dawo mana dake lafiya

 Ameen

Ta amsa tana danne abun da take ji a zuciyarta, sannan ta mike tsaye ta dauki hijabinta ta saka ta fara fitar da kayan Hurriya na taya ta kamin Hamad ya fito shi ma ya saka hannu suka dauka suka kai mata gurin mota. Ta saka wasu a bayan mota wasu kuma a back seat sannan ta shafa kan ?a?anta tana murmushi Hurriya ma murmushin take Hamad kuma ya hade rai kamar wadda aka yi ma laifi.

 Allah ya muku albarka ya tsare ku, kuma na fada muku zan kara jaddada muku ban da fada ku daina fada dan Allah

A nan din ma Hurriya ce ta amsa Hamad kuma yayi kamar be ji ba, shi dai sai kallon mahaifiyarsa yake fuska babu annuri.

 Toh Amma

Amma ta kalli Hamad tana jin wani yanayi na rashin jindadi.

 Hamad ba zaka ce komai ba?

Juyawa kawai yayi ya shige cikin falon ba tare da ya ce mata komai ba. Sai ta lumshe ido hawaye suka sauko mata.

 Hurriya shiga ciki idan ina ganinku ba zan iya tafiya ba

Ta fada still idonta na rufe, babu abun da take a zuciyarta sai ambaton Allah.

 Amma ko mu rakaki mu dawo

Ta bude idon da sauri.

 Aa zan tafi da kaina ku kula da kanku

 Toh Amma Allah ya baki lafiya ya dawo dake lafiya

 Ameen

Ta bude motar ta shiga tana share hawayenta. Hurriya ta daga mata hannu tana murmushi a tunaninta Amma na kewar rabuwa da su ne shiyasa take kuka, a kurciya da rawarkai irin nata bata damu sosai da tafiyar da Amma zata yi ba a yanzu, domin a ganinta gidan Gwaggo da gidan Appanta duk daya ne kara ma gidan Gwaggo tana musu gata tana barinsu su yi duk abun da suke so, ba kamar nan ba da wani abun Hajiya Kaltume ko Momy zata hana, wani abun kuma Amma ce da kanta zata hana. Juyawa ta yi ta koma cikin falon tana rufe kofar ta nufi dakinta ta cire uniform dinta ta dauki na islamiyarsu ta saka sannan ta sauko ta shiga Kitchen ta dauko cornflakes ta jika a two cups daya nata dayan kuma na Hamad, sai dai wanda yake na Hamad ya fi yawa domin shi baya wasa da cikinsa komai sai ya ci ya ji baya iya tashi yake bari, ita kuwa abinci be dame ta ba, bar ta ma ga kayan kwalama, ko abu mai ruwa dangin tuwo da shimkafa ba babinta ba ne shiyasa kullum gata nan kamar wadda ake diba ana miyar gidan. Jiki na rawa ta dauki cup din Hamad ta nufi dakinsa ta shiga sai ta same shi kwance ruf da ciki yana kuka.

 Hamad ga cornflakes na jika maka, ka ci mu tafi Islamiya...

Yana jin sautin muryarta sai yayi tsif numfashi ma a hankali yake fitarwa dan kar ta ji.

 Hamad kuka kake yi?

 Ina ruwanki bana shan ki dauke abunki ki fice daga dakina

 Na maka kirki ne fa, Amma ta ce mu zauna lafiya amman baka ji ba, miye laifina dan na kawo maka abu

 Ba zan sha ba bana so

 Kar Allah yasa ka sha din, wanda baya jin maganar Mamanshi ya ji haushi ai, ko Sallah be yi ba kalleshi

Sai a lokacin ya dago daga saman gadon ya sauko fuskarsa shabe-shabe da hawaye ya yi kanta, sanin dukanta zai yi ya saka ta saki kofin cornflakes din ta kama shi da kokawa daman sun saba, abu kadan idan ta yi masa sai ya ce zai daketa saboda ya fita girma jiki da karfi, idan ma ba wanda ya sani ba zai dauka ita ce kanwar shi ne yayan. Suna fara kokawa ya buga kanta ga kofar dakin sai kawai ta saka kuka ya fisge glashin idonta ya jefar a kasa ya saka kafarsa ya taka haka be masa ba sai da ya dauko talkaminsa ya saka ya bubbuga glass din ya fasa shi, domin zuciyarsa ta kawo idan kuma yayi fushi sai ya ji kamar ya tashi gidan, gashi baya tsoron kowa har Appa, idan za a masa dukan mutuwa sai yayi magana, sai dai yana da wata dabi'a na baya shiga safgar kowa sai idan an shiga ta shi.

 Wayyo Allah na...

Hurriya ta fada tana kuka tana lalaba kofar fita dakin, domin ta daina ganin komai da kyau a yanzu sai dishe dishe saboda Hamad ya cire gilashin idon dake bata damar banbance fari da baki. Ta bude kofar ta fita tana lalaben hanya irin yadda makafi suke yi tana kuka har ta sauka kasa, da lalaben ta isa kofar falon ta bude ta fita tana kuka, dishe-dishe ta fita daga part din ta shiga part din Hajiya Kaltume har lokacin kuka take kuma ta san by that time Appanta baya gidan balle ta kai masa karar Hamad, idan kuma Appa baya gidan Yassar ne mai yi ma Hamad hukunci yadda take so, wani lokacin ko Appanta ta fadawa cewa yake ta fadawa Yayanta.

