Showing 159001 words to 162000 words out of 279257 words

Chapter 54 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34680

fadan ba su san su tashi da asuba su yi sallah ba kullum sai an tashesu. A dolenta ta daure ta shiga ciki ta kai hannu ta taba jikinta tana bugawa.

 Umm Salma...

Nan ma bata amsa ba bata motsa ba, Hajiya ta juyo sai ta juyo kamar wanda ta sankare. Fuskar mamaki da tsoro Hajiya Kaltume ta yi, ta kama hannunta ta rika sai ta ji yayi sanyi kuma ya saki.

 Salma... 

Ta kirata da karfi, ta kai hannu ta taba zuciyarta, sannan ta zauna ta mirginota, ta kwantar da kanta a kirjinta bata ji zuciyar na bugawa ba, jiki na rawa ta saka hannu a hancinta nan ma dai bata ji numfashinta ba, ta kai hannu biyu ta daga idonta sai ta gansu a kafe babu alamar Salma ta san inda take. Duk wani nauyin jiki da kiba haka ta manta da su ta yi wani tsalle daga bakin gadon zuwa baki kofar dakin.

 Khairy.... Yasir ku zo ku duba yar'uwarku....

Ta fice da gudu kamar zata fadi tsabar tashin hankali har jin take kamar babu zuciya a kirjinta.






Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo...

31
Cikin tsananin tashin hankali aka kwashi Salma zuwa asibitin, duk kuwa da kasancewar alamun tafiyar da babu dawowa ya bayyana a jikinta amman Hajiya Kaltume bata yarda yarta ta mutu ba sai da likitoci suka tabbatar da haka. Tun a asibitin Hajiya Kaltume take kirewa tana faduwa ta tashi tana kuka irin na tashin hankalin da ba a saka masa rana, Appa ma duk juriyarsa sai da ya zubar da hawaye a cikin asibitin, dominta abun tausayi ne, yarinyar data kare makaranta few weeks ta dawo gida cikin aminci da koshin lafiya, babu ciwo babu komai an wayi gari babu ita a yau.
Hauka ne kawai Hajiya Kaltume bata yi ba a lokacin da aka iso da gawar yarta gida, Khairy ma idonta har ya canja kala, Ruma ma da kuka ta baro makaranta ta dawo gida, Namra da Hurriya ma duk sai da suka zubar da hawaye na tashin hankali da mamakin mutuwarta, abun ya taba kowa balle kuma Yasir da ya dauke ya kaita asibiti.

Da azahar aka yi mata sallah, a lokacin gidan na cike da jama'a domin wannan ne karo na biyu da Appa yayi rashi mai girma bayan na Hamad. Hankalin Hurriya ya tashi sosai a lokacin da ta yi arba da gawar Salma da aka daga aka saka a mota, kuma aka ja motar aka fita da ita wasu jama'ar na yi mata rakiya a cikin har da mahaifinta da dan'uwanta da kuma wasu daga cikin familynta na kusa da na nesa, ta tabbatar a yanzu Salma ta yi bankwana da kowa kenan har abada, lallai mutuwa akwai tashin hankali da bakinciki da kuma ban tsoro. Ana tafiya da ita sai ta dawo daki ta zauna gaba daya tsoro ya kamata kusan wannan ne karo na farko da ta yi arba da gawa ganin idonta. Ganin da ta yi mata jiya da dare a lokacin da ta shiga ta yi magana da Yasir kawai take tunawa. Misalin karfe biyu da mintuna tana dakinta kwance Inna Shatu ta shigo kiranta, sai a lokacin ta taso ta fito duk hayaniyar mutane da take ji na yan'uwan Momy wandanda suke kusa suna zuwa yi ma Appa da Hajiya Kaltume gaisuwa ba saka Hurriya lekowa ta ga ko su waye ba. Tana fara saukowa stairs din ta hango Mama Rukayya sai idonta ya cika da hawaye bata kula da kowa ba sai bayan da ta fada jikin uwar tata tana kuka domin mutuwar ta taba matuka.

 Mama Rukayya kin ji Yaya Salma ta rasu

 Gaisuwarta na zo, kowa baya wuce lokacinsa Hurriya, yanzu tsakaninku da ita sai addu'a

Tana fada tana sharewa Hurriya hawayenta. Sai a lokacin Hurriya ta lura da wasu daga cikin yan'uwan Momy da suke falon, ba kowa ta sani ba amman haka ta bisu daya bayan daya tana gaida su, wasu su amsa mata kai tsaye wasu kuma sai sun gama yanga saboda sun san wacece ita da matsayinta a gurin Momy.

