Showing 111001 words to 114000 words out of 279257 words

Chapter 38 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34717

zata yarda ta bar gidan, da bata da ni ya rayuwa zata zame mata? Ke kuma ya kamata ace kuna nunawa iyayenku wasu abubuwa be kamata su yi ba, wani abun ba za su lura ba sai an lurar da su

Hurriya dai kanta na kasa tana jin kamar ta rufe bakin Hajiya Binta. A kokarin Namra na kawar da maganar ta kalli Hurriya tana jin wani abu a zuciyarta game da Hurriya ta ce.

 Da bako nake fa, kuma ke yake jira magana ya zo yi da ke?

Hurriya ta dago ta kalleta. Hajiya kuma ta tambaya.

 Wane bako kuma?

 Ita tasan wa nake nufi, ya zo ne yayi magana da ita sai mu tafi

 Waye ne ban san waye ba?

 Salim Sarauta... Yana waje

Namra ta amsawa Hurriya kai tsaye kamar yadda ta bukata. Hajiya Binta kuma ta kalli Hurriya ta ce.

 Saurayinki ne?

 Aa Saurayin Yaya Namra ne, yana yawan tambaya ne, maybe ko yana son mu gaisa ne

 To tashi ki tafi, idan kun gaisa sai ki dawo

 Toh

Ta amsa umarni, Hajiya ta tashi ta shiga dakin ta dauko hijabinta ta saka sannan ta fito ta fice daga falon. Tana fita Hajiya Binta ta fara karantawa Namra sakon da zata bawa Momy da Hajiya Kaltume. Cikin natsuwa Hurriya ta fita harabar gidan, sai da ta gama kallon ko'ina sannan ta nufo gate domin bata ga bakuwar mota a gidan ba bayan motocin da Appa ya ajewa Hajiyarsa guda biyu. Sai da ta fita gate din gaba daya sannan ta yi arba da motar dake fake gefen gate din gidan, tun kamin ta fito zuciyarta ta raya mata a waje ya aje motar ganin babu bakuwar mota a harabar gidan Hajiya Binta. Kamin ta karaso ya bude motar ya fito yana taba wayar hannunsa, da alama wani abun yake typing amman idonsa yana kanta har ta iso, cikin far'a da sakin fuska ta yi masa sallama da muryarsa mai dadin sauraro.

 Wa'alaikissalam Young Lady

 Sannu da zuwa barka da dare

 Barka dai, fatar na same ki lafiya

 Lafiya Kalau

 Maa Shaa Allah

Ya fada yana raba ido, ko za su samu gurin da za su zauna.

 Ko zamu iya rabawa daga can kar na aje ki yi ta tsayuwa, saboda ina da tarin maganganu buhu buhu

 Allah yasa ba laifi na yi ba, Yaya Namra tace min zamu gaisa ne

 Laifi kika babba kuwa, kusa kisan kai ma

Ta zaro ido hankalinta ya fara tashi.

 Ni...

 Ke fa, amman yanzu mu fara zama tukuna

 Nan ma ya isa ka fada min laifina ni hankalina har ya tashi

Yadda take da kin sakin jiki zuciyarsa ta raya masa idan ya bukaci su shiga motar su zauna ba zata yarda ba, ba kuma zai iya forcing dinta suje cikin gidan su zauna ba. Dan haka ya bude mata mota ta gefen da yake ya matsa baya.

 Zauna nan, ni sai na tsaya zan yi magana da ke ne

Bata son ta musa masa a karo na uku, haka kuma sanin cewar shi din masoyin Namra ne yasa bata son ta aikata abun da zai fusata yar'uwarta. Juyawa ta yi ta kalli gate din gidan. Kamar ya san abun da take sakawa a ranta kamin ta juyo ta tsinkaye shi yana fadar.

 Karki damu, babu wanda zai fito har sai mun gama maganar da zamu yi

 Ni fa zan iya tsayuwa ko na awa nawa ne

 Shiyasa Namra ta kasa shawo min kanki, da alama dai kina da kafiya Hurriya kamar zan sha wahala, please ki zauna zaki fi fahimtar magana ta idan kina zauna

Ta taka ta zauna cikin motar kafafuwanta da fuskarta duka suna waje suna fuskar gurin da Salim yake tsaye. Wayar dake hannunsa ya duba sai ya amsa kira da sauri.

 Ka iso?

Ya juya bayansa.

 Oh na ganka

Ya fada tana daga hannu ya tare fuskarsa daga haske motar dake haske fuskarsa. Sauke wayar yayi ya saka aljihunsa.

