Showing 132001 words to 135000 words out of 279257 words

Chapter 45 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34711

wanda ya ce komai. Momy ce ta fara mikewa tsaye.

 Bari mu baku guri ku ci abinci

Namra ta bi bayanta suka haura sama, haka Salim ya bi abincin da aka jera musu ga kuma plate din plantain da Captain ya saka hannu ya dauki daya.

 Ni zan tafi Captain, bana jin zan iya cin komai kuma sai da na ci abinci sannan na fito, ya kamata na tafi

Ya mike tsaye tare da kallon ledodin dake gefen kujerar da suka zauna.

 Ka shigar mata da wannan

Captain ya dan motsa baki irin na wanda ya rasa abin cewa, ya bi Captain da kallo kamin ta mike tsaye ya bi bayansa.


HURRIYA POV.

Kofar windows dakinta ta tsaya tana kallon kasa, har lokacin gabanta be daina faduwa ba arba da ta yi da Salim da kuma mutumen da har yanzu bata san sunansa ba.
Each seconds sai ta juya ta kalli kofar dakinta tana jiran ta ji ko za a kwankwaso mata ace ta fito, gashi idan Momy ce ba ta isa ta ki fitowarba, hankalinta be kwanta ba sai da ta hango fitowar Salim, ta yi baya baya kadan daga windows din gudun kar ya ganta, sai kuma ta ga mutumen da yake tare da shi a dazun ma ya fito. Da sauri ta bar jikin window din ta cire dankwalin kanta ta jefar a gado ta bude kofar ta sauka kasa ita a nufinta ta samu abun da zata sakawa cikinta kamin ta su dawo ko kuma a cilasta mata fitowa a dakin da take da niyar shiga ta rufe kanta. Ganin babu kowa falon ya saka ta taka a hankali ta leka Kitchen nan ma babu kowa, ta dawo dinning har ta fara bude warmers sai kuma wata zuciyar ta raya mata cewar za a iya ganewa ita ta ci abincin ganin ba a taba shi ba, a take ta rufe ta dauki plate daya ta nufi abincin da aka jerawa baki ta zuba white rice ce da ta ji green beans da carrots sai pepper soup din hanta da aka yanka kanana kuma aka saka kaza sai kamshi take, ga plantain da aka soya. Komai sai da ta zuna, Jin kamar motsi a sama wato stairs ya saka ta dauke plate din tana kallon stairs din ta watsa da gudu kitchen ta rufo kofar.

Ta aje plate din a tana auna abincin da hannu biyu, idan ta ci da dama sai ta ci da haka bata ma tsayawa ta tauna burinta kawai ya kai ga cikinta kamin asirinta ya tsonu. Wani irin kuka ne ya tunkaro da ya fi karfin duk wani kokari nata na son hana kanta kukan saboda tausayin kanta, a take ta fashe da kukan marar sauti hawaye shar kamar magudanar ruwa. Kamar daga sama ta ji an bude kofar kitchen din tana kallon kofar suka yi ido hudu da Captain da shigo a zatonsa Momy ko Namra ce a ciki saboda ya ji karar rufe kofar a daidai lokacin da ya dawo falon.

Baya baya ta yi shimkafa a duka hannayenta guda biyu ga kuma bakinta ma cike da wata shimkafar ga fuskarta da ruwan hawaye suka yi mata ado, ka a ganinta ka san a firgice take. Be plate din da be gama zaunawa ba ne ya fado kasa saboda jikinta ya tana plate din kadan a lokacin da take yin baya baya, a take plate din ya fado ya fashe a kasa..

 Waye a kitchen waya fasa plate....?

Namra dake saukowa ta tambaya domin ta ji karar faduwar plate din na Momy mai tsada. Hurriya ta dauke numfashi da mugun karfi saboda tsoro. Captain yayi baya kadan ya leka falon ya amsawa Namra.

 Ni na fasa

 Subhanallahi Allah yasa baka ji ciwo ba?

Ta sauko da sauri, sai amsa kamar yadda ya saba amsawa mutane magana wani lokacin da bakar magana musamman idan baya son a shigar masa sabga.

 Na ji ciwo kin san ai yaro ne ni...

Tana jin haka bata karasa gurin ba, sai kawai ta yi murmushi tana masa wani kallo har lumshe ido take.

