Showing 183001 words to 186000 words out of 279257 words

Chapter 62 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34669

ransa, na kudirinsa akan yar'uwarta ba ita ba. A gurin da ya tashi ta zauna ta dafe kanta tana hawaye kurjin dake mata ruwa wanda Salim ya bar mata sai ya fashe a yau saboda Captain ma ya juya mata baya....
Yana fitowa falon ya nufi motarsa sai da ya bude motar sannan ya dago ya kalli windows din dakin Hurriya, sai ko ya hangota tsaye tana hawaye, kuma ita ma shi take kallo da alama ta dade a gurin tsaye tana jiran fitowarsa. Gambun motar ya saki ya kama kunnensa da hannu biyu ya rike duk da fuskarsa babu komai sai bacin rai haka dai yake kokarin ganin ya bata hakuri na fitowar da yayi dazun ba tare da ta ba shi izini ba, and be fada mata Momy ta san da zuwansa dakin ba ya barta tana ta wahala. Hannu ta saka ta share hawayenta tana cigaba da kallonsa tana murza awarwaron da ya bata. Da hannu yayi mata alama da ta yi murmushi shi ma yana kirkiron murmushin da kallonta ke kwararo masa shi yana wanke masa bacin rai, and she can't help it but to smile kamar yadda ya bukata, and this is the first time da take jin wani abu na dabam akan Captain. Daga inda yake tsaye yayi mata thumb up sannan ya shiga motarsa yayi reverse tana kallonsa har ya fice.





Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 36

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


CAPTAIN POV.

Da hannu daya yake tuki dayan hannunsa kuma yana amsa wayar da Salim yake masa.

 Matsalata da kai naci, tun muna Ethiopia kake damuna da maganar yarinyar nan, Salim ba zan iya forcing dinta ta soka ba, ya kamata ka hakura tun da har ta nuna maka bata kaunarka

 Ba wacan maganar ba ce Captain wannan mai girma ce, ba maganar soyayya bace, and yanzu na fahimci yarinyar nan bata cancance ni ba, kuma Alhamdulillah da bata yarda ta amince da soyyayata ba

Captain yayi dariyar da bata da sauti. Good Boy yanzu ka gane kenan. Ya fada a ransa a fili kuma sai ya amsa masa da.

 To akan me ne?

 Abun ba zai fadu ba, na kira Namra ina son ta sada ni da Hurriya na yi magana da ita bata amsa min wayar ba, kuma ina son naje gidansu ina tunanin kamar ba za a bari Hurriya ta fito ba

 Yanzu kana ina?

 Ina gida

Captain ya kalli agogon hannunsa.

 Masallaci zan je yanzu, idan mun fito Jumma'at zan kiraka

 Na so ka zo yanzu Captain wani abu ne da ba shi da kyau gani, ko na zo na same ka?

 What so ever it's, sai na fara gabatar da Sallah zan fuskance shi, so ka jirana idan na fito zamu yi waya

Be jira abun da Salim zai sake cewa ba ya kashe wayar, ya aje a cikin motar ya cigaba da tukunsa, a babban Masallacin kan wurin Sarki dake garin Gusau yayi Sallah Jumma'a sannan ya kira Salim at that Salim yana mosque domin ba masallaci daya suke sallah ba, and akwai banbancin lokacin sallah Jumma'a a Masallacin Sheik Umar Kanoma da na kan wuri. A kokarinsa na martaba lokaci ya nufo gidansu Salim din kai tsaye, a harabar gidan ya shiga ya faka sannan ya aika masa da sako.

 Idan ka gama ina harabar gidanku

Ya aje wayar ya bude gurin da yake cewa ajiye pistol dinsa ya dauka ya saka a jikinsa sannan ya dauki counter dinsa dake cikin motar ya laka a yatsansa yana tannawa, ya san yau ranar jumma'a ce ranar da aka ce a ninka salati ga Annabi Muhammad S A W, idan kuma baka yi ka yi domin shi salati haske ne a duniya da kiyama. Ya kusan minti talatin a gurin sannan reply din Salim ya shigo wayarsa.

