Showing 108001 words to 111000 words out of 279257 words

Chapter 37 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34650

sannan ta tashi ta dauke kayan ta shiga da su dakin Hajiya.

 Aa daki dabam zamu yi, wake zama da kishiya daki daya

 Dole ne ki yi hakuri da ni Hajiya daki daya zamu zauna

 Toh aje kayan ki fito ki ci abinci, na san cikin nan naki yana nan dauke da yunwa

Kusa da gadon Hajiya Binta Hurriya ta aje luggage dinta sannan ta cire hijab dinta ta jefa saman gado ta juyo ta fito.

 Hajiya me aka dafa miki?

 Zai wuce tuwo ne Hurriya kin san abincin tsufi ai ba kamar ku ba, idan ma baki son tuwon ki shiga Kitchen ki dafa indomie

 Toh

Ta amsa sannan ta nufi hanyar Kitchen din, tun da ta shiga bata fito ba har sai da Indomie dinta ta dahu ta zuba a plate ta dauko ta fito. Aje plate dinta yayi daidai da shigowar Yasir falon hankalinsa a tashe yana ganinta ya dafa zuciyarsa ya nemi guri ya zauna.

 Kin daga mana hankali, na je gidan Amma baki can, na dawo gidansu Husna aka ce baki zo ba, na dauka wani gurin kika tafi

 Allah yasa dai baka dagawa Iyami hankali ba, domin ba su san abun da ya faru ba

 No naje gurin ne in a code way, ban fada musu abun da ya faru ba

 Dadina da kai ai akwai hankali, ka kyauta

Hurriya ta dube shi.

 Yaya ina wuni?

 lafiya kalau shi ne kika kama hanya kika taho a madadin ki kirani

 Yaya ko na kiraka Appa ba zai saurara ba saboda ransa ya bace sosai, kuma ba ni da wayar da zan kiraka ma

 Duk gidan nan ki rasa wayar da zaki dauka ki kirani?

Hajiya Binta ta shiga tsakani ganin kamar Yasir yana neman mada abun fitina.

 Aa ba haka ba ne, ita kanta bata cikin hayyacinta a lokacin da ta baro gidan saboda tashin hankali, ta ina zata tsaya neman wayarka ma, kuma kana jin tana fadar cewar yayi fushi ba zai saurara ba

 Tsohuwa kokari kareta kawai kike yi, amman? da ta kira ni ai ba zata baro gidan ba, yanzu da wani abun ya sameta fa

 Laifin waye ba na mahaifinka ba? Akan me zai korota a dare yace ta tafi ta bar masa gida kamar wadda ta yi cikin shege

 Ita ma tana da laifi ai, Hajiya ta fada min duk abun da ya faru ba zai yiyu ka zauna ka yi ta fadawa kawa karya da gaskiya ba, gashi yanzu har mahaifinta ta dauko kafa ya zo ma Appa da wani zancen banza

Hajiya ta tabe baki.

 Uwarka kuma dai ai ba zata fada maka gaskiya ba, karya da gaskiya zata hada ta fada maka saboda ka yarda da ita ta karyarta Hurriya ka san sai ba son Hurriya suke ba

 Haba Hajiya wace irin magana ce wannan? Wannan ai hadin fada ne, sai ki hada Hurriya da Hajiya ta dauka ko gaske ne

 Yasir kai ma kasani da Khairiyyah ce ko Salma ko Rumana aka kora a gidan nan kana ganin Kaltume zata yarda ta fito a dare kamar wannan?

 Sai da na yi mata magana tace min ita ma bata san fitar Hurriya ba

Hajiya ta tabe baki, Hurriya kuma tana cin indomie ziri ziri. Yasir ya mike tsaye ko da ace Hajiya Kaltume karya ta fada masa ba zai so ya zauna a gurin da ake zagin mahaifiytarsa ba, domin komai lalacewarta mahaifiyarsa ce.

 Alhamdulillah tun da tana nan, ni zan tafi idan Appa ya huce sai na dawo na dauketa

 Toh a gaishe da gida

Hajiya Binta ta fada tana raka shi da kallo, Hurriya ma ta dago kai ta kalleshi.

 Yaya sai da safe

 Sai da safe

Ya amsa ba tare da ya juyo ba.

