Showing 240001 words to 243000 words out of 279257 words

Chapter 81 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34648

jarabawa ce ta rayuwa Alhamdulillahi

Appa ya fada cikin tsananin bakincikin da be isa ya boye a zuciyarsa kadai ba har sai da fuskarsa ta bayyana.



CAPTAIN JAMAL POV.

 Akwai wani abun da zan iya taimaka maka da shi ne?

Captain ya girgiza kai ya kwanta jikin kujera kamar mai jin bachi.

 Aa anyi komai, daman ba wata hidima za'ayi ba, Ammy ta hana taron biki ta hana komai ka ga babu bukatar yin wani abu

 Amman dazun ina jin ka a waya da Abdulkareem kake masa zancen gyaran gida

Captain ya zaburo masa da fada ganin yana son matsa masa ya shigar masa hanci.

 Already ina da gidan a nan da Kaduna Salim ka sani, na hannata masa komai ne saboda yayi kwangilar kula da komai idan akwai abubuwa da za a canja ko a saka yayi saboda sabon gidaje ne, kai kuma ba sana'arka ba ce to miye abun takuwara dole sai ka shiga ciki?

 Babu Allah bada zaman lafiya

Salim ya fada a fusace shi ma ya mike tsaye zai fice Ammy ta dakarta da shi.

 Salim karka fita dan Allah karka yi fushi, na san halin Captain ba tun yau ba, kar abun da yake yi a yanzu ya dame ka, mu kan mu tarewar da muka yi a wannan gidan na dole ne, na sani yaushe rabon d mu zo garin nan mu yi kwana uku ma amman gashi yau har mun tare a gidan nan saboda wannan auren, ka sha kuruminka idan zaka zai yi auren kwarai da za ayi taro ayi biki na gani na fada ku zaku yi komai

Salim be fita ba, sai dai kuma be dawo ya zauna a inda ya tashi ba, yayi karfin halin cika fuskarsa da murmushi.

 Ammy har yanzu kina kam bakinki dai?

 Shiyasa ai ban gayyaci kowa ba, sai idan zai sake aure

Captain ya karkato ya kalli Ammy yana murmushi.

 Allah Ammy?

Ammy ta masa banza ta cigaba da magana da Salim.

 Karka biye masa, kai ma kasan wanda ya ke a cikin hankalinsa ya san me yake yi ba zai auri yarinya irin Hurriya ba ko da kuwa an hada masa da buhun zinari da gidaje

Salim ya saka hannunsa aljihu yana fadin.

 Gaskiya kam, Captain ka yi jihadi babba

A take murmushin dake fuskarsa ya Captain ya gushe.

 Sosai kuwa, kuma kai har ka mutu ba zaka taba samu mace irin Hurriya ba, shiyasa abun yake ba ni dariya idan Ammy tace zan kara aure bayan domin bana jin zan iya ganin wata macen ta burge ni a yanzu, kuma ni ba zan auro macen da zata hana ni zaman farincikid Hurriya ba

 Baka ma bukatar kara aure Captain ko dan gudun a goranta mata, ni ma kuma bana fatan samun Hurriya a yanzu na fi karfinta, kai ma kuma ba zaka iya nunawa duniya ita a matsayin mata ba, ba zaka gane illar hakan ba sai nan gaba

Captain ya mike tsaye anger na dibanshi.

 Hey Mr Salim daga yau na yanke duk wata alaka dake tsakanina da kai, kuma karka kara fadar wata kalma marar dadi akan Matata, kawai kana kishi ne saboda ni na yi dacen auren Hurriya ba kai ba, dan haka na datse alakarmu daga yau kar ma wata rana ka ce zaka shiga gidana ka ga Matata

Salim yayi murmushi mai sauti.

 Kishi? Shiga gidan ka na ga matarka? Macen da kowa ya gama ganin tsiraicinta kamin ka gani? Ita kake cewa kar na shiga na gani?

Captain ya saka hannayensa aljihu yana jin kamar ace da bindiga a ciki ya raba kam Salim biyu a gurin.

 Gun?

Salim ya saka hannunsa aljihu ya dauko bindigarsa ya aje kasa ya turowa Captain, mai nema a duhu balle an haska masa Captain ya duka ya dauki bingidar ya saita Salim da ita ya danna sai ta amsa da kettttt alamar babu albashiru a ciki. Ko da acw akwai alhasashen harbawa Captain zai yi because he ?found ?it? hard?to?control? hia anger. Ammy ta fasa ihu.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Jamal miye haka? Kisan kai zaka yi?