 On my way

Ya karanta sakon ya sake maida wayar ya saka aljihu ya cigaba da salatin, yana kallon harabar gidan iyakarta rabin na su harabar dake Kaduna. Tsaki ya dan ja ya duba agogon hannunsa, wata zuciyar na ce masa ya kira Salim ya fada masa idan sun hadu a gurin aiki za su yi magana domin baya son bata lokaci a gurin, kamin ya kira motar Salim ya shigo harabar gidan ya faka daidai gurin da motar Captain take, kusan a tare suka bude motocin kowa ya fito, but jin kai irin na Captain ya hana shi isa gurin Salim sai da Salim din ya karaso gurinsa ya jingina jikin motarsa.

 Minene?

Captain ya tambaya ganin seriousness a fuskar Salim. Karamar ajiyar zuciya Salim ya sauke sannan ya fara taba wayarsa dake hannunsa.

 Ina dawowa na tararda wani labari marar dadi a gidan nan

Captain ya dauke kai.

 Kan da son jan zance, kai ba mace ba balle ace zan bika ina lallabaka, tun a mota ma ya kamata ka fada min ko minene amman baka yi ba yanzu kuma na zo kana abu kamar mai rubuta littafi, and you know bana son wannan bata lokaci

 Akan Hurriya ne, wani abu ta aikata ita da Cousin dina, so abun ya daure min kai na tura maka hotunan yanzu ta whatsapp ka duba

 Ba zan duba ba idan ba zaka fada ba zan tafi

 Tana mu'alama da cousin dina, ina tunanin shi ne reason din da ya hana ta amsar soyayya ta, and Alhamdulillah na jidadin haka

Captain ya tsaya cak yana kallonsa with so many questions zuciyarsa ta soma zafi kamin ta tafasa, idonsa na kokarin sauyawa, the word mu'alama kowa ya ji ya san bad thing ake nufi kalma ce ba mai kyau ba. Salim ya mika masa wayarsa

 Duba wannan

Captain ya karbi wayar ya sauke idonsa akan mugun abun da he wish be kalla ba, hotunan Hurriya ne a sirara tare da mutumen da yake ganin idan ya zo gurin Salim, wani gurin suna kwance a gado daya, wani gurin kuma ta kwanto jikinsa wani kuma ta yana kissing dinta ya tallabo kanta da hannunsa dake cikin gashin kanta, na karshen ne hannunsa yake kan kirjinta and duka hotunan daga ita har shi babu mai tufafi a jikinsu.

 Wannan ba Hurriya ba ce

 Ni ma hala na fada da farko domin yadda take da tarbiya da mutumci ba zaka yi zaton ta aikata ba

Captain ya dago ya kalleshi naman fuskarsa na rawa cikin wata kalar murya mai fita da sauti ya ce

 Waya turo maka wannan?

 Cousin dina ne fa, yanzu haka case din da na zo gida na tarar ana yi kenan, i was shocked da na ga abu kuma na yi magana da shi ya fada min gaskiyar itace amman be san ya aka yi hotunan suka fita ba

Captain ya hade yawun bakinsa sannan ya nuna wayar Salim dake hannunsa da yatsansa na hadu.

 Ina yaron nan yake Salim? I need to talk to him...

 Yana ciki bari na kira shi...

Salim ya nufi main house din da saurinsa shi kansa mamakin abun yake ta wani bangaren kuma yana gode Allah da be yi soyayya da Hurriya ba. Captain ya juya ya kife kansa jikin motar zuciyarsa na bugawa da karfi, wani numfashi mai zafi yana fita a hancinsa da bakinsa, wani irin kuna zuciyarsa take tana isarwa har cikin kansa. Can kuma ya juyo ya jingina da motar, kamin ya daga ya fara zagaya motar hannayensa nade a baya rike da wayar ta Salim.

 Hurriya....?

Ya furta mamakin zayyane a fuskarsa, juyowa yayi ya dawo gurin da Salim ya bar shi ya tsaya ya rumgume hannayensa yana kallon Salim din da ya fito tare da Adam, kamin su karaso Captain ya nufi gurinsu suka hadu a tsakiyar gidan.

 Abun da Salim ya nuna yanzu nake son na tambaye ka it's real or fake?

Adam ya kalli Salim ya sake kallon Captain.

 Wane irin tambaya ne wannan

Captain ya kawar da fuska yayi murmushi, Salim ya kalli Adam.

 Just answer him

 It's real

Captain ya kara matsawa kusa da Adam yana wasa kafafuwansa kamar wanda yayi shekara a tsaye.

 When how? Where?

 A inda muka saba haduwa?

 Da saninta ka dauki hotunan?

