Showing 138001 words to 141000 words out of 279257 words

Chapter 47 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34673



 Captain aiki ake take yi

 Aiki nake Momy akwai abun da ya kamata na yi typing na aika Abuja kamin gobe

Ita ma dai ya amsa mata ba tare da dago kai ba.

 Amman ka ci abinci?

 Za a dafa min yanzu

Momy ta kalli Namra dake tsaye.

 Namra tafi ki sama masa wani abun yanzu mana, kin san fa baya son tuwo

 Na ce zan yi yace kar na yi stressing kaina Hurriya zata dafa?

 Hurriya kuma? Bata gidan ma fa

 Ta dawo tana ciki, dazun ai Inna Shatu ta gama gage gurin data bata da ruwa saboda ta jika tufafinta

 Okay to kin fada mata

 Eh

 Bari na shiga ciki har ka gama aikin Captain

 Okay Momy

Still be dago ba, Momy ta juya ta koma ciki, Namra kuma ta zauna kusa da shi tana duba wasu daga cikin takardun da yake aikin. Captain be dago ba har sai da ya ji karar talkamin Hurriya tana saukowa daga stairs din, yadda sautin takun tafiyar ke fita ya fahimci ita ce, kamar an saka hannu biyu an rika fuskarsa da karfi an juyar da ita zuwa stairs din haka ya ji. Ba kwalliya ta yi ba amman green atamfar dake jikinta ta karbe ta sosai ta yi mata kyau, Brown hullar dake kanta ma ta fito da ita, ga dan gilashinta dake kara mata kyau a kullum. Ba tarbiyar ta bace yi ma wanda ya girmeta magana a tsaye ba, musamman ma ace mutumen a zaune yake dan haka ta risina a gabansa.

 Gani

 Me yasa baki yi sallah da wuri ba sai yanzu? Baki san babu kyau sallah a makare ba?

 Mun fita ne tare da Yaya Khairy kuma na yi bachi a can ban san an yi sallah ba

 Da kika dawo kuma kika tsaya wasa da ruwa, wuce ki dafa min taliya

Ya fada yana binta da kallo, ita kuma bata yarda ta kalleshi ba domin bata manta da kashedin da yayi mata dazun ba. Har ta fara tafiya sai kuma ta juyo.

 Momy tace na daina shiga mata kitchen fa, zata yi fada

 Ka ji wani salon munafurci, zaki tafi ki dafa ko kuma sai na kira Momy na fada mata?

Namra ta fada tana kokarin kare mahaifiyarta kar Captain yace suna yin abun da be dace ba. Captain ya kalleta

 Easy Namra

Sannan ya kalli Hurriya

 Shiga ki dafa ni na saka ki

 Toh

Ta juya ta shiga Kitchen kamar wanda bata son tafiya. Ta yi iya kokarinta wajen ganin ta yi girkin da kyau da kasancewar ta kwana biyu rabonta da dafa ko da indomie ce balle taliya ko wani abincin dabam, amman har yanzu bata manta da yadda Amma take koya mata ba a lokacin da take gidan, bata cika yaji ba domin bata san sani ba ko yana son yaji ko baya so. Sai da ta gama dafawan sannan dauko plate ta zuba masa ta dauko katon tray ta dora plate din akai ta saka fork a gafe ta dauki yajin dake kitchen din ta dora a tray ta zuba ruwa a wata karamar roba ta zuba ruwa ta dora a tray ta dauka ta fito da shi, bata dire shi a ko'ina ba sai gaban Captain, ya dan karkarto ya kalli yadda take aje ruwan dake roba.

 Gashi nan idan da hannu kake ci ga ruwa nan idan da fork gashi nan, kuma ga yaji nan ka kara idan be isa ba

Ta mike tsaye ta yi hakan ne na dan komai ba sai dan ta huta kar yace ta yi masa wani abun.

