Showing 177001 words to 180000 words out of 279257 words

Chapter 60 - HURIYYA Complete Hausa Novel

07 Oct 2024

34698

murmushi sannan ya aiko mata da sako.

 Za ku ji ba da jimawa ba Momy. Hurriya tana lafiya Momy?

 Hurriya???

 Na dauka zaka tambayi Namra ne

Ya turo mata murmushi shi dai yana kokarin isar mata da sakon zuciyarsa cikin hikima tun da har ta fada masa Ammynsa ta tsegunta mata wani abu a kansa.

 Duka daya ne Momy

 Aa ba daya ba ne, Namra yar 'uwarka ce jininka zaka iya juyata yadda ka ga dama ka tambaye ta ko ka saka ta yin wani abu, amman Hurriya baka da alaka da ita

 Alakar musulumci ta fi ta jini

Momy ta kashe data ta aje wayar da mugun mamaki a fuskarta. Kar dai ace abun da Namra yake hasashe ya tabbata kar dai ace Hurriya yake nufi da yarinyar? Idan ba haka ba me ya kawo zancenta a yanzu. Ta sake daukar wayarta ta bude data ta masa reply.

 Haka ne, amman ina son ka sani babu wata alaka tsakaninka da Hurriya, ya kamata ka sani matsayinku ba daya ba

Wannan karon bayan ya karanta be sake ce mata komai ba har ta gaji ta aje wayar ta mike tsaye fice daga dakinta. Dakin Namra ta shiga sai ta same ta kwance kan gado tana waya.

 Aje wayar nan ina son magana da ke Namra

Namra ta tashi zaune tana kallon Momy da already ta zauna gefen gadonta.

 Me ya faru Momy?

 Tafiyar da Hajiya Turai ta yi a yanzu ta fada min wata magana da Captain ya fada mata, na yi zaton da ke yake, sai dai a yanzu da na ke chat da shi sai ya ke tambayata ina Hurriya?

Namra ta yi murmushi.

 Ai na fada miki Momy baki yarda ba

 Ba wai yarda ne ban yi ba, ina ganin dai kamar Captain ba zai tsaya kula yarinya irin Hurriya ba

 Saboda me? Ga alama ya bar mana kamin ya tafi? Kuma shi Captain ba irin rayuwarku ce da shi ba, be cika duba arzikin gidansu ba

 Ba zan bar wannan ba

 To ya zaki yi Momy? Ba ayi ma Captain dole kuma iyayensa suna son farincikinsa fiye da na su babu wani abin da zamu iya yi

 Iyayensa sun fi ni kyamar talaka, kuma Hajiya Turai ta san yadda nake da Hurriya dan haka ba zata yarda danta ya aure ta ba, bana ma tunanin auren zai yiyu domin Captain baya iya jure komai, daga yanzu ina son ki yi duk wani abun da zaki dauki hankalinsa ki kwantar masa da hankali ita kuma zan yi maganinta na san yadda zan yi da ita

 Momy ni fa ba zan cusa kaina a gurin namiji ba, idan har zan yi haka miye amfanin amsa suna na mace? Idan yana ra'ayi shi zai kawo akansa a gareni, ba wai na shige masa na nuna masa so ba?

 Baki son sa ne? Ko kin manta burin da muke da shi akanku? Yanzu ma sai da mahaifiyarsa ta ce zata fi kowa farinciki idan hakan ta faru tsakaninku, haka kika yi saka har ta yi nasarar raba ki da Salim yanzu kuma haka zaki zuba mata ido ta rabaki da Captain? Karamar yarinya kamar Hurriya?

Namra ta sauke ajiyar zuciya.

 Momy idan yana ra'ayina shi zai kusanto da kansa a gareni kamar yadda yake kusantar da kansa gurin Hurriya

 Take dai jan hankalinsa, saboda ta fiki wayo da iya kisisina, ki zauna nan kina tunaninki na banza da shirme

A fucewa Momy ta mike tsaye ta fice daga dakin, cikin kufula da fusata ta tura kofar dakin Hurriya ta shiga.

 Ke...!

Hurriya ta tashi gaban madubin da take ta juyo ta kalli Momy dake kallonta kamar maciji yayi arba da kyanwa.

 Daga yau babu ke babu Captain, kar wata magana ta sake shiga tsakaninki da shi, kuma ko kallonsa kika sake yi sai kusa kasheki... Na fada miki

Hurriya ta daga kanta da sauri, Momy ta ja kofar dakin ta fice, Hurriya ta dafa zuciyarta domin ba kadan Momy ta tsorata ba.

