Showing 39001 words to 42000 words out of 279257 words

Chapter 14 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34630

fasa tayun wani saboda ya mareta, ita dai ta san bata jituwa da Hamad suna yawan yin fada da samun tsabanin amman kuma yana nuna damuwarsa da kulawa a duk wani abu da ya shafeta, idan wani ya taba ta yana jin zafi fiye da yadda shi idan aka masa yake ji. Yasir ya shiga tambayar me ta yi ma bakon yayi mata marin da ya saka gilashinta fashewa.

 By Misteke na fito... 

Shi kansa be ji dadin jin karami dalili da be taka kara ya karya ba ya saka bakon marinta marin kuma mai zafi.

 Mutane ba su da hakuri kuma ba su da hakuri...

Ya rufe baki yayinda yake tura kofar falon ya shiga.

 Toh Wallahi ba zan dauka ba, wannan wulakanci da rainin wayon da Nafisa take min yayi yawa

 Me ya faru?

Yasir ya tambaya domin shi kadai ne be san wainar da ake toyawa ba. A take ta amaye masa cikinta tana wani cika domin ba karamin cin mutunci ne a gareta ba Momy ta zargeta da haka duk kuwa da irin rashin zama lafiyar da suke. Yasir ya kalli Hamad, Hurriya ma ta kalli Hamad Hamad ya kalleta kowa yayi shiru, shi dai Hamad ba zai yi laifi yace shi yayi ba, kuma idan an gano shi yayi hakan ba zai dame shi ba, Hurriya kuma ba zata tonawa dan'uwanta asiri ba, balle kuma Yasir da ko da yaushe yake kashe wutar fitina.

 Toh Hajiya Ki yi hakuri, dan Allah ku daina wannan fadan, bana jin dadi haka Appa ma ba dadi yake ji ba, kuma dai ba yara kuke ba be kamata ace kuna biye zuciya ba

Hajiya ta daki cinyarta

 Wallahi ba zan hakura ba, sai ta dandana kudarta, kuma Wallahi na fi karfinta bokanta yayi karya Wallahi, Iyami ma ta kara da ni ta bar ni balle ita bukkar banza, mai karyar arziki sai ka ce kanta farau arziki duk ta fi ta cikawa mutane gida da bakin kuri da iyayi ita diyar mai kudi, mun ji karuna duk arzikin ubanta be kai karuna ba, ni kuwa sai na zame mata fir'auna a cikin gidan nan

 Subhanallahi Hajiya dan Allah ki daina irin maganar nan haba

Yasir ya fada cike da damuwa, domin baya jin yadda matan ubansa suke samun tsabani a gidan.

 Babu ruwanka babu ruwanka idan ba zaka taya ni yaki ba karka sake shiga tsakanina da kowa, dan iya. Ke kuma yar gadon munafurci bace min da gani

Ta karasa tana watsawa Hurriya dake tsaye tare da Hamad harara, babu bata lokaci Hurriya ta juya ta fice daga falon, Hamad kuma ya tsaya a gurin kamar ba zai tafi ba, irin yadda yara masu fama da rashin kunya suke yi, sannan ya fice yana wani tukuki saboda saka sunan uwarsa a fadan da Hajiya Kaltume ta yi kuma ta kira Hurriya da yar gadon munafurci.




____________________

Masu karatun suna hango abun da nake hangowa? =?3?
Akwai Bomb fa ba karami ba? Fatan dai kun shiryawa tafiyar? =??

Idan kun karanta ku yi sharing >?p?
[10/18, 6:16 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: &A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2? 5?
?5?!?5??5??5??5??5?#?5?? 5??5??5?'?5??5?2?

Hello Habibaties =?
?>?p?
Amin kara please ku yi following dina a Arewabook. @khadeejacandy

https://www.arewabooks.com/u/khadeejacandy


5???5???5???5??? 1?? 1??

Hanya Hurriya ta hadu da Hamad ya zo zai kirata domin ita Hajiya Binta ta fara tambaya daga isowarta gidan.