Cikin takaici Salim ya kalli Captain ya ce.

 Da gaske zaka iya harbina idan akwai halsashe a ciki?

Captain ya wurga masa gun din.

 Ga zahiri kana gani? And daga yau babu kai babu ni, and the rest ka jira na dawo bakin aiki

Salim ya duka ya dauki bindigar yana bakincikin da suka saka idonsa tara kwalla.

 Ban yi tsamman ni samun haka daga gareka ba Captain, wannan ne karo na biyu da ka nuna ni da gum saboda Hurriya, soyayyar wata be kamata be kamata ya rufe maka ido ba, har ka manta waye ni a gurinka, na gwada ne domin na ga idan zaka iya aikatawa da gaske, kuma gashi na nuna, a yau ka nuna min tsantsar kiyayya Captain, daman na lura da wannan babin tuna ranar da ka gane ina son Hurriya, amman karka manra har yanzu ina da sauran amfani a gurinka, be kamata ka manta wannan ba

Salim ya juya ya fice rike da bindigar. Captain da be karasa kawai kofar ya juyo ya kalli Ammy yana huci.

 He even got lucky ban fasa bakinsa ba, kuma ba laifin kowa ba ne sai na ki Ammy ke kika janyo har ya samu fuskar fada min magana haka kai tsaye

Ammy da mamaki be gama fitarta ta janye hannunta a baki cikin tashin hankali ta ce.

 Kisan kai fa ke nan zaka aikata Captain?

 Ammy idan idona ya rufe bana gane me zan aikata sai bayan sun bude nake ganin abun da na aikata, kin san wannan tun ina karami kuma dan Allah ina rokon alfarmar karki sake cewa zaki alakanta ni da Salim

Yana kaiwa nan ya nufi hanyar dakinsa. Ammy ta bishi da kallon tsoro, har lokacin jikinta rawa yake, bata tsamanin tsamanin fushin anta ya kai haka ba sai yau.

 Aikin soja ma be dace da kai ba, ba zan bari ka cigaba da aikin nan ba, idan ba haka ba wata rana zaka kashe wani ka bar mu da aiki

Ta juya ta dauki wayarta ta shiga kiran Daddy. Captain ya zauna a kujerar dakin yake yana jin zafin kalaman Salim kuma yana mamakin kansa da be canja masa kamanin ba. Ya mike tsaye ya halbi kujerar da kafa, ya cige bakinsa sosai yana jin kamar ace Salim din ne a gurin. Ya nufi bandaki ya wanke fuskarsa ya fito sai ya fito daga dakin gaba daya ya shiga kitchen ya bude fridge ya dauko ruwa ya zuba ya daga cup din sama yana sha...

 Amman karka manra har yanzu ina da sauran amfani a gurinka, be kamata ka manta wannan ba

Kalaman Salim na karshe sun dawo masa, sai yayi sauri aje cup din ya lalaba aljihunsa babu wayarsa da gudu ya fito Kitchen ya nufi wayarsa ya dauka ya kira wata number.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?  Alhamdulillah Thank you so much i trust you

Ya sauke wayar tare da ajiyar zuciya a lokaci daya. Kamin ya taba komai kiran Daddy ya shigo wayarsa ya daga kira Daddy ya rufe da fada duk yadda Captain ya so ya wanke kansa be samu haka ba a gurin Daddy domin be tsaya ya saurare shi ba.

 Amman Ammy bata fada maka abun da Salim yayi min?

 Ko miye yayi maka be kamata ka nuna shi da bindiga ba, ran mutum ba abun wasa ba ne kuma a yadda kake tare da Salim be kamata ace kana barin Sheidan ya shiga tsakaninku ba, kana jami'in tsoro amman kake wasa da rayuwar wani wanin ma abokin aikinki, da wani mugun mutum ne zai iya amfani da wannan damar yayi against dinka, kuma idan ba zaka sauko daga wannan zuciyar ba ta ina zaka iya uba kuma mai gida? Nan gaba matarka idan ta maka laifi sai ka ce zaka yi mata, ko kuwa ba zan lamunci wannan ba, ban wahalar da mahaifiyarka ba zan yarda ana ya auro yar mutane ya wahalar da ita ba, dan haka tun yanzu ka zubar da hallayen nan naka bana son su

 Zan kiyaye Daddy amman baka san Salim ba ne ya... 