 Allah ya baka hakuri

Ta juya ta fara hawa sama domin sanar da Momy abokinsa ya tafi Captain ne kawai. Sai da ta haye sama sannan ya juyo ya kalli Hurriya a take ta hade sai ta zubar da shimkafar a kasa ta hade hannayenta biyu waje daya ta daga su tana masa godiya tana kukan da ba shi da sauti sai hawaye. Kamin ta duka zata fara kwashe breaking plate din.

 Zo ki wuce

Ya fada yana matsa daga jikin kofar ta yadda zata samu hanya. Ta dago ta kalleshi ta girgiza kai

 Idan Momy ta gan ni a kitchen dinta sai ta kusa kasheni tace kar na sake shiga

Tana fadar haka ta mike tsaye ta nufi kofar baya ta bude ta fice. Juyawa yayi ya fice daga kitchen din kai tsaye ya nufi stairs ta nufi dakin Momy direct, yana dora hannunsa a jikin kofar zai murda kunnuwansa suka jiyo masa wani sauti na Momy da Namra yana fita.

 Wani sabon iskanci ya taso mata ba? Ai Wallahi sai na hanata numfashi a idan nan, saboda tana ganin tana da kyau dole maza su fara binta ganin take yi tana daidai da ni yanzu

 Daman laifin na waye ne Namra ba naki ba, ki rika jan yarinya a jiki matsayinku ma ba daya ba, uba kawai kuka hada balle kuma yanzu da take munafurci, gashi har ta samu bakin fada miki magana, da yaran Kaltume me da yanzu ba su sumar da ita ba, shiyasa ai bata yarda ta zauna a bangaren Kaltume ta shan wuyar da take sha a hannunsu

Cewar Momy tana mikewa tsaye. Namra ta ce

 Ko a nan sai na zahira ya fita jindadi, ai na riga da na gane halinta a yanzu

Slowly Captain ya dauke hannunsa a kofar ya juya ta fara sauka ba dan ya gama jin komai ba, sai dan baya bukatar jin wasu abubuwa da yawa a yanzu, daman he just want to talk to her akan Hurriya ya ji ko laifi ta yi Momy take mata hukunci da wannan. Be karasa sauka ba Momy ta bude kofar dakinta ta fara saukowa Namra na bayanta.

 Captain...

Ta kira sunansa da mamaki ganin ya rage few steps ya sauka. Sai ya juyo ya kalleta.

 Haurowa ka yi? Wani abun kake bukata ne?

 No da zan shigo ne sai kuma na ce bari dai na tafi kawai

 Sorry Namra ta fada min kana falo ban fito da wuri ba, abokin naka ya tafi?

 Yea ya tafi

Ya sauka ya tsaya a daidai inda suka zauna dazun tare da Salim, Momy ma ta sauko tana fadin.

 Ai da ma zaka ba shi shawara ya fita safgar yarinyar nan, wani rashin mutunci ne take ji yanzu, ko da yake ni ban ki ta samu miji an mata aure ta bar bangaren nan ba

Kamin Captain yace wani daman kuma ba shi da niyar fadar wani abu akan maganar. Hurriya ta turo kofa ta shigo falonta ta kofar da ake shigowa, bayan ta bata lokaci a Garden ta wanke hannunta a fanfo da fuskarta. Gaba dayansu dubansu ya koma kanta, tana isowa tsakiyar falon ta kalli Momy sai kuma ta yi saurin kauke kai kasa ta nufi hanyar stairs.

 Ke zo ki dauki abincin nan idan zaki ci

Captain ya fada in a game way, yana binta da kallo, ita ma juyowa ta yi ta kalleshi kamin ta kalli Momy dake kallonta.

 Zo ki dauka mana

Ya saka fada ganin tana jiran umarnin Momy, Namra ta yi karaf ta ce.

 Domin ku fa aka yi?

 To ai shi ya tafi be ci ba, kuma ni ma a koshe nake maybe next time

Hurriya na jin haka ta dawo ta duka a gurin ta dauki plate ta zuba rice din sai karamin bowl ta zuba miyar sai da tsame rabin naman kazar dake ciki miyar sannan ta dauki cup ta zuba fresh apple juice da Namra ta hada ta dauki wani plate din ta zuba plantain duk abun da ta zuba wanda ta san zai isheta ne har anjima, sannan ta dauka ta mike tsaye.