 Hurriya

Ta juyo

 Na'am

 Ina naki abincin? Kuma baki kawo min ruwa

Sai kuma ya kalli Namra

 A zubo miki ke ma?

 Aa

Hurriya ta koma kitchen din ta dauki plate ta zubama kanta abincin ta saka spoon sannan ta dauko masa ruwa da cup ta dauko ma kanta ita ma, tana aje masa nasa ta wuce da nata sama. Sai da abincin ya sha iska sannan ya aje laptop din ya dauki abinci ya dora a cinyarsa ya fara ci, sai ya ci ya ji ya koshi sannan ya mikawa Namra plate.

 Zan je na yi sallah an fara kira

Ya mike tsaye a daidai lokacin da Hurriya ta sauko rike da bokitin data matse kayan data jika, wuce su ta yi ta fita waje ta zagaya can baya gurin da igiyar gidan take ta dora kayan sannan ta juyo ta fito. Tana haura entrance din Captain na saukowa sai ta dan koma daga gefe so that ya wuce sannan ta shiga even tho gurin yana da fadi, a haka dai bata son ya zama ta jeru da shi. Kusa da ita ya matsa ya jefa mata wata takardar a cikin bokitin da take rike da shi ba tare da ya kalleta ba ya sauka yana warware hannun rigarsa bayan ya nade shi saboda alwalar da yayi. Tsayawa ta yi kallon takardar kamin ta kai hannu ta dauka.

 I rate your food 4/10 put more effort next time

Ta daga kai tana kallonsa har ya shiga motarsa yayi reverse ya bar gurin, sannan ta maida idonta ta sake karantawa wannan karon murmushi ta yi ya jimke takardar a hannunta sannan ta juya ta koma ciki.


HAJIYA KALTUME POV.

Malam ya girgiza kai yana dauke idonsa daga kasar dake gabansa.

 Hajiya shiyasa ban fada miki komai ba, idan baki manta ba ai na taba fada miki cewar duk wanda nake yi ma aiki ina bibiyarsa na ga halin da abubuwan suke ciki

Hajiya Kaltume dake lullube da farin mayafi ta daga kai.

 To ai shi ne abun da ya bani mamaki, na ce ya aka yi baka tuntune ni da maganar ba

Hajiya Fatee ta daga mata hannu.

 Dan saurara Hajiya bari yayi mana bayanin komai, shiyasa ai na kira shi na ce ya zo, gaki gashi ayi magana zai fi yi a waya, tun da mu ba zamu iya zuwa garin ba

 Wato Hajiya Fatee ina cikin tashin hankali ne, maganar auren nan Alhaji ta daga min hankali kwana biyun nan har mafarkinta nake, kuma ga ana Yasir ya sako ni gaba da zancen auren Rukayya kanwar Iyami

Hajja Fatee ya daki kirji.

 Kanwar Iyami fa kika ce Hajiya Kaltume

 Ita fa, kin san ai ba banza suke barin maza ba, ga fitinar Maama da fitinannne mijin nan nata, kai ni kam haukacewa ne kawai ban yi ba, amman hankali ba shi a kwance yanzu, idan na toshe wannan hanyar wata ce zata bullo

 Dole ki shiga cikin tashin hankali kam, Malam kana jin wannan lamari

Malam yayi murmushi.

 Babu abun da bana gani na a cikin kasar nan duk dare ina duba abubuwa kuma ina ganin yadda suke gudana, wasu abubuwan ina ta iya kokarina na ga na danne abin wani abun kuma idan ya gagareni sai dai na yi shiru, na shiga tunanin da bincike yadda zamu samu mafita, shiyasa ban fada mata ba

 Malam akwai matsala kenan?

 Matsalolin ba ma kadan ba, kuma ina gudun ki shiga tashin hankali ne shiyasa bana tunkararki da irin kalaman nan

Hajiya Kaltume ta kalli kawarta da ita kallonta take dukansu suna cikin tashin hankali da damuwa, musamman ma Kaltume da ita abun ya fi shafuwa.