 I don't care what Salim did to you, ko zaginka yayi be kamata ka yi wasa da rayuwarsa ba, be kamata ka nuna rayuwarsa bata da muhimmanci a gareshi ba, hankalin mahaifiyarka ya tashi wane irin abu ne wannan?

 Yi hakuri Daddy

Yadda Daddy ya kashe wayar kadai ya isa ya bayyana maka har lokacin ransa a bace yake, abun da Captain yayi kokarin aikata laifi ne babba a dokar kasa kuma laifi da zai iya sakawa a hukunta mutum ko a koreshi daga aiki ma a dokar aikin soja, idan ma ace ya aikata matsalar su zata fi shafa fiye da Captain din. Kansa ya dafa ya runtse ido ya bude shi kansa yayi nisa abun da ya aikata a gaban mahaifiyarsa a yau, be taba aikatawa wani haka ba sai Salim kuma shi ne karo na biyu, haka yake jin kamar ba zai iya rike kansa ba a duk lokacin da wata magana marar dadi ta fito daga bakin Salim zuwa kunnensa akan Hurriya. Tashi yayi ya nufi hanyar dakin da mahaifiyarsa take sai ya same ta zaune ta kifa kai da guiwa tana kuka. A take hankalinsa ya tashi daman kukan uwa shi ne tashin hankalin ko wane a na gari, ya duka a kusa da ita yana kallonta idonsa har sun fada tsabar tsoron da ya kama shi.

 Ammy lafiya... Kuka kuma? Me ya faru?

Ta dago ta kalleshi hawaye na zuba a idonta.

 Zuciyarka tana ba ni tsoro ni ba zuciya ba, mahaifinka ba zuciya ba kai ban san a ina ka dauko wannan rayuwar ba, ban san me zaka aikata a gaba ba, idan babu kowa wata rana zaka iya kashe wani, zuwanka garin nan ya bata abubuwa da yawa na farinciki na Jamal, soyayyarka da yarinyar nan ya lalata akala da Hajiya Nafisa a yanzu, saboda tana ganin zan iya cilasta ko kuma na yi fadi tashin hana tarewar nan amman na gaza, Namra muka so ka aura Jamal ba Hurriya ba, idan ba zaka so ta gida ba ka nemo ta waje mai mutunci mana ba wannan ba, yanzu kokarin tarewa kake da ita, ka bata da abokinka kuma nuna shi da gun miye amfanin haka? Duk akan yarinyar nan fa

Zaunawa yayi a gurin ya nade kafafuwansa ya duba mahaifiyarsa duba na tsanaki.

 Mutum baya aure sai matarsa Ammy ya kamata ki gane wannan, Allah ya rubuta ni da Hurriya zamu yi aure ko duk duniya za su taru ba za su iya tare wannan ba, zuwan da nake a gurin Momy ban taba zuwa saboda wata rana rana na so Hurriyya ba, haduwata da ita wani abu da Allah ya kaddara domin ban san da ita a gidan ba har sai da Mahaifiyarta ta fita, na san akwai yayan mijinta amman ban rike fuskar ko daya ba, Ammy ya kamata ki duba wani daura auren da aka yi ma bada sanina aka yi ba, amman duka Allah ya rubuta faruwarsu, farkon haduwarmu da yarinyar mari ne, na mareta da hannuna saboda ta taba ni ba ta gani ba, daga lokacin da Namra ta fada min bata iya gani sai da gilashi sai ta ba ni tausayi, ban tabbatar da ina tausayin yarinyar nan ba sai ranar da na je zan shiga dakin Momy da kunne na ji yadda take magana da Hurriya akan cewa zata musgunawa yarinyar nan kuma ba tare da ta mata komai ba, su kan hana ta abinci wani lokacin sai da taimakona take samu ta ci, kamin zuwa yanzu mahaifinta ya tsane ta aka kashe dan'uwanta ta koma bata da kowa a gidan Allah, ga mahaifiyarta ba lafiya, and now aka yi mata wannan abun yanzu a haka Ammy duk bata ba ki tausayi ba?

 Ta ba ni, amman ai bata dace da kai ba, ina magana ne akan dacewa

 Ta ina kike ganin bata dace da ni ba?