 Ina wuni

Ta fada a lokacin da kai gurin Captain dake zaune kusa da wata matar mai kama da Momy sai dai ita yarinya ce sosai da bata kai ace ta haife shi. Da kai ya amsa yana kallon idonta dake cikin gilashi
Hurriya ta juya gurin Rukayya.

 Mama Rukayya mu tafi daki

 Muje ki rakani gaisuwa tukuna

Rukayya dake fada ta mike tsaye suka jera da Hurriya suka fice daga falon. Sai da suka kusa fita harabar gidan sannan Rukayya ta kama hannun Hurriya ta tsayar da ita daga tafiyar da suke.

 Ni fa ban so zuwa gaisuwar nan ba

 Saboda me?

 Saboda Hajiya Kaltume kin san matar nan ba wani kirki ne da ita ba, zata ma iya cewa dadi muka ji, Yasir ne ya takura sai na zo, na fada masa bana son Hajiya Kaltume ta yi wata magana yace min babu abun da zai faru

 Ba zata yi komai ba, Mama Rukayya baki ga yadda ta yi kuka ba idonta ya kumbura sosai ni tausayi ma take ba ni

 Ke kiji tausayin kanki, ita ma ta dandana yadda muka ji lokacin da Hamad ya rasu, ni da na sani ma wata zan janyo ta rakoni ko ma na saka mask, ina gudun Gwaggo ta sani ne shiyasa na janyo twins na ce mata gidan kawata zan tafi, ba su san da maganar mutuwar ba, da Yasir ya fada min ban fada musu ba, saboda na san Gwaggo zata iya hanani zuwa amman ita ta zo, kuma Yasir ba zai jidadi ba idan ban zo ba, sai na koma na fada musu

Hurriya ta fara waige waige.

 Ina twins din suke?

 Suna can tare da Yasir, suna ganinshi suka bishi, muje ki raka ni na yi gaisuwar na koma

Hurriya ta bita suka taka har bangaren Hajiya Kaltume dake cike da mutane ta ko'ina domin wannan ne karo na farko da aka yi mata mutuwa mai nauyi, yan'uwa har nasa sun zo saboda sun san mai hali take aure kowa binta yake sau da kafa a familynsu. Hurriya bata san Hajiya Binta ta zo ba sai da ta shiga bangaren na Hajiya Kaltume, da sauri Hurriya ta karasa kusa da ita ta zauna tana gaisheta. Hajiya ta amsa da dan murmushi kadan.

 Hurriya tun dazun nake dubawa ban ganki, na ce kina can kin boya ko sarkin tsoron mutane

Hurriya ta share hawayen da suka zubo mata ta ce.

 Hajiya Salma ta tafi

 To ya aka iya, sai hakuri haka rayuwarma zata kare, shiyasa ake son mutum ya ji tsoron Allah ya bawa kansa lafiya, duniya ba gurin zama ba

Yan'uwan Appa dake kusa da ita suka amsa da cewar haka ne, suna dorawa da nasu sannan suka yi ma Hurriya ya hakuri ta amsa tana kuka kai kace Salma wani kaunarta take. Rukkayya ma ta gaishe da Hajiya Binta sannan suka haura sama tare da Hurriya suka shiga har cikin dakin Hajiya Kaltume, zaune suka sameta kan karamin Carpet Khairy na kwance a cinyarta, kallo daya zaka yi mata ka san mutuwar nan ta taba ba, ba karamin tabawa ba, domin ta fada a take ga ido ya kumbura kamar ya silala, har bata iya daga ta duba mutane da kyau, Khairy ma nata idon ba baya ba domin ta sha kukan da bata taba yi ba, Maama na zaune kan gadon Hajiya Kaltume ita ma kana ganin nata idon zaka san an yi rashi a familyn.
Rukayyah ta mika gaisuwa aka rasa mai amsa mata daga Hajiyar har Maama da Khairy, sai wasu yan'uwan Hajiyar ne suka amsa ta fara gaisuwa tana Allah ya jikanta suna amsawa da Ameen. Hajiya Kaltume ta dago wasu hawayen na zubo mata bakincikin rasa yarta na dawo mata farko, ganin Rukayya da ta yi, da yanzu su ne da kuka ba ita ba, amman gashi nan reshe ya juye da mujiya.