 Malam dan Allah dan Annabi karka rufe min komai ka fada min gaskiyar komai da komai

Malam ya sauke ajiyar.

 Gaskiya ne Alhajinki yana neman aure, kuma magana ta yi nisa yanzu haka yarinyar ma shi yake bata kudi tana hada lefe, yarinya ce karama da ba zata wuce sa'ar yarki ba....

Hankalin Hajiya Kaltume ya kara tashi domin ba ta yi zaton, da gaske Salma take ba sai a yanzu, wani gumi ya karyo mata mayafin dake kanta tana jin kamar yana shaketa.

 Malam ta ya muna da kai a garin nan? Kuma tuntuni baka fada min ba Malam sai yanzu da na tunkareka da maganar amana bata ce haka ba Innalillahi wa'inna Ilaihiraji'un, na shiga uku ni Kaltume ban gama warware wasu matsalolin ba wasu na son karuwa? Yaushe Iyami ta bar gidan? Ga Nafisa ma ta hana ni rawar gaban hantsi ita ma fata nake ta tafi, sai kuma ka ce min Alhaji na neman aure? Haba Malam ka dai sake bincikawa

 Babu bukatar sake bincikar abun da yake zahiri nake gani kowane dare idan na duba, ban sanar da ke ba ne saboda ina ta kokarin ganin na daidaita abubuwa, kuma ki kwantar da hankalinki yadda Iyami bata gagaremu ba, ita ma da take gidan balle wannan da bata shigo ba?

Hajiya Kaltume ta ranka tagumi kamar zata fashe da kuka. Hajiya Fatee ta kai hannu ta dafa ta

 Ki kwantar da hankalinki Hajiya babu abun da zai gagara, Malam yanzu me ye abun yi?

 Abun yi za'ayi aiki, amman zata kashe kudi sosai daga kan Mijin nata har zuwa kan danta, za a musu Farraqu da ita yarinyar, mijin nata ma za a masa irin aiki

 Amman Malam kai da bakinka ka ce mana yanzu babu kowa a gaban Alhaji yanzu sai ita, taya kuma har maganar aure ta shiga tsakaninsa da wata?

 Wato Hajiya Fatee akwai abubuwan da rufewa muke yi saboda kar hankalinku ya tashi, amman maganar gaskiya ita kanta yarinyar tsaye take akanta kuma da karfi da yaji so take sai ta shigo gidan mijinki, shiyasa kika ji na ce miki za a kashe kudi, domin aiki ne mai matukar nauyi, duk kokarina abun yana neman gagarata wata kila sai koma gudin malamina sai shi fa da rakuma gake aiki, sai dai babu makawa duk abun da aka bukata ana samu

Cikin wani irin yarinya na razanarwa Hajiya Kaltume ta kalleshi ta ce

 Malam wace irin yarinya ce da zata gagareka har sai ka tafi gurin malaminka? Malam ita ma bokanya ce ko kuma Aljana

 Ba ko daya, amman tabbas tana da karfi sosai, na gani shi kansa mijin naki hankalinsa tashe yake akanta, baya iya musa mata fiye da yadda baya iya musa miki, gashi kuma mun riga mun saka masa tsoronki balle ya tunkareki da maganar, duk wani abu da yake a boye yake yinsa, amman ki tunkare shi yau da maganar, zaki tabbatar da abun da nake fada

 Yanzu Malam babu yadda za'ayi a hana auren nan?

 Akwai fa, amman na fada miki za'a kashe kudi, dan haka ki je yi shawara idan kin ga zaki iya sai na sanar masa?

 Malam kana ganin za a kashe nawa?