 Ina zata fada maka gaskiya, wannan Kaltume ba baki na yi mata ba, amman da wahala ta gama lafiya

Hajiya ta fada bayan ya fice. Hurriya dai bata ce komai ba, ta cire hannunta daga taliyar tana kallon wani gafen na dabam, zuciyarta na raya mata yayanta ma yayi fushi da ita a yanzu.


WASHE GARI....

_Barka da safiya Namra, fatar kin tashi lafiya ya su Mama da Daddy, And my beautiful Young Lady, hope kowa yana kalau, a mika min gaisuwa gurin gimbiyar please_

Ta aje wayar a hankali bayan ta gama karanta sakon ta manhajar whatsapp dinta, sai ta nufi windows dinta ta bude curtains din tana kallon kasan bene zuciyarta na gabato mata da wani abu na rashin dadi da bata san dalilinsa ba.
Me yasa zata ji haka, shi ne abun da ya fara zuwa mata a rai, daman ai be ce yana sonta ba balle har tace ya koma gurin kanwarta ne. But at first alamunsa sun nuna ni yake so. Wata zuciyar ta fada mata. Ta kai hannunta tana taba karamar sarkar dake wuyanta.
Yana yawan tambayar Hurriya, amman ban yi zaton ita yake so ba, ko kuma dai ya juya kanta ne saboda ya ga ta fini kyau. Sai kuma ta juyo tana kallon dakin kamar wani bakonta sai sake sake take a ranta, wai it's normal ya so Hurriya domin be furta mata so kai tsaye ba, but why take jin babu dadi so disappointed? It's because of ta fara sabawa da shi kwana biyu, the way he approached her gashi da saka nishadi da iya kula da aika ko kuma saboda tana tsamanin ita zai ce yana so.

Ta bar jikin windows din ta nufi gurin da ta aje ledar da ya kawo ma Hurriya ta bude ledar ta ciro waya tana dubawa irin wyar Momy ce sak daga kala har model. Ta sake saka hannu cikin ledar ta ciro Perfume set masu kamshi sosai. Sai da ta shaka turare sannan ya maida komai yadda yake, ta nufi wayarta ta dauka. Ta rubuta masa.
_Bata karbi komai ba, na yi try bata karba ba, tace na aje maka_

After ta yi sending sakon sai kuma ta ga kamar be dace ta yi haka ba, but me zata yi? Ta karba da sunan Hurriya ta karba, yayi ta jiran kiran Hurriya ya ga shiru, ai kara ta fada masa gaskiya, ta jefar da wayar a kan gado tsakanin faduwar wayar da shigowar kiran Salim ba za a iya fadar wanda ya riga wani ba. Hannu ta kai ta dauka ta danna picking

 Are you free mu yi magana?

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa masa.

 Eh ina jinka

 Me yasa bata karba ba?

Ta daga kafadunta kamar ance nata yana tsaye gabanta yana kallonta.

 Ban sani ba, maybe she's not interested, kuma bata shirya ma hakan ba, domin wani be taba nuna yana som Hurriya ba, so ina tunanin ba abu ne mai sauki ta karbi abun ba, saboda tana da banbanci da mu, tana ganin abubuwan differently

 Amman da kika fada mata ya kika ga reaction dinta?

 Not good... Not Bad...

 How do you think zan iya shawo kanta

Ta taka zuwa gaba tana shafa goshinta.

 Ina ganin kamar ba a takurawa mutum akan soyayya she's 19yrs idan tana ra'ayinka zata sani

 Or Maybe i can talk to her by myself? Ya kika gani na fahimtar da ita abun da ke zuciyata kuma na nuna mata ba da wasa na zo nan ba, ko kuma kina ganin sai mun fara daukar permission gurin iyaye? Maybe ita ma zata fi yarda da ni

Ta yi shiru kamar mai tunani.

 Karka yi saurin tafiya gurin iyaye, ka fara magana da ita ka ji ta bakinta, domin Appanmu baya daukar komai da wasa

 Okay zan yi haka, zan shigo yau da dare ko na zo yanzu

Ya lumshe ido ta bude jin yadda yake rawar jiki.

 Da dare zai fi sirri, domin bata nan jiya ta koma gurin kakarmu da zama, zan kwatanta maka gurin

 Zan fi jin natsuwa idan muka tafi tare, and Kakarta ma zata fi daukar abun da muhimmanci, idan kina ganin babu matsala zan fara zuwa na dauke ki sai mu tafi tare

Samun kanta ta yi ta saka bijirewa rokonsa, duk kuwa da zuciyarta ta raya mata haka, domin tana son ta cire kanta ne daga duk wani abu da ya shafe shi a yanzu saboda ya nuna ba ita yake ra'ayi ba.