 All because of Captain? Ya Allah.... Kamar za su cinye ni ni miye nawa a ciki? Saboda kawai yana kula ni, su basa kaunar wani ya nuna min tausayi

Ta koma ta zauna tana busar da iskar bakinta, gaba daya ma sai ta ji gidan ya fita ranta. A karo na biyu ta mike tsaye sai dai banbancin wannan tsayin da na farkon wacan na shigor da Momy ta yi ne a birkice tana mata masifa wannan kuma na neman barin gidan dakin ne. Green hijabi dinta ta dauka ta saka ta saka shoes dinta ta fice daga dakin, ta san ba ta isa ta tambayi Momy permission din fita daga gidan ba daman babu ruwanta da ita ko da zata fita ta dade a waje balle kuma yanzu da take jin haushinta. Haka ma ba zata tunkari Hajiya Kaltume tace mata zata fita ba daman ba bangarenta take ba, kuma duka duka yau ta dawo daga gidan bayan shafi sati daya da ta yi a asibitin. Tana fita harabar gidan na Momy ta isa gate dinta sai yaja ta tsaya tana tunanin ta saci kafa ta tafi gidansu Husna ko kuma dai ta hakura ta koma a gidan da baya mata dadin zama a yanzu? Jingina da ta yi da gate din tana kallon Babban gate din gidan da masu gadi suka bude. Ganin Motar Appa ya kara karya mata guiwa daman shi baya son fitarta tun tana da gata a gurinsa balle kuma bayan da ya saka mata takunkumin zama gida da hana ta zuwa gurin Amma ba tare da dalili ba. A madadin direbansa ya nufi bangarensa sai ta ga akalar motar ta nufo gurin da take tsaye wato bangaren Momy, Hurriya ta bar jikin gate din da sauri ta juyo zata dawo ciki gabanta na faduwa zuciyarta na raya mata Momy ta hada ta Appa ne wata kila saboda Captain shiyasa har ya dawo yanzu kuma ya nufo bangaren yayi mata fada. Sai dai horn din da ta ji anyi ya katse hanzarinta na guduwa ta koma bangaren na Momy, a lokacin da ta juyo sai ta an faka motar daidai gate din Momy, an sake danna horn. Cikin karfin hali da hararon laifinta ta nufo motar ta mahaifinta da be cika hawa ba sai lokaci zuwa lokaci, daman haka yake idan ya hau wannan gobe zai iya hawan wata. Daidai gurin gilashin motarsa dake back seat ta tsaya domin ta san bangaren da mahaifinta yake zama a duk lokacin da direba yake tuka shi. Appa ya sauke gilashin motar ya kalli yarsa.

 Hurriya na ganki tsaye a nan kamar cikin damuwa, na saka direba na zo kuma sai kika gudu?

 Na dauka fada zaka min

Ta fada a shagwabe tana taba yatsun hannunta.

 Fada me kika yi?

Ta yi shiru tana kallon kasa, sai tausayinta ya kama shi, soyayyar da yake mata irin ta uba da ?a tana ta dawo masa a hankali.

 Shigo mota

Ta daga kai ta kalleshi sannan ta zagaya ta shiga ta dayan side din, direban yayi baya kadan ya canja akalar motar suka nufi bangaren Appa.

 Wani abun aka miki ne?

Ta kalli Appa tana mai mamakin yadda yake son ya ji damuwarta a yau, abun da aka haka rame aka binne shekaru hudu da suka wuce. Ta girgiza kai

 Aa

 To ya na ga duk kin bata rai? Wani abu kike so?

Ta sake dubansa neman sanin damuwarta da yake kokarin yi a yanzu ya fi komai faranta mata rai.

 Ina son na tafi na duba Amma ne!

Ta furta abun da ba da shi ta fito bangaren Momy ba, farko fitowarta na neman son tafiya gidansu Husna ne, sai dai kuma bata san kalma da zata fito a bakin Appa ba idan tace masa gidansu kawarta Husna zata ce bayan sun yi baran-baran da mahaifinta saboda munafurcin da aka mata sherin cewar ta kulla.