 Kudi mai yawa, domin sai an yanka rakumi kuma ba zan iya yanke hukuncin kudin yanzu ba, domin sai an bincika anji ko nawa yake, shi kadai za'ayi ba, bayan nan kuma za a bashi karam alkamin kamin a biya kudin aiki idan bukata ta biya

 Shikenan Malam zan yi shawara, zan kiraka daga baya

Cewar Hajiya Kaltume cikin tsananin damuwa, ta saka hannunta a jaka ta ciro kudin da ba za su wuce 5k ta aje masa.

 A kara a hau mota

Ta mike tsaye ta dauki jakarta, Hajiya Fatee na ganin haka ita ma ta mike tsaye ta bi bayan kawarta, sai da suka fito harabar gidan sannan Hajiya Fatee ta ce.

 Na so ki kwantar da hankalinki ki yarda ayi miki aikin nan kawai

 Rakumi kika ji fa yace na bayar Hajiya, kin san nawa ne kudin rakumi a yanzu?

 Biya bukata ai ya fi dogon buri, da ace Alhaji ya sake yin aure ya dauko muku wata ita ta zo ta fara nata yayan ana fifi ta ta akanku ai kara ma ba'ayi ba

Hajiya Kaltume ta leka bayan Hajiya Fatee sannan ta kama hannunta ta kara janta gefe.

 Ni fa ina ganin kamar mutumen nan akwai yaudara a lamarinsa? Bayan na min alkawarin cewar Alhaji ba zai sake auren wata ba kuma ba zai so wata ba sai ni? Ta ina to yaga yarinyar har ya so ta? Kuma yanzu ya na zancen na siya rakumi, yana kwance aikin da yayi ne saboda ya bukaci wani abu, haka kwanan baya yake ce min wai haske a dakin Hurriya kuma ya tare masa ganin komai, ke idan na yaudara ba ta ina zai ce baya ganin komai? Akwai abun da yake boye min dai shiyasa yake fadar haka

 Idan ma wani abun yake bukata, ki ba shi kawai, ke fa naki mai sauki ne, kudi ne kawai matsalar, ni fa aljannu ne da kansu suka bukace ni

 Ke tsaya wai ke me ya bukata a gurinki

 Aljannun da yake aikin ne da su suka bukaci sai sun kwanta da ni amman a jikinsa, kuma tun da na amince sai komai ya wuce, bukata ta biya ciki ya koma, ai na fada miki yadda Fadeel yake dokin auren Khairy a yanzu, da kuwa idan na masa magana kamar na fada masa mutuwa haka yake bata rai, wannan Afrah da ta gagara ma yanzu na samu kanta, ya juya mata baya, ashe daman a baibaiye nake aikin, wai ita baya kamata ni kuma ban gane kan zaren ba sai a yanzu shi da kansa yace Fadeel din ya kamata mu yi ma aikin ba ita ba, kuma yanzu komai ya daidaita

Hajiya Kaltume ta yi wani sukuku tana kallonta kamar wata mai tunani. Hajiya Fatee ta dafa kafardarta.

 Ki kwantar da hankalin, wannan mutumen amintacce ne, ni Wallahi na yarda da shi dari bisa dari, yanzu haka akwai kudin da na damka masa, zai siya min gona a kauye, wata shekara ni ma zan fara noma, yace min babbar gona ce zan yi mamakin abun da za a girba idan aka yi noma a gurin!

 Yanzu amincinki da mutumen nan ya kai har ki dauki kudi mai yawa ko bashi ya siya miki gona? Kuma da alama ma baki je kin ga gonar ba?

 Na yarda da shi ne fa

 Yarda? Mutumen da ba danki ba ba dan'uwanki ba? Kuma ba dan cikin gari ba? Anya kina cikin hayyacinki kuwa Hajiya Fatee? Mutumen nan fa abun da ke tsakaninmu da shi mu bashi kudi yayi mana aiki

A wani yanayi na rashin jindadi da kuma gamsuwa da maganar da Hajiya Kaltume take, Hajiya Fatee ta gyara tsayinta ta ce.