 Na gode

Ta furta with sweet voice dinta tana musa laSSanta masu kyau. Sannan ta nufi stairs sai da ta kusa haye sannan ta juyo ta kalleshi ta juya ta cigaba da tafiyarta.




Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar? MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne? cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai? shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃? 25
 Baka dai ci abincin ba

Ya kalli Momy yana saka hananyensa aljihu.

 Abokina ya tafi ransa a bace, taya zan zauna ni na ci abinci? Maybe next

Ya kalli Namra dake tsaye ya kira sunanta.  Namra

 Hmmm

 Be a good girl please

Ta yi murmushi mai kyau.

 I will as always

Ya mayar mata da murmushi sannan ya juya ya nufi kofa, da kansa ya bude ya fita Momy ta take masa baya ita da yarta. Momy na nade hannayenta ta aika masa tambaya.

 Sai yaushe kuma Captain

 Anytime kina iya ganina ma anjima, ai yanzu ina garin nan har na tsawon wata uku kuma ina tunanin wannan ne best place da zan iya zuwa na yi yadda nake so, ba kamar a bariki ba

 Me yasa ba zaka dawo nan gaba daya ba?

 Ban sani ba ko za a su bar ni zan gwada haka

Ya bude motarsa bayan ya amsawa Namra sannan ya shiga yayi mata key, Momy na daga masa hannu Namra kuma ta bishi da kallo da murmushi har ya fice. Momy ta juyo ta kalleta.

 Wata kila ya jidadin yadda kika karbi bakonsa a yau

 Ni ma na ga alama

 Yayi kyau

Momy ta fada tana murmushi sannan ta sauke kai kasa ta juyo cikin tafiyar kasaita ta shiga falonta. Namra ta dade a gurin tana ta karatun wasikar jaki kamin ita ma ta juya ta koma ciki. Hurriya ta ci abincinta yadda take so, sauran ta saka dayan plate din ta rufe domin idan ta tashi ci anjima ba ta nema ba, kusan ita da marainiya duk daya agidan, wata kila ma marainiya ta fita gata da samun kulawa. Hakan ya taimaka mata bata fito neman abincin dare, shimkafar ta sake ci da dare ta kwanta abunta. Da safe ma bata fito gudun kar ta yi wani laifin ko kuma Momy ta rufe ta fada saboda ta zuba abinci da yawa ta kwashe nama, tana zaune a dakin har karfe goma na safe, tana unkurin tashi ta yi wanka aka turo kofar falon aka shiga, da sauri ta kalli kofar tana zaton ganin Momy ko Namra ga mamaki sai ta yi arba da Khairy.

 Yaya Khairy

 Na'am Hurriya yanzu kika tashi?

 Tun dazun amman ban sauko ba sai yanzu

 Kin yi breakfast?

 Aa

 Ni ma ban karya ba, zo muje mu karya bangarenmu, idan mun gama ina son ki rakani wani gurin kin ji

Ta dan yi shiru kamar mai tunanin yadda zata amsa mata kamin ta daga mata kai.

 Okay

Ita kam gaba da ta kai ta ko ba komai zata karya, ba kamar jiya ba, already ta san Momy ko masu aikinta za su ce mata abincin safe ya kare kamar jiya, gashi kuma bata isa ta ce zata shiga kitchen ta girka ba ko ta saka a girka mata. Dan haka ta sauko saman gadon suka fice a dakin tare da Khairy, kamin su isa bangaren Hajiya Kaltume Khairy ta kama hannunta ta rike tana bata labarin guraren da za su da kawayenta da ta kwana biyu bata hadu da su ba. A dinning suka zauna ita Khairy da kanta ta hadawa Hurriya tea ta zuba mata komai na karyawa. Hurriya na tauna wainar kwai zuciyarta na raya mata akwai abun da Khairy take shirya mata, domin a iya saninta Khairy bata tana sonta ba ko na rana daya, idan ma kowa zai raga mata a gidan ban da Khairy amman me yasa take nuna mata kulawa tana janta a jiki yanzu? Anya ba wani abu take shirya mata ba? Ta mike tsaye sai Khairy ta kalleta da sauri.

 Ya aka yi baki sha tea ba fa?

