Showing 99001 words to 102000 words out of 279257 words

Chapter 34 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34682

kai ta bude motar, Hurriya ma ta bude motar zata fita.

 Fita zata yi idan kika fita, ki zauna sai na gama magana da ita

Ya fada da kamar fada yana kallon Khairy da bata fita motar ba, jin haka ya saka ta fasa fitar ta rufe motar, Hurriya kam bata tsaya ba ta fice ta tana ganin Adam ya bude motar ta ranta a na kare ta shige gida da sauri, a fusace ya dawo motar ya rufe Khairy da fada

 Kin ga abun da kike ja ko? Kin dauki tsanata kin sakawa yarinyar har guduna take

 Toh wai kai Adam duk yan matan duniya ka rasa wa zaka so sai Hurriya? Yarinyar da ko jami'a bata fara ba

 Ba ruwanki

Ya bude gurin da yake ajiyar kudi ya dauko rafar dubu daya ya mika mata

 Je ki gyara abun da kika bata ina son yarinyar nan ta so ni

Khairy ta kalli kudin ta kalleshi, kamar ta yi magana sai kuma ta saka hannu ta karba ta bude motar ta fita.

 Why Adam why...

Ta fada cikin yanayin damuwa da gajiyawa tana tafiya ba tare da ta juyo ba. _____________________

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5??


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


5??5??5? ?5?? 1?? 6?

Sai da Hurriya ta shigo gidan sannan ta daina gudu, sai dai hango Hajiya Kaltume tsaye a karamin gate din part dinta ya kara daga mata hankali sosai domin irin tsayin da Hajiya ta yi ya nuna kamar ita take jira. Rage tafiyar da take ta yi gabanta na faduwa tana ta sake sake domin ta san halin Hajiya Kaltume da ma Khairy din za su iya wanke kansu ita su jefata a ruwa. Tana daf da shigewa bangaren Momy Hajiya Kaltume ta yi kiranta da hannu, a lokacin ne tsoro ya kara cika zuciyar Hurriya, haka dai ta daure ta karasa gurin da take tsaye.

 Hajiya gani

 Ina kika fito?

 Yaya Khairy na raka waje gurin Saurayinta

Hajiya Kaltume ta yi fuskar mamaki.

 Saurayinta kuma? Waye?

 Ban san shi ba ni ma

 Okay. Je ki BQ din Nafisa ki kira min Kulu, kuma ban ce ki fadawa Nafisa ba, sannan ki fada mata ta same ni bangarena magana ce mai muhimmanci ki kirata dabam ki fada mata ba a cikin mutane ba

 To Hajiya

Ta mike tsaye tana jin sanyi a ranta, na rashin zafafa bincike ko binta da zagi da Hajiya Kaltume bata yi a yau. Tana shiga gate din da nufi BQ din Momy har karamar kofar bangaren masu aikin ta fara budewa ta shiga ciki, dukansu suna waje suna hira har da dare dare.

 Mama Kulu ina wuninku

Ta gaishesu, duk suka amsa mata har Kulu, sannan Hurriya ta ce.

 Mama Kulu wai ki zo

 Ni

Ta nuna kanta.

 Eh

 In ji wa?

Dayar dake zaune kusa da ita ta saka dariya.

 Ke ma dai da neman tsawaita zance kike, waye zai kiraki duk gidan nan ban da Momy? Kuma tun da kika ga Hurriya a kin san ita take nemanki

Hurriya dai bata ce komai ba ta juyo ta fara tafiya, a bakin kofar ta tsaya har sai da Kulu ta fito sannan ta tare tace.

 Ba Momy ke nemanki ba, Hajiya

 Hajiya kuma?

She asked with shock.

 Eh nima na dawo daga waje na ganta tsaye tace na kiraki kuma kar na bari kowa ya ji, ta ce ki same ta bangarenta magana ce mai muhimmanci

 Toh... Allah yasa dai lafiya

Hurriya dai ban da kallonta babu abun da ta yi, domin ita ma bata san dalilin kiran ba balle ta fada mata ita kuma bata daina faduwar gaba ba har ta isa bangaren na Hajiya Kaltume. Daman Hurriya tana isar mata da sako ta shiga bangaren Momy ta bar a guri..

Cikin tsoro ta shiga falon da Momy tana sallama. Ruma ce kadai zaune a falon tana cin abinci, hannu ta sauke ta aje plate a kasa bayan ta amsa sallamar Kulu, ita kanta mamakin ganinta a bangaren take.