 Yarda ta kawo haka? Idan babu yarda ai ba zamu bada kudin aikin ba ma, kuma ke ma da baki jidadin aikin da yayi miki ba a akan Hurriya da Iyami da baki kai shi makka ba, kuma ni ina ganin babu laifi a cikin shawara, shawara ce yayi min na abun da yake ganin ya dace ke kanki da kika kawata baki min irin wannan shawarar ba, kuma da babu yarda ba zan kira shi ya shigo har cikin gidana ba

 Duk wani abun da zamu masa a babin kyautata ba laifi ba ne, amman kulla kasuwanci ko fada masa sirrinki har ya san nawa ke ganinki wannan abu ne na sirri da be kamata ki yi ba, dan Allah Hajiya Fatee ki farka daga wannan bachin da kika fara

 Hmmm ba zaki fahimta ba Hajiya Kaltume, ke dai tafi kawai sai kin natsu zamu yi magana

Tana maganar tana girgiza kai tana mamakin yadda kawar tata ta kasa fahimtarta a yau.

 Shikena zan kira a waya

Hajiya Kaltume ta nufi motarsa ta bude ta shiga, direbanta dake zaune yana jiranta. Hajiya Fatee kuma ta juya ta koma gida. Ita dai har ta isa gida mamakin amince da yarda da kawarta ta dauka ta bawa Malamin da za a iya kira da boka, ita da bata da saurin yarda da mutane, ko da tsoronsa take ne. Can kuma wata zuciyar ta tuna mata da abin da ta manta.

 Ai ya kwanta da ita, wata kila ta nan ya samu sa'ar mallakarta da wannan mallaka ce kawai

 Ai ka ji matsalar, ba kwanciyar ba mallaka, da babu mallaka ma ai da sauki

Ta fada a fili, har direbanta ya juyo da sauri yana amsawa.

 Na'am Hajiya

 Ba da kai nake magana ba, kawai ka yi aikin gabanka

 Toh Hajiya

Ya cigaba da tukinsa. Suna isa ana sako ruwan sama Hajiya Kaltume ta fita motar ta shige bangarenta, a bude ta samu kofar falon babu kowa a ciki sai tv da ke kunne baturiyar dake screen din tana ta watsa labairai.

 Waye ya bar kofar a bude kuma?

Ya maida kofar ta rufe sannan ta nufi hanyar stairs, kamar jira ake ta kawo kofar dakinta, tana bude kofar sai ta tafi kamar an turata ta fadi kasa jibisssss. Irin faduwar da ta taba yi har ta ji ciwo a kafa, ita ta sake yi a yau kuma ta sake jin ciwon a kafa kuma ta fadi a daidai gurin.

 Wayyo..... Innalillahi Subhanallahi

Ta fada tare da tashi zaune da sauri tana yarfar da hannu saboda zafin da ta ji, idonta kamar za su fado saboda zarosu da take.

 Anya dai... Anya dai...

Tana ta fada, ta matsa can gaba da sauri tana kallon gurin, kamin ta hankare zanen lace din dake jikinta ta duba kafar, ba ruwa ta taka ba balle ta ce tsantsin tile din ne ya kwasheta ta fadi, haka ma ba kofar dakin ba ce, and this is the second time da ta ji haka bayan faduwar farko da ta yi a lokacin da Maama ta samu matsala da mijinta har ta dawo gida.

 Mai kishiya fa baya mutuwar Allah, anya dai? Faduwa irin haka har kana jin kamar an turo ka? Da a stairs na fadi yaya kenan?

Ta tambaye kanta kamin ta amsawa kanta.

 Ai zaka iya karyewa ma!

Ta murgina ta rarrafa ta isa gurin gadonta ta cira daker ta hau saman gadon tana taba kafar dake mata mugun ciwo.

 Anya ba karaya na yi ba? Wannan bala'in zafin? Ina da makiya da yawa

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login