Da kuka ta nufi bangaren Hajiya Kaltume ta isa har bakin kofar falon ta tura ta shiga. Hannu ta kai tana kokarin lalabawa ta ji waye a tsaye jikin kofar, sai ta ji an sauke mata lafiyayyen mari a fuska. Tsaye ta yi cak kamar wanda aka daukewa wuta tana kallon kasa, ta san kowa zai iya marinta a bangaren Momy ko Hajiya Kaltume, saboda suna ganin abun da take kamar da gangan take yi, shiyasa dole kawai ke kawo ta bangaren Hajiya, bangaren Momy kuma ko shiga bata yi idan ta shiga sai da wani kwarran dalili, domin Hajiya Kaltume na sake mata fuska irin na munafurci, Momy kam bata sakewa kowa fuska a gidan, har gobe ganin take level dinta ya fi na kowa a gidan, wannan na daga cikin dalilin da ya saka komai nata ko na ?a?anta take banbanta shi da na sauran, komai nata is unique and Expensive, gashi bata son ganin ?a?an Amma da Hajiya ko kusa da akinta, sai dai ita Hajiya tana karbar ?a?an Momy har so take suje a gurinta yanzu da suka girma.

 Haba Musib Haba Musib miye haka?

Musib dake rike da wayarsa a hannu ya kalli Yassar da ya doso inda suke tsaye cikin bacin rai.

 Baka ga abun da ta yi min ba?

 Amman dai ka san idan kana gani ba zata maka haka ba? So take ta gane waye a gurin, me yasa kuke kyarar yarinyar nan ne please? Ku ba ku tausayin halin da take ciki? Ba ku ganin lalura da take tare da ita?

 Tana tare da lalura take yawo babu glass? Ni fa bana daukar wannan iskanci

Ya amsa a fusace sannan ya saka talkaminsa ya fice daga falon, har lokacin Hurriya na tsaye bakin kofar ta kasa yin komai sai hawaye, a nan ta gane wani abun ake iya yi ma magana ko kuka, ta sani sarai tana kuka ko furta wani abun zai iya kara mata ko ya rufeta da duka, domin ba yau ya saba ba. Ko kwakkwaran motsi bata yi ba sai da ta ji ta a jikin Yassar ya rumgune yana bata hakuri sannan ta fashe da kuka.

 Yi hakuri Allah zai saka miki

Hajiya Kaltume dake saukowa rike da plate ta soma fadin.

 Ya saka mata ga wa? Wai Yassar ba zaka daina wannan bakin shisshigin ba? Yadda kake da alaka da ita fa haka yake da alaka da ita, idan ma kwantar da ita yayi ya yanka ina ruwanka?

Dagowa Yassar yayi ya kalleta.

 Haba Hajiya ai ko mai aikin gidan nan wani abu ba zai same ta na yi magana ki ce ina ruwana ba balle kuma Hurriya, marinta fa yayi kamar ya samu babbar mace

Hajiya Kaltume ta yi fuskar tausayi kamar gaske yadda ta tambaya sai ka rantse bata san abun da ya faru ba, bayan kuma tana sama a tsaye stairs tana magana da Umm Khairi lokacin da Hurriya ta shigo.

 Ayya ah gaskiya be kyauta ba, me ta yi masa?

 So take ta tantance waye a gurin kawai ya sauke mata mari

 Oh Subhanallahi, Sannu Hurriya ina glass din naki?

Cikin wani irin kuka mai tsarke numfashi Hurriya ta soma magana.

 Hamad.... Hamad... Hamad.. Ya fasa.. Shi..

 Saboda me? Kai Hamad akwai mugun hali ita Iyami tana aikin me yayi miki haka?

Line by line ta fada musu abun da ya faru tun a school har dawowarsu gida, ciki har da tafiyar Amma da hudubar da ta yi musu. Ciki wani yanayi na damuwa da rashin fahimta da kuma faduwar gaba a lokaci daya Yassar ya kalli Hajiya Kaltume, Hajiya Kaltume kuma ta juya ta kalli ?arta Umm Khairi, suna haWa ido fuskarsu ta soma fadada da murmushi, tunawa da Yassar na dakin ya saka Umm Khairi ta fara tarin karya, Hajiya Kaltume kuma ta daure fuska.
Yassar da ya tattara hankalinsa gaba daya gurin kanwarsa Hurriya ya ce

 Kamar ya sai ta haihu zata dawo?

 Haka tace mana, kuma bata jima da tafiya ba, har ya fara min duka, Wallahi kashe ni zai yi idan muka zauna a can mu kadai

Ya kalli Hajiyarsa cikin yanayin damuwa sai ta girgiza masa kai alamar bata san komai ba, hannun Hurriya ya rika.

 Zo muje part din na ku

Har lokacin kuka Hurriya take tana biye da yayanta dake rike da hannunta suka fice. Umm Khairi ta sauko da sauri tana murmushi ta dafa Hajiya Kaltume da ta kai zaune baki har kunne tana mamakin jin kalaman Hurriya.

 Hajiya Appa ya saki Amma kenan?

 Ina kyautata zaton haka, domin dazun da safe shi ya kira ni da kansa ya ce min na dauke Bedsheets dinta na kawo masa abun karyawa, har na ce masa bana son ta ga kamar ina shigar mata hakki, sai ya ce min baya son digon zance zan karbi girki a yau

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login