 Aa ba da saninta ba, kuma ban san ya aka yi hotunan suka fita ba

Captain ya juya baya ya busar da iskar bakinsa ya juyo ya kalleshi.

 Adam idan wani ya saka ka yi wannan abun i cam pay you fiye da abin da aka biyaka

Adam ya girgiza kai.

 Babu wanda ya biyani, kamar baka san waye ni ba? Wa zai biyani na yi wannan abun?

Captain ya kalli Salim, Salim ma ya kalleshi kamin ya kalli Adam a karo na biyu.

 Ina kuke haduwa da ita?

 Tudun wada low-cost

 Why not gidansu?

 Saboda iyayenta basa so na

 Ya aka yi ka san yarinyar nan ina ka santa?

 Hurriya...? Na hadu da ita a bikin birthday din yayarta Khairy daga lokacin muka fara soyayya sai kuma iyayenta suka fara nuna basa son alakata da ita, daga lokacin sai muka yanke gurin haduwa daga nan dai sai shedan ya shiga tsakaninmu

Captain ya maida dubansa gurin Salim cikin kalar yanayi dake sauya kyau fuskarsa da raunin idonsa.

 Idan kana son Hurriya bata so ka ba, wannan normal ne an saba haka, amman kokarin aikata wani abu, martabarta da ta gidansu kake tabawa

Ya matsa kusa da Salim irin matsawar da yan dambe suke yi idan suka kullace mutum a zuciya.

 Ba zan bar wannan ba, ba zan kyale kowa da hannu a lamarin nan ba

 What do you mean? Ni zan saka kanena ya aikata haka? Shi ma an taba martabarsa da ta gidanmu ko ka gane?

 I don't care shi namiji ne zai iya haka, ko kai ka saka shi ko kuma yana sonta a karan kansa zai iya haka? Hurriya ba zata aikata wannan abun ba ba zata yi hakan a cikin hayyacinta ba

 Saboda yana wearing innocent face tana nuna ita ta kwarai ce? Baka da wannan tabbacin Captain, miye alakarka da ita wai da kake ta wannan kokarin

Captain ya matsa baya ya watse wayar Salim dake hannunsa cikin daga murya da ya hankalonta da idon kowa a harabar zuwa garesu ya ce.

 Ubanta ne ni Salim.... Haka kake son ji?

Cikin zafin nama ya riko hannun Adam ya lankwashe hannun hoton da ya gani na hannuns aa kirjin Hurriya kawai yake ta gani a idonsa har yanzu. Salim yayi hanzarin rike Captain

 No no no no... Captain..

Captain ya fisge hannunsa ya rika hannun Adam dake ihu da hannu biyu ya daga kafarsa ya karya hannun Adam, da mutane suka yo kansu kamin su kawo ya dunkula hannunsa ya kai a bakin Adam a take ya barar masa da hakora daya jini ya wanke baki, Salim ya rike Captain da karfi amman hakan be hana Captain shimfidawa Adam duka a kirjin da ya kwantar da kan Hurriya ba. Mutanen suka rike Adam dake ihu kamar za a cire masa rai. Salim ya sake shi da karfi ya dawo gabansa ya tsaya

 Captain miye haka? Miye alakarka da ita? Dan me zaka rasa control akan wannan abun?

Sai kuma ya juya da sauri ya tare wani yayan Adam din dake son kaiwa Captain duka.

 Aa please matsala ce da za a iya magancewa dan Allah Kabir ka bar wannan abun a hannu

 Bar shi ya taba Captain din soja ya jawa kansa bala'i

Salim ya juyo gurin Captain dake maganar ya kalleshi ganin yana kokarin ballo masa wasu ruwan ballo masa ruwa a lokacin da yake son toshe wata hanyar, kowa dake gidan sai yayi ma Captain uzuri saboda suna zaton yayan Hurriya ne, shi kansu abun ya taba su balle kuma shi da yake da kanwa mace. Captain ya bude motarsa ya shiga ya bar Salim a tsaye yana bawa Yayan Adam din hakuri domin yau jumma'a wasu yan'uwa duk ba su dawo daga gurin Sallah ba, masu aikin gidan ne kawai sai wannan yayan nasa da kuma mahaifiyar Adam din wacce ta fito tana kuka tana fadin ba zata bar Captain ba.

 Yadda abun ya taba martabar gidansu haka ya tana martaba mu, kuma ai tare suka hadu suka aikata saboda me zai fadawa dana?