 Rukkaya karki sake shigowa gidan nan, munafurci ya kawo ki saboda ki zo ki ga zan yi tun da na rasa yata, kun jidadi ko? Azzaluman mutane, tun da Iyami ta auri Alhaji ba ni da kwanciyar hankali, kum bi kun hanani zaman lafiya, kuma Wallahi babu ke babu dana, ko mata sun kare a duniya Yasir ba zai auri karuwa yar iska irinki ba, kuma Wallahi ke da yayarki sai mugun abun ku ya koma kanku, sai kum ga abun da ba ku so, Allah ya isa

A nan jama'a suka shiga bata hakuri, Hajiya Fatee na fitowa daga bandaki ta dorawa Rukkaya da nata.

 Daman ban da iskanci da tsaurin ido, ke har kin isa ki taso tsugudi dake wai kin zo gaisuwa, wato ke yar iska yar daukar rahoto, to sai kije ki fada musu yadda kika tararda mu, mutuwa dai ta san gidan kowa

Wata yayar Hajiya Kaltume ta shiga yi musu fada tana tsawarta a matsayinta na babbar duk kuwa da bata san me yake faruwa ba amman zata iya auna wasu abubuwan a kalaman da Hajiya Kaltume ta fada cewar ko mata sun kare ba zai auri Rukayya ba, a lokacin ne suka gane cewar ita din kanwar Iyami ce. A fusace Rukkaya ta mike tsaye

 Ni ma zan tabbatar miki da wani abu yau, ko maza sun yi karamci a duniya ba zan auri Yasir ba, amman gida kam idan kika ga na daina shigowa, to babu Hurriya a cikinsa

Tana kawai ta juya, Maama da Khairy suka taso zasu yi kanta, sai da aka rike su. Hurriya ta kasa cewa komai ita dai sai mamakin yadda Hajiya Kaltume take tsanar mahaifiyarta da duk wani abu dake da alaka da mahaifiyarta take, me ye laifin Rukayya dan ta zo gaisuwa, wanda aka yi ma rasuwa da ya kamata ace ya natsu ya koma ga Allah shi ne suke haka, kamar Rukkaya ce ta yi sanadin mutuwarta. Ko da ta fito daga dakin ta sauko kasa har Rukkayya ta fice daga gidan gaba daya. A lokacin da ta fito ta duba ko'ina bata ganta ba sai ta koma bangaren Momy ta shige dakinta tana ta mamakin, ta ya Hajiya zata ce sun jidadi waye yake farinciki da mutuwar wani? Ko da kuwa nesa ne balle na kusa.
Bayan Sallah magariba Yasir ya shigo dakin nata shi ma kana ganinsa zaka san mutuwar ta taba shi, domin ya dan yi rama ga idonsa yayi ja alamar bacin rai da damuwa.

 Yayana

Ya maida kofar dakin ya rufe.

 Hurriya, Rukkaya ta tafi?

 Wani abu ya faru ne? Ta bar twins bata koma da su ba, kuma na kira wayarta bata daga ba sai text ta yi min yanzu wai na aiko da twins ana mata fada a gida

 Ina suke?

 Suna kasa, me ya faru?

Ta yi shiru kamar ba zata fada ba gudun kar ace ta yi munafurci ko gulma.

 Hajiya ta yi mata fada, ta ce wai ta jidadin an yi mata mutuwa ai ta zo daukar rahoto ne, har tana cewa ko ita kadai ta rage ba saka aureta ba, kuma ta daina zuwa gidan nan

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Ta furta da murya can kasa irin mai bayyana damuwa, sannan ya zauna gefeb gadon Hurriya ya dafe goshinsa.

 Ana cikin wannan halin na mutuwa me ya kawo magana irin wannan kuma? Daman sai da tace min bata son Hajiya ta yi mata wani kallo na ce ba za'ayi ba

Ya saka hannunsa aljihu ya ciro wayarsa ya mikawa Hurriya.

 Kira Amma idan Gwaggo ta daga ki ce mata twins za su kwana a gurinki

 Tou

Ta karbi wayar bayan ya cire mata password ta saka number Amma dake haddace a kanta ta kira, Gwaggo na dagawa suka gaisa ta fadawa Gwaggo kannenta za su kwana a gurinta.