 Baka ga yadda hotunan suka yadu a duniya ba? Kuma bata gani

 Rashin gani kar ya dame ki, ina da wani yakini cewar Allah ba zai kunyata bawansa ba, da yardar Allah idon Hurriya zai bude, yada hotunanta kuma ba ita ta aikata ba aikata mata aka yi saboda a bata mata suna, kuma an yi nasara tun da gashi matar da ya kamata ace ta fi kowa kaunarta ta tsane ta, abun da zai baki mamaki ma yar'uwarta ce ta aikata mata abun Ammy, hakan ya nuna yarinyar nan tana fuskantar kalulabe na rayuwa kala kala, ke kuma kina kara taya Momy kishi ne kawai shiyasa kike tsanar Hurriya da yawa, na tabbatar da Namra ce haka ta faru da ita Momy ba zata so na guje mata ba haka ne?

Ammy ta daga kai.

 Amman saboda Hurriya ba yarta ba ce shiyasa take fushi dake ni ma take yi da ni, a gabanki ta fadi cewar laifi ba nawa ba ne ni kadai har da Daddy, saboda tana ganin ya aura min yar kishiyarta ya bar yarta

Captain yayi shiru na dan lokaci idonsa na cika da hawaye.

 Wallahi Wallahi Wallahi Ammy ban san dalilin da ya saka nake kaunar yarinyar nan ba, ni dai kawai Allah ya saka min kaunarta, ina jin farinciki a tare da farincikinta ina jin damuwa a tare da damuwarta, idan wani ya tsane ta ina jin kamar ya tsani cigaba ne, ita kadai ce yarinyar da nake jin zan iya jure duk wani abu da ya shafe ta, zan iya daukar duk wani zagi da suka a duniyar nan, ban sani ba ko a nan gaba zan gane kuskuren hakan, amman a yanzu bana jin son kowa sai ita, shiyasa na kan kasa auna abun idan an tuna duk kaunar da kike min matsayinki na uwa kin tsani wandda nake so, to ina zan kama Ammy? Wani lokacin ina jin tsoron kar yarinyar nan ta dawo a gidana matsayin matata ki musguna mata ko ki wulankatata, kamar ni kika yi ma, na san ba zaki yi fatan danki ya wulakanta yar mutane ne balle ke kanki ki wulakanta matata Ammy ban taba tunani ba, ko da ace Hurriya tana aibu na yi tunanin zaki boye saboda kar na ji raina ya bace, amman ke da kanki Ammy kike yakar yarinyar nan? Kina fadar yadda zaki yi idan aurena ya zo yau duk kin kawar da wannan saboda Hurriya ce, a gabanki abokina yake zagin matata saboda ya samu fuska a gurinki Ammy, kina fada min irin kaunar da kike min kina gudun bacin raina amman yau babu wannan... 

Tuni hawayen Ammy suka kafe a idonta ganin anta yana kuka, bakinsa na furta kalaman dake kama kwakwalwarta.

 Kuka kake yi Jamal...? Hawaye kake zubarwa?

Ya kawar da fuskarsa gefe.

 Ammy ya yadda kika san zuciyata, tun da kika ga na shanye duk abun da aka yi ma Hurriya na kaunace ya kamata ki fahimci yadda tasirin sonta yake da karfi a zuciya, Ammy a yau zan miki rantsuwa da Allah na tabbatar miki da abun da kike da muradi... Wallahi Wallahi Wallahi Ammy idan fasa auren nan ne farincikinki, zan hakura da Hurriya Wallahi ba zata tare a gidana ba a matsayin matata zan hakura da ita! Amman tabbas zan roko Allah ya dauki rayuwata, na fi sha'awar mutuwa fiye da rayuwa babu Hurriyya a matsayin Matata...! Ko da na mutu zan tafi da tunanin wannan abun... 

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un

Ammy ta furta tashin hankali na kwance a idonta ta rika fuskar Captain da duka hannayenta sannan kamin ta tashi ta rumgume danta tilo daya tana hawaye.

 Abun be kai can ba, be kai can ba...

Ta dago ta kalli fuskarsa ta sake rumgume danta.

 Wannan irin so da kake yi ma yarinyar Allah yasa ta zame mata ?a, wannan son ya ba ni tsoro

Tsoro ba a furucinta kadai yake ba har a cikin zuciyarta yake, domin Captain be taba zaunawa da ita gaba da gaba ya karabta mata soyayyar wata mace da karfi kamar yadda ya yi mata a yau ba, a yadda zuciyarsa take idan ya rasa zai iya jefa kansa a cikin wani hali wata kila fushinsa da zuciyarsa su karu har aikata abun daba shi ke nan ba, wata kila kuma idan yayi addu'ar ya amsa masa ya tafi ya barta da bakincikin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login