 Me ya same ki? Hajiya na kiranki tana bangaren Appa

Ya tambaya kamar irin hankalinsa be tashi ba dan ya ga hawayenta.

 Momy ce ta yi baki shi ne namijin ya mare ni

 Me kika masa?

 Ban masa komai ba, kawai saboda na je fitowa da sauri shi kuma zai shiga na buge shi, shi kuma ya mare ni gilashina har ya fashe, da jikinki kamar itace mugu kawai

Ta farasa tana kuka ita ma kanta ciwo yake an karon da suka yi, balle kuma shi da bata san yadda ya ji ba.

 Ina yake?

 Yana bangaren Momy

Ta bashi amsa ta bar shi a gurin tsaye yana kallon apartment din Momy kamar mai tunani tafiya, ita dai ta yi gaba abinta, har Namra ma ta zo ta wuce Hamad na tsaye a gurin yana kallon part din. Hurriya na shiga bangaren Mahaifinta ta rungume Hajiya ta fashe da kuka. Hajiya Binta da tsayi ke neman gagararta sakamakon rikon da Hurriya ta yi mata kalli Alhaji Haruna.

 Kalli abun da ka yi

Appa ya sauke kansa kasa ba tare da ya ce komai ba.

 Allah ya kyauta

Hajiya Binta ta fada sannan ta taka a haka ta isa gurin kujera ta zauna Hurriya na rike da ita, har jikokinta da matar anta Momy suka shigo suka gaisheta, suka fita Hurriya bata dago daga jikinta domin ji take kamar Amman ce ta rumgume, wani gatan ma da kakanin suke mata Hajiya Binta da Gwaggo Amma bata mata irinshi.

 Kullum idan na zo gidan nan bangaren Iyami nake sauka, amman yau ka raba wannan a dole na sauka a nan, mace mai hankali da girmamawa, wannan matar ta san kimata, har abada ba zaka taba samu mace mai irin tarbiyarta ba tsoho

Appa ya sauke ajiyar zuciya domin ya san gaskiya Hajiyarsa take fada, iri irin Iyami masu son iyayen miji da girmamasu kadan ne a duniya ba su da yawa.

 Hajiya ga abinci ki bari na zuba miki

 Aa Hurriya zata zuba sai mu ci tare ai kasan da ita na saba cin abinci idan na zo

Appa yayi murmushi.

 Hurriya dago haka Hajiya ta ci abinci mana

Hurriya ta dago ta bude kulolin ta dauki plate ta fara zubawa. Sai a lokacin Appa ya lura da fashewar da gilashinta yayi.

 Me ya sami gilashinki Hurriya?

 Faduwa na yi

Ta yi karya kai tsaye. Hajiya ta kalli Hurriya sannan ta kalli Appa ta ce

 Kana da dai jin abun da Hamad ya fada min a mota, idan ba zaka dauki mataki ba ni zan zo da kaina na dauke yaran nan na maida su gidana, domin ba zan bari a rika wulakanta kamar wasu bare ba

Appa ya shiga mata rantsuwa domin kare kansa.

 Wallahi Hajiya, ban san da duk wannan ba, ai kin san idan na sani ba zan bari ba, ni kaina sai a yanzu nake ji a gurin Hamad din, kuma In Shaa Allahu zan dauki mataki, Hurriya me yasa baki fada min abubuwan da suke faruwa ba?

Hurriya ta kalli Appanta ta sauke kai ta cigaba da zuba abinci, daman ta sani ko da Hamad be yi ikirari ba zai iya fada balle ma har yayi.

 Wallahi ban sani ba, amman zan dauki mataki yanzu da yardar Allah

 Na dai fada maka, dan ba zaka saki uwarsu ba, kuma ka barsu ana musguna musu kamar wasu ba yi, har dokoki ake saka musu a gida, kuma duk tarin masu aikin gidan nan ace Hurriya sai ta share dakinta da na Hamad su sauran yaran ai ba haka take musu ba, shiyasa tun a lokacin da na ji ka saki Iyami na kira Nafisa da Kaltume na ja musu kunne akan yaran nan ashe na yi a banza, da Iyami ce ko ba zata jefar da magana ta ba

 Za a gyara Hajiya, amman dan Allah ki aje maganar daukarsu ko maida su gurinki, tun da Iyami ta bar gudan nan yaran nan kawai nake gani ina jin sanyi, idan kika dauke su karin wata damuwar ne a gareni

Hamad ne ya shigo falon rike da karamar wuka a hannu ya zauna kusa da Hajiya Binta ya aje wukar gefe.