 Hajiya na ciki ta ce tana son ganin

 Eh tana ciki bari na kirata

Ta mike tsaye tana tsude hannu ta nufi stairs, slowly ta tura kofar dakin Hajiya ta lake.

 Hajiya ga Kulu mai aikin Momy a kasa tana nemanki

 Je ki ce mata ta shigo

 Nan eh?

 Eh

Ta juya ta koma, tun kamin ta karasa saukowa ta fadawa Kulu sakon Hajiya Kaltume.

 Ta ce ki shigo

 Na shigo kuma?

Ruma ta daga mata kai, Kulu ta daga kai ta kalli stairs din da bata taba hawa ba, tun zuwanta gidan, shigarta bangaren Hajiya Kaltume ma za a iya kidayashi domin bata zuwa sai idan Momy ta aikota, kuma ba kasafai Momy take haka ba. Da tsoro Kulu ta taka ta hau stairs sai ta rasa wane daki zata shiga domin duka dakunan a rufe suke kuma bata taba kaiwa gun ba balle ta gane wanene dakin Hajiya Kaltume. Kwatantawa ta yi da dakin Momy sai ta isa bakin kofar dakin ta yi sallama ta kwankwasa.

 Shigo

Ta murda kofar ta shiga idonta na bayyana tsoronta a fili domin bata san dalilin kiran ba, gashi ance mata magana ce mao muhimmanci kuma har ba a son kowa ya ji. Kusa da kofar ta tsaya ta rigina tana zuba gaisuwa.

 Hajiya ina wuni

 Rufe kofar ki matso nan

Ta juya ta kalli kofar sannan ta saka hannu biyu ta rufe ta, ta matsa kusa da Hajiya ta zauna a kasa.

 In ce dai ba wani laifin na yi ba

Hajiya Kaltume ta kalleta tana murmushi.

 Aa ba ki yi laifi ba for now, na ma kiraki ne na yaba miki, sai dai nan gaba ban sani ba ko zaki yi laifin idan kika biyewa sherin zuciya

 Hajiya kin saka ni a hudu me ya faru?

Hajiya Kaltume ta gyara ta kalleta da kyau irin duban nan dake nuna babu alamar wasa a zancenta.

 Ke kika dauki kudin da yake uwar dakinki Nafisa, da sarkokinta da kuma sarkar Namra ko ba haka ba?

Hausawa suka ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. A take gumi ya karyowa Kulu ta fara hadeye yawu tare da dora hannu akai tana zaro ido.

 Ni Kuma? Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Allah Wallahi Hajiya... 

Hajiya ta daga mata hannu.

 Ban ce ki rantse min ba, abun da na sani ne nake fada miki, kuma bana bukatar ki jadadamin, idan kuma kin yi musu zan mu iya zuwa ni da ke da Nafisa da kowa ma na gidan na nuna gurin da kika boye kudin, bayan dakunanku cikin itacen fulawa

Jikin Kulu ya fara rawa irin rawar nan dake kara bayyana rashin gasjiyarta.

 Kin ga daga nan sai Alhaji ya koreki, daman kuma ita Nafisa na san ba zata kyaleki ba sai ta hadaki da Police, baki ga aikinki ba ki ga kudin da kika sata, kuma ga zubewar mutumci da zuwa gurin yan sanda

 Hajiya ki rufa min asiri dan girman Allah ki yafe min, ki dubi girman Allah ki rufa min asiri, Wallahi zan maida duk abun da na dauka, dole ce ta saka na sata, shekarata nawa a gidan nan amman ban tana daukar ko akaifa ba balle kudi

Ta karasa da kuka sosai ko'ina na jikinta yana rawa, ta dayan bangaren kuma tana mamakin ta ina Hajiya ta san da wannan bayan bata fadawa kowa ba, kuma babu wanda ya san gurin da ta binne kudin.

 Ban ce ki maida kudi ba, da ki maida kudi da karki maida kudi duk daya ne a gurina, ni ina ma jinjina miki da kika aikata hakan, domin Nafisa ban da bakar rowa da wulakanci bata aje komai ba, na kira ki a nan saboda na fada miki cewar na sani, kuma na jidadi da baki wahalar da kanki gurin bayyana gaskiya ba, ni nan da kika ganina har duniya ta nade ba zan taba fadawa kowa cewar ke kika saci kudin Nafisa ba ko sarkarta

 Hajiya ina kika ji wannan magana?