 Ki saki ranki, daman takardu na dawo na dauka ki jira ni a mota yanzu idan na fito sai mu sauke ki a can na wuce, amman karki kai dare

 Ba zan kai dare ba Appa

Ta amsa muryarta na karkarwa saboda kokarin danne kukanta da take. Ta manta when last ta shiga mota daya da mahaifinta, ta manta when last mahaifinta ya nuna damuwa da ita, ta manta rabon da magana mai taushi mai dadi ta shiga tsakaninta da mahaifinta. Ta zauna a motar na tsawon lokacin da ya fita ya shiga bangarensa ya dauko abin da zai dauko ya fita ya dawo cikin motar. A lokacin da ya dawo cikin motar sai ta karkarta idonta tana kallon mahaifinta irin kallon da an shafe mata yinsa a rayuwarta. Direba na tuki Appa yana duba takardun da ya dauko ita kuma tana kallonsa idan hawaye suka sauko mata sai ta share cikin hikima ba tare da ya gani ba, lallai a yau ta kara yarda da tabbatar da ko wace ?a a duniya gatanta uba ne, ko magana yake maka mai dadi zaka ji ka fi kowa rabo da dace a duniya.

 Hurriya ina tunanin dawowa da yaran nan a gidan nan, saboda ita can ba lafiya ta wadace ba, kuma ni ba wani sanina suka yi sosai ba, yadda nake rayuwa da duk yarana su ban yi rayuwa da su a haka ba, ya kamata su dawo nan ni daman bana son rikon ?a?a a gurin kowa, na fi son yarana suna hannuna, ballantana kuma su da suke kanana, yanzu suke bukatar gata

Da gaske Appa ne yake wannan maganar ko kuma dai mafarki take yi? Shawararta yake nema ko kuma fada mata ne yake abun da zai faru? Ta juyar da fuskarta ta matse kwalla sannan ta juyo ta ce.

 Za su fi jindadin zama a can Appa saboda Amma tana can kuma Gwaggo zata kula da su sosai

Sai a lokacin Appa ya dago ya kalleta.

 Ga ki zaki iya kula da kanenki ai kamin a sama miki admission, kuma za a iya daukar mai aiki ta kula da su, amman maganar gaske ni bana son zaman yarana a ko'in sai a gidana

Tabbas haka ne, ba ita kadai ba kowa ya shaida hakan a familynsu Appa baya bada rikon yayansa ga kowa ko da kuwa Hajiya Binta ce da ta kasance mahaifiyarsa, shiyasa a lokacin da aka haifi yaran be je duba su ba kuma be je duba mahaifiyarsu ba ya baya kowa mamaki, sannan ya kyale su be tana cewa bari ya dauko su ko shi ya tafi ya gansu ba. Wani mamakin be kamata ba sai da Appa ya katse mata hanzarin tunanin da take ta hanyar aje mata kudi mai kauri a dan space din dake tsakaninsa da yarsa.

 Ki bawa Hassan da Husaini wannan, kuma ki musu magana ina son zan shigo mu gaisa da yarana

 Toh Appa

Wannan karon bata iya taimako kanta ba har sai da hawayen suka zubo mata, ta dauki kudin ta bude motar ta fita ta shiga cikin gidan. Appa na zaune a motar yana kallon kofar gidan ya takure fuskarsa a yanayin damuwa kamar mai tunanin wani abu, can kuma ya sauke ajiyar zuciya.

 Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un, Allah ka raba mu da aikin dana sani

Ya fada yana kallon twins din da Hurriya ta fito tana rike da su ta nufo motarsa. Bude gefensa yayi sai suka zo da gudu kamar wasu wadanda suka saba rayuwa da shi, suka shige motar suna murna. Jinin alakar uba da ?a?a ya saka sun wayanci shi din ubansu ne tun a ranar da Rukayya ta tafi da su har suka kwana a gidan, daman kuma Gwaggo na nuna musu hoton mahaifinsu a wayar Rukayya saboda su san shi ko da ba su rabe shi ba.

 Gwaggo tace na kawo maka su ka gansu

Hurriya ta fada cikin rashin jindadi domin bata so Gwaggo ta hana shi shiga gidan ba. Appa yayi murmushi domin shi ba yaro ba ne ya gama fahimtar komai a kawo masa yaran da aka yi a waje.

 A haka ma na gode, na jikin Iyami?

 Da sauki....

 Me yake damunta?

Hurriya ta yi hankali da wayon sanin ba komai zata fadawa mahaifinta ba dan haka ta ce

 Ba wanda ya sani har yanzu

 An bincika komai nata lafiya kalau?