 Me ya hadaka da wuka Hamad?

 Apple na yanka

Ya amsa tare da daukar spoon ya saka a abinci da Hurriya ta zuba.

 Hamad abinci Hajiya ne fa kana ganin na saka nama da yawa shi ne kuma zaka saka spoon

A take ya daka mata tsawa.

 Toh ina ruwanki da ni, ba zaki daina shiga min hanci ba ko? Hajiyar ta ki ce ke kadai

Hurriya ta kalli Hajiya tana turo baki alamar ta fusata.

 Hajiya kin gani ko?

 Kyale shi zuba mana wani

Hamad yayi kwafa, Hurriya ma ta yi kwafa daman tana da haushin marin da aka yi mata zuginsa be gama wucewa a kuncinta ba. Ai a take Hamad ya daga hannu zai kai mata duka Appa yayi saurin rikewa.

 Kai Kai Kai Kul daga magana sai ka ce zaka duketa, ita ce yayarka fa, ba zan daukar maka wannan ba Hamad, haka Iyami ke ta fama da kai kai baka san ka ragawa kowa ba?

 Amman Appa ai ita ta fara

 Yi mata hakuri kyaleta ai yar'uwarka ce baka da kamar ta, kyaleta

Ba dan kakarsa Hajiya Binta ta saka baki ba zai bar Hurriya ta zauna lafiya ba, hakan kuma be hana shi sake yin kwafa ba sannan ya fara cin abinci.

 Ni wannan zuciya ta Hamad ban san gun da daukota ba, fushinsa har tsoro yake ba ni

Appa ya fada yana shafa kan dansa, Hajiya ta ce.

 Zai daina kurciya ce, da zarar ya girma ya mallaki hankalin kansa zai daina, wani lokacin yara idan suna jin tashin balaga haka suke jin kamar daidai suke da kowa, ka bar shi ya cike 20 ko 18 fushin nan duk zai hauka

 Allah yasa, ya shirya mana

Hajiya ta amsa da Ameen. Sai da suka gama cin abinci sannan Hajiya ta tashi tare da jikokinta Hamad da Hurriya Appa na gafenta suka fito daga bangaren na Appa zuwa bangaren Hajiya Kaltume domin yi mata jaja da kuma barka da kubuta. Ko da suka shigo falon na Hajiya Kaltume yana cike da yayanta da kuma yayan yan'uwanta da ma ita kanta sai hira ake har da Namra. Kamar ta Allah haka Hajiya Kaltume ta washe baki tana maraba da zuwan Hajiya Binta.

 Sannu da zuwa Hajiya, ai da ma baki zo ba, ga kafafuwa suna ciwo ni kaina idan na warware ai sai na zo na gaishe ki, kuma ai kin kira waya haka ma ya wadatar

 Aa kara dai na zo, fatar na same ku lafiya

 Lafiya Kalau Alhamdulillah, ya ciwon kafafuwan yayi sauki?

 Alhamdulillah

Sama sama dai suka yi ta gaisawa Appa na zaune kusa da Hajiyarsa daga kasa, Hajiya Kaltume kuma na daga kan kujera ita da duka yaranta, Hurriya da Hamad ne kadai a kasa domin haka Amma ta koya musu idan babba yana kan gado ko kujera to su kuma su zauna a kasa, kar su zauna tare da shi ko kuma a yadda yake zaune. Da hira ta yi hira ne Hajiya Kaltume ta dauko zancen wahalar da suka sha a dajin tana fadar yadda aka rika mistreated dinsu kamar wasu dabbobi.