 Ina zuwa Young Lady bari na mikawa wani, sako

Ya zagaya da sauri dayan side din, hakan ya bawa motar mai tsananin haske haske fuskar Hurriya har sai da ta saka hannu ta tare idonta da ba lafiyayyen ba. Gammm ta ji an rufe mota sai dai ba zata iya fadar motar da aka rufe ba, ta Salim ce dake neman sako kamar yadda ya fada mata ko kuma ta wanda za a bawa sakon ne? Ganin Hasken dake hasketa ya dauke yasa ta janye hannunta daga idonta sai ta yi arba da mutum tsaye a gabanta nesa kadan da gurin da Salim ya tsaya a dazun, kasansa ta fara kallo har ta daga kanta sama ta kalli fuskarsa, akwai hasken wutar gidan dake haska ko'ina ta bawa kowa damar ganin abun da yake wakana a harabar, sai dai hasken be kai ya tantance mata fuskar waye tsaye a gabanta ba, saboda lafiyar idonta, sai dai tabbas zata iya shaidar wani abu da ba zata kira da shi tsoro ba, kuma ba fargaba ba ce, wani abu ne da ya cika idonta ya aikawa zuciyarta da sako ta fara bugawa da karfi, a rashin zato da tsammani ta samu kanta a tsaye gabansa numfashinta na kokarin sarkewa.

 Me kike yi a nan?

Muryarta ta daki dodon kunnensa, a nan ta gane duk wani abu da ta ji gabanin fitar sautin muryarsa shimfida ce.

 Ka santa ne?

Salim ya tambaya yana rufe motar ta dayan bagaren sannan ya zagoyo.

 Ba nan ne gidansu ba, me take yi a nan?

Ta daga kai da zimmar tantance waye tsaye a gabanta jin furta cewar ba nan ne gidansu ba, wannan abun dai irin na dazun ya sake tare idonta daga kallon fuskarsa idanuwanta suka shammaceta ta sauke su a fadaddan kirjinsa mai matukar fadi da yalwatacce damtse, cikin wani yanayi da yafi kama da sihiri jikinta ya fara kyarma kadan ta kasa tsayar da idanuwanta guri daya.

 Ba magana nake miki ba?

Muryarsa bata yi kama da muryar da ta taba ji ba, idan ma ta taba to ta manta, balle kuma fuskarsa da kwarjinsa be bari ta kalleta da kyau ba balle ta tantance waye shi.

 Ni na sallamota magana zan yi da ita

Salim ya fada yana kallon Saurayin dake gabansa da ba zai wuce sa'ansa ba.

 I said ba nan ne gidansu ba

 Eh amman ta dawo nan a yadda na ji Namra ta fada?

Mutumen ya kalleshi da kamar mamaki.

 Namra?

 Ita ma ka santa kenan?

 Cousin dita ce

 Wow baka taba fada min ba

 Dole ne sai na fada maka alakata da kowa? Ina tarkadun?

 Shikenan kuma ka dawo ba zama lafiya, sai bakar magana kamar dan kishiya, ga su

Ya mika masa takardun dake hannunsa.

 Tun da ka dawo ba mu samu zama ba, gashi ni kuma an min transfer

Be ce da shi komai ba har ya gama duba takardun sannan ya juya. Salim ya bishi da kallo yana fadin.

 Ajiyarka ta nan Captain, he's living healthy amman...

Ya juyo da karfi ya kalleshi fuska babu annuri.

 Ban tambaye ka wani abu game da haka ba, idan ina bukatar sani wani abu game da haka ni zan tuntuba watch your mouth Ethiopian...

 Akwai maganar da nake son mu yi ne, akwai abun da ya kamata ka sani

 Ba a nan ba

Ya nuna gurin da ya tsansa, sai da ya kalli Hurriya sannan ya dauke idonsa ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Hurriya ta daga hannunta da sauri saboda haske motar da ya dawo yana haska idonta, sai da ya ja motarsa ya bar gurin sannan Hurriya ta sauke hannunta.

 Sorry na bata miki lokaci, wasu takardun ne na bashi na aikin mu

Ita dai bata ce uffan ba sai mamakin inda ya santa take.

 Ashe ya sanki, he's very good friend of mine, yana da kirki sosai sai dai akwai zuciya abu kadan ya bata masa rai, yana gaba da ni a aiki amman dai abokina ne sosai

Ta dauke idonta daga dayan gefen ta kalli kasa.