 Aa ki zo ki kawo su yanzu

 Gwaggo dan Allah, haba Gwaggo ba su tana kwana a nan ba, zan jidadi idan suka kwana za su rage min kewarku

 Shikenan gobe amman su dawo gida, kuma ki kula da su

 Toh Gwaggo na gode sai da safe

Ta kashe wayar ta mika masa, ya karba ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi kofar dakin ya bude, ita ma ta sauko daga kan gadon ta bi bayansa tana jin farinciki kanenta za su kwana a tare da ita. Ko da suka sauko falon babu kowa sai Momy, yan'uwanta da suka zo gaisuwa sun tafi tun dazun. Hamid Momy na ke yi ma fada wai yana ta yi mata kiriniya a kitchen ya ki ya natsu. Yasir ko kallonsu be yi ba ya fice domin ta shi ta isheshi ga rashin yar'uwa ga damuwar abun da ya ji Hajiya Kaltume ta yi ma Rukayya, ga fadan da Rukkayya ta rubuto masa ana yi mata a gidansu, goma ta hade masa da ashirin.

 Momy ai dole su yi, saboda ba su saba ba, gidansu ko rabin kyau wannan be yi ba, kuma ba a saba ganin kayan dadi ba, sai bude fridge yake yana rufewa kamar wani tsohon bakauye

Cewar Namra dake zaune dinning tana lasa wayarta. Maganar ta soki Hurriya irin tsokar da take jin bata zata iya mata kara ba, domin ita ma bata ti mata ba.

 Can inda suke zaune ba gidan mahaifinsu ba ne, gidan kakarsu ne, nan din dai shi ne gidan mahaifinsu

Hurriya ya rufe na rufe baki, Momy ta matsa ta wanke mata fuska da mari.

 Dan Ubanki Namra ba yayarki ba ce kike fada mata magana any how?

Hurriya ta dafe kuncinta ta fashe da kuka.

 Amman Momy baki ji me take fada ba? Gidan uwata take kushewa

 Karya ta fada? Kuna da irin wannan daular a gidan uwar taku ne? Da yara sun saba da jindadi za su zo suna wannan rashin natsuwar ne? Me kuke da shi a gidan uwar taki?

Cikin kuka Hurriya ta matsa ta rika hannun kanenta zata ja su zuwa sama sai duk suka bata fuska ganin an daki Hurriya har tana kuka, dayan ya ware hannunsa ya daga sama alamar zai daki Momy saboda ta doki Hurriya, Namra na ganin haka ta bar dinning din ta nufo inda suka ta yi masa dudu a baya.

 Marar kunyar yaro, Momy zaka daka

Dayan ta doka kamin ta dauke hannunsa Hamad ya fashe da kuka ya zageta da hannu, shi ma ta rikoshi zata dunduma masa dudu a baya, Hurriya na ganin hakan ta shiga tsakani ta tare shi, sai fadan ya koma tsakaninta da Namra.

 Okay hana ni zaki yi na dake shi? Ko baki ga zagina yayi ba?

 He's just a child, daukar alhaki ne kawai Yaya Namra

 Okay to bari ke na dauki alhakinki na lura ganin kike kamar ni din nan sa'arki ce ko?

Namra ta kama wuyan rigar Hurriya ta shaketa har sai da ta fada baya kan kujera, Hurriya na kokarin kwantar kanta tana kuka saboda karfi ba daya ba
Momy kuma na tsaye ta ki ta raba sai zuga Namra take wai idan ba duka ta yi mata ba zata daina raina ta ba. Hamid da Hamad kuma suka hau kuka suna dukan Namra ta bayanta, dayan ya dauko remote din dake Center table ya jefi Namra da shi.

 Kin ga wadanan berayen babu tarbiya a tare da su sam... ban san me ya saka Yasir ya shigo min da su nan ba

A tsakanin rufe bakin Momy da turo kofar falon da Captain yayi ba a iya shaidar wanda ya riga wani ba, shigowa yayi cikin falon ya bayan ya rufe kofar yana kallon Namra da ta danne Hurriya har a ganinta.

 Me yake faruwa?

 Captain

Momy ta fada, sai Namra ta dago da sauri ta juya ta kalli kofar, hakan ya bawa Hurriya damar silalowa kasa tana tari kamar zata mutu, ba karamin shaka Namra ta yi mata ba, a kokarin ganin ta kece rainin a tsakaninsu ta kusan aikata lahira ba da niya ba. Captain na hango Hurriya ya nufi gurin ya saka hannunsa ya dago kafadunta sai nishi take daker tana tari hawaye na fitowa a idon da bata iya shaidar waye a gabanta saboda babu gilashi a idon nata. Hamid ya dawo gurinsa yana dukansa yana kuka a zatonsa shi ma wani abun zai mata. Captain ya juyo ya kalli Momy.

 Momy kina kallo ana kokarin yin kisan kai?

 Hurriyar ce bata jin magana Captain rashin kunya take yi ma Namra kamar ba yayarta ba, saboda yaran

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login