 Shikenan Allah ya kaimu

 Ameen thank you

Ta sauke wayar tana kallon kiransa har sai da ya yanke sannan ta dauke fuskarta tare da ajiyar zuciya. Bata kara raina kanta ba sai bayan Sallah Isha'i a lokacin da ya kira wayarta ya sanar mata yana waje yana jiranta, sanin ba dan ita ya zo ba, ya saka bata cilastawa kanta shafa ko da hoda ba, balle kuma ta canja tufafi ko saka turare. Tun bayan wanda ta saka sa rana bata sake saka wani ba, mayafi kawai ta dauka ta yafa a saman gowns din atamfar dake jikin sannan ta saka shoes din da suka yi shige da atamfar. Sannan ta fito dakinta ta nufi dakin Momy, kamar jiya yau ma waya ta same ta tana yi. Daga bakin kofar dakin ta tsaya rike da kofar

 Momy zan leka waje ina da bako?

Wani kasaitaccen murmushi ya bayyana a fuskarsa Momy, ba tare da ya yanke kiran ba ta ce.

 Haka nake so, na jiya ne ko wani dabam?

 Shi ne na jiya

 Yayi kyau, amman ki sake fuskar mana, ki yi far'a ba fuskar damuwa ba

Ta amsawa Momy da kai, Momy ta kara mata da cewar.

 Make sure kuma wanda ya cancanta ne, kin san dai waye iyayenki

Nan da kai ta amsa mata, sannan ta juya ta fice idonta na cika da hawaye a karo na biyu. A jiya ta kwadaita ma Momy cewar gurinta aka zo, saboda zatonta ne, yanzu kuma Momy ta sake zaton hakan a karon kanta. Har ta fito falon rike da wayarta a hannu bata daina fadawa kanta ajinta ya wuce ta tsaya irin wannan tunanin da damuwar akan namijin da ba shi ne autan maza ba, kuma ba ita ce a gabansa ba. A kokarinsa na karramata ya fito daga motarsa ya zagaya ya bude mata front seat, tana kusantar gurin da motar take buri na kusantota. Bude mata motar kawai da yayi kamin ta karaso wani abu ne da ba a taba yi mata ba, and to her wani abu ne dake bayyana halinsa na kula da mace yadda ya kamata.

 Barka da dare

Kamar wanda ta fado daga wata duniyar haka ta farko daga duniyar tunaninta ta dan kalleshi and a lokacin ne ta fahimci ta karaso kusa da shi.

 Barka dai

Ta amsa a takaice fuska ba yabo ba fallasa sannan ta shiga motar ta zauna, shi kuma ya rufe murfin motar gently, sannan ya zagaya ga shiga bangarensa, ya kalleta bayan ya rufe bangarensa ?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? yana tunanin ko zata masa wani karin bayani ko shawar before su tafi.

 Za mu oya tafiya?

 Da gaske umarni na yake jira? Wai duk wannan na miye ne? Meye haka? Why why?

Ta tambayi kanta, a zahiri kuma sai ta amsa masa ba tare da ta yarda ta kalleshi ba.

 Yea...

Yayi baya da motar tare da juya kanta sannan suka fice daga gidan.



HURRIYA POV.

Hurriya na kwance jikin Hajiya Binta tana game da keypad dinta, Hajiya ta ce.

 Wato da wani gurin kika fada shi ke nan babu wanda zai biyo bayanki ya binciki lafiyarki, shi sun rufe masa ido su kuma babu wanda Allah yake ranta kowace daga ita sai Yayanta take hange

 Haka kwanan baya suka laka min sata, Momy ta ce na sace mata sarka da kudi, kuma ban dauka ba, amman Hajiya ma cewa ta yi wai zan iya yi saboda na canja hali, Appa ne kawai ya wanke ni, da Allah kadai ya san dukan da zan sha a gurin Yayana tun da shi ne mai hukunta mutane, kuma da kowa sai ya rika kallo a matsayin barauniya

Hajiya Binta ta daki kirjinta.

 Sata Hurriya? Sata dai sata? Ke Nafisa ta zarga da sata?

Hurriya ta tashi zaune tare da amsa mata da kai.