 Zauna please

Ta girgiza masa kai alamar ba zata zauna ba, ga bakin nata yayi gum kamar an daure mata shi. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya ce.

 Okay, back to our business, Hurriya ina son ki saurare ni da kyau ne, na zo nan ne saboda ina son mu fahimci juna da ke

Ta kalleshi kai tsaye jin kamar yana kokarin kauce hanya.

 Fahimtar da nake nufi shi ne, ki fahimce manufata da abun da yake tafe da ni, na san Namra ta yi magana da ke jiya, and ta fada min cewar baki karbi sakon da na aiko miki ba, sai dai ban dauke shi a komai ba, maybe saboda baki gama sanina ba ne ko kuma saboda ba wasu dokokin gidanku ne

Ya gyara tsayuwarsa yana aika mata da kalamai cikin natsuwa.

 Hurriya ba na zo nan ne saboda na bata miki lokaci ko tarbiya ba, Allah ya san abun da yake zuciyata son gaskiya nake miki babu wasa a ciki... 

 So kuma...

Ta amsa da karfi with confused.

 Eh na fara sonki ne tun a ranar da na fara ganinki, a Sarauta Mall, shiyasa na biyo motar yayarki, kuma na gwada wasa da ku and...

Ta daga masa hannu tana jin kamar kalaman sun mata girma.

 Wait... Yaya Namra fa?

 Ban gane ba?

A cikin rashin fahimta yayi tambayar ba tare da ya amsa mata nata tambayar ba.

 Yayata fa kake so take sonka, why are you here kana fada min magana haka?

 Ni... Aa Wallahi ba Namra nake so ba, ke nake so ke na biyo ba ita ba, kawai na lura da ke baki son magana ne ya saka na raba ta hannunta saboda na samu isowa gareki, ita kanta ta san da wannan ai

Hurriya ta girgiza kai.

 Bata sani ba, ni da ita mun gina fahimtar mu ne akan ita kake so ba ni ba, dan Allah karka saka yar'uwata ta tsane ni, ita ce ta dace da kai ba ni ba, ita ce aka shirya yi ma aure a yanzu ba ni ba, ni ce auta yanzu a gidanmu idan ka cire kane na da baya nan, ina yayyu hudu mata, ban da maza uku ba za a tsallake su ayi min aure ba

Ya matsa kusa da ita da sauri.

 Zan jira Hurriya zan jira har zuwa lokacin da za'ayi miki aure...

 Aa ni wani be ma taba cewa yana so na ba, ni ba aure ko soyayya ne a gabana ba, akwai kalubalen da yawa da yake fuskatata su ya kamata na fara samun mafitarsu ba soyayya ba I'm just 19yrs old

 Yes but you're not a baby, wasu guraren ma wadda bata kai ki ba za a iya mata aure, and zan jira ki Hurriya har zuwa lokacin da kika tashi ko iyayenki suka tashi

 Aa ka rushe duk wani gini na soyayyata da ka yi a zuciyarka, ka gina na yar'uwata don't break her heart, Hurriya babu kowa yanzu a gabanta, bata taba son kowa ba, kuma ba ta shirya son kowa ba, kai ba ma zata taba son kowa ba har abada... Sai an jima

Ta raba gefensa ta wuce ta bar shi a gurin tsaye speechless... Tana isa gate din ta tura ta shiga, a yayinda Namra kuma ta fito falon Hajiya Binta ranta a bace har wani halkalo take, a tsakiyar harabar gidan suka hadu da Hurriya, Hurriya ta tsaya ita ma ta tsaya suka kalli juna, Hurriya ta dan yi murmushi kadan zata yi magana Namra ta tari numfashinta.

 Zaki yi dariya mana, tun da kin zama munafuka munafurcin da kike yi a gidansu Husna har yayi sanadin Appa ya koreki shi kika zo kina yi a nan ko? Kina son hada Hajiya da Momy kuma kina son Hajiya ta yi fushi da Appa, kin kyauta idan halin da kike yi abun kwarai ne ki cigaba, Hajiya ta fada min baki, ja, da yello na sakon da zan fadawa Momy da Hajiya, kuma zan fada musu...

Ta dauke kai ta nufi gate.. Mamaki da fargaba ya hana Hurriya cewa komai sai binta da ta yi da kallo har ta fice. Tsaye Namra ta samu Salim a gurin da Hurriya ta bar shi

 Lafiya?