 Shiyasa ake son a samu soji masu kishin kasa da za su iya yakarsu idan ba haka ba, kasar nan da wahala ta gyaru domin Shugabannin ma sun zama sai a hankali

Cewar Yasir. Cikin murmushi Hajiya Binta ta kalli Hamad ta ce.

 Da yardar Allah Hamad soja zai yi, wannan fushi da zuciyar ta soja ce

Hamad ya girgiza kai.

 Aa ba soja nake so ba?

Namra ta ce.

 To me kake so? Wannan zuciyar taka Hamad ai soja ya dace da kai

 Aa ni Likitan idanu nake son zama, idan na kware zan yi ma Hurriya aiki ta, ita ma ta rika gani kamar kowa

Tsit katon falon na Hajiya Kaltume yayi domin babu wanda ya za ci abun da zai fito daga bakin Hamad kenan. Hurriya ta yi murmushi tana masa kallo irin na so da kaunar dan'uwa, ita kanta ba yi zaton Hamad yana sonta kuma ya kula da damuwarta har haka ba.

 Come here my friend

Yasir ya mika masa hannu, sai ya taso ya iso gurin Yasir din Yasir ya rumgume yana buga bayansa.

 Yayi kyau babban mutum


Cikin jindadi da alfahari Appa ya kalli Hamad ya ce.

 Da yardar Allah da yardar Allah, Hamad ba zaka yi karatu a kasar nan ba, waje zan kai ka ka sha ilmin akan idanuwa har ka gaji, da ikon Allah wannan kudirin naka sai ya cika ko da bana raye

Hajiya Kaltume da ta rasa abun da zata yi ta kalli Appa da murmushin dole.

 Za a karya dokar fitar da yara waje karatu kenan Alhaji akan Hamad?

 In Shaa Allah, ba shi kadai ba Hurriya ma ba zata yi karatu a kasar nan ba, yadda take da kokarin nan waje ya kamata ta yi karatu, kuma ko ba ni ba Principal dinsu ya fada min suna sa ran da zarar ta gama secondary school zata samu scholarship mai kyau a manya kasasshe saboda kokarinta da yadda take cin gasa ta bangaren lissafi

 Maa Sha Allahu, Allah ya nuna mana yara masu albarka Allahu akbar Allah dai yayi albar....ya bar zumunci

Sai ta kasa karasa da Allah yayi albarka ta canja zuwa Allah ya bar zumunci, domin ta san hausawa sun ce addu'ar makiyi karSaSSiya ce, ita ko ba zata so su yi albarka ba. Gashi abun da Appa ya fada cewar yaran Iyami za su karatu a waje ya daki zuciyarta mugun daka irin dakan da ace mashi ne, babu abun da zai hana ya bullo ta bayanta, yanayinta ma gaba daya sai ya sauya hankalinta yayi mugun tashi, ba dan ta yaki zuciyarta ba wata kila ma da ta rasa sukuninta har kowa ya gane halin da take ciki.

 Allah sarki dan'uwa mai kaunar yar'uwarsa, duk da fadan nan da kuke da rashin jituwa wannan soyayyar da kaunar tana nan a zuciyarsa, Allah ya kara hada kanku, ya shirya mana

Kowa ya amsa addu'ar da Hajiya Binta ta yi da Ameen ban da Hajiya Kaltume da gume ma ya karye mata kamar wadda aka kwancewa zane a kasuwa. Daga bangaren Hajiya Kaltume Hajiya Binta ta fito ta shiga bangaren Momy suka gaisa sannan ta fito tana jin kewar Iyami. Sai addu'a take ma Appa idan dawowar Iyami alheri ce Allah ya daidaita tsakaninsu, ya kasa amsawa da ameen bayan kuma abun da yake nema kenan a zuciyarsa. Mota daya suka shiga Hurriya bayan ta dauko mayafinta, ita da Hajiya suka zauna a back seat, Appa da Hamad kuma suka shiga gaba, Appa yana jan motar suka fi daga gidan.