 An bincika amman yawanci suna cewa hawan jini ne, ya saka jikinta yayi haka, tana shan magani kullum sai dai har yanzu babu sauyi

Appa yayi shiru ya sauke ajiyar zuciya.

_Hawan jini? Wata kila saboda ni ne_ ya fada a ransa feeling guilty. Kadan ya taba wasa da yaran ya sauke su a motar saboda jiran da ake masa gurin kasuwancinsa.

 Hurriya ki yi magana da Gwaggo, idan ta aminta an ba ni dama sai mu fitar da ita waje ko za a dace

 Appa da gaske?

Hurriya ta amsa da karfi, sai ya daga mata kai da dan damuwa a fuskarsa. Da sauri ta saki hannun yaran ta fada motar ta rumgume shi ta fashe da kuka.

 Appa na gode, Alhamdulillah Appa na gode da ka sake nuna mana kulawa, kada Allah ya kawo wani abun da zai tare idonka daga son farincikinmu....

Kuka take sosai da ya saka zuciyar Appa karaya, Direban ya juyo ya kallesu kadan yana jin tausayinta, daman ya dade yana tausayin Hurriyya da halin da yake ganin tana ciki.

 Hakkina ne Hurriya, abun da ya kamata na yi ne tuntuni, kuma In Shaa Allahu zan yi

Ta dago daga jikinsa.

 Na gode Appa

Ta fita daga motar ta rufe masa, direbansa ya juya motar suka bar unguwar.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... =؃?
35
Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

5??5?+?5??5?0?5??5??5?(?5?(?5?$?5?,? @5?$?5?!?5??5??5??5??5?#?5??5??5??5?'?5??5?2?


Hindu ta rike haba tana mamaki.

 Shi da kansa?

Gwaggo ta amsa mata

 Ni ma abun ya ba ni mamaki, sai dai ba a mamakin ikon Allah, kuma daman shi maganin dan kwana arba'in ne, idan ba a zafafa ba to sanyi yake daga nan har ya karye

Hindu ta taba hannu.

 Hmmm a haka ma mun gode Allah mutunen nan ya fara dawowa hankalinsa mugun abun ta na magani ne ya koma mata

 Ya fa koma, yanzu haka saki biyu yayi mata kuma idan na yanzu aka sallame ta ba tana can asibiti kuma an ce be je ba

Hindu ta daki kirjin idonta a waje tsabar mamaki har da su gyara zama.

 Ya saki Kaltume fa kika ce Gwaggo?

 Wallahi

Hindu ya daga hannu sama.

 Allah na gode maka da baka kashe ni ba sai da na ga wannan ranar, sai ta dandana ta ji idan akwai dadi, wulakancin da ta saka aka yi ma Iyami yau an mata shi, Allahu Akbar Allah baka da dole, Allah na gode maka

 Ni ma dai haka na ce, kuma karshenta ba zai yi kyau ba domin ba, domin hakkin Iyami ba zamu yafe ba kuma ga Hamad ma zai bibiyeta

 Shiyasa aka ce idan zaka haka ramen mugunta ka gina gajere, ba a farinciki da mutuwar aure amman na jidadin mutuwar na Kaltume, saboda ta san yadda ake ji yanzu, dazun da ya zo har fadar yake wai a min magana yana son ya fitar da ita waje

Hindu ta kara girmaman lamarin Ubangijina.

 Tabbas wanda ya aje kayansa a gurin Allah baya kunya, kuma mai hakuri mawadaci, gashi nan Alhaji ya fara dawowa hayyacinta, Allah mai iko, ai tun da kika ce yace a kawo masa yara su gaisa na san asiri ya fara karyewa

 Hurriya tace ya fada mata zai dauke yaransa ya maida su gurinsa, ni kam ba zan yarda ba aje a musu wani sherin kuma karshen daga haka zai iya cewa saboda Iyami ta koma

 Ah.. Gwaggo to ai abun da muke nema kenan, Iyami ta koma gidan Mijinta ta rumgume yayanta ta haifo masa wasu, idan bata koma ba ai bukatar Kaltume ta biya ta samu abun da take so kenan!

Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya ta girgiza kai.

 Hindu ba zan iya da sha'anin magani ba, mace idan aka ce miki tsafi take a gidan mijinta to zaman aure baya dadi ga abokan zama,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login