 Da wa kika yi maganar?

Ta daga hannayenta sama.

 Wallahi ban yi da kowa ba.. 

 Karki damu da inda naji, ba wani ya fada min ba, abun da nake son ki damu da shi ne, abun da zan fada miki yanzu

Ta kara gyara zama tana hade yawu da karfi.

 Toh Hajiya

 Daga yanzu ina son ki zama karkashin ikona ba ikon Nafisa ba, ita kike yi ma aiki amman ni nake da iko dake, ina son ki saka min ido sosai akan uwar dakinki, kuma nan gaba duk abun da na ce ki aikata zaki aikata shi

 An gama Hajiya Wallahi an gama.. Komai kike so shi za'ayi

 Yayi kyau, ke kuma asirinki zai yi ta rufuwa har ki mutu, kuma zan cigaba da biyanki bayan biyan da Nafisa take miki

 Hajiya ni ba sai kin ba ni komai ba, kawai dai ki rufa min asiri idan kika min haka kin biya ni

Hajiya Kaltume ta yi murmushi ta dauke fuskarta ta dauki wayarta tana latsawa, haka ta kyale Kulu a gurin tana ta share gumi har na kusan minti biyar sannan ta kalleta ta ce.

 Wake share dakin Hurriya?

 Ni ce Hajiya ni nake sharewa na yi mopping ko'ina na saka turare

 Yayi kyau da ba ke ba ce zan ce ki karba ki share saboda, aikin da nake son ki fara min a yanzu shi ne, ki shiga dakin Hurriya ki bincike min komai na dakinki idan kika ga wata laya ko wani kullin magani ko wani abun na dabam ki dauko min shi

 Toh Hajiya amman sai gobe, saboda dare ne yanzu, kuma Momy bata son kowa ya shiga bangarenta idan tana nan

 Ni ma ban ce ki yi yanzu ba, amman dai ki tabbatar kin samo wani abu karki zo min hannu sake, domin ni na san akwai abu a dakin shiyasa na ce miki ki dauko, kamar yadda na san ke kika yi sata kuma na san gurin da kika boye kudin

 Toh Hajiya, Wallahi zan yi

 Shi ke nan tashi ki tafi

 To na gode Hajiya na gode Allah ya saka da alheri Allah ya rufa mana asiri, Allah ya kareki daga duk shari

Hajiya Kaltume bata ji zata iya amsa addu'ar ba dan haka bata amsa ba, sai kawai ta daga mata hannu. Kulu ta tashi ta fice rike da zanen da ya kwance kuma ta kasa daurawa sai rike shi da ta yi a jikinta ta sauka haka. Hajiya Kaltume bata sake fitowa dakin ba sai da ta auna lokacin da ya kamata ace Khairy ta dawo cikin gidan sannan ta fito dakinta ta nufi dakin Khairy, sai ta same ta kwance ruf da ciki bandir din 1k a gafenta wayarta ma a gafenta aje. Sai da Hajiya ta gama kallon komai sannan ta zauna kusa da ita ta kai hannu ta taba ta

 Ke Lafiya kike?

Khairy ta bude ido.

 Lafiya kalau

 Waye ya zo gurinki?

 Waya fada miki wani ya zo gurina?

 Na ga Hurriya na tambaye ta ina ta fito tace min ke ta raka gurin saurayinki, waye wannan?

Khairy bata son jin magana dan haka ta ce.

 Baki san shi ba

 Hakan yayi, danan bana son saninsa, domin bana son ganin kowa a tare da ke sai Fadeel

Da far'a Hajiya Kaltume ta fadi haka tana kai hannu ta shafa bayan yarta irin na uwa mai alfahari. Sai a lokacin Khairy ta zabura ta tashi zaune ta kalli Hajiya Kaltume.

 Wane Fadeel kuma Hajiya?

 Fadeel dai, dan wajen Hahiya Fatee yayanki

Khairy ta lumshe ido ta bude alamar gajiyawa.

 Hajiya ina tunanin na nuna miki tun ranar da kika min maganar nan cewar Fadeel baya a cikin tsarina, namiji mai mata da yara uku me zan yi da shi?
*I know littafin nan zai fito, i know zai yi yawo har ya iso gareki. Na fada kuma zan saki repeating Wallahi duk wanda ya karanta min littafi ba tare da ya biya ba, na barshi da mai mafaWar rana da fitowarta. Daga masu sharing har masu karantawa ba tare da biya ba na barku da Allah...!*
Hajiya Kaltume ta juyo da kyau ta fuskance ta tana kokarin lurar da ita duniya.