After mintuna goma da tafiyar Hajiya Binta, Momy ta fito tare da bakuwarta da kuma Wanta da be ci komai ba a cikin abubuwan da Momy ta saka a shirya musu, Miwan na bayansu tare da dan'uwansa Musib sun yi ma bakuwar Momy da anta rakiya ban da Namra da har yanzu tana can bangaren Hajiya Kaltume.

 Captain ai yana yawan zuwa nan, duk lokacin da zai zo garin na ba ya tafiya sai ya shigo, ina jindadin haka Wallahi

Hajiya Turai ta yi murmushi.

 Ai danki idan yana son mutum to ya huta, Allah ya hada jininku

 Sosai kam, Allah dai ya nuna mana lokacin auren nan mu rakwashe

Cewar Momy, Mutumen da aka ta maganar akansa be ce uffan ba ya fara sauko Entrance din hannu dafe a kirjinsa yana murza a hankali domin ba karamin zafi ya ji ba a lokacin da suka yi karo da Hurriya, taku daya biyu uku hudu yayi kamin ya ja ya tsaya yana kallon yadda tsaddadiyar motarsa ta yi ta kasa gaba daya, saboda tayun motar da aka succe duka hudu. Ya juyo ya kallesu.

 Waya taba motar nan?

 Wace motar?

Kusan a tare suka kalli motar Musib yayi sauri sauka ya karasa gurin motar da mamaki.

 Lafiya kalau kuka zo da ita?

 Idan bata da lafiya zamu zo da ita ne? What kind of stupid question is this!

 Subhanallahi, garin ya haka ta faru!

Cewar Momy tana saukowa ta nufi gurin motar. Miwan ya ce

 Gaskiya wannan succe tayun aka yi

 To waya aikata haka? Wannan dai rainin wayo ne da neman mutum yayi magana ace ya cika masifa

Ya fada da karfi wani karin bacin dai na tunkarosa, cikin bakinciki ya sauka ta isa gurin motar. Momy ta kai hannu ta dafa karjikinsa.

 Kwantar da hankalinka Captain, a cikin yaran nan dai wani ba zai yi gigin yi maka haka ba, akwai dai matsalar da aka samu

Momy na rufe Hajiya Turai ta miko masa hannu kamar wani karamin yaro dan yaye.

 Captain shigo ka zauna, sai mu shiga wata motar

Ya sauke ajiyar zuciya tare da jan dagon numfashi ya fi sau goma, sannan ya shuri motar da kafarsa da karfi.

 Duk wanda yayi min haka da gangan yayi, saboda a bata min rai

 Toh waye zai maka haka Captain? Dan Allah karka bata ranka, na gano, yanzu haka ba zai wuce bakar matar can ba Kaltume, domin na dade da lura da yar bakinciki ce ta karshe

Momy tana maganar tana jin kamar ta yi tsalle taje ta shake wuyan Hajiya Kaltume.

 Oh kekam baki zaune cikin mutane kwarai Hajiya Nafisa, rayuwa a gidanku tana da wahala

Momy ta amsawa Hajiya Turai tana kwafa.

 Barta na san yadda zan yi maganinta, da ni take zancen, Captain yi hakuri shigo ka huta sai ka dauki motata ku tafi da ita, idan an gyara wannan Musib zai kai maka ita gida

Jameel ya juyo ya nufo hanyar falon, sai duk suka dugunzuma suka biyo bayansa, ban da Hajiya Turai da bata matsa daga inda take tsaye ba tun bayan da suka fito daga falon. Cikin natsuwa da kamala ya shiga falon, sai ka rantse ba shi ne ya gama bacin rai a waje ba, zaunawa yayi ya hade hannayensa ya sadda kai kasa ya rufe ido yana motsa bakinsa a hankali, kokari yake na ganin be bar bacin ransa ya ninku a zuciyarsa ba...
[10/20, 6:25 PM] Nana 5??5??5?'?5??5?2? 1: &A' 5???5???5???5???5???5???5??? A'&
? ? ? ? ? ? ? ? ?

5??5?2?

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login