Ta tambaya ganin yanayin dake nuna kamar ba su rabu da dadi ba. Ya juyo ya kalleta

 Ba komai, zagaya ki shiga mu tafi

Ya shiga side din da Hurriya ta zauna wanda shi ne side din mai tukin mota, Namra kuma ta zagaya ta shiga front seat, tun da suka kama hanya bata ce masa komai ba, shi ma kuma be ce mata ba, be kuma kalli inda take ba gaba daya yanayinsa ya sauya, ta lura da hakan ta hanyar satar kallonsa da take time to time har suka isa. A gurin da ya faka dazun ya sake fakawa ba tare da ya ce da ita komai ba.

 Anya dai lafiya ko wani abun ta yi maka ne?

 Zamu yi waya

Ya fada a takaice, sai ta bude motar ta fita ta rufe kuma ta tsaya a gurin tana kallon motar har yayi reverse ya isa babban gate aka bude masa ya fita. Ita dai mamaki da tunani ya hana ta tsinkayo abun da ya faru, bata amsa masa ba ne ta biyo shi da bakar magana ko kuma dai wani abun ya faru, to amman ai ta ga Hurriya ta shigo normal har tana mata murmushi, ita har tana zaton murmushin jindadi ne. Tana tafiya tana tunani kamin ta waiga, to amman me yasa ta ganshi a wannan yanayin? Idonta ya sauka a wata sabuwar motar da zata iya shaidar ta waye ba. Ta isa kofar dakin ta murda ta tura ta shiga, tana yin arba da Captain dake zaune a cushion hannunsa rike da takardu ta sake fuska ta karasa gurinsa da far'a.

 Captain sannu da zuwa

Ya dago ya dubeta cikin wani yanayi da ba na wasa ba ya nuna ta da yatsa ya ce.

 Idan kika sake kai yaron nan gurin Hurriya sai na ci ubanki....

Namra ta tsaya a gurin kamar hoto ta kalli Momy da ita ma kallonta take tana kuma kallon Captain ta gafen ido.

 Momy zan samu?

Momy ta kalleshi.

 Yanzu na fada maka duk abun da ya faru fa Captain!

Ya kalli Momy ya ce.

 Ko zina take yi be kamata a koreta daga gidan ubanta ba, kuma yanzu kika gama fada min cewar mahaifiyarta bata da lafiya ko magana bata iya yi, to yanzu waye zai kula da ita idan bata gidan nan?

 Gurin da ka ganta hannun kakarta ne mahaifiyart Appanta

 Ba zata iya riketa yadda ya kamata ba, tarbiyarta zata iya tabuwa, dan Allah Momy dan ni ki bawa mahaifinta hakuri ki yi duk yadda zaki iya yarinyar nan ta dawo gidan nan.. 

Namra ta yi katsalanta ta ce.

 Momy ta fada maka abun da ta yi...

Captain ya mike tsaye ya daka mata tsawa, har sai da matsa baya da sauri gabanta na bugawa da karfi.

 One word from your mouth sai na cika miki baki da jini, baki ji kunya ba kina gidan ubanki zaune yar'uwarki jininki tana wani gurin da sunan mahaifinta ya koreta? Baku san darajar jini ba saboda kina da yan'uwa da yawa, ni da aka haifa ni kadai a cikin uwata, kuma ni kadai a gurin ubana na fi ki sanin darajar yan'uwa, dan'uwa da kuka hada uba ko uwa shi ne an'uwa na jini makusanci, the rest are red oil

Ya wuce yana taka kasa da karfi kamar wata giwa, Momy da Namra suka bishi da kallo har ya fice.

 Yaushe ya dawo?

Namra ta tambaya, Momy ta kalleta ta ce.

 Ni ma yanzu ya shigo min, ina kika je? Da waye ya ganki?

Namra ta nufi gurin da ya tashi ta zauna yana yawo da idonta tunani kala kala a ranta.

 Gidan Hajiya na je, amman ni be gan ni ba sai dai idan Hurriya ce ta yi wani munafurci, shiyasa na ga ran Salim ya bace, ita kuma ta shigo tana murmushi... To me ma ya kai shi gurin ina ta san shi, shi ina ya san Salim?

 Ni ba gane wannan shabbatun baki zan yi ba, ki yi min bayani kawai na fahimta

Sai a lokacin Namra ta kalli Momy ta fara fada mata dalilin zuwanta gidan Kakarta Hajiya Binta daga karshe ta rufe da sakon da Hajiya Binta ta bata ta fada musu.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar? MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne? cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai? shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login