 Ruwa zan dauko a kitchen

 Zauna bari na dauko miki

Ta mike tsaye, Hurriya kuma ta koma ta zauna tana kallonta, Khairy na shiga kitchen ta dauko ruwan da cup ta fito, sai mamaki ya kara rafe Hurriya. Haka dai ta karya ba dan zuciyarta natsu da yadda Khairy take mata ba.

 Yaya Khairy saboda Adam ne?

Khairy ta kalleta

 Ban gane ba?

 Kike min haka kuma kike son na rakaki mu fita

 Haba Hurriya Adam din da Appa yace kar ya sake ganinki da shi, kuma yaya ma yayi gargadi akan haka, shi ne zan hadaku? Na rantse miki da Allah indai ni ce ba zaki taba ganin na kawo miki Adam da idonki biyu ba, haba Hurriya kawai ina kokarin ganin na kyautata miki ne, ni yar'uwarki ce be kamata ace muna samun tsabani ba, kin ga yanzu ni aure zan yi, duk kuwa da ba a saka rana ba, amman ban san ya rayuwata zata zama a gidan auren ba, kuma hausawa suna cewa idan kana son gani da kyau to ka aikata mai kyau, and trust me daga yanzu an fara kenan har gaban abada da yardar Allah sai kin ji cewar baki da wata yar'uwa kamar ni a duniyar nan

Hurriya ta dan yi murmushi ba dan ta yarda ba.

 Amman ina tsoron wani abun da zai saka Appa yayi fushi ko yayi fada, musamman ma ni na batawa Appa rai da yawa idan an sake ban san abun da zai biyo baya ba

 Hakan ba na fatan ya faru, komai zai zama labari Hurriya, tashi ki shirya da wuri dan bana son mu yi latti

 Tou

Ta tashi cikin sanyi jiki ta fice daga falon, ko da ta dawo bangaren Momy mai aikin gyara dakuna ta gyara mata dakinta ta fitar da plate din da ta ci abinci. Tufafinta kawai ta cire ta fada bandaki ta dauki lokaci a bandakin dakin tana Khairy, bata son zafafawa akan negative mind, dan haka take kyautatawa yar'uwarta zato. Ko da fito wanka wani bachi mai dadi ke ziyartarta haka dai ta murje ido ta hana kanta bachin ta shirya cikin ready-made bata damu da daukar jaka ba ganin bata da kudi ko wayar da zata saka a ciki, ta fito tana tafiya a hankali har ta sauko falon. Gaban Momy dake zaune a falon ta fara risinawa ta gaisheta.

 Momy ina kwana?

 Lafiya kalau

Ta amsa mata a takaice.

 Zamu fita da Khairy tace na rakata wani gurin

Nan kam Momy bata ce mata je ko karki je ba, balle ta tambayi inda za su je, a lokacin da Hurriya ta gaji sai ta mike tsaye ta fice daga falon ga bachi ga hawayen da suka cika idonta suna son zubo mata, ba dan komai ba sai dan abin da Momy ta yi mata, ta tabbatar da uwarta ce ba zata bari ta fita ba ba tare da ta tambaye ta me za su je yi ina za su je yaushe za su dawo, ko ma ta hana ta zuwa gaba daya. Amman bata yi ba saboda ita din ba uwarta ba ce

 Na yi marmarinki Amma

Ta fada tana tsayawa ta kalli bangaren da mahaifinyarta dake zama a da.

 Na yi marmarin rayuwarmu ta baya, a lokacin da kike nan kuma kike cikin koshin lafiya da farinciki, Hamad ma yake nan

Ta sauke ajiyar zuciya tare da saka hannunsa ta share hawayen da suka zubo mata, sannan ta dauke kai ta shiga bangaren Hajiya Kaltume kamin ta karasa kofar falon Khairy ta bude kofar ta fito da nata shirin tana rike da keys din mota.

 Oh yanzu fa nake cewa zan biya na kiraki na ga kin dade ga garin da hadari

Hurriya ta daga kai ta kalli sama dake cike da hadari da alama za a iya sako ruwa at any time kuma za a iya yaye hadarin duk cikin ikon Allah ne da abun da ya zo. Ta sauke kai tana hamma.

 Bachi ma nake ji?

 Bachi yanzu? Ko zaki koma ki kwanta next time sai mu tafi

 No mu tafi kawai zai sake ni ai

 Okay

Suka nufi motar Khairy sai da ta fara shiga ta yi mata key ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login