 Irinsu ai sun fi rikon aure, balle kuma shi da muka san halinsa ciki da waje? Baki ga yadda yake zaune da matarsa ba? Sannan yayansa ai ba ke zaki rika su ba ko da ya rabu da matar, sannan yaron nan yana da kyau ga kudi, irin sa mata suke rubibi fa amman ke Allah ya kawo miki shi a arha

 Ko duniya yake da ita, ni baya cikin tsarina bana sonsa, ina da wanda nake so... Saurayi matashi be taba aure ba kuma shi ma mai kudi ne dan masu kudi da baya jin zafin kashe naira

Hajiya Kaltume ta yi murmushi.

 Yaro yaro ne, ke Khairy ban da yarinta irin naki, har akwai saurayin da zai fi Fadeel a garin nan? Ke dai ki bude idonki kuma ki ba zuciyarki hadin kai nan da nan zaki ji kina sonsa, kuma ki duba ko amincin dake tsakanina da mahaifiyarsa

A karo na biyu Khairy ta runtse ido ta bude da karfi, cikin ihu ta ce.

 Hajiya bana son Fadeel kuma ba zan so shi ba, baya cikin mazanjen da nake so, ni ina da wanda nake so

 Khairy lafiyarki kuwa? Ni kike yi ma magana da daga murya haka?

 Toh Hajiya kina son cilasta ni auren wanda bana so, na fada miki bana ra'ayin Fadeel, ba a auren dole yanzu

Rai a bace Hajiya Kaltume ta mike tsaye tana nuna Khairy da wayarta a hannu

 Baki isa ba, shi da yake namiji be bijirewa mahaifiyarsa ba balle ke da kike mace, kuma duk samarinki nan naki na banza ba, domin babu wanda ya nuna alamar da gaske yake har kika gama karatunki, kowa na ganki da shi sai ki ce abokinki ne, sai yanzu da na gabatar miki da wanda nake son ki aura mutumen kwarai wanda zai rike ki da gaske sai ki gabatar min da wata maganar banza, to baki isa ba dole ne ki bi zabina, ni na haife ki ba ke kika haife ni ba

Fuuu Hajiya Kaltume ta fice daga dakin kamar walkiya rai a matukar bace. Khairy ta fashe da kuka gaba daya Hajiya tana son rikita mata lissafi bayan wanda Adam yayi mata. Kuka ta yi sosai sannan ta shiga bathroom dinta ta yi alwala ta fito ta gabatar da sallah Isha'i tana gamawa ta nufi jakarta ta bude ta dauko kwayar magani ta balla ta jefa a baki, sai da ta fara taunawa sannan ta kora da ruwan bandaki ta hade ta hau gado ta kwanta.



Some weeks Later....

Hurriya tana zaune rike da kofin ruwa tana kallon MBC 4 Namra ta fito zauna kusa da ita tana murmushi.

 Hurriya dan gidanki kullum sai yace na gaisheki, kuma ya ce yau zai shigo mu gaisa saboda an ki gayyatarsa gurin gatsar tsire

Hurriya ta dago ta kalleta da alamar tunani domin bata gane wa take nufi ba.

 Dan gidana kuma?

 Yeah Ethiopian...

 Oh... Hmmmm Yaya Namra ashe yau akwai daukar wanka?

Namra ta harareta hana dariya.

 What do you mean?

 Yaya Namra na ga taku ta zo daya fa, all my life a yanzu babu wanda nake son ganin aurensa ko partner dinsa kamar ke da Yayana

 Shi ke nan sai kuma aka ce miki wani abu ne tsakanina da shi?

 Hmmmm ai yau idan ya zo fita zan yi na tsareku da ido har na gane komai

 Okay ai tare zamu tafi, daman yace yau sai ya ga kanwata da nake ta masa rowa, but bari na fada miki Gaskiya babu komai tsakaninmu fa, gaisawa kawai muke shikenan

 Hmmm Yaya Namra i can read your eyes fa, shi ma alamunsa suna nuna akwai abu a zuciyarsa fa

Namra ta watsa ido da mamaki.

 Ke Hurriya yaushe kika zama haka? Wato ko kunyata

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login