 Har da cewa ta yi ba zata bari da Allah ba, amman ni dai har yanzu ban ji ance an gane barawo ba

 lallai rashin uwa a gida kukumi ne, saboda suna ganin baki da kowa shi ne suke kwaso sharar sai ya sauke kanki, ai baki gadi sata ba Hurriya uwa da uba, yanzu da uwarki bata da rai haka mutanen nan zasu rika ki? Ke ta ce kin satar mata?

 Sakar zinari da kudi mai yawa, har da sarkar Yaya Namra kuma ban shiga dakin kowa ba... 

Ta fadawa Hajiya yadda komai ya faru, idon Hajiya Binta ya cika da kwalla.

 Ashe haka kike ta rayuwa cikin matsuwa a gidan nan? Duk fadin gidan nan da ma'aikatan cikinsa a rasa waye za a zarga sai ke?

 Ai Appa ya wanke ni yace ni ba barauniya ba ce

 Me yasa baki fada min ba? Amman ko yanzu bata bace ba

Hurriya ta kalleta da sauri.

 Hajiya ai ya wuce

 Be wuce ba, uwarki bata min komai ba sai alheri, Allah ya mata albarka ya bata lafiya, ta kula da ni kamar ni na haifeta, ba zan taba bari yayanta su wulakanta ba, ba zancen sata kadai ba ko wannan korar da aka yi miki ba zan kyale ba, domin idan aka kyalesu nan gaba za su aikata wanda ya fi wannan ma, gobe zan yafa mayafina na tafi duk sai na ci musu mutunci

Hurriya ta fasa kuka da yafi kama da shagwaba.

 Hajiya Wallahi zaki ja min ne kawai ace na zo na yi minahicci

 Uwarki bata min komai ba sai alheri, matukar ina raye ita ko yayanta ba za su wulakanta ba

 Aa Hajiya ni dai dan Allah kar ki yi

 Ba gidan zaki koma ba balle su ganki su wulakantaki, nan zaki zauna kuma yadda wannan abun ya tsaya min a rai idan ba amayar da shi ba ba ni da kwanciyar hankali

Duk yadda Hurriya ta so lallaba Hajiya Binta ta hakura da maganar, bata saureta ba.

 Ni da na sani ba zan fada miki ba Hajiya

 Ai shi yake cutarki, ta nan kika sha banban da dan'uwanki, Hamad komai aka yi masa sai ya rama kuma sai ya fada min, bawan Allah Allah ya masa rahma

 Ameen

Hurriya ta amsa cikin rashin ji dadi tare da daga kai ta kalli kofar falon da Namra ta turo ta shigo da Sallama.




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar? MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne? cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai? shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
5?
?5??5??5??5??5??5? ?5?? 5??5??5?
?5??5??


Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


5??5??5? ?5?? 1?? 9?


 Yau Namra ce a gidan na mu

Hajiya ta fada tana kallonta, cikin karfin hali Namra ta yi murmushi ta nemi guri ta zauna. This is the first time da ta ji bata sha'awar hada ido da Hurriya.

 Hajiya barka da dare

 Barka, yau na ci arzikin Hurriya kin zo gidan nan kenan

 Haba Hajiya daman can na kan zo na duba ki fa, karki ce saboda Hurriya na zo

 To ssboda wa kika zo tsakaninki da Allah?

 Sabosa Hurriya

Cewar Namra tana dariya, Hurriya kuma dadi ya cika ranta jin cewar yar'uwarta ta biyo sawunta, sai dai abun da bata sani ba shi ne ba tafiyace ta zuwa gurinta kai tsaye ba tafiya ce ta Salim ba dan ita ba.

 Yaya Namra ina wuni

 Lafiya Kalau Hurriya

Ta amsa tana murmushin da ya fi kama da an mata dole.

 Ato ke dai kin kyauta da kika biyo sawu, daman ke kin fita dabam ba da yan'uwanki, amman Nafisa kam da Kaltume rayuwarsu tana ba ni mamaki, yanzu Hurriya ta gama karanta min abun da ya faru, ashe abun har ya kai a laka mata sata Namra?

Namra ta kalli Hurriya ba tare da tace komai ba ta dauke ido.

 Ban yi zaton zamu yi ma yarinyar nan haka ba, saboda kawai bata da uwa cikin gida sai ta zama abar wulakantawa, ban jidadi ba, yanzu ko korar nan da aka yi mata da ke ce ko Khairy ai babu wanda uwarta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login