 Ba kyale maganar za'ayi ba, dole za a bi kadi ai, yanzu dai abun da ya fi a dauki Adam din a kai shi asibiti

Su biyu suka kama shi, Salim da yayansa Kabir suka saka shi a motar Salim din suka nufi asibiti da shi. Suna isa Emergency Salim be tsaya an karbi Adam ba ya bar Kabir da Adam din a gurin ya juyo da motarsa ya bi bayan Captain ya san ba zai wuce ya tafi gidansu Hurriya ba.

Kamin Captain ya iso gidansu Hurriya ya kusa balla sitiyarin motar saboda yadda yake dukansa da mugun karfi yana fisgarsa, gaba daya ya rasa ta ina zai fara tunani. Yana yin fakin be tsaya kashe motar ba ya bude ya fita ya bar motar a bude, yadda ya tura kofar falon Momy da a rufe take zai iya ballata. Hurriya dake tsaye a dinning rike da plate ta juyo cikin tsoro ta kalli kofar falon, domin yadda ya turo kofar falon ya shigo ya firgitata even though bata san waye ba har sai da ta kalli kofar. Kai tsaye ya nufeta daman zuwan domin ita ne!

 Waye Adam.....!

Ta daga kai ta dubeshi gaba daya muryarsa ta cika dodon kunnenta ta cika falon tsayen da yayi a gabanta kuma ya cika duniyar idonta. Sai tsaya baya da sauri at that time ne ya fisge plate din hannunta ya bugashi a kasa.

 Waye Adam....!!

Ta yunkura zata ranta ana kare, ya rikota kamar wata bulala haka ya jujjuyata ya jefar a gefen kujera ta fadi kasa tana kwala ihu.

 Subhanallahi? Captain Lafiya?

Amadadin ya amsawa Momy dake saukowa tana tambayarsa tare da Namra sai ya nufi gurin da Hurriya take kwance ya mikar da ita tsaye ya dauketa mari.

 Waye Adam?

Ta kai hannu zata taba fuskar ya wanke mata fuska ta dayan gefen sai ta fasa taba fuskar yawu da jini suka gangaro mata lokaci daya, yadda yake daka mata tsawa gurin tambayarta da kuma marin da yayi mata a yanzu ya mantar da ita Adam, domin ta dade ta tattara lamarinsa ta aje a gefe daya tun da dadewa. Momy ta iso da sauri ta rika Captain ta matsar da shi gefe ta kalli Hurriya.

 Me kika masa?

Hurriya kallon Momy ta yi ta fashe da kuka domin ba zata iya fadar abun da ta yi ba, tambayarta yake wanda bata sani ba. At that time ne Captain ya samu damar runtse ido ya bude ya zauna a kujera ya kasa cewa komai, zuciyarsa na masa wani irin bala'in zafi.

 Wai me ya faru ne can anyone explain?

Momy ta tambaya a tsawace tana kallon Captain kamin ta juyo gurin Hurriya.

 Me kika yi?

Hurriya ta girgiza kai. Captain ya dago daker ta danna wutae da yake ji ya kalli Momy yana nuna Hurriya.

 Waye saurayin yarinyar nan Momy?

Momy ta daga kafadunta.

 I don't know, waye saurayinki? Miye matsalarka da saurayinta? What's going on here?

 Ba ni da saurayi Wallahi Allah

Hurriya ta amsa cikin kuka, Captain ya daka mata tsawa.

 Karya kike yi waye Adam?

Namra dake saukowa stairs ta amsa masa.

 Adam Sarauta? Wanda yayi miki ruwan kudi a birthday Khairy ina tunanin shi yake nufi

Captain ya kalli Namra yana kara tabbatar da zancen da Adam din ya fada masa cewar a birthday yayarta suka hadu.

 Ba sarauyina ba ne....

Ta amsa cikin kuka bakinta na mata mugun ciwo yana zubar da jini, kana ta kai hannu ta rike rigar Momy ganin Salim ya shigo cikin falon sai zuciyarta ta raya mata taruwa za su yi su duketa. Momy ta juyo ta kalli Salim Namra ma da mamaki take kallom yadda ya shigo falon dake bude babu sallama babu neman izini, hakan kuma yana karantar da ita akwai abun da yake faruwa.

 Ita ma ka fasa mata baki ko Captain? Wai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login